3. NANA AISHA, ALLAH YA QARA YARDA A GARE TA, UWA CE GARE NI FITOWA TA 2
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=844

 
3. NANA AISHA, ALLAH YA QARA YARDA A GARE TA, UWA CE GARE NI FITOWA TA 2

(Masoyinki ya rabauta, mai makiyin ki ya yi hasara)

SOYAYYAR MANZON ALLAH, TSIRA DA AMINCIN ALLAH, TABBATA A GARE SHI, GARE TA:

Allah ta'ala shi ya zabawa ManzonSa, tsira da amincin Allah su tabbatar a gare shi, Nana Aisha ta kasance Matar Aure a gare shi kamar yanda ya zo a cikin ingantattun littafan hadisin Bukhari da Muslim, Allah ya yi rahama a gare su. Ga lafazin Imamu Muslim:

Daga Aisha, Allah ya kara yarda a gare ta, ta ce: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce:

''An nuna mun ke a cikin mafarki, har darare uku (3), Mala'ika yana zuwa mun dake lullube cikin mayafin alhariri, sai ya ce dani:
''wannan matarka ce, idan na bude fuskar wanda ke lullube cikin wannan mayafi sai in ga ke ce, sai in ce matukar wannan daga Allah ne, to zai zartas da shi''

Sannan an karbo daga Amru dan 'Aas, Allah ya kara yarda a gare shi, ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbatar a gare shi, ya tura ni Yaki…….. Sai na zo wurinsa na ce da shi: Yaa Manzon Allah, wane mutum ne mafi soyuwa a gare ka daga cikin mutane?, sai ya ce: ''AISHA'' sai na ce daga cikin Maza fa?, sai ya ce: ''MAHAIFINTA'' (wato Abubakar al-Siddiq, Allah ya kara yarda a gare shi), sai na ce sannan wane? Sai ya ce: ''UMAR'' daga nan sai Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ambata mutane Masu yawa''. Bukhari da Muslim suka ruwaito.

A saurari fitowa ta 3 in sha Allahu ta'ala, Bana so muna tsawaita rubutun domin kada Masu karatu su kosa.

Daga dan uwanku: Umar Shehu Zaria
Batun: Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai