**DUNIYAR MUTUWA**(3)
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=852

 
**DUNIYAR MUTUWA**(3)

Chan sai ga wani mutum ya zomin, cikin tsananin duhu da nake gani, yazo min da Gemuna fari Fat, Ya ce dani: Yaa kai Daana, wannan itace qarshen rayuwarka, kuma nazo maka ne ina mai maka nasiha kafin ka hadu da Uban-gijinka, Haqiqa na sanka, kai mutum ne mai hazaaqa, kana son Alkhairi, don haka da sannu zan maka wasiyya da wata wasiyya, domin Allah ne ya aikoni wajenka.

Sai nace: Menene kake so?

Sai yace: Kace: ''Na yi Imaani da Cross'', domin na rantse da Allah shine kubutarka, idan kai Imaani dashi zan maisheeka ga iyaalanka da yaaranka, sannan in mayas maka da ranka, ka fadi haka da sauri, bamuda lokacin tsaiko!.
Na san wannan shine Shaidan, dukda irin radadinda nake fama dashi na fitar raina, ban gushe da Yarda ga Ubangijina ba da Annabina s.a.w.
Nace masa: Maza juya kabani waje ya maqiyin Allah, haqiqa na rayuwa musulmi, kuma da izinin Allah zan mutu akan haka.

Sai Fuskarsa ta chanza yace: Ka saurareni, bazaka kubuta ba a yanzu, face ka mutu banasare ko bayahude, in kuwa kaqi, zan qaara maka radadi kuma in dauki ranka.

Nace: Rayuwa da Mutuwa duk suna hannun Allah ne, ba a hannunka ba, ni bazan mutuba sai akan Musulunci, sai fuskarsa ta yamutse, shaidaanin yace: idan ka fitineni (kaqi bin umarnina) to Daruruwanka bazasu iya ba! Kuma ya isheni tunda na iya sanyaka kana saabawa Allah da yawa, kuma kana keta iyakokinsa.

Sai naga ya kalli sama, kamar ya hango wani abu da yake tsoro, sai ya gudu da sauri, sai nai mamakin saurin wucewarsa, kuma nai mamakin menene abinda ya tsoratashi haka! Ban dauki wani lokaciba, sai naga wasu fuskoki baaqi agreni masu girman Halittaar jiki sun sauko a gareni, suka ce min: Assalaamu Alaikum.

Nace: Wa'alaikumus-Salaam.

Sai sukai Shiru basu ce komai ba, taredasu akwai Likafani, sai nasan wannan itace qarshe ba makawa, sai wani malaa'ika mai matuqar Girma ya sauko, yace: ''Yaa ke rai natsatstsiya, ki fito zuwa ga gaafara daga Allah da Yarda….

Wallahi sai naji Amince wanda bazan iya misaltawa ba a sanda naji wannan Kalmah daga gareshi, nace masa: Bushaararka ya Malaa'ikan Allah!

Sai ya cire raina, na kasance tsakanin yanayin barci da Haqiqa, naji Tamkar ina miqewa daga jikina ina hawa sama, na waigo qasa sai naga jikina mutane sun dabai-bayeshi, sun sanya mayaafi akan jikina, inaji wasunsu na cewa: Innaa lillaahi wa innaa ilaihi raaji'un!!!!

Naga Tamkar Malaa'iku 2 sun daukeni sun sanyani cikin likafanin cikin sauri, sun daga sama dani, ina waiwayawa daama da hagu, na hango rufin sama chan nesa, ahaka suna qaara dagaawa dani, muna keta giraagizai, tamkar ina cikin jirgi, har na soma ganin mutane qananaa-qanaana a qasana, sukaci gaba da gudu dani zuwa sama, har na soma ganin qasa tamkar qwallo qarama, sai na cewa Malaa'ikun: Shin Allah zai shigar dani Aljannah? Sukace: wannan saninsa na wajen Allah, mudai Malaa'ikune da aka wakiltamu don daukan ran Musulmai kadai.

Dukanmu sai Hankalinmu ya karkata ga wasu Malaa'iku da mukaga sunzo sun wucemu da sauri, dauke da wata Ruhi mai tsananin Qamshi, inda na shaqi qamshin miskinda ban taba shaaqar tamkarsaba a rayuwata, nacewa Malaa'iku: Wanene wannan? Nidai banda nasan cewa Annabi Muhammad s.a.w shine qarshen Annabaawa, da nace wannan Ruhin Annabi ne! Sabida Rakiyar Malaa'iku da na gani sun mata, da Qamshinta gamida yanda suke riqe da ita cikin Girmamawa da Karramaawa!

Allahu Akhbar! Jama'a Kunsan Wannan Gaawar wacece? Mu hadu a kashi na 4! Sannan maji yanda wannan Bawan Allah tafiyar ruhinsa zuwa sama ta kasance, da yanda zai dawo bayan Mutuwa!

Naku: #Abu_Umayrah
Batun: Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi