**DUNIYAR MUTUWA**(4)
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=853

 
**DUNIYAR MUTUWA**(4)

Dukanmu sai Hankalinmu ya karkata ga wasu Malaa'iku da mukaga sunzo sun wucemu da sauri, dauke da wata Ruhi mai tsananin Qamshi, inda na shaqi qamshin miskinda ban taba shaaqar tamkarsaba a rayuwata, nacewa Malaa'iku: Wanene wannan? Nidai banda nasan cewa Annabi Muhammad s.a.w shine qarshen Annabaawa, da nace wannan Ruhin Annabi ne! Sabida Rakiyar Malaa'iku da na gani sun mata, da Qamshinta gamida yanda suke riqe da ita cikin Girmamawa da Karramaawa!

Sai suka ce: wannan Ruhin shahidi ne da yayi shahaada a Palastine, dazunnan Yahudawa suka kasheshi, yana mai kaariya ga Addininsa da Garinsa, Haqiqa Allah ya sa yanada yawan Ibaadah gashi Mujaahidi!

Sai nace: kaicona ma ace nayi mutuwar Shahaadah ne!
Ba'a jimaba sai naga wasu Malaa'ikun dauke da wata ruhi abar qyama, wani wari mai doyi na tashi daga gareta! Sai nace waye wannan?

Sai sukace: Wannan Mutumin Handusa ne, yana daga cikin Masu bautar shaanu, ya mutu ba da jimawa ba bisa tsawa da Allah ya turo masu, sai na gode Allah bisa ni'imar Musulunci.

Sai nace masu: wlh duk yanda na karanta wadannan abubuwa, banyi zatonsu haka ba, sai malaa'ikun sukace: Bushaararka da Alkhairi, amma ka sani Al'amarindake gabanka mai tsayi ne

Sai nace ina mai mamaki: Yaya kenan?

Sukace: duk zaka ga haka, sai dai munaso ka kyautata zatonka ga Ubangijinka.

Muka wuce wata jamaa'ah ta mala'iku mukai masu sallama, sai sukace: waye wannan? Sai mala'ikun sukace: wani mutum ne musulmi, dazunnan yayi hatsari sai Allah ya Umarcemu da muje mu dauko ransa daga mala'ikan mutuwa, sai malaa'ikun sukace: Lallai Allah mafi ni'ima ne da Karamci ga musulmai, domin su Alheri ne kuma Alherine qarshensu!

Sai nacewa Mala'ikun nan 2: suwa wadannan? Sukace: wadannan mala'ikun sune masu gadin sama, kuma sune masu wurga shahab (taurari da ake jifan aljanu dasu) ga shaidanu!

Sai nace: Lallai halittarsu mai girma ce, sai sukace: ai akwai wadanda suka fisu girma ma! Sai nace: su waye? Sukace: Jibril da masu riqo da Al-arshi! Kuma su halittane daga halittun Allah basu saba masa bisa umarninsa kuma suna aikata abinda aka umarcesu! Nace: Tsarki ya tabbata gareka ya Allah, haqiqa bamu bauta maka ba kamar yanda ya kamata!

Sannan muka isa saman Duniya, haqiqa na kasance tsakanin shauqi da mamaki! Sabida abinda na gani, kuma tsakanin tsoro da da firgici..

Naga saman duniya mai girmace matuqa, tanada qofofi a rufe, akan kowace qofa akwai Mala'ika mai matuqar girma a tsaye, sai Malaa'ikun nan 2 sukace: Assalamu alaikum wr wb, nima nai sallamar tare dasu, sai suka amsa mana: Wa'alaikumus-salaam wr wb, sukace: maraba da Malaa'ikun rahmah, suka dubesu suka ce: ba makawa wannan Musulmi ne! Sukace: Tabbas kuwa, is Malaa'ikun (dake gadin qofofin sama) suka ce:ku shigo, domin ba'a bude qofofin sama face ga Musulmai, domin Allah na cewa: ((Lallai ne wadanda suka qaryata ga ayoyin mu, kuma suka bijire mata, ba'a bude masu qofofin sama, kuma bazasu shiga Aljannah ba har sAi raqumi ya fita ta kafar Allura, hakan ne muka sakankawa masu laifi)) A'araaf:40.

Sai muka shiga, naga abin mamaki, naga wani gini babba tamkar ka'abah, mala'iku masu yawa na dawafi akewayenta, nace: wannan lallai shine BAYTUL-MA'AMUR, mala'ikun sukai murmushi sukace eh, Alhmdlh, mafi yawan wadanda mukazo dasu nan daga Musulmai suna gane wannan wuri, wannan kuma falalar Allah ne kuma falalar Mutumin qwarai Annabinku Muhammad s.a.w wanda bai bar wani abu ba face ya sai ya sanar daku! Sai nace dasu: mala'iku nawane ke zuwa nan kullum? Sukace: Dubu 70, kuma da sun wuce basu dawowa! Sai muka daga cikin tsananin sauri zuwa sama ta biyu.

Mu hadu a kashi na 5!
Batun: Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi