001 JININ DABI'A GA MATA RUBUTU NA 1 -- ^^^ZAUREN MUSLIM UMMAH^^^
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=854

 
001 JININ DABI'A GA MATA RUBUTU NA 1

001 JININ DABI'A GA MATA RUBUTU NA 1

FASALI NA FARKO
ACIKIN MA'ANAR JININ HAILA DA HIKIMARSA !!!
.
HAILA A LUGGA: shine kwararar abu da kuma gudanarsa.
.
A SHARI'A: shine jini da yake faruwa ga mace na dabi'a ba tare da wani sababi ba acikin wasu sanannun lokuta. Shine jini na dabi'a ( mai zubowa) ba tare da wani sababi na rashin lafiya ba ko rauni ko zubewar ciki ko haihuwa ba.
.
Saboda cewa shi jinine na dabi'a don haka yana sa6awa gwargodon halin mace da yanayin tasowarta da tsufanta, saboda haka mata suna sassa6awa a cikinsa sassa6awa mabanbanta na zahiri.
.
HIKIMA A CIKINSA: yayin da dan tayi ya kasance acikin mahaifiyarsa bazai yuwu ya ringa yin kalaci da irin abunda mutum na wajen ciki yake yin kalaci dashi ba. Kuma bazai yuwu ga wanda yafi kowa tausayinsa ba ya iya sadar da kalaci gare shi (ta kowace hanya ba) saboda haka sai ALLAH (SWT) ya sanya jijiyoyin jini acikin mace wanda ta hanyar sune dan tayin da yake cikin mahaifiyarsa zai dinga yin kalaci acikin mahaifiyarsa ta hanyar cibiya jinin zai dinga shiga ta jijiyoyin d'an cikin yayi kalaci dashi. Tsarki ya tabbata ga ALLAH mafi kyawun masu halitta.
Wannan shine Hikimar wannan HAILA saboda haka idan mace ta dauki ciki sai haila ta yanke mata sai 'yan kadan ne ke yin Haila idan suna da ciki haka kuma masu shayarwa kadan ne ake samun wacce take yin Haila a cikinsu, musamman a farkon lokacin shayarwa.
.
Anan zan dakata, zan cigaba inshaa ALLAH.


^^^ZAUREN MUSLIM UMMAH^^^
.
LITTAFI: JININ DABI'A GA MATA WALLAFAR: SHEIKH MUHAMMAD SALIH AL'UTHAYMEEN.
.
FASSARAR: UTHMAN MUSA GABARI
.
MAI GABATARWA: FARIDAH BINTU SALIS
(Bintus~sunnah)

IDAN KANA SON GANIN TSANTSAR MAKIYA AHLULBAITI KIYAYYA A FILI TO KA KALLI 'YAN SHI'A

Idan kana son ganin tsantsar makiya Ahlul baiti kiyayya afili dasunan kaunarsu to kakalli ya'n shi'a…

1. Sun jefi sayyidna Ali da ragwantaka…

2. Sun siffanta fadima da kwadayi…

3. Sun yi ta shaftarawa Ahlul baiti karya…

4. Sun raba Ahlul baiti da ya'ya'nsu.

5. Sun tsinewa wadanda Ahlul baiti ke matukar kauna…

6. Sun kashe Ahlul baiti.

7. Sun jefi Ahlul baiti da bakin zalunci.

8. Sun jefi Ahlul baiti da rashin iya mu'amala.

9. Sun dau siffofin Allah sun baiwa Ahlul baiti.

10. Sun karyata abunda Ahlul baiti sukai imani dashi.

11. Sun raba kan Ahlul baiti bayan azahiri ahade yake.

12. Sun kuntace ma'anar Ahlul baiti.

To mene ma basuyi ba?

Idan akwai dan shi'ar da yake da ja to yabayyana kansa tunda nasan akwai ya'n shi'a dadama a zaurennan…

Idan kuma kayi shuru kuma kana dan shi'a to ka nuna yardarka dangane da wadannan abubuwan da na kidanya…Batun: Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc