015 DA'AWAH BISA KOYARWAR ALQUR'ANI DA SUNNAH FITOWA TA 15
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=858

 
013 DA'AWAH BISA KOYARWAR ALQUR'ANI DA SUNNAH FITOWA TA 15

Malam ya cigaba da bayani akan HUKUNCIN DA'AWAH bisa aiki na wajibi ga dukkan musulmai.
.
Amma malamai sunyi sabani akan cewa shin wannan wajabcin ya game kowa da kowa ko kuma wasu al'umma daga cikin musulmai zasu iya daukewa sauran awajen wajibci.
.
Daga cikinsu akwai masu ganin cewa wannan Umurni ya game dukkan musulmai, don haka wajibcin da'awah gamamne ne ba a daukewa kowa ba.
.
Alal Misali Sheikh Muhammad Abduh wani shahararren malami da ya rayu a Misra yana cewa acikin tafsirinsa ''Da'awa zuwa ga aikin alkhairi, umurni da kyawawan ayyuka da hani zuwa ga munana farilla ne da ya game dukkan musulmai, kamar yadda zahirin ayar alkur'ani ya nuna.
.
Masu irin wannan fahinta suna ganin cewa Umurnin da ALLAH ya bayar cewa '' Kuma wata jama'a daga cikin Ku'' yana nufi ne Yaku al'ummar musulmi Ku kasance masu da'awah zuwa alkhairi, ku zama masu umurni da kyawawan ayyuka da hani zuwa ga munana. Wato wannan umurni daga ALLAH gamammen umurni ne kuma kalmar daga cikinku ko ﻣﻨﻜﻢ (Min kum) a larabce, an kawo ta ne don Karin bayani amma badon takaitawa ko kebancewa ba, suka ce irin wannan salo yazo acikin alkur'ani a suratul Hajj aya ta 30 a inda ALLAH (SWT) Yake cewa:
ﺫَٰﻟِﻚَ ﻭَﻣَﻦ ﻳُﻌَﻈِّﻢْ ﺣُﺮُﻣَﺎﺕِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻓَﻬُﻮَ ﺧَﻴْﺮٌ ﻟَّﻪُ ﻋِﻨﺪَ ﺭَﺑِّﻪِ ﻭَﺃُﺣِﻠَّﺖْ ﻟَﻜُﻢُ ﺍﻟْﺄَﻧْﻌَﺎﻡُ ﺇِﻟَّﺎ ﻣَﺎ ﻳُﺘْﻠَﻰٰ ﻋَﻠَﻴْﻜُﻢْ ﻓَﺎﺟْﺘَﻨِﺒُﻮﺍ ﺍﻟﺮِّﺟْﺲَ ﻣِﻦَ ﺍﻟْﺄَﻭْﺛَﺎﻥِ ﻭَﺍﺟْﺘَﻨِﺒُﻮﺍ ﻗَﻮْﻝَ ﺍﻟﺰُّﻭﺭِ
.
''Wancan ne, kuma wanda ya girmama hukunce-hukuncen ALLAH, to shine mafifici agare shi, awurin Ubangijinsa. Kuma an halatta muku dabbobin ni'ima, face abunda ake karantawa akanku, saboda haka Ku nisanci kazanta daga (cikin) gumaka, kuma ku nisanci kazanta daga shaidar Zur.'' [Hajj:30]
.
Wato kamar yadda akayi amfani da kalmar ﻣﻦ ﺍﻷﻭﺛﺎﻥ Minal authan wato ''daga cikin gumaka'' badon ana nufin kebance wasu gumaka daga kazanta ba. Haka shima kebancewa da akayi a ﻣﻨﻜﻢ (Min kum) wato ''wata jama'a daga cikin ku'' ba yana nuni ne da takaita Umurni ga wasu mutane kawai ba. Sai dai maganar mafi yawan malamai shine bata wajaba ga kowa da kowa ba, domin da'awah tana bukatar ilimi, kuma ba kowa bane yake da wannan ilimin, sannan gashi kima ﻣﻦ tazo acikin ayar.
.
Wasu malamai kuma suna ganin da'awah na iya zama wajibi ga musulmi a Inda ba babu wanda zai iya da'awar sai shi a wurin, ko kuma babu wanda yafi wannan mutumin cancantar gudanar da da'awar a tsakanin mutanen dake a wannan wurin sai shi.
.
Mu had'u a FITOWA TA 16 Inshaa ALLAH.

^^^ZAUREN MUSLIM UMMAH^^^
.
LITTAFI: BAYANI AKAN
WALLAFAR: SHEIKH ALIYU SA'EED GAMAWA.Batun: Al'Adun Musulmi Da Darajoji