HADARIN FATAWA {2} & 001 KADDARA TA RIGA FATA -Shimfida
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=862

 
HADARIN FATAWA {2} & 001 KADDARA TA RIGA FATA -Shimfida

Fatawa ta kasance aba mai hadari ne saboda wadannan sababai kamar haka:-
Mai fatawa yana wakiltar Allah {Ta'ala} ne ko Manzonsa {S.A.W} a wajen yin hukunci game da addini.
Fatawa akwai halastawa ko haramtawa a ciki.
Fatawa na bada amsar abin da in akwai; za a shiga aljanna ko wuta ne a ranar gobe qiyama.
Fatawa na bada amsa a game da abin da ya shafi rayuwa ne duka, kamar Aqeedah, da Ibadah, da Mu'amalah.
Fatawa na zama sanadiyyar qarewar aure, ko cigabansa.
Fatawa na zama sanadiyyar mallaka wani haqqi zuwa ga wani, kamar a rabon gado, da ciniki, da kyauta, da bashi, da sauransu.
Tirqashi !! yanzu yan'uwana masu girma ya kamata mai hankali da tsoran Allah {Ta'ala} da tunanin makomarsa yai wasa da wannan aba da take da irin wadannan siffofi da aka lissafta a sama? a'a wannan ita ce amsar kowa ! To mai yasa magana take sabama aiki? Ka yarda da wannan magana cewa : FATAWA ABA CE MAI HADARI. amma kuma ka kutsa ciki, kai !!! a bi a hankali !!
Allah ya tsare mu, ya fitar da mu daga damuwa.

Sai Allah ya hada mu a gaba.
.
Rubutawar :
Basheer Lawal Muhammad Zaria.


001 KADDARA TA RIGA FATA -Shimfida

i. Farkon Jinyar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Bayan da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kammala aikin hajjinsa da ya yi a shekara ta Goma bayan hijira wanda a cikinsa ya ce ma Musulmi ''Ku yi koyi da aikin hajjina domin ban sani ba watakila ba zan sake haduwa da ku bayan wannan shekarar ba'' sai masu zurfin ilmi daga cikin Sahabbai suka fara ji a jikinsu cewa fa lokacin ciratar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama daga wannan duniyar ya kusanto.

Ga shi kuma ana cikin aikin hajjin sai ayar Alqur'ani ta sauka tana ba da labarin cewa, addini kam ya cika, kuma duk wata ni'imar da Madaukakin Sarki yake son yi wa bayinsa ta fuskar dora su a kan shiriya to an kammala ta. Sai suka fahimci cewa, aikin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya zo yi na isar da manzanci ya kare kenan, don haka ajalinsa ya kusa.

Komawar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama Madina ke da wuya kuwa sai ya kwanta
ciyon ajali wanda ya dauke shi tsawon watanni uku, amma dai bai tsananta ba sai a cikin watan Rabi'ul Awwal, wata na uku ke nan bayan aikin hajji.

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya gamu da zafin ciwo fiye da yadda za a kamanta don ko har sai da aka tambaye shi ya ce, mu Annabawa muna da lada biyu ne, don haka a ciwo ma Allah cikin adalcinsa yake ribinya mana nauyinsa.

Mai jinyarsa Uwar Muminai A'ishah ta ba da labarin yadda jikinsa ya gashe, har a kan dauko ruwa mai sanyi a ajiye a gabansa yana sanya hannunsa a ciki don ya dan ji sanyi, amma kuma nan take sai ruwan ya sauya yanayi saboda zafin masassara daga hannayensa masu tsarki.

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya rinka fadin cewa, tabbas mutuwa kina da zafi. Ya Allah ka taimake ni a kan zafin mutuwa!

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya suma a cikin wannan lokaci har sau uku, a ko wanne ya kan tambaya idan ya farka, ''Shin ko mutane sun yi Sallah?'' akan ce masa, suna nan dai suna jiranka ya Manzon Allah! Sannan ya yi wanka da nufin ya fita zuwa Masallaci. Sai bayan da haka ta faru har sau uku ne, ya hakikance gajiyawarsa a kan fitowa, sannan ya yi umurni a gaya ma Abubakar ya ba mutane Sallah.

_Madogara_
Duba Sahihul Bukhari a littafin yaqe – yaqe, Babin Mutuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.

_Mu hadu a rubutu na gaba…………_

Rubutawa:
Dr. Mansur Ibrahim Sokoto.


Yadawa:
YHBKTN

Duniya Makaranta Whatsapp GroupBatun: Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi