001 LADUBBAN TAREWA Rubutu na 1
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=866

 
001 LADUBBAN TAREWA Rubutu na 1

بسم الله الرحمن الرحيم
DA FARKO
Godiya ta tabbata ga Allaah, muna gode masa muna neman taimakonsa muna neman gafararsa kuma muna roƙon Allaah ya tsare mu daga sharrorin kawunanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allaah ya shiryar babu mai ɓatar da shi, wanda kuma ya ɓata babu mai shiryar da shi.

Na shaida babu abin bautawa bisa cancanta sai Allaah, shi kaɗai ba shi da abokin tarayya, kuma na shaida lallai Annabi Muhammad (Sallal Laahu Alaihi wa Aalihi wa Sallam) bawansa ne, kuma manzonsa ne.

Bayan haka, haƙiƙa! Mafi kyawun magana shi ne Littafin Allaah, kuma mafificiyar shiriya ita ce shiriyar Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi wa Alihi wa Sallam), kuma mafi sharrin al'amura su ne ƙirƙirarrunsu, kuma dukkan wata ƙirƙira bidi'a ce, kuma dukkan wata bidi'a ɓata ce, kuma dukkan ɓata tana cikin wuta.¹

Bayan haka, tun a shekarun baya ne na gabatar da wata muhaadara a Cibiyar Koyon Musulunci (ILC) wadda ta ke kan titin Katuru, U/Sarki, Kaduna mai taken: LADUBBAN TAREWAR AURE A MUSULUNCI. Wannan darasin ya dogara ne kacokan a kan littafin 'Aadaabuz Zifaaf' na babban malamin Salafiyyah, masanin Hadisi da Sunnah As-Shaikh Muhammad Naasiruddeen Al-Albaaniy (Rahmatul Laahi Alaihi). Domin saƙon da littafin nasa ya ƙunsa ne na taƙaice shi a cikin kaset a lokacin, saboda amfanin masu fahimtar harshen Hausa daga cikin 'yan uwa musulmi.
Daga baya ne kuma buƙatar fassara wannan taƙaitaccen saƙon ta taso. Don haka, sai na fassara shi, kuma aka yaɗa shi a cikin jama'a. Na tuna cewa waɗansu aminaina sun riƙa raba wannan kofen rubutun ga ɗalibai da sauran abokai da 'yan uwa, musamman ma waɗanda suka zama sababbin angwaye da amare. Wannan duk domin ƙoƙarin yaɗa Sunnah Sahihiya a cikin al'ummarmu. Allaah ya saka mana da alheri tare da su, da sauran 'yan uwa mabiya Sunnah a duk inda su ke.

To, yau kuma cikin yardar Allaah da ikonsa, wannan saƙon ne na ɗauko, da manufar mayar da shi ɗan ƙaramin littafi, domin ya yi sauƙin ɗauka ga mutane a cikin halayensu na tafiya da zaman gari. Haka kuma domin sauƙaƙewa ga duk mai sha'awar rabawa a lokutan bukukuwan aure da tarewa ga abokan ango da ƙawayen amarya.

A ƙarshe ina son in faɗakar da mai son ƙarin bayani da neman gamsassun bayanai game da hujjoji ko dalilai a kan mas'alolin da na kawo a nan, da ya koma cikin littaffan Shaikhul Islaam Al-Albaaniy (Rahimahul Laahu Ta'aala), musamman ma asalin wannan darasin, watau: Aadaabuz Zifaaf fii Sunnatil Mutahharah. Allaah ya taimake mu.

Amma a nan na ga ya dace mu fara shimfiɗa da waɗansu kalmomi a kan:

• Yadda Ake Yin Bikin Aure

• Munanan Al'adun Bikin Aure

• Hukuncin zuwa wurin bikin Aure na saɓo

Waɗanda na kalato daga cikin littafina Zuwa Ga Sabuwar Budurwa 2.
Allaah Maɗaukakin Sarki nake fata ya sanya wannan aikin ya zama sanadiyyar gyaruwar al'amuran tarewar aurenmu waɗanda, kamar yadda kowa ya sani, cike suke da bidi'o'i da kuma munanan al'adu.

Sannan kuma ina roƙon Allaah (Subhaanahu wa Ta'aala) ya saka wa As-Shaikhul Muhaddithul Albaaniy da alherinsa, saboda irin himmarsa da ƙwazonsa wurin farfaɗowa da yaɗa Sahihiyar Sunnah a cikin duniyar wannan zamanin. Allaah ya sanya ayyukanmu su zama tsantsa saboda shi ne kaɗai. Allaah ya karɓa kuma ya ba mu cikakken lada.
Ya Allaah! Tsarki ya tabbata gareka haɗe da godiyarka. Ina shaidawa babu abin bautawa bisa cancanta sai dai kai. Ina neman gafararka kuma ina tuba gareka.
Wallafar: *Shaikh Muhammad Abdullah Assalafiy*

*zauren majlisin sunnah*
Daga:
Muhammad Abdullahi Assalafiy,
Markazu Ahlil Hadeeth,
Kaduna.
10/Sha'abaan/1433H.
____________________­____
1. Wannan fassara ce ta abin da ake kira 'Khutbatul-Haajah' wadda Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi wa Aalihi wa Sallam) ya riƙa koyar da Sahabbansa don su riƙa gabatarwa a farkon jawabansu, saboda albarkarta. Shaikhul-Islaam Ibn Taimiyah da Shaikh Albaaniy (Rahimahumal Laah) duk sun yi wallafa a kan lafuzzanta da bayanin riwayoyinta da sahihancinta da falalarta da wuraren da ake yin ta.

Zaku iya kasancewa da Majlisin sunnah

WhatsApp 08164363661
Facebook : www.facebook.com/­majlisinsunnah

Ko zauren admin Muneer
www.facebook.com/­Muneer-Yusuf-Assalafy­-502666713417261/?reBatun: Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar