YIWA IYALAN MAMACI GAISUWA (TA-AZIYYA)
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=875

 
YIWA IYALAN MAMACI GAISUWA (TA-AZIYYA)

Ya halatta ayiwa iyalan wanda akaiwa rasuwa gaisuwa amma akula da abubuwa kamar haka:-

1-Yin gaisuwa da abinda zai sanyaya musu rai ya rage musu zafin rabuwa ya sanyasu cikin yadda da kaddara da hakuri da duk abinda ya kamata in bai sabawa sharia ba.

2-Yin addua kamar haka:(INNA LILLAHI MA AKHAZA WA LILLAHI MA A ADA WA KULLU SHAI IN INDAHU ILA AJALIN MUSAMMA FALTASBIR ALTAHTASIB).

3-Ta aziyya bata wuce kwan uku duk lokacin da aka hadu sai ayita.

4-Akauracewa abubuwa biyu:
1-Taruwa awaje keban tacce kamar gida ko masallaci ko maqabarta.
2-Yin abici da yan uwan mamacim sukeyi dan walima ga wanda suka zo ta aziyya.

5-Sunnah shine yan uwa da makota su hadawa iyalan mamacin abinci.
6-Mustahabbine ashafi kan maraya da girmamashi.

ABINDA ZAI ANFANAR DA MAMACI.

1-Adduar musulmi na gari.

2-Ramuwar azumin bakance da waliyin mamaci zaiyi masa.

3-Biya masa bashi daga dan uwansa ko wani daban.

4-Duk abinda ya bari na alkhairi ko sadaqa jariya.

Allah yasa mubar abinda zai amfa nemu kafin mu mutu.

Dan uwanku Bashir Hassan Bashir kurawa

WANKE MAMACI (WANKAN GAWA)

Idan Allah ya yiwa mutum rasuwa wajibine akan wasu daga cikin jama'a suyi gaggawar zuwa wankeshi saboda umarnin manzan Allah (saw).
DUK WANDA ZAI GABATARDA WANKAN GAWA YA KULA DA:-

1-Wanke gawar sau uku ko sama da haka yadda akaga fitar sa.

2-wankan yakasance watri maana ×(3/5/7/9).

3-A sanya magarya acikin ruwan ko makamancin ta kamar sabulu.

4-A sanya kafur ko turare awankan karshe.

5-Warware kitsan kai tareda wanke wa.

6-Taje kashi idan namiji ne.

7-Yiwa gashi kitso gida uku (kalba) idan macace sannan asanyashi baya.

8-farawa gabban alwala da daman gawa kafin hagu.

9-namiji ya wanke namiji mace ta wanke mace sai dai in ma aurata ne ya halatta.

10-Mai yin wankan ya sanya safa ko wani abun a hannunsa kada ya taba jikin mamacin kai tsaye.

11-ba a yiwa mai ihrami wanka.

12-Anasan wanda zaiyi wankan ya kasance yasan yadda sunna ya koyarda shi musamman dan uwansa ko makocinsa.

DUK WANDA YAYI WANKAN YANA DA LADA MAI GIMA AMMA DA SHARADI BIYU:

1-ya siturta dak abinda ya gani karya bada labari. Saboda manzan Allah (saw) yace:(duk musulminda ya wanke mamaci sannan ya boye abinda ya gani Allah zai gafarta masa sau arba'in 40.).
2-yayi wankan dan Allah badan abiyashi ba ko ayi masa godiya.

13-mustahabbine wanda ya wanke gawa shima yayi wanka.

14-Ba'a wanke shahidin da aka kashe afilin yake koda yana da janaba.saboda hadisin Abdullah ibn zubair lokacin da hanzalah yayi shahada a yakin uhudu.manzan Allah (saw) yace:(hakika abokinku mala iku ne suke masa wanka.ku tambayi matarsa. Sai tace: ya fita yanada janaba ajikinsa lokacinda yaji anyi kira afito zuwa yaki.manzan Allah (saw )yace: shiyasa mala iku suke masa wanka yanzu.

Allah yasa mu cika da imani ya bamu shahada.
Dan uwanku Bashir Hassan Bashir kurawa.
Batun: Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai