BIDI'O IN DA AKEYIWA MARA LAFIYA KAFIN YA RASU DA BAYAN YA RASU
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=876

 
BIDI'O IN DA AKEYIWA MARA LAFIYA KAFIN YA RASU DA BAYAN YA RASU

1-Fadin wasu cewa shedanu suna zuwa a siffar iyayan mara lafiya dan su batar dashi.
2-Sanya alqur'ani awajan kan wanda zai mutu.
3-Laqqanawa fadin sunan Annabi da alayansa.
4-karanta YASIN .
5-Sanya wanda zai mutu ya kalli gabas.

BIDI O INDA AKEYI BAYAN MUTUWA

1-Fadin yan shi'a dan adam idan ya mutu najasa ne.
2-Futarda masu haila da haihuwa da janaba daga gidan.
3-Daina aiki ga wanda agabansa akai mutuwa.
4-Fadin wai ruhin yana yawo awajan.
5-Sanya turare tun dare har safe.
6-Sanya koran mayafi adakinda akai mutuwa.
7-Karatun alqura'ni har sai anyi masa wanka.
8-Yanke farcen mamaci da aske gashin hammatarsa.
9-Shigar da auduga cikin dubura ko hanci ko huyansa.
9-Sanya kasa a idan mamaci.
10-Daina cin abinci har sai an bunne shi.
11-Yin kuka lokacin cin abincin rana dana dare.
12-Yaga kayan iyaye kina yan uwa.
13-Zama cikin bakin ciki tsawan shekara daya adaina kwalliya dasa kaya mara kyau.
14-Rage gemu.
15-Daina anfani da ruwan randa.
16-Daina cin nama da kifi tsawan wani lokaci.
17-kyale kayan mamaci ba wanki sai bayan kwana uwa wai hakan zai rage masa azaba.
18-cewa wanda ya mutu ranar jumaa ko daren ta azabar qabarin da awa daya za ayi masa.
19-Cewa mumini ba'a yi masa azaba ranar juma'a da darenta.
20-Sanar da mutuwar akan mambari ko lausifika.
21-Fadin akaranta su fatiha da kulhuwallahu da sauransu.

DUK BIDI ANE BAI HALATTA BA MUHADU ACI GABA

Dan uwanku Bashir Hassan Bashir kurawa

Ziyara zuwa maqabarta dan wa azantarwa da tuna lahira batare da yin abinda zai sabawa Allah kamar kiran matattu da naiman taimakon su ko yanke musu hukuncin su yan aljannah ne dss ya hallata.

Ziyara zuwa maqabarta dan wa azantarwa da tuna lahira batare da yin abinda zai sabawa Allah kamar kiran matattu da naiman taimakon su ko yanke musu hukuncin su yan aljannah ne dss ya hallata

Maza da mata ahukuncun zuwa maqabarta duk mustahabbine.saboda fadin manzan Allah (saw)ku zuyarci maqabarta.baice mace ba baice namiji ba duksu biyun ake nufi.
Ya halatta aziyar ci qabarin wanda ya mutu yana kafiri dan wa azantarwa.

ME YASA AKE ZIYARAR QABARI ?
1-Anfanuwar wanda yaje maqabartar dan zan tuna mutuwa da mamatan yasan dabbas dayan biyu ko aljannah ko wuta.Allah ya kiyaye.
2-Anfanar da mamacin da yi masa sallama da addua da naiman gafara amma musulmi kwai ake nemawa gafara.
ADDU'AR ZUWA MAQABARTA
(ASSALAMU ALAIKUM AHLA DARA QAUMIN MUUMININ YARHAMULLAHU ALMUSTAQDIMINA MINNA WAL MUSTAAKIRINA WA INNA INSHA ALLAH BIKUM LAHIKUN.).

Ya halatta daga adaga hannu idan za ayi addua a maqabarta sanna abawa qabarin baya akalli alqibla.
Ba a yawo tsanin qabarurruka da takalmi wannan shine ladalin da akewa qabari.

Bai halatta sanya turaran wuta kina tsinke bashidaga cikin aikin salaf.

ABUBUWANDA HARAMUNNE AYISU A MAQABARTA.
1-yanka ko wana iri.
2-Daga qabarin da kara kasa akansa.
3-Rubutu ajikinta.
4-Gini akanta.
5-Zama akanta.
6-Sallah ana kallanata ko a kusa da ita.
7-Gina masallaci akai ko a gefanta.
8-Sanyata wajan biki da taruwa.
9-Yin tafiya zuwa maqabarta banda masallaci uku: masallacin makka madina kudus.
10-Balla kasusuwan mamata.
11-Ya halatta abaje maqabartar kafirai.

Allah yasa mu kiyaye.

Dan uwanku Bashir Hassan Bashir kurawa
Batun: Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin