044 HUKUNCE-HUKUNCE DA SUKA KEBANCI MATA MUMINAI FITOWA TA 44
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=880

 
044 HUKUNCE-HUKUNCE DA SUKA KEBANCI MATA MUMINAI FITOWA TA 44

✺✺FASALI NA GOMA (10)✺✺
.
Malam Ya cigaba da Bayani akan Hukunce-Hukuncen da suke kiyayewa Mace Martabarta, kuma suke tsare mutuncinta.
.
4● Daga cikin matakan da suke sawa a tsare farji hana kad'aituwa tsakanin mace da namijin daba Muharraminta ba.
.
● Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: ''Wanda ya kasance yana imani da ALLAH da ranar Lahira to kada ya kuskura ya kad'aita da mace ba tare da muharraminta na tare da ita ba, domin na ukunsu shine shaid'an.''
.
● Amir Ibn Rabi'ah Yace: Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: ''Kada wani namiji ya kad'aita da macen da bata halatta gare shi ba, domin shaid'an shine na ukunsu, sai dai muharrami.''
.
Al-Majid ya fad'a acikin Al-Muntaqa cewa: Imam Ahmad ne ya ruwaito wad'annan hadisan, kuma an ruwaito ma'anarsu daga hadisin Ibn Abbas acikin Bukhari da Muslim.
.
→ Imam Al-shaukani Yace: ''Kad'aituwa da mace ajnabiya ga mutum (wato matar da ba muharrama ba ga namiji) abu ne da malamai suka gamu akan haramcinsa, kamar Yadda Al-hafiz ya fad'a acikin Fat'h.
Dalilin haramcin kuwa shine abunda yazo acikin hadisin na cewa shaid'an shine na ukunsu, zuwansa wajensu kuma shine zaisa su afka cikin sa6on ALLAH. Amma idan akwai muharrami tare da su, to kad'aituwa da ajnabiyya ta halatta, saboda idan yana nan ba zai yuwu su aikata sa6o ba.''
.
[Nailul Awd'ar 6/120]
.
★ Wasu Matan da Waliyansu su kanyi sassauci wajen wasu halaye na kad'aituwa sune:
.
[A]→Kad'aituwar mace tare da 'Yan uwan mijinta, da yaye fuskarta gare su. Wannan kad'aituwa tafi ko wace iri had'ari.
.
● Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: ''Ku kiyayi shiga wajen mata. Sai wani mutum daga cikin Al-ansar Yace: Ya Rasulullah! To d'an uwan miji fa? Sai Yace: 'Dan uwan miji mutuwa ne.''
.
[Ahmad da Bukhari da Tirmizi suka suwaito shi]
.
Wato Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yaqi d'an uwan miji ya kad'aita da ita.
.
→ Al-Hafiz Ibn Hajar (Rahimahullah) Yace: ''Nawawy Yace: Dukkan malamai masana harshen larabci sun gamu akan cewa abunda ake nufi da d'an uwan miji shine kamar Ubansa da bappansa da d'an uwansa da d'an d'an uwansa da d'an baffansa da makamantansu. Kuma yace acikin wannan hadisin abunda ake nufi da d'an uwan miji sune 'Yan uwansa da ba iyayensa ba, ko 'Yayansa, domin su muharramai ne ga matarsa, ya halatta garesu su kad'aita da ita, kuma su ba a kamanta su da mutuwa. Sannan Yace al'ada ta gudana an saba da sassauci sai qanin miji ya kad'aita da matar Wansa, to sai aka kamanta shi da mutuwa, kuma shi yafi chanchanta a hana.''
.
[Fat'hul Bari 9/331]
.
→ Al-Shaukani (Rahimahullah) Yace: ''Abunda ake nufi da cewa: d'an uwan miji mutuwa ne, ai shi yafi cancanta aji tsoronsa fiye da waninsa, kamar yadda tsoron mutuwa yafi ko wani irin tsoro.''
.
[Nailul Aud'ar 6/122]
.
Don haka kiji tsoron ALLAH Ya 'Yar'uwa musulma, kada kiyi sassauci acikin al'amarin, koda kinga mutane suna sassauci, domin abun lura shine hukuncin shari'a ba al'adun mutane ba.
.
[B]→Wasu Mata suna sassauci da su da waliyansu wajen hawan mace mota it's kad'ai tare da direba Wanda ba muharrami gareta ba, gashi kuwa yin haka kad'aituwa ce data haramta.
.
→ Sheikh Muhammad Ibn Ibrahim Aalul Sheikh, babban malami mai fatawa na qasar saudiya (Rahimahullah) Yace acikin Majmu'ul Fatawa [10/52] nasa:
.
Yanzu babu sauran shakka cewa hawan mace ajnabiyya mota tare da mai Jan motar ita kad'ai ba tare da muharrami ba bayyanannen munkari ne, kuma akwai nau'o'in 6arna masu yawa awajen yin haka, wad'anda bai kamata ayi sake dasu ba, kuma koda macen mai kame kanta ce, ko mai yawan fita. Kuma duk namijin da yake yarda da irin wannan ga muharramansa mata to mai raunin addini ne, kuma ragon maza ne maras kishi ga yan'uwansa mata dake qarqashinsa.
.
Haqiqa Annabi (Sallallahu Alaihi wasallam) Yace: ''wani namiji bai ta6a kad'aituwa da mace ba face shaid'an ya zama na ukunsu.'' Kuma kad'aituwarsa da ita acikin mota yafi kad'aituwa tare dashi acikin d'aki ko makamancinsa.
.
Domin acikin mota zai Samu ikon tafiya da ita inda yake so, ko cikin gari ko wajensa, ko taqi ko taso. Kuma irin 6arnar dake samuwa daga wannan tafi wadda ta ke samuwa daga kad'aituwa kawai.
.
Kuma nutumin da ake Neman ya kasance yana wajen da za'ayi hukunci da halaccin kad'aituwa da mace, dole ne ya zama babba ba d'an yaro ba. Abunda wasu mata suke zato na cewa idan suka d'auki yaro tare da su, kad'aituwar ta gushe, wannan zato ne na kuskure.
.
→ Imamun Nawawy (Rahimahullah) [9/109] Yace: ''Idan namiji ajnabi ya kad'aita da mace ajnabiya ba tare da wani na uku ba, to wannan haramun ne wajen ga baki d'ayan malamai. Haka kuma idan tare dasu akwai Wanda baza'aji kunyarsa ba saboda qanqanta to anan ma kad'aituwar da aka haramta tana nan.''
.
Mu had'u a FITOWA TA 45 Inshaa ALLAH..
WALLAFAR: SHEIKH SALIH FAUZAN AL-FAUZAN.
.
FASSARAR: DR. BASHIR ALIYU UMAR.
.
GABATARWA: FARIDAH BINTU SALIS (Bintus~sunnah)Batun: Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen