FASSARAR AQIDAR DAHAWIY
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=881

 
Littafan Aqidah

FASSARAR AQIDAR DAHAWIY

Malaman Hadisi sun yi rubuce-rubuce masu yawa akan aqidah. Akwai taqaitattu, akwai masu tsayi. Sannan akwai wadanda ke ruwaitowa da isnadi. Akwai kuma wadanda malaman baya suka rubuta ta hanyar naqaltowa daga littafan magabata. An kuma sami wadanda suka zayyana aqidar salaf a waqe.
Daga cikin liffafan aqida masu isnadi akwai:
– Assunnah Na Abdullahi Dan gidan Imamu Ahmad
– Assunnah na Ibn Abi Asim
– Khalq Af'alil Ibad Na Al-Imamul Bukhariy
– Usulus Sunnah Na Ibn Abi Zamanin
– Sharh Usuli I'itiqadi Ahlis Sunnah Na HibatulLaahi Al-Laalaka'iy
– Kitabut Tauhid Na Ibn Khuzaimah
– Kitabul Arsh da Kuma Al'ulu dukkansu na Al-Imamuz Zahabi
– Kitabut Tauhid Na Ibn Mandah
– Zammul Kalam Na Abu Ismail Al-Harawiy
Da sauransu da yawa kwarai. Kamar littafan Al-Imamul Baihaqi da na Daraqudni da na Darimiy da Ibn Dattah da makamantansu.
Akwai kuma littafai taqaittatu wadanda ke dunkule bayani ba tare da dogon sharhi ba.
Alal misali
– Lum'atul I'itiqad Na Al-Imamul Maqadisi
– Al-Ibanatus Suqrah Na Ibn Battah
– Tajreedut Tauheed Na Maqariziy
– Tadheerul I'itiqad Min Adranil Ilhad Na Muhammad Bn Al-Amiris San'aniy
– Al-Aqidatul Wasitiyyah Na Shaikul Islam Ibn Taymiyah
Da ire-irensu da yawa.
Dangane da waqen aqidah akwai littafai kamar
– Al-Ha'iyyah Na Abubakar Ibn Abi Dawud
– Annuniyyah Na Ibn Qayyimil Jauziyyah
– Annuniyyah Na Al-Qahtaniy
– Sullamul Wusool Ila Ilmil Usool Na Al-Hafiz Hakamiy
Da makamantansu.
Allah Ubangiji ya saka wa dukkan malaman nan da alheri, Allah ya gafarta musu da su da sauran malaman musulunci na da da na yanzu
DR KABIR ASGARBatun: Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc