018 DA'AWAH BISA KOYARWAR ALQUR'ANI DA SUNNAH FITOWA TA 18
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=883

 
T018 DA'AWAH BISA KOYARWAR ALQUR'ANI DA SUNNAH FITOWA TA 18

Malam ya cigaba da bayani game da HUKUNCIN DA'AWAH A MATSAYIN AIKIN ALKHAIRI:
.
Kuma don a sake fito da alkhairin dake cikin wannan aiki na da'awah, sai ALLAH (SWT) yayi yabo ga al'ummar Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) ta fuskar siffanta al'ummar da muhimmin aikin ta na umurni da kyawawan ayyuka da hani zuwa ga munana a inda yake cewa:
.
كُنتُمْ خَيْرَ أُمَّةٍ أُخْرِجَتْ لِلنَّاسِ تَأْمُرُونَ بِالْمَعْرُوفِ وَتَنْهَوْنَ عَنِ الْمُنكَرِ وَتُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَلَوْ آمَنَ أَهْلُ الْكِتَابِ لَكَانَ خَيْرًا لَّهُم مِّنْهُمُ الْمُؤْمِنُونَ وَأَكْثَرُهُمُ الْفَاسِقُونَ
.
''Kun kasance mafi alkhairin al'umma wadda aka fitar ga mutane. Kuna umurni da alkhairi kuma kuna hani daga abunda ake ki, kuma kuna imani da ALLAH, kuma da mutanen littafi sunyi imani, lallai ne da haka ya kasance mafi alkhairi agare su, daga cikinsu akwai muminai, kuma mafi yawansu fasikai ne.'' [Ali-imran:110]
Imamu Tabari ya ruwaito cewa a lokacin aikin hajji, Umar Bin Al-khaddab (RA) ya karantawa jama'a wannan aya, sai yaga mutane suna ta matsowa gare shi (don jin dadin abunda ke cikin ma'anar ayar). Sai Umar Bin Al-khaddab (RA) yace musu: duk Wanda yake son samun alkhairin dake cikin wannan ayar to sai ya siffantu da abunda (Ayar) ta kunsa. Wato Wanda yake son kasancewa cikin mafifitan al'umma dole ne ya kasance ya siffantu da aikinsu na umurni da kyawawan ayyuka da hani zuwa ga munana. Idan kuma ba haka ba a maimakon ya shiga cikin wannan rukunan al'ummar ta Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi wasallam), sai ya samu kansa acikin rukunin masu aiki irin na ahlul-kitabi, wanda ALLAH Ya siffanta su da cewa:
.
كَانُوا لَا يَتَنَاهَوْنَ عَن مُّنكَرٍ فَعَلُوهُ لَبِئْسَ مَا كَانُوا يَفْعَلُونَ
.
''Sun kasance basu hana junansu daga abun Ki, wanda suka aikata. Hakika abunda suka kasance suna aikatawa ya munana.'' [Ma'idah:79]
.
Sheikh Abdul'aziz Bin Baaz (Rahimahullah) acikin wata fatawarsa, yana cewa alokacin da wani yanki na jama'a ya rungumi aikin da'awah acikin al'ummah, ya saukewa sauran jama'a hukuncin wajibcin da'awah, don haka ga sauran mutane a wannan lokaci hukuncin aikin da'awah ya koma sunnah mai karfi kuma aiki daga cikin kyawawan ayyuka masu amfani. Amma idan babu wani rukuni na jama'a da yake gudanar da aikin da'awah acikin wata al'ummah ta musulmi. To nauyin zunubin da hakan zai jawo sai ya game kowa da kowa. Kuma wannan hali wajibcin yin da'awah ya hau kan kowane musulmi.
.
Kuma mu sani cewa da'awar da tafi kowacce cancanta akan musulmi ita ce wanda mutum zai yiwa kansa ta hanyar yin yaki da zuciyarsa don bin ALLAH da yi masa da'a tare kuma da hana kansa munanan ayyuka na sabo ga ALLAH. Bayan wannan kuma sai a gangara zuwa ga wadanda suke karkashin kulawarsa na daga cikin iyalai da makusantan sa. Babban abun misali shine umurnin da ALLAH (SWT) ya bayar zuwa ga Manzon ALLAH a inda yake cewa:
.
وَأَنذِرْ عَشِيرَتَكَ الْأَقْرَبِينَ
.
''Kuma kayi gargadi ga danginka mafiya kusanci.'' [Shu'ara:214]
.
A lokacin da aka saukar da wannan umurni, sai Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya mike yana cewa: ''Ya Fadima diyar Muhammad, Ya Safiyyah diyar Abdul-mudallib, Ya 'Yayan Abdul-Mudallib bana iya mallaka muku (taimakon ku da) kome a wurin ALLAH, don haka Ku tambaye ni game da dukiya (zan iya baku) gwargodon iko na.'' [Imam Muslim]
.
Mu had'u a FITOWA TA 19 Inshaa ALLAH.

^^^ZAUREN MUSLIM UMMAH^^^

.
WALLAFAR: SHEIKH ALIYU SA'EED GAMAWA.
.
Zaku iya liking page dinmu a:-
.
https://­m.facebook.com/­Zauren-Muslim-UMMAH-8­16256835116345/



Batun: Al'Adun Musulmi Da Darajoji