Wai Da Gaske Ne Ja'far Mahmud Adam Da Albaniy Zaria Ba 'Yan Salafiyyah
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=889

 
Dr Kabir asgar wrote

Wai Da Gaske Ne Ja'far Mahmud Adam Da Albaniy Zaria Ba 'Yan Salafiyyah Ba Ne?

1- Mutane da yawa suna ta tambaya ta ta hanyoyin sadarwa dabam-dabam akan maganganun da wasu suke ta yi na kokarin fitar da Mal. Ja'afar Mahmud Adam da Mal. Auwal Albaniy Zaria (Allah ya gafarta musu) daga tawagar salafiyyah.

2- A kashin gaskiya ni ba na ganin dacewar yin ce-ce-ku-ce akan ire-iren maganganu na mutane masu bin irin wannan tafarkin. Saboda ni ba malami ba ne, ballantana a ce mujtahidi wanda zai iya yin hukunci na jarhi da ta'adili akan mazaje. Sannan kuma ina da abubuwa masu tarin yawa da na sa a gaba nake yi wadanda nake ganin sun fi mini muhimmanci fiye da shiga sharo-ba-shanu. Bugu da kari, a dabiata ina matukar kyamar jayayya da kokarin kare wani mutum ko aibata shi don kashin kansa ko don cim ma wata manufa wacce ba ta da alaqa da asalin addini ko kuma jayayya da mutumin da ya riga ya gamsu da abin da ya fahimta. Don haka, zan yi wannan tsokacin ne bisa tilas, ba dan ina so ba sai da bayyana abin da na fahimta ga wadanda ke da budaddiyar zuciya da ke iya sauraron bangarorin sabani ba tare da jafa'i ko son zuciya ba.

3- Gaskiya ne aqidar Ahlus Sunnah ta tsayu akan lazimtar da jama'a da hani akan fito-na-fito da masu mulki. Kuma gaskiya ne akwai wasu maganganu da Mal. Ja'afar ko Mal. Albaniy Zaria suka yi wadanda a zahiri za ka ji su da zafi ko kausasawa ko fushi, musamman in ka dubi maganganun a tsurar su ba tare da la'akari da abin da ya haifar da su ba. Irin wannan zantukan na iya zamowa abin kafa hujja ga wanda bai san su ba ko kuma wanda dama can yana da wata manufa, ko kuma wanda ya riga ya yanke hukunci sannan ya tafi neman dalilin da zai goyi bayan hukuncinsa.

4- Amma dai kam a kashin gaskiya irin wannan tuntuben ko maganganun da suka yi masu zafi bai kai a ce wai shi kenan sun fita daga tawagar Salafiyyah ba. In ko har aka bude wannan babin to ina tsammanin wadanda za su saura a ciki suna da karanci kwarai.

5- Masu wadannan maganganun na san suna cewa ba mujtahidi a Nigeria!. To waye yai wannan hukuncin? Shin su din ne suka sa rigar mujtahidai? Ko kuwa an aika da fatwa ne Madina aka tabbatar da haka? Ko kuwa yanzun an sami mujtahidan ne a Nigeria?

6- Mal. Ja'afar Mahmud Adam da Mal. Auwal Adam Albaniy Zaria malamai ne da ke bin tafarkin salafiyyah. Akan shi suka rayu kuma a kanshi a ka kashe su. Muna adduar Allah ya ji kansu da gafara. Allah ya ba su darajar shahidai.
Ina ganin kasusuwan wadannan malamai da ke yawo a hannun mutane sun isa shaida akan irin ra'ayoyinsu da aqidarsu da tafarkinsu da sauran abubuwan da ke da alaqa da da'awarsu ko rayuwarsu. Kuma sune manazarta ta farko da ya kamata a dogara da su wajen fahimtarsu da yi musu hukunci.

7- Wannan kuma ba ya nufin ba su da kuskure ko gazawa ko zamiya kamar yadda duk wani malami bai rasawa. Malamai na iya yin kuskure, rafkannuwa, zamiya, gazawa, son zuciya ko tawili da sauransu.

8- Ya kamata 'yan uwana kananan dalibai su san cewa wannan mas'ala ta batun khuruji da jarhu wat ta'adeel ta fi karfin iliminmu da gogewarmu. Kuma ta wuce kawai mutum ya nada kansa a matsayin me sannafa mutane. A babin shawara, kowa ya tsayu akan abin da ya iya, kowa ya san matsayinsa.

9- Wani abin mamaki shine Mal. Saidu Maikwano da suke cewa shi yana daga cikin wadanda ke kan turbar salafiyya sahihiya, shi kuma ya yarda da salafiyyacin Mal. Ja'afar da Mal. Albaniy. Mal Saidu Maikwano babban amini ne ga Albaniy Zaria, suna girmama junansu. Hasali ma, Mal. Saidu shi yai wa Albaniy sallar janaza!. Haka shima Dr Abubakar Birnin Kudu yake girmama Mal. Albaniy. Wannan kuma bai nufin wai dayan su bai da wani bambamci na dabi'a ko fahimta ko sabani da dayan kamar yadda kowa ke da shi da dan uwansa ko abokin aikinsa ko makamantansu.

10- Mal. Ja'afar da Mal. Albaniy suna cikin na kan gaba cikin malaman kasan nan wajen yin wa'azi da kalubalantar akidun boko haram. Suna da ruwa da tsaki akan yayata karantarwar sunna da salafiyyanci da alkairi a kasar nan. Sun yi iya yin su wajen karantar da abin da Allah ya sanasshe su da kuma yada sunna da koyi da magabata iya rayuwarsu.

Allah ya saka musu da alheri. Allah ya gafarta musu kurakurensu. Allah ya ji kansu ya sa su cikin rahama da aminci.
Batun: Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai