A Ganin - Dr. Kabir Asgar - A Ganina
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=890

A Ganin - Dr. Kabir Asgar - A Ganina

Kisan kai mummunan laifi ne, ba wai a musulunci kawai ba, har a cikin daukakin dokokin al'ummonin Dan Adam.

Akwai haqqin Allah, ga kuma haqqin wanda aka kashe din ga kuma na 'yan uwa da iyalansa da danginsa.

Shi ya sa shariar musulunci ta yi hani akan kisan kai ta ko wane hali. Kuma tai tanadi na hukunce-hukunce a kan kisan kai. Tun daga ramuwa, diyya da kuma kaffara gwargwadon yanayi.

A ganina, yadda mutane suka kutsa cikin batun kisan gilla da ake zargin wata mata mai suna Maryam Sanda ta yi wa mijinta kwanakin baya a Abuja ya saba wa qaidoji da yawa na rayuwa da addini.

Musulunci ya yi horo da kamewa daga zance maras amfani da yada labarai marasa dadi da kutse cikin al'amuran da ba su shafe ka ba da muguwar addua da sakin baki da ba da labarin dukkan abin da ka ji da yada hotuna barkatai da kuma mai da komai abin zolaya da tattaunawa da ire-iren su.
Abin da ya dace da musulmi shine daukan izina daga ire-iren wadannan ayyukan da kuma adduar da za ta zama alheri ga wanda abin ya shafa da ma sauran musulmai sannan kame baki da alqalami daga aikata laifin da zai iya yawo wa mutum matsala tsakaninsa da Allah.

Allah ubangiji ya sa mu dace

Allah ubangiji ya sa mu daceBatun: Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi