Azumin Watan Rajab
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=891

 
Azumin Watan Rajab

Watan RAJAB, daya ne daga cikin watanni masu alfarma guda 4, wadanda tun a jahiliyya Ana girmama su, sauran sune: Zul Qa'ada, Zul Hajj, da kuma Muharram. Abinda ake nufi da rajab shine mai girma ko abin Qimantawa. Kuma ana ambatar shi da wannan sunan ne saboda yadda tun wancan lokacin larabawa suke girmama shi cikin watanni.

Zamu kara gane haka idan muka lura da sunan watan da ke biye da shi wato Sha'aban, daga kalmar

شعب يتشعب بمعنى يتفرّق، أي يتفرّقون لإغارة بعد عقودهم في رحب. Wato suna fita su warwatsu cikin garuruwa Don Maida gari bayan dogon Hutu da akayi na kin yin yaki.

Shin RAJAB yana da wata falala akan sauran watanni?
Amsa shine : Eh! Amma falalar bata wuce abinda Ubangiji Ya ambata cikin littafinSa ba, na cewa yana daga cikin watanni masu alfarma, Don haka wani Magabaci cikin manyan malaman tafsiri mai suna Qatada bni Da'aama assadusiy yake cewa: '' Allah kan zabi Wasu cikin mutane Ya fifita su, kamr yadda yake fifita Wasu daga cikin Mala'iku, haka Ya ke fifita Wasu wurare kan Wasu, Don haka duk abinda Allah Ya fifita yakan girmama laifinsa, kamar yin laifi a haramin Makkah Ya dara yin sa a sauran wurare, haka yin laifi cikin wata Mai alfarma Ya data yin sa cikin wani wata da ba shi ba. Shin Me Ya kamata ayi a wannan watan?

Babu wata kebantacciyar ibada da ta inganta cikin wannan watan, Misali yin wata sallah da ake cewa RAGA'IB, a Juma'ar farkon wannan watan bata da Asali.

Haka ikirari da ake cewa cikin wannan watan ran 27, akayi mi'iraji da Manzon tsira bashi da asali.

Haka yin aumtar watan gaba1, shims bashi da asali, sede idan mutum Ya saba yin azumi ranar Littinin ko yin azumi 3 kowanne wata, ze iya cigaba da ibadarsa, ba tare da Ya kara komai akai ba Don alfarmar wannan watan.

Haka ke6ance wannan watan da yin Umara, shima bashi da asali.
Haka addu'a da mutane ke yawo da ita wai Annabi alaihissalatu was salaam ko wani daga cikin magabata yayi cewa: اللهم بارك لنا في رجب وشعبان وبلّغنا رمضان…، duk basu da asali.

Ba Don gudun tsawaita Wa ba da na kawo zantuttukan magabata daga kowace mazhaba da take nuni kan abinda na ambata a sama, amma lura da cewa Malikiyya ake yi a wuraren mu, ga zancen daya daga cikin malaman su.
قال شيخ المالكية في وقته أبو بكر الطرطوشي ـ رحمه الله ـ :دلت هذه الآثار على أن الذي في أيدي الناس من تعظيمه ـ يعني: شهر رجب ـ إنما هي غبرات من بقايا عقود الجاهلية.
Ma'ana: Dalilai na nuni kan cewa abinda mutane suka jima akansa suna yi na girmama shi (wato watan RAJAB) abinda Ya saura cikinsu ne na qurar lokacin jahiliyya.

Don haka yan uwa mu guji kirkiro wata ibada wacce magabata basu bautawa Allah da ita ba. Don gurin gyaran gira se mutum Ya Rasa ido gaba 1, wajen neman lada se Ya jefa kansa cikin hallaka. Allah Ya tsare mu.

sheikh Abdulwahab Abdallah
Batun: Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin