Nigeria Ba Ta Bukatar Maha'inta Maciya Rashawa
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=897

 
Dr. Jamilu Zarewa, Fatawoyi

Nigeria Ba Ta Bukatar Maha'inta Maciya Rashawa

Har yau har gobe nigeria tana bukatar jagorancin mutanen da sam ba a san su da cin hanci da rashawa ba; mutanen da suka yi kuruciyarsu, da manyantakarsu cikin hidimar kasa da 'yan kasa ba tare da mahankalta sun tuhume su da ha'intar al'ummar da suke jagoranta ba domin arzutta kawunansu.

Har kullum idan talakawa suka sami damar yin zabi tsakanin: 'yan siyasar da suka yi kuruciyarsu da manyantakarsu cikin hidimar kasa da 'yan kasa ba tare da ha'intar al'ummah ba, da kuma 'yan siyasar da mahankalta ke tuhumar su da ha'intar al'ummah, to lalle wajbi ne a kan su talakawan su tashi tsaye su zabi kaso na farkon, su yi watsi da kaso na biyun komin kaifin bakinsa da iya yin sharri da yarfensa.

Sam babu alheri cikin dukkan wani kawance, ko hadaka da yake yin kokarin kawar da masu kokarin yin yaki da rashawa da ha'intar al'ummah domin dasa kishiyoyinsu.
Allah muke roko da ya taimaka wa nigeria da al'ummarta da kuma nagartaccen jagorancinta. Ameen.

Sanarwa! Sanarwa!! Sanarwa!!!

Shugaban kungiyar Izala ta jihar Gombe Alhaji Salisu Muhammad Gombe.

Shugaban majalisar malamai ta jihar Sheikh Abubakar Abdullahi Lamido.

Shugaban majalisar agaji ta jiha

Alhaji Maigari Usman Malala

Amadadin kungiyar Izala ta jihar Gombe. Suna farin cikin gayyatar al'ummar musulmai zuwa gagarumin wa'azin jiha a garin Billiri dake karamar hukumar Billiri.

Aranan lahadi 24/jimada- ula/1439 / 11/02/2018.

Allah yabada ikon zuwa ameen

Sanarwa daga ofishin sakataren kungiya ta jiha alhaji abubakar adamu d.o. hinna.

Jibwis gombe

Mabda'i Da Tunanin Kungiyoyin Tarzoma Abin Mamaki Ne Matuka

Lalle mabda'i da tunani irin na kungiyoyin tarzoma a duk inda suke a kasashen duniya abin takaici ne da kuma mamaki.

Mutane ne kuna cikin wata kasa mai rubutattun dokoki domin tsare maslaharta amma kuma ku ce ba za ku bi wadannan dokokin ba koda kuwa ba su yi karo da nassin alkur'ani mai girma, da hadithai masu daraja ba!

Mutane ne da a shirye suke su tsare hanya domin hana gwamnan jiha wucewa saboda kawai su nuna wa duniya cewa dokokin wannan kasa da suke cikinta su ba za su yi aiki da su ba! Mutane ne da a shirye suke su tsare hanya su hana shugaban sojojin kasar da suke cikinta wucewa saboda kawai su nuna wa duniya cewa dokokin wannan kasa da suke cikinta su ba za su yi aiki da su ba!!

Mutane ne da abu mafi bayyana a cikin shi'arinsu shi ne neman mutuwa a fagen gwagwarmaya da tarzoman da suka kirkira wa kansu, suka kuma lazimtar wa kansu, to amma kuma babban abin mamaki shi ne: idan sun gamu da ajalinsu a cikin wannan tarzoma tasu sai a ga cewa sun fi kowa raki da kuka, maimakon a ga cewa suna nuna farin ciki saboda sun sami abin da su ne suka neme shi da kansu, abin da kuma shi ne babban buri a gare su!!

Lalle musulunci ba ya goyon bayan hamayyar jahiliyya, ba ya kuma goyon bayan tarzomar jahiliyya, ba ya kuma goyon bayan taka dokokin da ba su yi karo da nassin alkur'ani da hadithi ba.

Allah muke roko da ya taimaka wa wannan al'ummah tamu ya cusa mata kyakkyawar fahimta cikin dukkan al'amura. Ya kuma taimaka wa wannan kasa tamu ya ni'imta ta da dawwamannen zaman lafiya. Ameen.

Kur'aniBatun: Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai