Me Ya Sa Yan Shi'a Suke Kin Banu Umayya?! -Dr Mansur Sokoto
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=899

 
Dr Mansur Sokoto

Me Ya Sa Yan Shi'a Suke Kin Banu Umayya?! -Dr Mansur Sokoto

Me ya sa Yan Shi'a suke kin Banu Umayya?!

Daga SHEIKH DR MANSUR IBRAHIM SOKOTO
(Rubutun Babban Masanin Tarihi, Dr. Ali as-Sallabiy).

Ibnu Kathir (r) yana cewa:

''Kabilar Banu Umayya sun ci kasuwar Jihadi; ba su da abin yi sai shi. Sun kaskantar da kafirci da kafirai. Kwarjinin Musulmi ya cika zukatan kafirai. Ba sakon da Musulmi su ka sa a gaba face sun ci shi da yaki.''

Ba a san wata Kabila da ta yi mulki ta yi wa mutane abin da Kabilar Banu Umayya (r) ta yi musu ba. Banu Umayya suna da falala a kan al'ummar Musulmi tun kafuwar Musulunci har zuwa ranar al-kiyama.

* Uthman dan Affan dan kabilar Banu Umayya ne. Shi ne ya tattara al-Kur'ani.

* Ummul Muminina, Ummu Habiba 'yar Abu Sufyan (r) 'yar kabilar Banu Umayya ce. Ta ruwaito mana sunnonin Manzo (SAW) ma su yawa.

* Mu'awiya dan Abu Sufyan dan kabilar Banu Umayya ne. Daya ne daga marubuta wahayi.

* Abdullahi dan Sa'id dan al-As dan Kabilar Banu Umayya ne. Daya ne daga shahidai goma sha uku na Badr.
* Yazid dan Abu Sufyan dan kabilar Banu Umayya ne. Shi ne ya shigar da Musulunci Lebanon; ya jagoranci rundunonin Sham.

* Yazid dan Mu'awiya dan kabilar Banu Umayya ne. Shi ne kwamandan rundunar farko da ta yaki Kusdandiniyya (Istanbul); Annabi (SAW) kuma ya ce ''An gafarta wa rundunar farko da ta yi yaki a Kusdandiniyya).

* A cikin Banu Umayya a ke da Khalid dan Yazid. Shi ne ya kirkiro ilimin kimiyya.

* A cikin Banu Umayya a ke da Ukbatu dan Nafi'u (r). Shi ne ya kai Musulunci arewacin Afirka.

* A cikin Banu Umayya a ke da Umar dan Abdul Aziz.
* Wanda ya gina 'Kubbatul Sakhrah' (ta Masallacin Kudus), Abdul Malik dan Marwan, dan kabilar Banu Umayya ne.

* Banu Umayya ne suka kai Musulunci Andalus da Armenia da Azerbaijan da Georgia. Haka ma Turkiyya da Afghanistan da Pakistan da Indiya da Ozbakistan da Turkumanistan da Kazakhstan. Duka sun shiga Musulunci ne a hannun mahayan Banu Umayya.

* Banu Umayya ne suka kai Musulunci Turai; dama dai Andalus Banu Umayya ne suka bude ta.
Kudancin Faransa bai taba zama kasar Musulunci ba sai zamanin mujahidan Banu Umayya.
* Abdurrahman Addakhil dan kabilar Banu Umayya ne. Shi ne ya ceto Andalus daga rugujewa.

* Abdurrahman Annasir dan kabilar Banu Umayya ne. Ya kasance daga manyan sarakunan duniya. Banu Umayya sun baza manzanninsu a lungu da saqon duniya suna kiran mutane zuwa ga addinin Allah (SWT); Manzannin Banu Umayya sun kai Musulunci China, wadanda su ka musu lakabi da *(masu fararen kaya)*.

* Ilimi ya yadu an yi mulki da adalci a zamanin Banu Umayya, a ka fara tattara hadisan Annabi a mulkin Banu Umayya.
* A zamanin Mulkin Banu Umayya a ka fara tattara hadisan Annabi, suka fassara kundaye zuwa larabci, su ka yi takardun kudin na Musulunci, su ka kera jirgin ruwan yaki na Musulunci na farko a tarihi.
* A zamanin mulkin al-Walid dan Abdul Malik dan kabilar Banu Umayya Musulunci ya yi kasaitar da bai taba yin irinta ba a tarihi.

* A zamanin Banu Umayya aka yi kiran sallah a duwatsun Himalayan kasar Sin, da qungurmin yankin Afrika da dazukan kasar Indiya da ganuwar Kusdundiniyya da kofofin Faris, da jigayin Portugal da gabban bakin kogi da fakon Georgia da bakin kogin Cyprus.

*A duk wadannan garuruwan farar tuta ce ta Banu Umayya dauke da kalmar *(La ilaha illallah Muhammadun Rasulullah)* ke kadawa.

*Allah Ya sakawa Banu Umayya kan abin da suka yi wa Musulunci da Musulmi.*

Da wannan na ke ganin dalilin da ya sa suka kafawa Banu Umayya kahon zuka.
Batun: Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi