Buhari da Muslim: Babi na Dari da Tamanin da Uku, Babi na Dari da Tamanin da Biy
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=904

 
Buhari da Muslim: Babi na Dari da Tamanin da Uku, Babi na Dari da Tamanin da Biyu, Babi na Dari da Tamanin da Shida, Babi na Dari da Tamanin da Bakwai, Babi na Dari da Tamanin da Takwas

Tare da Sheikh Yunus Is'hak Almashgool, Bauchi

Babi na Dari da Tamanin da Biyu: Lallai Allah zai karfafa wannan addini ko da ta karkashin fajiri ne:

15. An karbo daga Abul Yaman ya ce: "Shu'aib ya ba mu labari daga Zuhuri, Hawwala Sanad.

16. An karbo daga Mahmud ya ce: "Abdurrazak ya ba mu labari ya ce, Ma'amar ya ba mu labari daga Zuhuri daga Dan Musayyab daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: "Mun halarci wani yaki tare da Manzon Allah (SAW) sai ya ambaci wata magana ga wani mutum da ke da'awar Musulunci (Annabi SAW) ya ce: "Wannan yana daga cikin mutanen wuta. Lokacin da ya halarcin yakin nan, mutumin nan ya yi yaki mai tsanani sai aka yi masa rauni. Sai aka ce ya Manzon Allah, wanda ka fadi wata magana game da shi dazu cewa yana daga cikin mutanen wuta, ya mutu." Sai Annabi (SAW) ya ce: "Wuta zai tafi," har sai da wadansu mutane suka kusan su yi kokwanto (bisa ga abin da Annabi SAW ya fada). Ana cikin haka sai aka ce, bai mutu ba amma dai yana da rauni mai tsanani. Lokacin da dare ya yi sai ya gaza hakuri bisa raunin sai ya kashe kansa. Da aka ba Annabi (SAW) labarin haka sai ya ce: "Allahu Akbar, na shaida lallai ni bawan Allah ne kuma ManzonSa ne." Sa'an nan ya umarci Bilal ya yi shela ga mutane cewa: "Babu wata rai da za ta shiga Aljanna face rai Musulma. Kuma lallai Allah zai daukaka wannan addini ko da ta karkashin mutum fajiri."

Babi na Dari da Tamanin da Uku:

Wanda ya shugabanci mutane wajen yakin daukaka kalmar Allah, ba tare da an shugabantar da shi ba, idan ya ji tsoron abokan gaba:

17. An karbo daga Yakub dan Ibrahim ya ce: "Dan Ulayyatu ya ba mu labari daga Ayyub daga Humaid dan Hilal daga Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi), ya ce: "Manzon Allah (SAW) ya yi muna huduba (a lokacin Yakin Mu'atata). Ya ce: "Zaid dan Haris ya dauki tutar yaki amma an kashe shi. Sa'an nan Abdullah dan Rawah ya karba shi ma an kashe shi. Sa'an nan Khalid dan Walid ya karba ba tare da an nada shi ba, Allah Ya bayar da cin nasara ta wurinsa. Kuma lallai su da aka kashe ba zan so a ce suna raye tare da mu ba, ko ya ce: "Ba za su so a ce suna raye tare da mu ba (Saboda abin da suka iske na alheri.) Lokacin idanuwarsa na zubar da hawaye."

Babi na Dari da Tamanin da Hudu: Neman taimakon karin mayaka a lokacin yaki:

18. An karbo daga Muhammad dan Basshar ya ce: "Dan Abu Addiyu da Sahlu dan Yusuf sun ba mu labari daga Sa'id daga Kattada daga Anas (Allah Ya yarda da shi), cewa: "Lallai Annabi (SAW) kabilar Ri'ilu da Zakawan sun je masa tare da kabilar Usayyatu da kabilar Lahyan. Sai suka riya cewa lallai su, sun musulunta (amma karya suke yi). Kuma wai mutanen suna auka (fada) musu da yaki don haka suke neman taimakon (Annabi SAW) da wadansu mayaka. Sai Annabi (SAW) ya taimaka musu da mutum saba'in daga mutanen Madina. Anas ya ce: "Mun kasance muna kiransu da sunan: Makaranta Alkur'ani. Sun kasance suna dauko itace da rana da dare suna ta Sallah. Sai suka tafi da su har sai da suka isa rijiyar Ma'unatu sai suka yaudare su, suka kashe su (Makaranta Alkur'anin). (Annabi SAW) Ya rika musu kanuti kusan wata guda yana addu'a a kan Ri'il da Zakawan da Lihyan. Kattada ya ce, Anas ya ba mu labari ya ce: "Lallai su, sun karanta musu Alkur'ani da cewa: "Ya Allah! Ka isar da wannan abin da ya faru da mu ga jama'armu. Lallai mun hadu da Ubangijinmu Ya yarda da mu, kuma mun yarda da abin da Ya yi mana." Sa'an nan wannan aya aka dauke (shafe) ta.

Babi na Dari da Tamanin da Biyar:

Wanda ya samu rinjaye a kan abokan gabansa sa'an nan ya kwana nan gari har kwana uku.

19. An karbo daga Muhammad dan Hatim ya ce: "Rauhu dan Ubadatu ya ba mu labari ya ce, Sa'ad ya ba mu labari daga Kattada ya ce, "Anas dan Malik ya ambata mana daga Abu Dalhat (Allah Ya yarda da su) daga Annabi (SAW) cewa: "Lallai shi ya kasance idan ya samu nasara a kan abokan gaba, yakan zauna a farfajiyar gari kamar kwana (dare) uku."

Babi na Dari da Tamanin da Shida:

Wanda ya raba ganimarsa ta yaki ko a bisa ga hanya (komowarsa) daga tafiya. Rafi'u ya ce: "Mun kasance tare da Manzon Allah (SAW) lokacin da muka iso Zul Hulaifa, mun samo taguwa da tumaki, kuma ya daidaita tumaki goma bisa rakumi daya."

20. An karbo daga Hudabat dan Khalid ya ce: "Hammam ya ba mu labari daga Kattada cewa: "Lallai Anas ya ba shi labari ya ce: "Annabi (SAW) ya yi Umara daga Ji'ranata inda ya raba ganimar yakin Hunain."

Babi na Dari da Tamanin da Bakwai:

Idan kafiri ya samu ganimar dukiyar Musulmi sa'an nan shi (Musulmi) ya iske ta. Dan Numair ya ce: "Ubaidullahi ya ba mu labari daga Nafi'u daga Dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce: "Doki ya taba gudu masa, sai abokin gaba ya kama shi. Ana nan haka Musulmi suka samu nasara a kan kafiran. Sai aka mayar masa a zamanin Manzon Allah (SAW). Kuma bawansa ya taba gudu ya fada hannun Romawa, lokacin da Musulmi suka samu nasara a kansu, Khalid dan Walid ya mayar masa bayan rasuwar Annabi (SAW)."

21. An karbo daga Muhammad dan Basshar ya ce: "Yahaya ya ba mu labari daga Ubaidullahi ya ce, Nafi'u ya ba ni labari cewa: Lallai wani bawan Abdullahi dan Umar ya taba gudu ya fada hannun Romawa. Khalid dan Walid ya samu nasara a kansu, ya mayar da shi ga Abdullahi. Kuma lallai wani dokin Abdullahi dan Umar ya taba gudu ya fada hannun Romawa da aka ci su da yaki aka mayar da shi ga Abdullahi."

22. An karbo daga Ahmad dan Yunus ya ce: "Zuhair ya ba mu labari daga Musa dan Ukba daga Nafi'u daga Dan Umar (Allah Ya yarda da su), cewa: Lallai shi ya ya kasance a bisa wani doki ranar haduwar Musulmi da shugaban Musulmi Khalid dan Walid a wannan yini Abubakar ya aika shi (Khalid). Sai abokin gaba ya karbe shi (doki), da aka ci abokan gaba da yakin, Khalid ya mayar masa da dokin."

Babi na Dari da Tamanin da Takwas:

Wanda ya yi magana da harshen Farisanci ko da wata salon magana na Larabci. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: "Da sabanin harsunaku da launukanku…" (K:30:23). Da fadarSa cewa: "Ba Mu aiko wani Manzo ba face da harshen mutanensa…" (K:14:4).

23. An karbo daga Amru dan Aliyu ya ce: "Abu Asim ya ba mu labari ya ce, Hanzalatu dan Abu Sufiyan ya ba mu labari ya ce, Sa'id dan Mina'u ya ce: "Jabir dan Abdullahi (Allah Ya yarda da su), ya ce: "Na ce, Ya Manzon Allah! Mun yanka wata tinkiyarmu kuma na gasa garin sha'ir sa'i daya. Ka zo da jama'arka mu ci, sai Annabi (SAW) ya daukaka muryansa ya ce: "Ya ku masu hakar Khandak (gwalalo)! Ku zo, Jabir dan Abdullahi ya girka mana Su'r." (kalmar Su'r da harshen Farisanci shi ne abinci)."

24. An karbo daga Habban dan Musa ya ce: "Abdullahi ya ba mu labari daga Khalid dan Sa'id daga babansa daga Ummu Khalid 'yar Khalid dan Sa'id ta ce: "Na tafi ga Manzon Allah (SAW) tare da babana lokacin ina sanye da wata taguwa fatsa-fatsa. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: "Sanah! Sanah!" Abdullahi ya ce: "Kalmar (mutanen) Habasha ce, ma'anar ya yi kyau." Ta ce, "Sai na tafi bayansa ina wasa da hatimin Annabci, babana ya hane ni. Manzon Allah (SAW) ya ce, "kyale ta." Sa'an nan Manzon Allah (SAW) ya ce: "Ki sanya ta har sai ta rududdege, ki sanya ta har sai ta rududduge, ki sanya ta har sai ta rududduge (mutu)." Abdullahi ya ce: "Ta rika sanya taguwar nan kuma ta yi karko har ta kode ta zamo baka, (saboda addu'ar Annabi)."Batun: Al'Adun Musulmi Da Darajoji