Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
 
Wannan Labari Ya fito Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
URL na Wannan Labari Shine:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=937

 
Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni'imarSa kyawawan abubuwa suke cika. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Manzon Allah, Muhammadu dan Abdullahi (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jinkai ga talikai, kuma manuni zuwa ga samun alheran duniya da Lahira; (Amincin Allah ya tabbata ga alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsa cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.

Lallai ne, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah (Alkur'ani), kuma mafi alherin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al'amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira cikin addini bata ne, dukkan bata kuma karshenta wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta, amin.

Bayan haka, yau mukalarmu za ta gudana ne kan amsar tambayar da aka yi wa marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam kamar haka:

Mene ne hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla? – Daga baya kuma sai mu ga abin da wadansu malaman suka ce, in Allah Ya so.

Amsa: Addu'a bayan an kammala sallar farilla (ta danganci) nau'in addu'ar da Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) yake yi, (wanda) shi ne ‘Du'a'u Ibada,' ba Du'a'u Mas'ala ba.
Duk inda ka karado, ka biyo Hadisan Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), za ka iske cewa tabbataccen abin da yake yi, ad'iyya (addu'o'i ) ne wadanda suke cikin babin ‘Du'a'u Ibada.' Ana gama sallama, zai yi istigifari uku: Astagfirullah! Astagfirullah! Astaghfirullah! Sannan ‘Allahumma antassalamu wa minkassalam tabarakta ya zaljalali wal ikram. La'ilaha illallah….. da sauran addu'o'i da suka tabbata Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) na yi, wadanda dukansu za ka samu azkaar ne, sun kunshi yabo ne ga Allah. Bayan ya gama, sai ya zo ya yi wannan tasbihi, Subhanallaah (33); Alhamdulillah (33); Allahu Akbar (33). Wani lokacin goma, goma yake yi. Ko ka yi goma, goma; ko talatin da uku-uku, ko ashirin da biyar-biyar; duk Hadisai sun zo da su.

To, wadannan addu'o'i su ne aka samu Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), na yi. Al'ad'iyya (addu'o'i) din da ake yi. Ya karanta wannan, ya karanta wannan. In ya kammala su, shi ke nan sai ya tashi, ya yi tafiyarsa. Amma (kai ya zamo) bayan ka kammala, kuma ka daga hannu, ka ja ‘Lakad ja'akum; Li'ilafi; Ayatul Kursiyyu; ko kai kadai ne ka yi, ba ka da nassi kan wannan! Ba wai da jama'a ba, cewa liman ya karanto; wannan kari ne a kan kari. Ko kai kadai, abin da ya tabbata Annabi (SWA) na yi, shi ne wadannan ad'iyya din.

Ku gane cewa dadewa ana yin abu, ko sabonsa, ba shi ke sa ya zama addini ba. Kada ma mu bi ta Hadisi, kila shi ne wadansu ke ganin ‘kawai ana cewa a kawo Hadisi don a kure mutane.' Ka bi littafin fikihu, ka kawo guda daya na Malikiyyarka da ka karanta, wanda ya ce in ka kammala sallama, kuma ka daga hannu ka yi addu'a! Guda daya, ba ka da shi… karshen dai kalubale ke nan! Ka kawo littafin fikihu guda daya, a Malikiyance da ya ce, in ka gama Sallah (ka daga hannu) ka yi addu'a. Dukkansu suna magana ne a kan ka yi tasbihi; ka yi hailala; ka yi istighfari ne, (Subhanallaah, Alhamdulillah, Allahu Akbar) da sauran zikirorin da Annabi (SAW) ke yi. Wadannan wurare ne na zikiri da shi ake kira Du'a'ul Ibada, amma Du'a'ul Mas'ala, (ita ce) addu'a da ka yi ta roko,wadda tun a cikin Sallah ka yi ta. Tun lokacin da kake karatun Fatiha ka yi ta! Don (in) ka karanta Fatiha, akwai Du'a'ul Ibada, akwai Du'a'ul Mas'ala. Ayoyi hudu na farko duk Du'a'u Ibada kake yi, sauran ayoyi ukun kuma Du'a'ul Mas'alah. (Ka duba Hadisin Muslim – Hadisul kudsiy, inda Allah Ya ce Ya raba Sallah tsakaninSa da bawanSa….). Tun kana tsaye, sai aka tsara maka, ga shi da ma za ka yi roko… Duk abin da za ka roka, ai a bayan (samun) shiriya yake – Ihdinassiradal mustakim…. In ka samu wannan, ka samu arzikin duniya da Lahira gaba daya! Duk da wannan, ba a hana ka yin addu'a ba. Sai ka zo cikin sujada, ka yi addu'a kuma, tunda Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce, shi ruku'i ku girmama Ubangiji, sujada kuma, in kun zo, ku nace cikin addu'a, "Ya dace a amsa muku duk addu'ar da kuka yi cikin sujada."

Duk wannan ba ta kare ba, idan ka kammala tahiyyar karshe, ka yi salatin Annabi, haka kuma wannan rarar wurin, duk na addu'a ne. Ka roki Allah Ta'ala, kafin ka yi sallama. Kana gama sallama, wuraren addu'a sun kare cikin Sallah kuma, yanzu sai Du'a'ul Ibadah za ka yi, ba Du'a'ul Mas'alah ba. Tun farko, ko da ad'iyyatil istiftahi (addu'o'in bude Sallah), dukansu za ka samu sun kunshi Du'a'ul Ibadah ne da Du'a'ul Mas'alah…

Batun ayoyin surar Alamnashrah na karshe, ba ta magana kwata-kwata a kan addu'a bayan Sallah, wani abu take magana a kansa daban. Kuma surar tana cikin surorin farko-farkon wahayi, Makkiyya ce ba Madaniyya ba, lokacin ma da ta sauka, in ka bi a tarihance, ba a riga an wajabta Sallah ba, ballanta ka ce maganar Sallah ake. Ko ma an wajabta Sallah dai, ba ta nufin cewa ka yi addu'a bayan Sallah. Kai, ko ma dai tana nufin ka yi addu'a bayan Sallah, cewa aka yi ka yi Du'a'ul Ibadah, ba Du'a'ul Mas'alah ba.

Ta kowane hali dai Du'a'ul Ibadah ake yi, ba Du'a'ul Mas'alah ba, a hadisance, duk wanda yake inkarin haka, sai ya kawo ko da Hadisi mai rauni da ya nuna akasin haka.

Ibnul kayyum ne kawai ya ba masu jayayya wata mafaka, ya ce, "Masu irin wannan, sai dai mu ba su mafaka, mu ce: Bayan mutum ya gama Sallah, da ma abin da yake yi zikirori ne (irin dai yadda muka yi bayani), to mu dauka, wadannan zikirorin da mutum zai yi bayan ya kammala Sallah, wata ibada ce mai zaman kanta, wadda ba ta da alaka da Sallah, don Sallah dai ta riga ta kare daga lokacin da ka yi sallama, don Annabi (SAW) ya ce, ‘Wa tahliluha taslimu' wato yin sallama shi ne karshenta, ka riga ka yi sallama, Sallah ka kare. Lokacin da ka zo wadannan zikirorin, wadansu ibadoji ne masu zaman kansu, to kuma bayan ka gama su, sai ya darsu a cikin zuciyarka kana da bukata (iri) kaza, sai ka yi tawassuli da wannan ibadar da ka yi, ta wadannan addu'o'in (zikirorin) ka yi tawassuli da su, don wata bukatarka." Ya ce to, ‘sai dai in haka za ka yi.'

To yanzu kuwa wa zai yi Sallah, mu ga yana addu'a, mu ce ‘don me kake addu'a?' Ka ga dai shi addu'arsa, ta Sallah yake yi, ba ruwansa da cewa ta wadancan abubuwan (bukatunsa) yake yi (wato Azkaru na Du'a'ul Ibadah, ba na Mas'alah ba). To wannan shi ne masakatar da Ibnul kayyim ya dan bayar a cikin littafin Zadul Mi'ad fiy Hadyi Siyaril Ibad. (8.46).

Wannan shi ne karshen bayanin tambayar, sai mako na gaba mu ci gaba.

Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh!


 

Batu: Al'Adun Musulmi Da Darajoji


Comments 💬 التعليقات