Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Al'Adun Musulmi Da Darajoji
[ Al'Adun Musulmi Da Darajoji ]

·Falalar Darare Goma na Zul-Hajji
·Dabbobin Layya da kwanakin 10 na farkon Zul-Hajji
·Azumi da abubuwan da yake koyarwa (4)
·Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
·Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
·Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
·Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
·Buhari Da Muslim: Babi Na Hudu 140 - 142 & 148
·Buhari da Muslim: Babi na Talatin da Biyu 114 - 124

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Tuesday, April 26
· Gargadi Ga Azzalumi Da Tausar Wanda Ake Zalunta (1)
Wednesday, December 09
· Me Ke Kawo Rauni Ga Musulmi?
· Wani Sashe Na Mahalarta Taron Tunawa Da Zuwan Boko Kasar Hausa
Wednesday, December 02
· ''BAN SAKI AHLULBAITI BA NA KAMA SAHABBAI''
· SAHIHIYAR AQIDA ITA CE JIGO CIKIN ADDINI
Sunday, September 20
· MAFITA GA CUTAR EBOLA
Sunday, May 31
· Musulmi nagari da ke kan Sunnar Annabi (SAW)
Monday, April 27
· BAYANI DAGA MAJALISAR MALAMAN AFRIKA GAME DA BARAZANAR DA 'YAN UWANMU MUSUL
Friday, June 06
· HUDUBA DAGA MASALLACIN ABU HURAIRA (R.A): Ina Kadiradawa? Ga sako na musamman zu
· KALUBALEN DA KE FUSKANTAR MATASA MUSULMI A YAU (2)
Sunday, March 30
· Mahimman abubuwa daga khudbar Juma’an yau 20/12/1434 wanda ya dace da Masallacin
· DABI’UN MUMINI A LOKACIN FITINTINU
Thursday, November 07
· Shari’ah Itace Mafita Ga Bil’adama
· SAKO GA MASU FAMA DA WASWASI
Monday, September 30
· Soyayya Da Kiyayya Don Allah
· Kula Da sana’a
· Jagoranci
· YAYA TSAKANIN KA DA AL’UMMA.?
· WAYE BAYA SON SAMUN RABO NA ALHERI..?
· LADABI DA BIYAYYA HALAYE NE ABIN KOYI GA MUTANEN KIRKI
Thursday, June 06
· Abun Farinciki Daga Wa'azin Lokoja! Kashi na (1)
Wednesday, June 05
· Mummunan Fushi: Farkon Sa Haura Ne Karshen Sa Nadama Ne
Thursday, March 21
· Mene Ne Hukuncin Zance?
· Ko Kasan Daga Ina Aka Gano Maukibi?
Friday, February 15
· Mu’yan Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah Sai Mu Yi Murna Mu Y
· Alamomin Cikawa Da Imani Guda 21
Sunday, May 13
· Bikin aurar da matasa (3000) Lokaci Guda: Wasu daga cikin angwaye “Nakasassu”
· Ya Mutu Ya Dawo! Martabar Iyaye: Yaushe Ne 1000000=1000???!!! (Kalu-Bale Ga Wasu
Tuesday, March 27
· Matsayin gemu a Musulunci (5)
· Matsayin gemu a Musulunci (4)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai

EsinIslam Media: Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

Search on This Topic:   
[ Go to Home | Select a New Topic ]

Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni'imarSa kyawawan abubuwa suke cika. Madalla da Allah, Wanda Ya sanya laushin zukata a cikin yawaita yi maSa da'a, kuma muna neman tsarinSa daga kutsawa cikin saba maSa, wanda ke sa kekasar zuciya.Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Manzon Allah Muhammadu dan Abdullahi, (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jinkai ga talikai, kuma manuni zuwa ga samun alheran duniya da Lahira; Amincin Allah ya tabbata ga alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsa cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.

Lallai ne, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah (Alkur'ani), kuma mafi alherin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al'amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira cikin addini bata ne, dukkan bata kuma karshenta wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta. Amin.

Bayan haka, mun kwana a daidai inda muka fara bayani a kan sinadari na shida, a cikin wannan mukala, to bari mu somo daga farkonsa. In mai karatu ya tuna mun jero sinadarai kamar haka: Sinadarin zikiri da na kiyaye gabobi daga sabo da na yawaita karanta tafsirin Alkur'ani Mai girma da na halartar darussan malamai da kuma na karanta littattafan malamai masu aiki da iliminsu wajen tsoron Allah. To, ga karashensu:


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

Asalin Hausa (3)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Asalin Hausa (3)

Farfajiyar Kasar Hausa a zamanin Kankara da Ruwan Dufana

Tattaki da tuntuɓa da gawarwakin mutane da dabbobi da albarkatun ƙasa da duwatsu da ke turbuɗe a ƙasa wasu makamashin gina tubalin tarihin mazauna duniya ne. Akwai zamanin da ƙanƙara ta lulluɓe wurare da dama da tsaunuka (Glaciatios of mountains). Mahadi Adamu ya ce: "Tsaunin Ayar yana daga cikin tsaunuka da ƙanƙarewar tsaunuka ta auka wa duniyar Sahara. Ƙanƙarewa a Sahara ta ci gaba har zuwa shekarar 18 B.C. Tsaunin Ayar yana daga Arewacin farfajiyar ƙasar Hausa ta gado."

Ashe ke nan, Hausawa (da Kasar Hausa) sun shiga yanayin ƙanƙarewar tsaunuka kimanin shekara miliyan biyu da suka shuɗe.

Wannan taƙaitaccen bayani ya kore tatsuniyar Bayajidda da aka ƙirƙira jiya. Haka kuma, zancen zuwan Gabasawa daga Makka ko Bagadaza ko Iraƙi bai taso ba, a irin shekarun da aka ambata. A wani dogon saƙon da Mahadi Adamu ya yi cewa ya yi:

"Za mu fara kirdadon haƙa tarihin ƙasar Hausa na wani lokaci (mai tsawo) kimanin shekara miliyan 430, lokacin da ƙoƙon duniyar wannan farfajiya tamu ɗaya ne, har ya soma rarrabuwa zuwa farfajiya biyar da muke ciki a yau.

Lokaci da ake zaton duniyar mutane ta mamaye da ruwa gaba ɗaya, bayan janyewar ruwan sabon kundin tarihin mutane ya fara aiki. Masu bincike sun tabbatar da cewa, garuruwan Dange Shuni da Sakkwato da Kware da Wurno da Gwaranyo da Illela da Gudu da Tangaza a mazauninsu na yanzu can da ƙarƙashin wannan makeken kogi suke. A 1920 an ƙara samun hujjojin da suka ƙarfafa wannan da'wa ta Mahadi Adamu.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

Asalin Hausa (2)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Asalin Hausa (2)

Zuriyar Harshen Hausa

Masana ilimin harsuna sun karkasa harsunan duniya zuriya-zuriya. Kowane harshe na duniyar mutane dole da rukunin da yake. A rukunin da ya fito nan ake kirdadon tushensa da tushen masu magana da shi. Masana ilimin harshe sun ce:

"Hausa harshe ne daga cikin zuriyar harsunan Chadi, waɗanda sun kai fiye da harsuna ɗari da ake magana da su a Arewacin Najeriya da Arewacin Kamaru da kuma tsakiyar Chadi."

Daga cikin harsuna iyalan Chadi, Hausa ta fi kowane bazuwa da yawan jama'a da karɓuwa da mamaye ƙasa. Daga cikin fahimtar sanin asalin harshe shi ne a san tarihinsa. Babban muhimmin abu shi ne gano dangantakar harshe da sauran harsunan da suke zuriya/iyali ɗaya. Babu makawa ga mai son sanin tushen Hausa ya yi ƙwaƙƙwaran nazarin harsuna iyalan Chadi. A tsarin ilimin harsuna an ce:

"Idan aka ce harshe (kaza) ɗan iyalan gungun harsuna (kaza) ne, ana son a tabbatar da cewa, a da can baya harshe ɗaya ne kacal daga gare shi ne sauran harsunan zuriyarsa suka tsira."

Abubuwan da ke sa masu magana da harshe su warwatse, harshen ya ragaice, sun haɗa da yaƙe-yaƙe da yunwa da annoba da mulkin mallaka da kuma buƙatar ɗan Adam ta sauya mazauni ko babu dalili. Idan aka duba, sojojin Romawa a kai da kawonsu na yaƙe-yaƙe suka tsirar da harshen su Spanish da French da Italiya da Portuguese da kuma harshen Latin. Paul Newman (1977) ya karkasa harsunan iyalin Chadi kamar haka:


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

Asalin Hausa (1)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Asalin Hausa (1)

Binciken gano diddigin tarihin mutane wata matsala ce mai cin rayuwar masu bincike da waɗanda ake yi wa binciken. A lokacin da ilimi ya bunƙasa, kowace al'umma ƙoƙari take ta taskance tarihin asalinta.

Wurin da gizo ke saƙa shi ne, babu mai nunin gidansu da hannun hagu. Maimakon a yi canjaras ga abu guda, sai a ga kowane bakin wuta da irin nasa hayaƙin. A ƙarshe, a kasa rarrabe tatsuniya da tarihi da tarihihi da ƙari-faɗi da kintaci-faɗi da jita-jita hadisin Bamaguje.

Ƙudirin wannan bayani ko bincike ba suka ba ne, ko kushe ga ƙwazon magabata a kan asalin Bahaushe da harshensa. Ganin cewa, abu ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa ake son a sake farfaɗo da matakan al'ada na tantance tarihi da bibiyar diddigin asalinsa.

Asalin asali a al'ada

Asali, kalmar Larabci ce, gangariyar Hausa ita ce "tushe" ko "dugi." A al'adar mutanen duniya, a tsarin ƙabilu, akwai manya da ƙanana. A siyasar zamaninmu, akwai masarauta da talakawa. A tattalin arziki, akwai mawadata da kuma moro (talaka). A addini, akwai masu bi akwai makangara. A wayewa, akwai ƙauyawa akwai 'yan birni. A sani, kuma akwai malamai 'akwai jahilai. A ɗiyauci, akwai 'yantattu akwai bayi. Bugu-da-ƙari hatta a zaman gari, akwai 'yan gida akwai baƙi. Inda matsalar take a al'adance babu mai yarda ya ce, asalinsa na da cikas. Shin wace ƙabila za ta yarda a ce da ita ƙarama? Wa ke son a danganta shi da talauci? Wa zai yarda da cewa matsiyaci ne tushensa? A addinance, wa zai so a kira kakanninsa makangara ne? Ko ɗan kauye. A ko yaushe dan Adam ya ƙi jinin a ce shi jahili ne. Da an ce wa mutum bawa, za a ga fushinsa bayyane. An san da cewa mai rai baƙon duniya ne, idan mutum ya yi kaka-gida a wuri ba ya son a kira shi baƙo mai suna tafaffe a ma'aunin 'yan gida zaunannu.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

Yadda Musulmi Zaiyi Ta'amuli A Bukin Kiresriti
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Daga: Dr. Mansur Sokoto

Yadda Musulmi Zaiyi Ta'amuli A Bukin Kiresmiti

Daga: Dr. Mansur SokotoDa yake a Nigeria ana zaman cakuda ne tsakanin

al'ummar Kirista da al'ummar Musulmi. Sannan da yake shi Musulunci addini ne da ya bayyanar da hukuncin dukkan wani lamari da ya shafi rayuwar dan Adam, ko dai ta hanyar nassi, ko ta hanyar zahiri, ko ta hanyar ishaarah da iimaai. Sannan da yake akwai karkatattu da dama da suke halatta abin da Shari'ah ba ta halatta ba, ko haramta abin da Shari'ah ba ta haramta ba, lalle ya dace a yi wa al'ummar Musulmi bayanin hukuncin abin da ya shafi wannan Idi na Kirsimeti ta bangarorinsa da ke iya shafar wasu al'ummar Musulmi.

To amma kafin mu shiga bayanin wadannan hukunce-

hukunce ya kamata Musulmi su san abubuwa kamar haka:-

1. Shi dai bukin kirsimeti wata bidi'ah ce da bata da

Kiristoci suka kirkira sannan suka maida ita wata ibada da ake samun lada ta hanyar yin ta kamar dai yadda wasu Musulmi suka kirkiri bidi'ar idin Maulidi, Kiristoci sun kirkiri wannan bidi'ar ce kuwa a shekarar Miladiyyah ta 360, watau a cikin karni na hudu bayan haifuwar Annabi Isa alaihis salam.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

08 SHIN KASANCEWA SAYYIDUNA MU'AWUYA DAN ALJANNA NE ????
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Muawiyya bn Abi Sufyan

08 SHIN KASANCEWA SAYYIDUNA MU'AWUYA DAN ALJANNA NE ????

KASHI NA BIYAR.

الحمد لله رب العالمين. و الصلاة والسلام على سيد محمد وعلى آله و أصحبه اجمعين.

ACIGA BA DA KAWO DALILAI NA ALQUR,ANI DA KUMA HADISAN MA,AIKI DA MAGANGANU NA MAGABATA NA QWARAI AKAN KASANTUWAR ZAMANTOWAR SAYYIDINA MU'AWUYA DAN ALJANNA NE YAU ZAMU DORA A INDA MUKA TSAYA.

ALALHAQIQA HADISI YAGWADAMANA FALALA MAI GIRMA GAWANDA YAYI YAQI DAN DAUKAKA KALMAR ALLAH HAR MA,AIKI YAKE YIMASA BUSHARA DA CEWA

وعن ابي عبس عبدالرحمن بن جبر قال.قال رسول الله ما اغبرت قدما عبد في سبيل الله فتمسه النار.

TO LALAI MA,AIKIN ALLAH YANA CEWA QAFAR BAWA BAZASUYI QURABA AKAN TAFARKIN ALLAH KUMA WUTA TA SHAFESHI.

ALLAHU AKHBAR, TO INDAI KUWA HAKANE TO S.MU,AWUYA KO QANSHIN WUTA MA BAZAI JIBA DOMIN SHI NE WANDA YAHADA RUNDUNA TA YAQI DOMIN AJE AKAI SAQON ALLAH HARGARIN مدينة قيصر. KUMA MA,AIKI DAMAN YAFADA WADANDA ZASUYI WANGA AIKI TO مغفورلهم ANGAFARTA MUSU KO MA CIKIN فتح الباري /٦/١٢٠
KASHA QARIN BAYANI KO البداية والنهاية ٥/٦٢٩،٦٣٠


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

002 LADUBBAN TAREWA Rubutu na 2
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
002 LADUBBAN TAREWA Rubutu na 2

*Yadda Ake Yin Bikin Aure*

Bikin aure wanda ya ƙunshi yayata shi da bayyana shi abin so ne, in ji malamai saboda dalilai masu yawa kamar haka:

Maganar Annabi (Sallal Laahu 'Alaihi wa Aalihi wa Sallam) cewa: Bambancin da ke tsakanin halal da haram shi ne, buga dundufa da jin muryar (waƙa a wurin aure). ²

Kuma a lokacin da su A'ishah r.a suka kai wata amarya gidan mijinta sai Annabi (Sallal Laahu 'Alaihi wa Aalihi wa Sallam) ya ce: A'ishah! Ba ku da wadda za ta yi ɗan waƙa ne, domin su Lansarawa mutane ne da suke sha'awar wasa. ³

Wannan ya nuna abubuwa kamar haka:
° Ya halatta waɗansu mata masu mutunci su raka amarya zuwa gidan mijinta a ranar tarewarta. ⁴

° Kuma in aka samu wata mai rera waƙar aure irin na al'ada a cikinsu duk ya yi daidai.

° Daidai ne kuma matan da suka kai amaryar su zauna a gidan amaryar kuma su saurari irin wannan waƙar.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

001 LADUBBAN TAREWA Rubutu na 1
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
001 LADUBBAN TAREWA Rubutu na 1

بسم الله الرحمن الرحيم
DA FARKO
Godiya ta tabbata ga Allaah, muna gode masa muna neman taimakonsa muna neman gafararsa kuma muna roƙon Allaah ya tsare mu daga sharrorin kawunanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allaah ya shiryar babu mai ɓatar da shi, wanda kuma ya ɓata babu mai shiryar da shi.

Na shaida babu abin bautawa bisa cancanta sai Allaah, shi kaɗai ba shi da abokin tarayya, kuma na shaida lallai Annabi Muhammad (Sallal Laahu Alaihi wa Aalihi wa Sallam) bawansa ne, kuma manzonsa ne.

Bayan haka, haƙiƙa! Mafi kyawun magana shi ne Littafin Allaah, kuma mafificiyar shiriya ita ce shiriyar Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi wa Alihi wa Sallam), kuma mafi sharrin al'amura su ne ƙirƙirarrunsu, kuma dukkan wata ƙirƙira bidi'a ce, kuma dukkan wata bidi'a ɓata ce, kuma dukkan ɓata tana cikin wuta.¹

Bayan haka, tun a shekarun baya ne na gabatar da wata muhaadara a Cibiyar Koyon Musulunci (ILC) wadda ta ke kan titin Katuru, U/Sarki, Kaduna mai taken: LADUBBAN TAREWAR AURE A MUSULUNCI. Wannan darasin ya dogara ne kacokan a kan littafin 'Aadaabuz Zifaaf' na babban malamin Salafiyyah, masanin Hadisi da Sunnah As-Shaikh Muhammad Naasiruddeen Al-Albaaniy (Rahmatul Laahi Alaihi). Domin saƙon da littafin nasa ya ƙunsa ne na taƙaice shi a cikin kaset a lokacin, saboda amfanin masu fahimtar harshen Hausa daga cikin 'yan uwa musulmi.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

GASKIYA KENAN! YAU 'YAN IZALA NE AKE RIGIMA DASU WAJE KARE MARTABAR MANZON
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
GASKIYA KENAN!!!!

GASKIYA KENAN! YAU 'YAN IZALA NE AKE RIGIMA DASU WAJE KARE MARTABAR MANZON ALLAH (S.A.W)

Wai yau ya'n ixala ne ake rigima dasu akan kare martabar manzon allah (s.a.w)....
wai ayau ne ake ganin cewa ya'n izala xasu tada hargitsi agari saboda an zagi manzon allah (s.a.w).

wai yau malamin izala ake kai kara gurin ya'n sanda saboda ya tashi tsaye wjen bayarda kariya ga manzon allah (s.a.w).

INA MASU KURURUWAR CEWA : YA'N IXALA BASA SON MANZON ALLAH (S.A.W)???
yanzu dai gaskiya ta fito tarwar ga mai nemanta..
ada idan an bayyana jama'a cewa ya'n dariqa basa ganin girman ma'aiki irin yanda suke kimanta shehinnansu sai ka iske wasu jama'a suna ganin baiken hakan… shin har yanzu zaku cigaba da musanta hakan??
ada ana kaiwa ya'n izala hari dasunan cewa zasu zagi manzon allah a guraren karatukansu, amma kuma yau su ake kaiwa hari saboda sun kafa majlisi don bayarda kariya ga manzon allah din.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

Babu sabani a tasakanin Malamai cewa yin tabligi a bayan liman ba tare da wata b
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
By Dr. Ibrahim jalo jalingo

Babu sabani a tasakanin Malamai cewa yin tabligi a bayan liman ba tare da wata bukata ta Shari'ah ba bidi'ah ce a bar kyama

Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya ce cikin Majmuu'ul Fataawaa 23/403 ((. : )). Ma'ana: ((Amma Tabligi bayan liman ba tare da wata bukata ba hakan bidi'ah ce ba mustahabbah ba a bisa ittifakin Shugabanni. Abin da aka sani Liman ne zai rika bayyanar da kabbara kamar yadda Annabi mai tsira da amincin Allah da Khalifofinsa suka kasance suna yi. Babu koda mutum guda da ya kasance yana yin tabligi a bayan Annabi mai tsira da amincin Allah, sai dai a lokacin da Annabi mai tsira da amincin Allah ya yi rashin lafiya sautinsa ya yi rauni Abubakar Allah Ya kara masa yarda ya kasance yana jiyar da kabbararsa. Hakika Malamai sun yi sabani game da cewa: Ko sallar mai yin tabligi tana baci? A bisa zantuka biyu cikin mazhabar Malik da Ahmad da wasunsu)).

Saboda abin da muka ji yanzu yana kyau al'ummarmu su sanya girmama sunnar Manzon Allah cikin dukkan ayyukansu na ibadah, su daure su daina yin tabligi a lokacin da mamu ke jin kabbarorin limaminsu, wannan ita ce Sunnah ta Annabi mai tsira da amincin Allah da babu sabani a cikinka adai gurin Malamai ba murakkaban jahilai ba.

Lalle muna sane da cewa wasu awaam su kan kafa hujja da cewa: Ai a Kasar Saudiyya ma ana yin tabligi, tunda kuwa haka babu ta yadda za a ce tabligi bidi'ah ce! A gaskiya irin wannan magana babu hujja a cikinta a dai gurin masu ilmin Musulunci; musamman ma ida aka san abubuwa kamar haka:-


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

AL-GHADIR: KALUBALE GA 'YAN SHI'A INGANTACCEN LABARIN GHADIR
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Dr. Mansur Sokoto

AL-GHADIR: KALUBALE GA 'YAN SHI'A INGANTACCEN LABARIN GHADIR:

Kalmar Ghadir a larabce, tana nufin wurin da ya tara ruwa da ciyawa.

''Ghadir Khum'' sunan wani tafki ne da yake a yankin Juhfa, kilomita 15 daga Rabigh. Nisan sa daga Makka kilomita 160 ne.

Labarin Ghadir:

Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallam ya aiki Khalid dan Walid a matsayin kwamandan rundunar da za ta yi yaki a kasar Yaman daf da fara aikin Hajjin shekara ta 10H, hajjin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam da kansa ya jagoranta.

Bayan da rundunar musulmi ta ci nasara sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ya aika Sayyidi Ali don ya kula da sha'anin Ganimar da aka samu.

Ali Radhiyallahu Anhu ya raba Ganima, kuma ya cire hakkin Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam na Khumusi kamar yadda Alkur'ani ya zayyana. Daga ciki kuma ya cire ma kansa wata kuyanga da ta ba shi shawa.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

LADDUBAN MUSULMI: LOKACIN SANYI
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
LADDUBAN MUSULMI: LOKACIN SANYI

* ﺑﺴﻢ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ*


Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Wanda yake jujjuya yanayi yanda yaso, Wanda cikin hakan ayoyi da izinoni, yabo da aminci Annabi Muhammad da iyalansa da sahabbansa, lokacin sanyi lokacine mai falala da mumini ke iya ribatarsa wajen neman yardar Allah, hakika magabata sun kasance suna bushara da murna da zuwansa ﻗﺎﻝ ﻋﻤﺮ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ:

) ﺍﻟﺸﺘﺎﺀ ﻏﻨﻴﻤﺔ ﺍﻟﻌﺎﺑﺪﻳﻦ )
ﻭﻗﺎﻝ ﺍﺑﻦ ﻣﺴﻌﻮﺩ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ : )ﻣﺮﺣﺒﺎً ﺑﺎﻟﺸﺘﺎﺀ ﺗﺘﻨﺰﻝ ﻓﻴﻪ ﺍﻟﺒﺮﻛﺔ ﻭﻳﻄﻮﻝ ﻓﻴﻪ ﺍﻟﻠﻴﻞ ﻟﻠﻘﻴﺎﻡ ، ﻭﻳﻘﺼﺮ ﻓﻴﻪ ﺍﻟﻨﻬﺎﺭ ﻟﻠﺼﻴﺎﻡ).

ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﺤﺴﻦ ﺍﻟﺒﺼﺮﻱ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ : ) ﻧﻌﻢ ﺯﻣﺎﻥ ﺍﻟﻤﺆﻣﻦ ﺍﻟﺸﺘﺎﺀ ﻟﻴﻠﻪ ﻃﻮﻳﻞ ﻳﻘﻮﻣﻪ ، ﻭﻧﻬﺎﺭﻩ ﻗﺼﻴﺮ ﻳﺼﻮﻣﻪ ).


Akwai ladduba da HUKUNCE-HUKUNCE daya kamata mu kiyaye daga cikinsu:

1: *RIBATARSA DA IBADU MUSAMMAN AZUMI,*


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

KANASON ALJANNAH CIKIN SAUKI??
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Abdullahi Muhammad Auwal

KANASON ALJANNAH CIKIN SAUKI??

TO GA MAFITA...

Manzon Allaah sallallaahu alaihi wasallam yana cewa:

A wani hadisin kuma yana cewa:

Ma'ana: (Duk wanda yabi wata hanya ko ya ri'ki wata hanya wanda yike neman ilmi a cikinta; to Allaah zai sau'ka'ke yakuma yassare mishi da wannan ilmin hanya zuwa Aljannah).

Wannan hadisin ya nuna mana girma da falala da ilmi ke dashi, daga cikin falalar – wadda kuma itace mafi girma – shine samun Aljannah.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

KEBANTACCIYAR SALLAH A DAREN NISFU SHA'ABAAN
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Dr. Mansur Sokoto

KEBANTACCIYAR SALLAH A DAREN NISFU SHA'ABAAN.

Malaman hadisi sun ce:

Babu wani hadisin da ya tabbata daga Manzon Allah (saw) game da wannan sallar da ake kira Salatul Alfiyya. Sai hadisai qagaggu da raunana. Kadan daga cikin irin wadannan hadisai akwai hadisin da aka jinginawa Sayyadina Aliyyu wai ya ce: Manzon Allah (saw)
ya ce; ﺇﺫﺍ ﻛﺎﻥ ﻟﻴﻠﺔ ﺍﻟﻨﺼﻒ ﻣﻦ ﺷﻌﺒﺎﻥ ، ﻓﻘﻮﻣﻮﺍ ﻟﻴﻠﻬﺎ ﻭﺻﻮﻣﻮﺍ ﻧﻬﺎﺭﻫﺎ ، ﻓﺈﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﻨﺰﻝ ﻓﻴﻬﺎ ﻟﻐﺮﻭﺏ ﺍﻟﺸﻤﺲ ﺇﻟﻰ ﺳﻤﺎﺀ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ، ﻓﻴﻘﻮﻝ ﺃﻻ ﻣﺴﺘﻐﻔﺮ ﻓﺄﻏﻔﺮ ﻟﻪ ، ﺃﻻ ﻣﺴﺘﺮﺯﻕ ﻓﺄﺭﺯﻗﻪ ، ﺃﻻ ﻣﺒﺘﻠﻰ ﻓﺄﻋﺎﻓﻴﻪ ، ﺃﻻ ﺳﺎﺋﻞ ﻓﺄﻋﻄﻴﻪ ، ﺃﻻ ﻛﺬﺍ ﺃﻻ ﻛﺬﺍ ﺣﺘﻰ ﻳﻄﻠﻊ ﺍﻟﻔﺠﺮ Ma'ana:


''Idan daren Nisfu Sha'aban ya zo ku raya darensa da Qiyamullaili, kuma ku azumci yininsa, domin Allah Madaukakin Sarki yana saukowa zuwa saman duniya daga zarar rana ta fadi, yana cewa: shin akwai mai neman gafara ana gafarta masa, ina mai neman arziki na arzuta shi, ina wanda Allah ya jarrabe shi na yaye masa, ina mai kaza da kaza har zuwa ketaowar alfijir." Amma sallar da ake kira Salatul Alfiyya, salla ce da ba ta da asali a cikin addinin musulunci, kuma an rawaito hadisai masu yawa game da bayanin siffarta da falalarta, sai dai dukkaninsu babu wanda ya tabbata daga Manzon Allah (saw).

Daga cikin wadannan hadisan akwai hadisin da aka jinginawa Sayyadina Aliyyuyu Ibn Abi Dalib wai ya ce:


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

KANA SADA ZUMUNTA?
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
DAGA SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA

KANA SADA ZUMUNTA ?

1-Allah taala yayi Umarni da sada zumunta.

Suratul bakara 36, Suratul Isra'i 26, Suratul Rum 38, Suratul bakara 210, Suratul Nisa'i 2 .

2- Sada zumunta yana kara tsawon rai, Bukari 5986, Muslum 2557.

3- sada zumunta yana kara arziki, Bukari 5986 

4- sada zumunta yana cikin abubuwan da akayi Umarni dashi, tun farkon musulunci, bayan tauhidi, Bukari 7 

5- sada zumunta dalili ne na shiga Aljannah, Bukari 5983 

6- sada zumunta yana cikin abubuwan da Allah yake so. Sahihut-targib 2/667.

7- sada zumunta yana tseratarwa daga azaba, Abu Dauda 4902 

8- sada zumunta wasiyyar da Annabi saw yayi wa Al'ummarsa. Sahihut-targib 2/669 

9- Sada zumunta siffar muminai ce.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

TAMBAYOYI DA AMSA, SHEIK ABDULWAHAB ABDULLAH FALALAR SAHABBAI
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
SHEIKH ABDULWAHHAB ABDULLAH

TAMBAYOYI DA AMSA, SHEIK ABDULWAHAB ABDULLAH FALALAR SAHABBAI

Alhamdu lillahi rabbil A'lamin, wa Sallallahu wa sallama ala Nabiyyina Muhammadin Wa ala a'alihi wa sahbihi ajma'in.

Amma ba'ad, hakika hadisi ya tabbata daga Anas Bin Malik radhiyallahu anhu ya ce; ﻛﺎﻧﺖ ﺍﻷﻧﺼﺎﺭ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺨﻨﺪﻕ ﺗﻘﻮﻝ ﻧﺤﻦ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺑﺎﻳﻌﻮﺍ ﻣﺤﻤﺪﺍ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺠﻬﺎﺩ ﻣﺎ ﺣﻴﻴﻨﺎ ﺃﺑﺪﺍ ﻓﺄﺟﺎﺑﻬﻢ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻻ ﻋﻴﺶ ﺇﻻ ﻋﻴﺶ ﺍﻵﺧﺮﻩ ﻓﺄﻛﺮﻡ ﺍﻷﻧﺼﺎﺭ ﻭﺍﻟﻤﻬﺎﺟﺮﻩ Ma'ana Ansar sun kasance a yayin da suke haka ramin khandaku suna cewa;


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

TASKAR FADAKARWA, TASKAR RUBUTUKAN MALAMAI FADAKARWA GA 'YAU UWA MUSULMI
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
TASKAR FADAKARWA, TASKAR RUBUTUKAN MALAMAI FADAKARWA GA 'YAU UWA MUSULMI

1). Karka rinka yin fitsari a wurin da kake yin wanka, domin hakan yana gadar da yawan mantuwa.

(2). Karka rika kwantawa barci bayan ka cika cikinka da abinci, domin yin hakan yana gadar da mutuwar zuciya. (3). karka rika yawaita kallan al'auranka ko ta wasu, domin yin hakan yana sa dakikanci da nauyin kwakwalwa wajen fahimtar abubuwa. (4.).


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

SANIN MUHIMMANCIN LOKACI
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
SANIN MUHIMMANCIN LOKACI

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM Ba wani mutum a duniya da ya kamata ya san muhimmancin lokaci kamar musulmi.

Idan musulmi ya wayi gari abu na farko da zai yi shi ne sallar asuba, can bayan rana ta gota ya yi azahar.. haka har wuninsa ya kare yana bibiyar lokuta don ya gana da ubangijinsa. A sati kuma akwai sallar jumu'ah.. a shekara akwai watan azumi, akwai idi, akwai layya, akwai aikin hajji. Idan musulmi yana da jari kuma akwai fitar da zakkah duk shekara. Allah ya rantse mana da lokaci don mu san muhimmancinsa. Lokaci ga dan adam shi ne jarinsa, kai ma dai shi ne rayuwarsa. A cikinsa ne kake murna ko ka samu damuwa. A cikinsa ne kake ciwo ko ka samu lafiya. A cikinsa ne kake talauci ko ka samu arzikin duniya. A cikinsa ne kake shuka alheri ka girbe shi lahira ko ka shuka sharri ka same shi can yana jiran ka gome alkiyama. Don haka a cikin lokacin duniya ne ake samun aljanna ko a fada cikin jahannama. Allah ya kiyaye mu. Lokaci ya fi komi saurin wucewa. Ba ya jira, kuma in ya tafi ba ya dawowa. Sannan kuma Allah bai sanar da kowa lokacin da ya diba ma sa ba.

Lokacin da Allah ya ba ka shine tsawon shekarun rayuwarka. Idan ka kwantar da hankalinka sai ka ga dan lokaci ne da ba ya da yawa. Wanda aka ba shi shekaru sittin misali nawa ne za a cire daga ciki na kuruciyarsa? Nawa ne yake kararwa a barci?


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

Sakon Sarkin Saudiyya Ga Shugaban Nigeria Buhari: Mukurkushe 'yan Shia da A
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Sakon Sarkin Saudiyya Ga Shugaban Nigeria Buhari: Mukurkushe 'yan Shia da Akai a Zaria, Yaki ne da ta'addanci

Jibwis Nigeria ta leka kasar saudiyya, Inda na ruwaito wannan labari, kamar yadda Kuka sani Wannan shine karo na farko da Sarki salman yayi jawabi tun bayan murkurkushe 'yan shi'a a kwanakinnan. A tattaunawarsa da shugaba Buhari ta hanyar wayar salula, sarki Salman ya ambaci cewa kashe daruruwan yan Shia a birnin zaria shima yaki ne da ta'addanci , kamar yadda hukumar yada labarai ta kasar Iran ta shaida.

Kafar watsa labarai ta Ahlul Bayt ta ruwaito cewa shugaban Nigeria Muhammadu Buhari yayi tattaunawa ta wayar tangaraho ta takwaransa na Saudi Arabia, Salman bin Abdul Aziz Al Saud.

A yayin tattaunawar, dukkan shugabannin guda biyu sun mayar da hankali ne kan muhimman alamura da suka shafi alaka tsakanin kasa-da-kasa, gami da harkokin da ke faruwa a fadin kasashen guda biyu.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

KUNDIN TARIHIN KWAMANDOJIN SALAFIYYAH KASHI NA 'DAYA (PART 1)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
SHEIKH ISA ALI PANTAMI

DAGA BAKIN SHAYKH DR HUSAIN BN ABDUL'AZIZ ALUSH- SHAYKH (HAFIZAHULLAAH)

KUNDIN TARIHIN KWAMANDOJIN SALAFIYYAH KASHI NA 'DAYA (PART 1)

DAGA MIMBARIN SALAFIYYAH NETWORK NIGERIA KUNDIN TARIHIN KWAMANDOJIN SALAFIYYAH KASHI NA 'DAYA (PART 1)
Wannan Shine Ash- Sheikh Abu Abdullahi, Muhammad 'dan Saalih 'dan Muhammadu 'dann Uthaymeen at-Tamimi.

Al-Uthaymeen kamar yadda aka sani mutumin 'kasar Saudiyyah ne wanda ya fito daga cikin 'kabilar Banu Tamim.

An haife shi ne a ranar ashirin ga watan Ramadan hijiriyya ta dubu 'daya da 'dari uku da arba'in da bakwai (1347) a garin Unayzah.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

Zararren Takobin Sunnah Akan 'Yan Shiah!!!
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Sheikh (Dr.) Mansur Sokoto

Zararren Takobin Sunnah Akan 'Yan Shiah!!!

Idan akwai wani Malamin Sunnah wanda kai tsaye zaka ce 'yan Shiah suna kwana da tararrabin bankado irin abinda miyagun litattafansu suka kunsa dan ankarar da al'ummar Musulmi illa da mugunya da ke tattare da wannan ADDINI na Shiah to kai tsaye zaka iya cewa shi ne Dr.

Mansur Sokoto.

Hakika, Malam Mansur Sokoto ya yiwa Addinin Allah hidima wajen bankado irin miyagun aqidun 'yan Shiah dan Ilmantar da al'umma da nuna musu irin mugun hadarin da yake tattare da 'yan Shiah da kuma shi'anci, Malam ya kutsa cikin tafka- tafkan litattafan 'yan Shiah da suke dauke da guba mai karya garkuwa da lalata tsiga da lakar jikin Imani na hakika, Imani na kadaita ALLAH da Bauta da cikakken Tauhidi.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

AZUMIN ASHURA A LITTAFAN SHI'A
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Shaykh Dr. Mansur Sakkwato

AZUMIN ASHURA A LITTAFAN SHI'A

Bismillahir Rahmanir Rahim.

Jiya na bibiyi muhawarori masu dinbin yawa da aka tafka a shafuka daban daban tare da 'yan Shi'a masu musun azumin wannan rana. Kuma suna da'awar cewa, Ahlussunna ne suka kirkiro shi don su rufe makokin da su 'yan Shi'a suke yi a wannan rana. Don haka nake so in tabbatar masu da cewa, wannan azumi ya tabbata har a cikin littafansu ba tare da wani kokwanto ba.

Bismillah:

1. Daga Abu Abdillah (Ja'afar As- Sadiq A.S) daga babansa (Muhammad bn Ali bn Husain) daga Ali (AS) ya ce: ''Ku yi azumin Ashura shi ne tara da kuma goma ga wata, domin hakika yana kankare zunuban shekara. Duba: Al- Istibsar 2/134.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

ISBALIN TUFAFI YANGA CE A MAHANGAR MUSULUNCI
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Daga Dr. Ibrahim Jalo

ISBALIN TUFAFI YANGA CE A MAHANGAR MUSULUNCI

Tabbas yin aiki da ingantattun hadithan Annabi mai tsira da amincin Allah cikin Aqidah, da Ibadah, da Mu'amalah shi ne alheri ga mutane duniyarsu da lahirarsu.

Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce Isbalin tufafi yanga ce. Imamu Abu Dawuda ya ruwaito hadithi na 4086 da isnadi sahihi daga Sahabi Jabir Bin Sulaim Allah Ya kara masa yarda cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce:-
(( ﻭﺍﺭﻓﻊ ﺍﺯﺍﺭﻙ ﺍﻟﻰ ﻧﺼﻒ ﺍﻟﺴﺎﻕ ﻓﺎﻥ ﺍﺑﻴﺖ ﻓﺎﻟﻰ ﺍﻟﻜﻌﺒﻴﻦ ﻭﺍﻳﺎﻙ ﻭﺍﺳﺒﺎﻝ ﺍﻻﺯﺍﺭ ﻓﺎﻧﻬﺎ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺨﻴﻠﺔ ﻭﺍﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻻ ﻳﺤﺐ ﺍﻟﻤﺨﻴﻠﺔ)).

Ma'ana: ((Ka dage zaninka zuwa tsakiyar kwabrinka, in ka ki to zuwa idon sawunka, ka nisanci isbalin tufa lalle shi daga yanga yake, kuma lalle Allah ba ya son yanga)). Babu Musulmin kirki da zai san wannan hadithi ingantacce sannan ya ci gaba da kiran mutane cewa su rika yin isbali matukar dai isbalin da suke yi ba saboda yanga ba ce suke yin sa! Saboda Annabi mai tsira da amincin Allah ya riga ya gama magana cewa zatin isbalin kansa yanga ce.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

Ko Kafiran Zamanin Jahiliyya Ba Su Dauki Karya Hanyar Rayuwa Ba
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Sheikh Muhammad Ibn Salihu Al-Usaimin

Ko Kafiran Zamanin Jahiliyya Ba Su Dauki Karya Hanyar Rayuwa Ba

Babi na Hudu:

Musulmi ba ya zaluntar Musulmi kuma kada ya mika Musulmi ga azzalumi:

162. An karbo daga Yahya dan Bukair ya ce: ''Laisu ya ba mu labari daga Ukail daga dan Shihab cewa: ''Lallai Salim ya ba shi labari cewa, lallai Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su) ya ba shi labari cewa: ''Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce, ''Musulmi dan uwan Musulmi ne ba ya zaluntarsa kuma ba ya mika shi zuwa ga azzalumi. Wanda ya kasance a cikin kula da bukatar dan uwansa, Allah Zai kasance cikin kula da bukatarsa. Wanda ya kwaranye (shafe) wa wani Musulmi bakin cikin (duniya) Allah Zai shafe masa wani bakin ciki daga bakin cikin Ranar kiyama. Wanda ya boye asirin wani Musulmi Allah zai boye masa asirinsa Ranar kiyama.''

Babi na Biyar:

Bisa fadar (Annabi SAW) cewa: ''Ka taimaki dan uwanka azzalumi ko wanda aka zalunta:

163. An karbo daga Usman dan Abu Shaiba ya ce: ''Hushaim ya ba mu labari ya ce, Ubaidullahi dan Abubakar dan Anas da Humaid ya ji Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi) yana cewa: ''Annabi (SAW) ya ce: ''Ka taimaki dan uwanka azzalumi ko wanda aka zalunta.''


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

Adalci Kinshikin Zaman Lafiya
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Daga Hudubar Ustaz Muhammad Sulaiman Abu Sulaiman, Masallacin Al-Bayan Jos

Adalci Kinshikin Zaman Lafiya

Godiya ta tabbata ga Allah Mai kowa Mai komai, wanda Ya sanya adalci ginshikin tsayuwar sama da kasa. Mun shaida babu wanda za a bauta masa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad bawan Allah ne kuma Manzon Allah ne.

Salati da sallamewa da tsira su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW) da alayensa da sahabbansa da matansa da duk wanda ya yi imani da shi ya yi aikin kwarai har tashin kiyama.

Bayan haka, ya ku bayin Allah! Allah Ya umarce mu da yin adalci a bayan kasa, kuma da adalci sama da kasa suka tsayu. Allah na taimakon daular da ta tsayar da adalci koda kafira ce, a yayin da Yake durkusar da daular da take zalunci koda Musulmi ke shugabancinta.

Hudubarmu ta yau tana bayani ne kan abubuwa uku: Kan adalcin da Musulmi suka rasa a duniya da tsaron kasa da aminci ga 'yan kasa da kuma wadanda masifa ta shafa.

Game da adalcin da Musulmi suka rasa a duniya, Allah Madaukaki Ya umarci Musulmi su yi adalci a kowane hali, inda Ya ce: ''Ya ku wadanda suka yi imani! Ku kasance masu tsayin daka domin Allah, masu shaida da adalci. Kuma kada kiyayya da wadansu mutane ta dauke ku a kan ba za ku yi adalci ba. Ku yi adalci shi ne mafi kusa da takawa.''


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

WAYE YAKE DA MATSALAR DA TA ADDABESHI? GA MAFITA!
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Daga Nibras Muhammad

WAYE YAKE DA MATSALAR DA TA ADDABESHI? GA MAFITA!

Wani Mutum Yazo wurin hasan albasri yace masa: Ba'a ruwan sama ma'ana fari ya damesu, sai hassan yace masa kuyawaita istigfari, Sai wani ya sake zuwa yace masa talauci ta dameni, sai hassan yace masa Kayawaita istigfari, Sai wani ya sake zuwa yace masa matata bata haihuwa, sai hassan yace masa Ka yawaita istigfari, Sai mazauna awurin sukace ma hassan albasri, kai kenan duk wani wanda ya kawo maka koke sai kace masa yayita istigfari? Sai hassan Albasri yace Shin baku karanta fadin Allah bane da yake cewa:
ﻓﻘﻠﺖ ﺍﺳﺘﻐﻔﺮﻭﺍ ﺭﺑﻜﻢ ﺇﻧﻪ ﻛﺎﻥ ﻏﻔﺎﺭﺍ.

''Sai na ce, ´Ku nħmi gãfara daga Ubangijinku, lalle ne shi Ya kasance Mai gãfara ne.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

DA WAYE YA DACE KAYI ABOKANTA? KUMA A WANI MAJALISA YA DACE KA ZAUNA?
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Daga Nibras Muhammad

DA WAYE YA DACE KAYI ABOKANTA? KUMA A WANI MAJALISA YA DACE KA ZAUNA?

Da yawa daga cikinmu sun haddace suratul kahfi, toh amma da yawa basu tsayawa suyi tunani kan karen Da Allah ya ambaceshi cikin wannan surah, da kuma meye dalilin da yasa ya sami wannan matsayi mai girma haka? 

Amsa itace ya sameta ne sabida kasancewarsa tare da mutanen kirki, aduk lokacin daka lazumci mutanen kirki, toh alherin da suke tattare dashi sai ya shafeka, haka kuma aduk lokacin da ka lazumci mutanen banza, to laifinsu da halakansu sai ta shafeka. 

Haka majalisa. Kada ka yadda ka lazumci majalisar barna, domin A karshe kaima sai ka zama daga cikinsu… Allah(subhanahu wata'ala) yace:


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

TAKAITACCEN TSOKACI A KAN JAWABIN SHEIK DAHIRU BAUCHI
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Daga Dr. Ibrahim Jalo Jalingo

TAKAITACCEN TSOKACI A KAN JAWABIN SHEIK DAHIRU BAUCHI

Jawabin da Malam Dahiru Bauchi ya yi a shirin safe na BBC hausa a yau 21/5/2015, hakika ya fadi daidai cikin wani sashi nasa, ya kuma kasa fadin daidai cikin wani sashi nasa.Ya fadi daidai a inda ya kafirta ‘yan Tijjaniyyar nan da suka yi bukin maulidin Sheik Ibrahim Inyas a garin Kano, sannan a wajen wannan buki nasa wasunsu suka yi ta furta kalaman batunci ga Annabi Mai tsira da amincin Allah.

Amma bai fadi daidai ba a inda ya ce babu abin da ake kira Ahlul Hakikati cikin Darikar Tijjaniyyah, ya kuma fadi hakan ne duk kuwa da cewa a cikin Darikar tijjaniyyah a kwai yarda da abin da ake kira Wahdatul Wujudi, shi kuwa Wahdatul Wujudi tabbas yana daga cikin lazimin wannan akida yarda da irin maganar cewa Ibrahim Inyas Allah ne.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

Gargadi Ga Azzalumi Da Tausar Wanda Ake Zalunta (4)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Abdulmuhsin bin Muhammad Alkasim Masallacin Annabi, Madina

Gargadi Ga Azzalumi Da Tausar Wanda Ake Zalunta (4)

Hakuri mabudi ne na fita daga kunci, kuma ana karfafa shi a lokacin aukuwar fitina da masifu. Kuma addu'a ce makami mafi karfi ta yakar abokan gaba ko adawa. Mai tsira da amincin Allah ya ce: ''Ka ji tsoron addu'ar wanda aka zalunta, domin lallai ita babu hijabi a tsakaninta da Allah.'' Muttafakun. Ibnu Akil (RH) ya ce: ''Ana amsa wa wanda aka zalunta cikin sauri.''

Kuma fa'alun Annabinmu (SAW) hakika shi ne an yake shi, an sanya masa takunkumi, an yi masa rauni, an cutar da shi, an yi masa makirci, an fitar da shi daga garinsa, an yi masa kaidi, an yi masa sammu, an yi masa sihiri. 'Ya'yansa shida sun rasu, amma ya kasance a cikin dukkan wadannan abubuwa yana cewa: ''Fa'alu yana ba ni mamaki.'' Sai aka tambaye shi kansa, sai ya ce: ''Kalma dayyiba.'' Muttafakun.


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

Gargadi Ga Azzalumi Da Tausar Wanda Ake Zalunta (3)
(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )

 
 
Daga Hudubar Abdulmuhsin bin Muhammad Alkasim - Masallacin Annabi, Madina

Gargadi Ga Azzalumi Da Tausar Wanda Ake Zalunta (3

Hakuri mabudi ne na fita daga kunci, kuma ana karfafa shi a lokacin aukuwar fitina da masifu. Kuma addu'a ce makami mafi karfi ta yakar abokan gaba ko adawa. Mai tsira da amincin Allah ya ce: ''Ka ji tsoron addu'ar wanda aka zalunta, domin lallai ita babu hijabi a tsakaninta da Allah.'' Muttafakun. Ibnu Akil (RH) ya ce: ''Ana amsa wa wanda aka zalunta cikin sauri.''

Kuma fa'alun Annabinmu (SAW) hakika shi ne an yake shi, an sanya masa takunkumi, an yi masa rauni, an cutar da shi, an yi masa makirci, an fitar da shi daga garinsa, an yi masa kaidi, an yi masa sammu, an yi masa sihiri. 'Ya'yansa shida sun rasu, amma ya kasance a cikin dukkan wadannan abubuwa yana cewa: ''Fa'alu yana ba ni mamaki.'' Sai aka tambaye shi kansa, sai ya ce: ''Kalma dayyiba.'' Muttafakun.

Musulmi mai yakini ne da samun taimakon Allah, kuma haramun ne a kansa ya karkata ga azzalumai. Allah Madaukaki Ya ce: ''Kada ku karkata zuwa ga wadanda suka yi zalunci har wuta ta shafe ku.'' (k:11:113). Kuma Allah bisa kudirarSa Yakan taimaki mai rauni koda tsanani ya yi masa daurin goro ko an wulakantar da shi. Allah Madaukaki Ya ce: ''Kuma Allah ne Marinjayi a kan al'amarinSa, kuma amma mafi yawan mutane ba su sani ba.'' (k:12:21).


(Don Karanta Cikakken... | More | Kuna So Ku Yi Sharhi? | Esin )
 
 


 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: