Topic: Ladubban Shiga Gida Da Ziyara A Musulunci (2)
Timeline: 2012-06-19 02:24:13
Ladubban Shiga Gida Da Ziyara A Musulunci (2)
A Rubuce Da Salihu Is’hak Makera
A makon jiya ne muka fara gabatar da wannan darasi kan ladubban shiga gida da ziyara a Musulunci, to yau za mu ci gaba kamar haka: Ya kamata a fahimci cewa a duk lokacin da ka ce Assalamu alaikum ma’ana Amincin Allah ya tabbata ga mutanen gidan nan kafin ka nemi izinin shiga gidan, za ka sanya soyayya ta shiga zuciyar mazauna gidan. Kuma da yin sallamar kana ba su tabbacin cewa sun kubuta daga cutarwar harshenka da hannuwanka da kowace cutarwa.
Ke nan da wannan tabbaci bai kamata ka kutsa kai kafin su masu gidan su yi maka izini ba. Kuma ba za su yi maka izinin shiga gidan ba, har sai ka nuna kana son shiga gidan na su ne. Don haka laifi ne daga cewa Assalamu alaikum ka fada cikin gidan mutane don gadarar na ’yan uwanka ne ko iyayenka ko abokanka, saboda kana iya iske su a halin da ba za su so ka gansu ba.
Sallamarka tana iya ba su damar su fara kintsawa, amma neman izinin yana ba su damar su gama kintsawa su amince ka shigo ko su ce ka dakata. Kai in sun fahimci shigowar taka za ta takura musu suna iya cewa ka koma. Kuma kamar yadda ayar da ta gabata ta ce, sai ka koma don hakan ne mafi alheri gare ka. Wannan ya nuna kaiwa matuka wajen kare hakkin dan Adam a addinin Musulunci da ba shi damar shakatawa a gidansa ba tare da an matsa masa ba. Idan kuma aka samu akasi wani ya kutsa gidan mutane ba tare da izininsu ba, to daidai yake da ya yi musu tajassusi wato leken asiri, kuma Allah Madaukaki Ya hana tajassusi a cikin suratu Hujrati aya ta 12.
Imam Khurdabi (Allah Ya yi masa rahama) ya ruwaito cewa: “Annabi (SAW) ya ce: “Kada ku yi giba, kada ku bibiyi al’aurar (sirrin) mutane, domin duk wanda ya bibiyi al’aura ko sirrin Musulmi, Allah zai tona nasa asirin. Kuma idan Allah Ya bibiyi al’aura ko sirrin mutum, wannan mutum zai kunyata koda a cikin gidansa ne kuwa.”
Don haka wajibi ne ga Musulmi ya rika kokarin ganin bai keta sirri ya kai ga al’aurar mutane ba, kuma hakan zai samu ne ta kiyaye wannan ka’ida ta yin sallama da neman izinin shiga gida. Haka Manzon Allah (SAW) da sahabbansa suka yi a rayuwarsu, wanda hakan ne ya samar da kyakkyawar al’umma a bayan kasa.
Imam Malik ya ruwaito a cikin Muwaddansa daga Adda’u bin Yassar cewa: “Wani mutum ya zo wurin Annabi (SAW) ya tambaye shi cewa: “Shin yanzu sai na nemi izini idan zan shiga gidan mahaifiyata?” Annabi (SAW) ya ce: “Eh.” Sai mutumin ya ce: “Ya Manzon Allah! Ina fa zaune ne tare da mahaifiyar tawa a wannan gida.” Sai ya sake ce masa kada dai ya shiga wannan gida ba tare da neman izini ba. Sai mutumin ya sake cewa: “Ya Manzon Allah! Kusan koyaushe ina fa tare da mahaifiyata ce ina yi mata hidima.” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wajibi ne ka nemi izininta kafin ka shiga gidan. Ko kana son ka ga mahaifiyarka tsirara ne?” Sai ya ce: “A’a.” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wannan ne ya sa neman izinin ya zama tilas don a kauce wa abin kunya irin wannan.”
Don haka shiga gida ba tare da neman izini ba, koda gidan iyaye ne yana iya sanya mutum ya ga abin da bai kamata ya gani ba, kuma hakan yana iya jefa mai kai ziyarar da shi kansa wanda ya kai ziyarar a cikin wani hali marar dadi.
Ke nan koda gidan haya da mutum biyu zuwa sama ke zaune ne, wajibi ne idan daya zai shiga gidan ya yi sallama ko ya buga kofa ko ya kada kararrawa, in an leko an ce ya shiga, sai ya shiga? Ba daidai ba ne don kawai mutum yana takama akwai matarsa a gidan ya kutsa kai ba tare da sallama da neman izini ba, domin yana iya iske matar abokin hayarsa a yanayin da bai dace ba, kamar yadda ba zai so a iske matarsa a cikin irin wannan hali ba.
Kuma duk da cewa Ibnu Kasir ya ce ba wajibi ba ne ga mutum ya nemi izinin shiga gidan da matarsa ce kadai a ciki ba, amma yana da kyau Musulmi ya yi hakan. Misali matar Abdullahi bin Mas’ud (RA) ta ce: “Mijina yakan buga min kofa kafin ya shigo ta yadda ba zai gan ni a halin da ba zai so ba.”
Sannan a lokacin da ka yi sallama kuma ka nemi izinin shiga gida, amma mazauna gida suka ce wane ne? Sai ka ce “ni ne wane,” ka fadi sunanka ba ka ce “ni ne” kawai ko ka yi shiru ba.
Sannan idan ka yi sallama ka ji shiru sai ka kwankwasa kofa ko ka ja kararrawa kamar sau uku, saboda kila suna can cikin gida muryarka ba za ta iya isa gare su ba, nan ma idan ka ji shiru kada ka shiga gidan, sai ka jira a ba ka izini, ko ka koma.
Kuma idan ka kai ziyara gidan wani, kada ka tsaya daidai kofar gidan ko daki, ka kuma gefen hagu ko dama kadan, don kada ana bude kofa ka hango cikin gida ko dakin. Haka Manzon Allah (SAW) yake yi kamar yadda Sahlu bin Sa’ad ya fada a Hadisin da Buhari da Muslim suka ruwaito.
Amma da mutum zai aika a kira wani ba tilas ne wanda aka kira ya nemi izinin shiga gidan ba, suna zuwa tare da dan aika za su shige wurin mai kiran.
Amma idan wani bala’i kamar gobara ko fadawa a rijiya ta auku a wani gida, a nan ba a tsayawa ga neman izinin shiga, sai kawai mutum ya gaggauta shiga ya kai dauki.
Addinin Musulunci addini ne da ya ba kowa hakkinsa mai ziyara da wanda ake ziyarta. Don haka su ma masu kai ziyara suna da hakki kamar yadda shugabanmu Annabi Muhammad (SAW) ya ce: “Lallai masu ziyartarka suna da hakki a kanka.”
Don haka wajibi ne a kan masu gidan da aka kai musu ziyara su kuma su fito su gaisa da shi. kada su kore shi ku su juya masa baya ba tare da wani dalili mai karfi ba.
**{Legacy activities, comments etc counter: 2028; topic series: 4; forum: MediaHausa; legacy score: 5; legacy ratings: 1; rating_ip: ***.*14.6.229; associated: 4- /*}