Minista Matawalle ne ya sanya hannu a madadin Najeriya, yayin da Dakta Khaleed H. Al-Biyari ya sanya hannu a madadin Gwamnatin Masarautar Saudiyya.
Gwamnatin Tarayyar Najeriya da Masarautar Saudiyya sun sanya hannu kan wata sabuwar yarjejeniya domin ƙarfafa dangantakar tsaro da haɗin gwiwar soja tsakanin ƙasashen biyu.
A wata sanarwa da mataimaki na musamman ga Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle kan yaɗa labarai Ahmed Dan Wudil ya fitar, ta bayyana cewa yarjejeniyar za ta shafi muhimman fannoni kamar musayar bayanan leƙen asiri, horas da sojoji, haɗin gwiwa a harkar samar da kayan yaki da kuma gudanar da ayyukan tsaro tare.
Minista Matawalle ne ya sanya hannu a madadin Najeriya, yayin da Dakta Khaleed H. Al-Biyari ya sanya hannu a madadin Gwamnatin Masarautar Saudiyya.
Ministar ya bayyana cewa, wannan ci gaban babbar dama ce da za ta ƙara ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu da kuma taimakawa wajen fuskantar ƙalubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu.
Ya ce, ma’aikatar tsaron Najeriya tana maraba da wannan ci gaba, tare da fatan hakan zai taimaka wajen kawo ƙarshen matsalolin tsaro da ake fama da su a sassa daban-daban na ƙasar.

