Topic: Matsayin gemu a Musulunci (2)
Timeline: 2012-03-27 19:06:17
Matsayin gemu a Musulunci (2)
A Rubuce Da Ahmad Muhammad
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubangijin halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin halittu, Muhammadu dan Abdullahi, sallallahu alaihi wasallam, tare da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya bi tafarkinsu har zuwa ranar karshe.
Ga ci gaban tsokaci kan matsayin gemu:
Boko: Hikaya ce, wadda aka wallafa a cikin wadansu littafan addinin Musulunci, cewa a kasar Indiya ko Pakistan (ban rike sunan takamaiman kasar ba) wata budurwa da Allah Ya sa ta sami tarbiyyar Musulunci ta amince da auren wani matashi (shi ma yana da ilmi gwagwadon hali) wanda ya yi zurfi a ilmin boko. Yana da gemu da kuma kamala ta mutumin kirki.
Bayan da aka yi aure, irin ranar da ango zai shiga wajen amarya din nan, sai abokansa (’yan boko, abin bakin ciki), suka “yaudare” shi, wai “he should be clean-shaben” (wato ya kyautu ya kwalkwale fuskarsa ta yi fes, kafin ya shiga wajen amarya) ya aske fuska tas, bai bar komai ba. Ai kuwa da ya shiga wajen amarya, sai aka sami akasi. Ita dai ta san wanda ta aura ya tsayar da sunnar gemu, amma ga shi wani matashi (da fuskarsa kamar ta ‘Kande’) ya shigo mata, ranar da take sa ran gamuwa da mijinta. Ai kawai sai ta kwarma ihu! Ango ya rude, ya kama bayanin cewa ‘ai shi ne’, amma ina! A takaice dai, auren da aka fasa ke nan, don yarinya ta nuna, in dai har zai iya yin wannan haramci kai tsaye haka, yana iya yin fiye da haka, musamman game da hakkinta!
A cikin littafinsa Adaabuz-zufaaf (wato Ladubban Angunci), Shaikh Muhammadu Nasiruddinil Albaniy, a karkashin bayani kan ladabi na 38, wanda ya yi magana dangane da hanin saba wa shari’a, ya yi tuni kan batun aske gemu, shi ma a karkashin karamin sashe na biyar (5).
Malam ya ce: Na biyar – Aske Gemu:-
Misalin wannan al’amari na aske gemu yana daga cikin munanan al’amura –kai, in ma dai ba a ce mafi muni, a wannan sha’ani na aure, a wajen ma’abuta kyakkyawar dabi’a kubutacciya daga zargi ba. Musamman dangane da abin da aka fitini mafi yawan mazaje, kan “yin kwalliya” a wajen aske gemu, saboda dabi’ar takalidancinsu da Turawa kafirai. Har al’amari ma ya kai ga wai abin kunya ne gare su wai a ga ango ya shiga wajen amaryarsa, alhalin bai yi “gyaran fuska” ya share gemunsa da sauran gashin da ke fuskarsa tas-tas ba.
Kai, a kan haka ma wadansu suna nuni (a kan bata) cewa kyautata ko kyale ko kula ko cika gemu, yana daga cikin munasaba ta mutuwa a kan kamala ta mutum (Allah Ya ce, “lallai ba idanu ne ke makancewa ba, sai dai zukata da ke cikin kiraza”).
A cikin wadannan zantuka da kuma musamman saba wa wannan tsari na tsayar da gemu da kyautata masa da kyale shi da girmama ko tausasa ko cika shi, akwai hukunce-hukunce da shari’a ta yi manuniya da su kamar:
(a) Canja halittar Allah: Allah Ta’ala Yana cewa (a cikin hakkin shaidan), (118), “Allah Ya tsine masa (Ya la’ane shi) sai (shi shaidan) ya ce, “Lallai ne, zan riki rabo yankakke, daga bayinKa. (119) Kuma lallai ne ina batar da su, kuma lallai ne ina sanya musu guri (buri), kuma lallai ne ina umurnin su domin su katse kunnuwan dabbobin, kuma lallai ne ina umurnin su domin su canja halittar Allah.” Kuma wanda ya riki shaidan majibinci, baicin Allah, to hakika ya yi hasara, hasara bayyananniya.” Surar Nisa’.
Wannan nassi bayyane yake a fili karara cewa canja halittar Allah ba tare da wani izni daga gare Shi (Ta’ala) ba, to yin biyayya ne ga umurnin shaidan, kuma saba wa Allah ne Mai rahama, Mai girma da daukaka. Sannan babu shakka ko kokwanto a kan maganar cewa Manzon Allah, sallallahu alaihi wasallam, ya tsine wa masu canja halittar (siffarsu) da Allah Ya yi musu don yin kwalliya, wato wai su kara kyau, kamar dai yadda zance ya gabata nan baya kadan.
Saboda haka kuma babu shakka, a cikin shigar da zancen askewar gemu don kwalliya da karin kyau, cikin al’amarin canja halittar Allah da kuma tsinuwar da aka yi a kan haka. Ko da na ce, ba tare da wani izni daga gare Shi (Ta’ala) ba, don kada wani ya yi wahamin (batacciyar) fahimta cikin abin da aka bayar da izni na aske shi na daga gashin mara da abin da ya yi kama da haka, wanda shari’a ta yi izni da yinsa. A’a, hasali ma dai abin so ne da ake samun lada (mustahabbantarwa) wajen aiwatar da shi, ko kuma a ce wajabtawa a cikin wadansu al’amura.
(b) Saba wa umurnin Manzon Allah, sallallahu alaihi wasallam, a yayin da ya ce, “Ku datse gashin baki, kuma ku yalwata gemu.” Bukhari (10/289) kuma lafazinsa ne; da Muslim (1/153) da Abu Awanah (1/189) da waninsu suka ruwaito hadisin daga dan Umar, Allah Ya kara musu yarda.
Ai, abin nufi da kalmar ankahuu, shi ne ‘ku kai matuka wajen datsewa’. Akwai kuma kwatankwacinta wato kalmar jazzuu – wadda ita ma tana nufin kaiwa matuka ga datsewar abin da ya tsawaita a kan lebe na gashin baki, amma ba aske shi dukansa ba, domin yin hakan shi ma saba wa sunna ne, wadda take aiwatatta, tabbatatta daga Ma’aiki, sallallahu alaihi wasallam”, inji malam.
Da wannan dalili ne ma, a yayin da aka tambayi (Imam) Malik dangane da wanda yake yalwata (baza) gashin bakinsa (ba ya datse abin da ya bazu a kan lebe), sai ya ce, “ina ganin a hore shi da duka.” Sai kuma ya ce, dangane da wanda yake aske gashin bakinsa, “wannan wata bidi’a ce, wadda ta bayyana a tsakanin mutane.” Baihakiy (1/151), kuma a duba Fatahul Bariy (10/285-286). A dalilin haka (Imam) Malik ya kasance, ya saki (salebar) gashin (gefen) bakinsa. A yayin da aka tambaye shi game da haka sai ya ce, “Zaidu dan Aslam ya ba ni labari daga Amir dan Abdullahi dan Zubair cewa Umar (dan Khaddab), Allah Ya yarda da shi, ya kasance idan ya yi fushi, sai ya murza gashin bakinsa kuma ya hura.” dabaraaniy ya ruwaito shi a cikin littafin Almu’jamul Kabiir (1/4/1) da isnadi ingantacce. Haka nan ya ruwaito, shi dabaraaniy (1/329/2) da Abu Zar’ah a cikin Tariikhinsa (46/1) da Baihakiy, cewa “mutum biyar daga sahabbai suna sakin gashin bakinsu wato a gefen lebbansu.” Kuma isnadinsa mai kyau ne. Akwai kuma irinsa a Ibnu Asaakir (8/520/2).
**{Legacy activities, comments etc counter: 1877; topic series: 6; forum: MediaHausa; associated: 6- /*}