Topic: Son Maso Wani Koshin Yunwa!: Gidan Annabi Mohammad (SAW)
Timeline: 2012-05-13 06:05:40
Ina ma’auratan da suke zaman doya-da-manja? GA SHAWARA:
Son Maso Wani Koshin Yunwa!: Gidan Annabi Mohammad (SAW)
Ibnu Jauzi Allah ya jikan sa (Ya rasu: 597 AH) ya ce:
Wani mutum ya kawo min kukan tsanar matarsa da ya yi, ya kara da cewa: Ba zan iya sakin ta ba saboda abubuwa da dama, daga ciki dai akwai tarin bashinta da na ci, kuma gaskiya ni ba ni da hakuri, tana fahimtar irin tsangwamarta da nake yi ta hanyar furucin dake fitowa daga bakina idan ina korafi.
“Ibnul Jauzi ya ce: Sai na ce masa: wannan ba zai tsinana maka komai ba! Gidaje ta kofofinsu ake shigarsu, don haka ya kamata ka zauna ka kebe da kanka, ka yi tunani don ka san an dora ta a kanka ne saboda zunubanka, don haka ka dage wurin neman hanzari da tuba zauwa ga Allah”.
“Nunkufurci, da cutatar da ita ba zai wani amfani ba, kamar yadda Alhasan ibnul Hajjaj ya ce: “(Halin da kuka samu kanku a ciki) ukuba ce daga Allah gareku, don haka kada ku tinkari ukubarsa da takobi, ku fuskance ta da istigfari”
Ka sani cewa kai kana matsayin wanda aka jarraba ne, kuma kana da ladan hakuri (Ya kusanta ku ki wani abu amma kuma alheri ne a gareku) kamar yadda Allah ya ce.
Don haka ka mu’amalanci Allah Subhanahu da hakuri akan abin da ya kaddara maka, kuma ka nemi ya yaye maka. Idan ka hada tsakanin istigfari da tuba, da hakuri akan hukncin Allah, da neman yayewa, nau’o’i uku na ibada sun hadu, kuma a ba ka lada akan kowace daya daga ciki.
Kar ka bata lokacinka da abin da ba zai amfane ka ba, kada ka ce kuma wai za ka yi dabara don ka tsere daga abin da aka kaddara maka. Allah yana cewa “Idan Allah ya dora maka wani abin da zai cutar da kai ba mai ya ye shi sai shi” …
“Amma cutatarwar da kake yi wa matarka ba ka da wani dalili a kai, saboda dora ta aka yi a kanka, don haka ka mayar da hankali akan wani abu ba wannan ba”.
An rawaito daga wani daga cikin magabata cewa wani mutum ya zage shi, sai ya turmuza kundukukinsa a kasa ya ce: “Allah ka gafarta min zunubin da na yi maka da saboda shi ne ka ]ora wannan mutumin akaina”
“Sai mai neman Shawara ya ce: wannan matar tana mutuwar so na, kuma zagewa take haikan wurin yi min hidima, amma kin ta ya gama girkuwa a zuciyata!”
“Sai na ce masa: Ka mu’amalanci Allah ta hanyar hakuri da ita sai ka samu lada”.
“Wata rana an ce da Abi Usman Annaisabori: Wane aiki ne ka fi sa rai da shi (ranar tashin }iyama?) Sai ya ce lokacin ina matashi ’yan uwana sun sun yi, sun na yi aure na ki, (wata rana) sai wata mace ta zo gurina ta ce da ni: “Ya Aba Usman Lallai sonka ya gama zuciyata, har na kasa bacci, na rasa inda zan sa kaina, ina rokon ka don mai juya zukata, ka aure ni”!
“Sai na ce mata mahaifinki yana raye”?
Sai ta ce: ee; telan nan na guri kaza ai shi ne mahaifina
Sai na aika wa da mahaifinta wasika ina neman aurenta, sai ya yi farin ciki da wannan magana, ni kuma na kawo shedu, aka daura mana aure.
Da na tare da ita sai na ga ashe: Ido daya ne da ita! Ga ta mai kambale!! (gurguwa-gurguwa) ga ta kuma mummuna ta inna naha!!! Sai na ce: Allah na yi maka godiya bisa abin da ka kaddara min!
’Yan uwana sun ta zargina akan haka, ni kuma sai kara kyatata mata da mutunta ta nake yi, haka dai har ta kai ba ta bari na na fita saboda }aunar da take min. Na daina zuwa majalisai don fifita abin da take so (na na zauna kusa da ita), kuma don kada ta ji wani abu a zuciyarta.
Haka na ci gaba da zama da ita tsahon shekaru goma sha biyar, wani lokacin (idan ina tare da ita) kai ka ce ina kan garwashi ne, saboda kin da nake mata, amma ban taba nuna mata ba, har dai Allah ya dauki ranta, don haka ba wani aiki da na fi sa rai da shi a lahira irin wannan na kiyaye abin da yake zuciyarta na kaunata (duk da ba son ta nake yi ba)
Ibnul Jauzi ya ce: Sai na ce wa mutumin nan: haka mazaje suke, amma menene amfanin rakin wanda aka jarraba, da korafi, da nuna kiyayya kuru kuru. Hanyar dai da na gaya maka ita ya kamata ka bi; na ka tuba, ka yi hakuri, ka roki Allah ya yaye, kuma ka tuno zunuban da ka yi wa Allah har ka samu kanka a cikin wannan hali sakamakon haka.
Idan ka samu yayewa da waraka to, in kuma ba haka ba, to yin hakuri bisa abin da Allah ya kaddara ibada ne, kuma ka rika kokarin nuna mata soyayya a zahiri ko da ba soyayyarta a zuciyarka, yi kokari ka tabbata akan haka.
Shi sasari ba shi ne mai laifi ba ballantana a zarge shi, kamata ya yi ka shagala da wanda ya garkama maka sasarin. A sauka lafiya.
صيد الخاطر ص: 399
Gidan Annabi Mohammad (SAW)
Anas Ibn Malik (RA) ya ce: Wata rana Annabi (SAW) ya zo fucewa sai ya tarar da ni tare da yara, sai ya yi mana sallama, sannan sai ya kama hannuna, (ya ja ni gefe) ya aike ni da wani sa}o, ya ce kada ka gayawa kowa sirrin Annabi, ya zauna a inuwar wani garu (yana jira na), da na dawo gida sai Ummu sulaim (Babata) ta ce: Garin yaya yau ka da]e a waje (ba ka dawo ba sai yanzu) sai na ce mata: Annabi (SAW) ne ya aike ni kai wani sako. Sai ta ce: sa}on menene? Sai na ce mata: Sirri ne! sai ta ce: Kiyaye sirrin Annabi (SAW) Anas ya ce: Haka kuwa aka yi wannan sirrin bai ta~a fita daga bakina ba. 5205 المسند، 13817 وسنن أبي داود .
**{Legacy activities, comments etc counter: 32065; topic series: 8; forum: MediaHausa; legacy score: 24; legacy ratings: 5; rating_ip: ***.*67.107.153; associated: 8- /*}