Topic: Hikima Da Maslahar Da Ke Cikin Fitar Da Zakkar Fidda-kai
Timeline: 2012-08-24 02:06:36
A Rubuce Da Salihu Is’hak Makera
Hikima Da Maslahar Da Ke Cikin Fitar Da Zakkar Fidda-kai
Godiya ta tabbata ga Allah Tsira da aminici su tabbata ga Shugabanmu Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa. Bayan haka, yau za mu gabatar da wani abu ne kan Zakkar Fidda Kai ko Zakkar Kono kamar yadda wadansu ke fada.
Kalmar zakkah a lugga tana nufin tsarki da karuwa da yabo da albarka. Wadannan kalmomi duk Alkur’ani ya yi amfani da su.
Kalmar Fitr a lugga kuma tana nufin bude wani abu, kuma daga nan ne aka jinigna ta ga mai azumi saboda yana bude bakinsa don cin abinci.
A shari’a kuma Zakkatul Fitri na nufin zakkar da ake bayarwa bayan kammala azumin Ramadan.
Zakkar Fidda Kai, Sunnah ce ta Manzon Allah (SAW), Allah Ya farlanta azumi, shi kuma ya farlanta zakka bayan kammala azumin. Bin Manzon Allah (SAW) kuma bin Allah ne, saboda Allah Madaukaki Ya ce: “Abin da Manzon (Allah) ya zo muku da shi, ku rike shi, kuma abin da ya hana ku, to ku hanu.” (Hashri:7). Kuma Allah Ya sake cewa: “Wanda ya yi da’a ga Manzon (Allah), hakika ya yi da’a ga Allah.” (Nisa’i: 80).
Annabi (SAW) ya farlanta Zakkar Fidda Kai a kan daukacin Musulmi ba tare da lura da ajujuwan da suke ba, ba tare da lura da bambancin shekaru ba. Ya farlantata a kan namiji da mace da yaro da tsoho da da da bawa na Musulmi. Kuma ya farlanta ta a kan duk wanda ya mallaki sa’i a kana bin da ya saura na abincin yini da dare Idinsa. Amma wanda ba ya da shi kada ya ce zai ci bashi don ya yi, domin Allah Ba ya kallafa wa rai sai abin da za ta iya.
Abdullahi dan Umar (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya farlanta Zakar Fidda Kai sa’i daya na dabino ko sa’i daya na alkama (da sauran nau’o’in abinci) a kan da da bawa da namiji da mace da babba da yaro na al’ummar Musulmi.” Buhari ya ruwaito shi a Kitabuz Zakkah Babin Farlancin Sadakatul Fitri, Hadisi na 1503. Muslim ma ya ruwaito makamancin haka, a Kitabuz Zakkah, Babin Zakkatul Fitri ala Musulimina min sha’irin wa tamrin. Hadisi na 984.
Maigida zai fitar wa kansa da wadanda ciyar da su suka lizimnce shin a daga mata da ’ya’ya da masu yim masa hidima. Wannan wajibi ne a kansa, domin wani Hadisi da Imam Shafi’i ya ruwaito a Al-Ummu, littafin Zakkah Babin Fitr mujalladi na 4 shafi na 228 ya ce: “Ku fitar da Zakkah ga wanda kuke lamunce musu. (ma’ana wadanda suke karkashin kularku).” Darul kudni ya ruwaito shi a Sunan, Baihaki kuma a Al-Kubra. Sai dai Darul kudni ya ce: rafa’anta shi da Alkasim ya yi, ba mai karfi ba ne, abin da yake daidai, shi ne Maukufi ne. Baihaki kuma ya ce, Isnadinsa ba ya da karfi, yayin da a cikin Al-Talkhisul Habir, mujalladi na 2 shafi na 184 Alhafiz ya ce: “A cikinsa akwai rauni da irsali.” Sannan As-San’ani ya raunana shi a cikin As-Subl, mujalladi na 2 shafi 138.
Wannan zakkah tana da hikima da maslaha, daga ciki akwai yin godiya ga Allah bisa ni’imar da Ya yi ga mutum na kammala azumi da tsayuwar dare da godiya cewa Ya raya ka zuwa wannan shekara a cikin koshin lafiya da aminci. Sannan kuma tana tsarkakake wasu abubuwa da mai azumi ka iya aikatawa na yasassar magana da rafasu. Sannan kuma ciyar da miskinai ne don su wadata daga roko ko bara a ranar Idi, sai ya zamo ranar Ranar Idi ce ga kowa da kowa.
Ibnu Abbas (RA) ya ce: “ Manzon Allah (SAW) ya farlanta Zakkar Fidda Kai domin tsarkakewa ne ga mai azumi daga yasassar magana da rafasu, kuma ciyarwa ce ga miskinai. Wanda ya bayar da ita kafin Sallar Idi, to ita zakkah ce abar karba, wanda ya bayar da ita bayan sallar, to ita sadaka ce daga cikin sadakoki.” Abu Dawuda ya ruwaito a Babin Zakkatul Fitr, Hadisi na 1609. Ibnu Majah ma ya ruwaito shi a Babin Sadakatul Fitr, Hadisi na 1927. Kuma Hakim ya inganta shi, sannan Albani ya hassana shi a cikin Sahihu Abu Dawuda Hadisi na 1420.
Kamar yadda muka fada a baya ana fitar da Zakkar Fidda Kai ne daga irin abincin da mutane suke ci kamar alkama da shinkafa da masara da dawa da gero da maiwa da dabino. Kuma bai halatta a musanya su da kudi ko wata kima ba, domin hakan ya saba wa abin da Annabi (SAW) ya farlanta, kuma ya saba wa ayyukan halifofi shiryayyu da sahabban Annabi Muhammad (SAW) databi’ai da wadanda suka biyi su da kyautatawa.
Zakkar Fidda Kai tana da lokacin fitar da ita guda biyu: lokacin falalanci da lokacin halacci. Abin da aka fi so, a fitar da ita a Ranar Idi kafin yin Sallah ga wanda ya samu iko. Abdullahi dan Umar (RA) ya ce: “Annabi (SAW) ya yi umarni a bada Zakkar Fitr gabanin Sallar Idi.” Buhari da Musulim suka ruwaito shi. Kuma Abu Sa’id ya ce: “Mun kasance muna fitar da ita a Ranar Idi a zamanin Annabi (SAW). Buhari ya ruwaito shi a Babin Sadaka Gabanin Idi. Hadisi na 1510.
Ya halatta a fitar da ita gabanin Idi da yini biyu ko yini daya, wato ranar 28 ko 29 ga watan azumi. Kuma a zabi nau’in abinci mai kyau ba sayo ruba-ruba ba saboda Allah Madaukaki Ya ce: “Kada ku cudanya mummuna daga cikinsa ku rika ciyarwa, alhali ku ba za ku so ku karbi irinsa ba...” (Bakara: 267).
Kuma ana son a kebe fakirai mabukata da ita, a kai musu kafin Sallar Idi. Bai halatta a yi wasa ko sako-sako da ita ba.
**{Legacy activities, comments etc counter: 516; topic series: 7; forum: MediaHausa; associated: 7- /*}