Aliyu (r.a) Yayi Mubaya'a Ga Khalifancin AbuBakar (r.a)!
An buga: Litini Feb 09, 2026 2:26 am
*Legacy Post Number 100 from MediaHausa
Topic: Aliyu (r.a) Yayi Mubaya'a Ga Khalifancin AbuBakar (r.a)!
Timeline: 2012-10-14 21:44:01
Aliyu (r.a) Yayi Mubaya'a Ga Khalifancin AbuBakar (r.a)!
Daga Yasir Ramadan Gwale
Ko shakka babu akan cewa, Sayyiduna Ali [R.A] yayi mubaya’a ga Abubakar, sai dai an sami sabanin ruwayoyi akan lokacin da ya yi mubaya’ar. Ga dai karin bayani akan yadda ta kasance.
A lokacin mubaya’ar farko da ta biyu, Aliyu da Zubairu basu sami damar halarta ba, kasancewar suna gidan Fatima (R.A) basu san irin wainar da ake toyawa ba. kuma a lokacin...
da cikakken labari ya zo musu, sai suka ga cewa ai bai dace ba – ko kadan – ayi wannan al’amari ba tare da basu damar tofa albarkacin bakinsu ta hanyar sanar dasu ba. Abin lura anan shine, su basu da masaniya akan irin hadarin da aka kusa fadawa, da an amince da cewa kowa ya samar da nashi shugaba.
Duk dai yadda akayi, Abubakar (R.A) ya kira su ya yi musu gargadi, ya kuma gaya musu cewa: “Ni Wallahi ban taba kwadayin Shugabanci ba ko a wani dare ko a rana. Ban kuma taba rokon Allah shi ba a bayyane ko a boye”.
Aliyu da Zubairu suka bayyana cewa, su ba don komai suka yi hushi ba, sai don anyi ba da shawararsu ba, amma duk da haka sun sakankance cewa Abubakar, shine yafi kowa dacewa da cancanta a wannan lokaci. Daga nan sai sukayi masa mubaya’a.
Mafi yawan Sahabbai ba su san da cewa Ali yayi mubaya’a ba, domin yawan shagaltuwarsa da jinyar matarsa fadima, abinda yayi sanadiyyar rashin ganinsa a wurin khalifa Abubakar yana kusantarsa tare da bashi shawara. Da Ali ya fahimci hakan tasa wasu mutane sun fara yi masa fuskar shanu, sai ya nemi Abubakar ta fuskar musalaha da ya zauna a kan mimbari bayan kare sallar la’asar, a inda ya kara zuwa ya sabunta mubaya’arsa a bainar jama’a, wannan kuwa ya faru ne bayan rasuwar mai dakinsa watau Fadima (R.A).
A takaice, wannan dai shi ne abinda ya faru game da mubaya’ar da akayi wa Abubakar, ba a kuma sami mutum daya wanda ya yi masa jayayya ba. Amma an ruwaito cewa, Ibnu Ubaida wanda Ansar suka kusa ajiye Magana akan nada shi bai yi mubaya’a ba. Sai dai wata ruwaya tazo da cewa, khalifa Abubakar ya tunatar da shi cewa, Manzon Allah yace: “ shugabanni daga cikin kuraishawa suke” sai yace: “kayi gaskiya” kayi gaskiya” ya kuma yi masa mubaya’a. Duk da haka wasu marubuta tarihi na ganin cewa bai yi mubaya’a ba. Abubakar kuma yasa masa na shafin kwalli.
Da wannan kwarya-kwaryan bayani, muna iya fahimtar maganar Umar (R.A) da yake cewa: “mubaya’ar da aka yiwa Abubakar girshi ce” Muna kuma iya fahimtar cewa, Ali (R.A) shi kansa yayi mubaya’a ga Abubakar. Da kuwa ya san cewa Manzon Allah ya yi masa wasiyya da khilafa (kamar yadda shi’awa ke cewa) da ba ya halatta ga reshi ya yi mubaya’a ga wani.
TUSHEN BAYANI
1. “Tarikh Al-Islam” (2/6)
2. Duba “ Tarikhul Islam” (2/8)
3. Wannan Magana ta fito ne daga bakin sayyidina Ali. Duba “Tarikhul Islam” (2/12)
Da kuma “ Al Dabakat Al kubra” na Ibnu Sa’ad (3/183)
4 “ Sahih Al Bukhari”,kitabu fada’il Al sahaba Babi na biyar.
5 Wannan ita ce ruwayar Hakim a cikin “ Al mustadrak” (3/76), A ruwayar Bukhari wannan maganar tazo cikin hudubar Abubakar din ne shi kansa. Duba kitabu Fada’il Al sahaba babi na biyar.
6 Duba “Albidayah wal nihayah” (6/301), Amma a wata ruwayar an nuna cewa Zaid Dan Sabit ne ya fara yin mubaya’a kafin Umar.
7 Duba “ Al mustadrak” (3/67).
8 Mubaya’ar Ali ta farko ta zo a cikin “Al bidayah wan nihayah” (6/301) kuma Ibnu khuzaima ya ruwaito ta da isnadi ingantacce.
9 Duba “ Fathul Bari” (7/39). Ibnu Hajar kuma ya bayyana cewa: ya tattara hanyoyin hadisin “ shugabanni daga cikin kuraishawa suke” sai ya same su ta hanyar sama da Sahabi arba’in (40). Ya ce ya yi hakan ne domin yaji wani ya na cewa: Abubakar ne kawai ya ruwaito wannan hadisin “Fathul Bari” (7/39).
DAGA LITTAFIN: HUJJOJIN SHI’A A MA`AUNIN SHARI`AH
NA MUHAMMAD MANSUR IBRAHIM
Daga Yasir Ramadan Gwale.
**{Legacy activities, comments etc counter: 15786; topic series: 3; forum: MediaHausa; legacy score: 8; legacy ratings: 2; rating_ip: ***.*14.31.188; associated: 3- /*}