Fatawoyin Aikin Hajji da Umara da Ziyara (9)
An buga: Litini Feb 09, 2026 2:32 am
*Legacy Post Number 99 from MediaHausa
Topic: Fatawoyin Aikin Hajji da Umara da Ziyara (9)
Timeline: 2012-10-14 21:36:14
Fatawoyin Aikin Hajji da Umara da Ziyara (9)
Daga Sheikh Abdulwahhab Abdullah
Godiya ta tabbata ga Allah Wanda bisa ni’imarSa muka kammala azumin Ramadan a farkon wannan mako. Allah Ya sa dominSa muka yi ibadojinmu ta yadda zai karbe su. Bayan haka, yau cikin ikon Allah za mu koma ga darasinmu na fatawoyi kan aikin Hajji da Umara da Ziyarar Annabi (SAW) da muka faro watannin baya, kafin mu dakatar saboda azumin watan Ramadan. Muna gabatar da wannan darasi ne don ganin maniyyatanmu sun samu damar gudanar da aikin Hajji bisa umarnin Allah da koyarwar wanda ya kawo mana wannan addini Annabi Muhammad (SAW). Ya kamata maniyyata su fahimci cewa ba yawon bude-ido ake zuwa Makka da Madina ba, ana zuwa ne don yin ibada, don haka wajibi ne su tsaya su koyi abin da zai kai su can, ba kawai su dauka cewa tunda suka lale dukiyarsu, suna da ikon su yi yadda suka ga dama a can. Allah Ya datar da mu ga abin da yake daidai:
Tambaya ta 28: Shin akwai wani dawafi da ake kira bakwai sau bakwai, domin neman biyan wata bukata?
Amsa: A gaskiya babu wani dawafi a shari’a da ake kiransa bakwai sau bakwai. Domin irin wannan dawafi bai tabbata ba a cikin Littafin Allah ko kuma koyarwar ManzonSa (SAW). Sai dai akwai dawafin nafila wanda za a iya yi. Amma shi dawafin nafila, ba a kayyade adadin da za a yi ba. Illa iyaka idan an yi dawafi bakwai, sai a yi nafila, idan an kara yin wani bakwai, sai a yi nafila. Haka za a yi, gwargwadon yadda aka samu dama, domin neman kusanci da Allah
A duba Al-Istizkar, Mujalladi na 12 shafi na 166, mas’ala ta 17181.
An tambayi Imam Malik cewa: Mutum zai iya yin dawafi bakwai sau biyu, ba tare da ya yi raka’a biyu a kowane bakwai ba? Sai ya ce: Yin haka bai kamata ba, domin Sunnah ita ce yin raka’a biyu bayan yin kowane dawafi bakwai. A duba Al-Istizkar: Mujalladi na 12 shafi na 171, mas’ala ta 17177.
Kuma wajibi ne a yi hattara da malaman da ke karbar kudi a wurin jama’a da nufin wai za su yi musu dawafin bakwai sau bakwai, ba tare da an yi raka’a biyu a tsakani ba, don neman biyan wata bukata. Hakika yin haka, kauce wa umarnin Allah da ManzonSa (SAW) ne da kuma aikin magabatan kwarai.
Tambaya ta 29: Idan mutum ya yi Sallah raka’a biyu a bayan Makama Ibrahim, sai ya tuna dawafinsa bai cika ba, yaya zai yi?
Amsa: Idan haka ta faru, sai ya koma ya cika dawafin, sannan ya zo ya sake yin raka’a biyun, don ita raka’a biyun ba a yin ta sai bayan yin dawafi. A duba Al-Istizkar, Mujalladi na 12 shafi na 171, mas’ala ta 17201
Tambaya ta 30: Idan aka fara Sallah alhali mutum na dawafi, yaya zai yi?
Amsa: Idan haka ya faru, sai ya tsaya ya bi liman Sallah. Idan aka gama Sallah, sai ya ci gaba da dawafinsa daga inda ya tsaya. Amma idan Sallar Jana’iza ce, to mutum yana da zabi: ko dai ya tsaya, ko ya ci gaba da dawafinsa.
Tambaya ta 31: Mene ne hukuncin wanda alwalarsa ta karye alhalin yana cikin dawafi?
Amsa: Hakika malamai sun yi sabani a kan hukuncin wanda alwalarsa ta warware, alhali yana cikin dawafi. Wadansu malaman na ganin ya sake jaddada alwala, sannan ya karasa dawafinsa, saboda suna ganin cewa alwala, mustahabbi ce, ba sharadin ingancin dawafin ba.
Dalilinsu shi ne Hadisin da aka karbo daga NanaA’isha (RA) ta ce: “Farkon abin da Manzon Allah (SAW) ya fara, yayin da ya zo Makka shi ne alwala, sannan sai ya yi dawafi…” Sahihul Bukhari: Kitabul Hajji, Bab ad-dawafi Ala Wudu’in, Hadisi na
1641da Sahih Muslim: Kitabul Hajji, Babu Ma Yalzamu Man dafa Bil Baiti Wa Sa’a Minal Baka’i Alal Ihrami Wa Tarkit Tahulluli, Hadisi na 1235.
Wannan ya sa wadannan malaman suka ce, wannan Hadisin ya nuna cewa yin alwala mustahabbi ne, ba wajibi ba, tunda yake babu wani umarni a ciki. A duba Al-Istazkar Mujalladi na 12 shafi na 178.
Amma Imam Malik da Imam Shafi’i da Imam Ahmad, a daya daga fatawoyinsa biyu suna ganin alwala sharadi ne na ingancin dawafi, tunda Manzon Allah (SAW) ya aikata hakan, kuma ya ce: “Ku riki ayyukan hajjinku daga gare ni…” Sahih Muslim: Kitabul Hajji, Babus Tihbabi Ramyi Jamratil Akaba Yauman Nahri Rakiban, Hadisi na 1297 da Sunan Abu Dawud: Kitabul Manasiki, Babun Fi Ramyil Jimar, Hadisi na 1970.
To, tunda Manzon Allah (SAW) sai da ya yi alwala kafin ya fara dawafi, wannan ya nuna mana cewa ashe yin alwala yana daga cikin ayyukan Hajji.
Dalilinsu na biyu kuma shi ne, Manzon Allah (SAW) ya ce wa mai jinin al’ada ta yi kowace irin ibada ta Hajji, amma ban da dawafi. Wadannan malamai suna ganin cewa rashin yin alwala shi ne ya sanya aka hana ta yin dawafin.
Sannan suka kara da cewa: “Wadansu daga cikin Sahabbai suna ganin cewa dawafi Sallah ne, sai dai shi ana magana a cikinsa, saboda Hadisin da ya tabbata daga Abdullahi Ibnu Abbas (RA) ya ce: “Hakika Manzon Allah (SAW) ya ce: “Yin dawafi a dakin (Ka’aba), Sallah ne, sai dai ku kuna yin magana a cikinsa.” Sheikh Albani ya inganta shi a cikin littafinsa mai suna Irwa al-Ghalil: Juzu’i na 4, Hadisi na 1102.
Daga bayanan da suka gabata, muna rinjayar da cewa idan hakan ya faru ga mai dawafi, mustahabbi ne ya sake alwala, sannan ya ci gaba da dawafinsa. Wallahu a’alam.
Tambaya ta 32: Alhajin da ya gama dawafin umararsa ko na hajjinsa, sai cinkoso ko rashin lafiya suka hana shi gabatar da Sa’ayi tsakanin Safa da Marwa a wannan lokacin, to, shin idan ya samu dama zai yi Sa’ayin Safa da Marwan ne kawai, ko kuma sai ya hada dawafin da Sa’ayi?
Amsa: Idan ya samu dama ko ya samu sauki ba sai ya maimaita dawafin ba, Sa’ayi tsakanin Safa da Marwa kawai zai yi. Domin jeranta su ba wajibi ba ne. Saboda Hadisin da ya tabbata daga Usamatu Ibnu Sharik (RA) ya ce: Na fito aikin Hajji tare da Manzon Allah (SAW), sai mutane suka rika zuwa wurin Manzon Allah (SAW), wani ya ce masa: Ya Manzon Allah (SAW), na gabatar da Sa’ayi kafin dawafi? Ko ya ce na gabatar da wani abu, ko kuma na jinkirtar da wani abu? Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Babu Komai! Babu komai…” A duba Sunan Abu Dawud, Kitabul Manasik, Babu Fi man kaddama Shai’an kabla Shai’in Fi Hajjihi, Hadisi na 2015.
Abin fahimta a wannan Hadisi shi ne jeranta dawafi da sa`ayi ba wajibi ba ne. Sai dai an fi so a jerantasu, idan an samu iko.
Tambaya ta 33: Wadanne addu’o’i ne suka tabbata daga Manzon Allah (SAW yayin Sa’ayi tsakanin Safa da Marwa?
Amsa: Shi dai Sa’ayi tsakanin Safa da Marwa an yi bayaninsa a can baya, amma ga zikirai da addu’o’in da Manzon Allah (SAW) ya yi a lokacin da yake yin Sa’ayi a tsakanin Safa da Marwa. Da farko dai ana fara yin Sa’ayi ne daga Safa, domin haka idan mutum ya tunkari dutsen Safa, sai ya ce: “Innas safa wal marwata min sha’a’irillah, faman hajjal baita au itmara fala junaha alaihi ayyadawwafa bihima. Wa man tadawwa’a khairan, fa innallaha shakiran alim.”
Ma’ana: “Lallai ne Safa da Marwa suna daga cikin alamomi na ibadar Allah, to, wanda ya hajjaci daki ko kuwa ya yi Umara, to, babu laifi a kansa ya yi Sa’ayi a tsakaninsu. Kuma wanda ya kara yin wani aikin alheri, to, lallai ne Allah Mai yawan gode wa bayinSa ne, kuma Mai yawan Sanin (abin da bayinSa suke yi na ayyukan alheri ne)”. (Bakara: 158).
**{Legacy activities, comments etc counter: 539; topic series: 2; forum: MediaHausa; associated: 2- /*}