Fatawoyin Aikin Hajji da Umara da Ziyara (10)
An buga: Litini Feb 09, 2026 2:35 am
*Legacy Post Number 101 from MediaHausa
Topic: Fatawoyin Aikin Hajji da Umara da Ziyara (10)
Timeline: 2012-10-14 21:46:06
Fatawoyin Aikin Hajji da Umara da Ziyara (10)
Daga Sheikh Abdulwahhab Abdullah
Sannan, idan an hau kan dutsen, sai a fuskanci Ka’aba a ce: “Allahu Akbar! Allahu Akbar! Allahu Akbar! La’ilaha illallahu wahdahu la sharikalahu, lahul mulku wa lahul hamdu, yuhyi wa yumitu wa huwa ala kulli shai’in kadir. La ilaha illahu wahdahu lasharikalahu, anjaza wa’adahu wa nasara abdahu wa hazamal ahzaba wahdahu.”
Ma’ana:
“Allah Shi ne Mafi girma! Allah Shi ne Mafi girma! Allah Shi ne Mafi girma! Babu wanda ya cancanta a bauta masa sai Shi, Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya, dukkan mulki da dukkan godiya sun tabbata a gare Shi. Shi ne Mai rayawa Mai kashewa, kuma Shi Mai iko ne a kan komai. Babu wanda ake bautawa bisa cancanta sai Shi kadai, ba Ya da abokin tarayya, Ya cika da alkawarinsa, kuma Ya taimaki bawanSa, kuma Ya ruguza rundunar (kafirci) Shi kadai…” Sahih Muslim: Kitabul Hajji, Babu Hajjatin Nabiyyi (SAW), Hadisi na 1218; da Sunan Abu Dawud: Kitabul Manasik, Babu Siffatul Hajjatin Nabiyyi (SAW), Hadisi na 1905.
Bayan ya gama wannan, sai ya roki Allah gafara da alherin duniya da Lahira. Haka zai yi har sau uku. Idan mahajjaci ya gama wadannan addu’o’i, sai ya gangaro zuwa dutsen Marwa. Idan ya iso wurin da aka sa koriyar fitila a sama, a tsakanin Safa da Marwa, sai ya yi sassarfa (amma mata ba sa yi). Idan ya kusa hawa Marwa, sai ya karanta irin addu’ar da Manzon Allah (SAW) ya yi a lokacin da ya nufo Safa. Idan ya hau kan Marwa, sai ya sake fuskantar Ka’aba ya yi kabbara sau uku, sannan ya kara yin irin addu’o’in da aka ambata ana yi a kan dutsen Safa.
Haka za a yi ta yi har sau bakwai. Ma’ana, idan aka fara daga Safa zuwa Marwa, daya ke nan; idan aka dawo daga Marwa zuwa Safa, biyu ke nan.
Tsakanin Safa da Marwa kuma babu wata kebantacciyar addu’a da ake yi, sai dai mutum zai iya yin tasbihi da istigfari da hailala da salatin Annabi (SAW) da addu’o’in da yake so na bukatarsa.
Shi Sa’ayi, wanda ke yin aikin Hajji ko Umara ne kawai yake yin sa. Amma ba za a iya yin sa da niyyar nafila, kamar yadda ake yin dawafi na nafila ba.
Tambaya ta 34: Wace irin ibada ya kamata mahajjaci ya shagaltu da ita ranar Arfa?
Amsa: Filin Arfa, fili ne babba wanda aka iyakance shi, aka kuma sa masa alamu gabas da yamma, kudu da arewa. An yi rubutu a wurin da harshen Hausa da Larabci da Turanci. Domin haka, bai kamata a tsaya a wani wuri daban, ba inda aka iyakance ba. Ko ina aka tsaya a cikin wannan filin da aka iyakance, ya yi daidai. Haka kuma, ba a hawa kan dutsen, domin Manzon Allah (SAW) bai hau kan dutsen ba. Ya tsaya ne a bayan dutsen daga gabas, ta yadda ya sa dutsen tsakaninsa da Makka, alhali yana kan rakuminsa. Manzon Allah (SAW) ya ce: “… Na tsaya a nan, kuma duk filin Arfa wurin tsayuwa ne…” Sahihu Muslim: Kitabul Hajji, Babu Hajjatin Nabiyyi (SAW), Hadisi na 1218.
Ana fara addu’a a ranar Arfa da zarar an gama Sallar Azahar da La’asar wadanda ake yin su a hade, wato a farkon lokacin Azahar. Ana son a tsaya a kan abin hawa, alhali ana fuskantar alkibla. Idan ba a samu abin hawa ba, sai a tsaya a bisa duga-dugai, a fuskanci alkibla, a ci gaba da addu’a. Idan kuma babu hali, sai a zauna a fuskanci alkibla, a yi ta addu’a. Domin Manzon Allah (SAW) a kan taguwarsa ya zauna. Haka kuma, ana son a kasance cikin alwala, ana son a daga hannuwa sama a yayin da ake yin addu’ar.
Addu’ar da aka fi so a wannan ranar kuwa ita ce: “La ilaha illallahu wahdahu la sharikalahu lahul mulku wa lahul hamdu wa huwa ala kulli shai’in kadir.” Ma’ana: Babu wanda ya cancanta a bauta masa sai Allah Shi kadai, ba Ya da abokin tarayya, mulki gare Shi yake, kuma godiya ta tabbata gare Shi, kuma Shi Mai iko ne a kan komai.”
Ita za a yi ta maimaitawa, sannan, a yi ta neman gafarar duk abin da aka yi na sabo, wanda aka sani da wanda ba a sani ba. Kuma a roki dukkan bukatu na duniya da Lahira da neman kyakkyawan karshe da nema wa iyaye da suka mutu gafara. Haka kuma, a hada da ’ya’ya da ’yan uwa a cikin addu’a, kuma kada a manta da ’yan uwa Musulmi da ke cikin gwagwarmaya da jihadi a kowane bangare na duniya, da wadanda ake zalunta suna yakin kwatar kai daga hannun kafirai. Haka kuma, zai yi matukar fa’ida idan aka hada da wannan zikiri na:
“Subhanallahi wal hamdu lillahi, wa la’ilaha illahu wallahu akbar, wala haula wala kuwwata illa billahil aliyyil azim.”
Ma’ana: “Tsarki ya tabbata ga Allah, dukkan godiya ta tabbata ga Allah. Kuma babu wanda ake bauta wa bisa cancanta sai Allah, kuma Allah Shi ne Mafi girma. Kuma babu dabara, babu karfi sai ga Allah, Madaukaki, Mai girma.”
Kuma a yi kokarin yawaita salatin Annabi (SAW). Daga cikin salatai da addu’o’in da suka tabbata daga bakinsa mai albarka (SAW). Misali a ce:
“Allahumma salli ala Muhammadin wa ala ali Muhammadi kama sallaita ala Ibrahima wa ala ali Ibrahima fil alamina innaka hamidun majid. Wa barik ala Muhammadin wa ala ali Muhammadin kama barakta ala Ibrahima wa ala ali Ibrahima fil alamina innaka hamidun majid.:
Ma’ana: “Ya Allah Ka yi salati ga Muhammad da alayen Muhammad, kamar yadda Ka yi salati ga Ibrahim da alayen Ibrahim a cikin talikai, hakika Kai Abin yabo ne, Abin girmamawa. Ka yi albarka a bisa Muhammad da alayen Muhammad, kamar yadda Ka yi albarka a bisa Ibrahim da alayen Ibrahim a cikin talikai, hakika Kai Abin
yabo ne, Abin girmamawa.”
Da kuma: “Allahumma inni a’uzu bika minal hammi wal huzini, wa minal ajazi wal kasli wa minal jubni wal bukhuli wa minal ma’asmi wal magarami wa min galabatid daini wa kaharil rijali. Wa a’uzu billahi minal barasi wal jununi wal juzami wa min su’il askami. Allahumma inni as’alukal afwa wal afiya fid duniya wal alkhira.”
Ma’ana:
“Ya Allah, ina neman tsarinKa daga bacin rai da bakin ciki da gajiyawa da kasala da tsoro da rowa da sabo da bashi da rinjayar bashi da rinjayar mazaje (abokan gaba). Kuma ina neman tsari a wurin Allah daga albaras da hauka da kuturtar mai datse gaba da miyagun cututtuka. Ya Allah! Ina rokonKa afuwa da lafiya a duniya da Lahira.”
Da kuma: “La’ilaha illahu wala na’abudu illa iyyahu, lahun ni’amatu wa lahul fadlu wa lahus sana’ul husna. La’ilaha illallahu mukhlisina lahud dina wa lau karihal kafirun. Lahula wala kuwwata illa billah. Allahumma aslihli dinil lazi huwa ismatu amri, wa aslihli duniyaya allati fiha ma’ashi, wa aslihli akhirati allati ilaiha ma’adi. Waj’alil hayata ziyadatan li fi kulli khairin wal mauta rahatan li min kulli sharrin. A’uzu billahi min jahadil bala’i wa darkis shika’i wa su’il khada’i wa shimatal a’ada’i.”
Ma’ana: “Babu wanda ake bauta wa bisa cancanta sai Allah. Kuma ba mu bauta wa kowa sai Shi kadai; ni’ima da falala da kyakkyawan yabo duk sun tabbata a gare Shi. Babu wanda ake bauta wa bisa cancanta sai Allah. Muna masu tsarkake addini a gare Shi, koda kafirai sun ki. Babu dabara, babu karfi, sai ga Allah. Ya Allah Ka kyautata mini addinina, wanda shi ne kariyar al’amurana. Ka kyautata mini duniyata, wadda a cikinta ne nake rayuwa. Ka kyautata mini Lahirata wadda a cikinta ne makomata take. Ka sa rayuwa ta zama kari a gare ni cikin dukan alheri. Ka sa mutuwa ta zama hutu ne a gare ni daga dukkan sharri. Ina neman tsarin Allah daga tsananin bala’i da afkawa cikin tabewa da mummunan karshe da dariyar keta ta abokan gaba.”
**{Legacy activities, comments etc counter: 1684; topic series: 2; forum: MediaHausa; legacy score: 9; legacy ratings: 2; rating_ip: ***.*14.31.188; associated: 2- /*}