Fatawoyin Aikin Hajji da Umara da Ziyara (11)
An buga: Litini Feb 09, 2026 2:36 am
*Legacy Post Number 103 from MediaHausa
Topic: Fatawoyin Aikin Hajji da Umara da Ziyara (11)
Timeline: 2012-10-14 21:51:00
Fatawoyin Aikin Hajji da Umara da Ziyara (11)
Daga Sheikh Abdulwahhab Abdullah
Haka kuma, kada a kosa wajen rokon Allah ana kankan da kai, ana komawa zuwa gare Shi, ana rokonSa, ana furuci da dukan abin da aka aikata na laifuf*****a, sannan ana neman gafararSa. Manzon Allah (SAW) ya tsaya a kan taguwarsa, tun bayan sallar azahar, yana rokon Ubangiji (SWT), har faduwar rana, har ana zaton ma ko azumi yake yi. A Duba Sahih Muslim: Kitabul Hajji, Babu Hajjatin Nabiyyi (SAW), Hadisi na 1218; da Sunan Abu Dawud: Kitabul Manasik, Babu Sifati Hajjatin Nabiyyi (SAW), Hadisi na 1905.
Saboda haka, idan Manzon Allah (SAW) zai dage a kan yin addu’a da rokon Ubangiji (SWT), to, ina kuma ga mu, wadanda ba mu san yadda makomarmu za ta kasance ba? Abin takaici shi ne sai ka ga wadansu mutane suna yawo a cikin filin Arfa, wasu suna barci, wasu suna surutu ko hira, wasu kuma suna kokarin su je su hau dutsen Arfa, wadansu kuwa ba su yin komai, sun gafala da yin addu’a. Wadansu kuma ka ga sun tara mata suna karanta musu addu’o’in da ba su da asali a shari’a, su kuma matan suna amshi; alhali kuwa hakan cutarwa ce ga matan, tun da dai ba a bar su sun roki Allah bukatunsu ba. Sannan kuma mafiya yawansu ba su san ma’anar abin da ake karanta musu ba. Irin wannan dabi’a ita ce asara kan asara, domin shi mai koyarwar bai tsaya ya yi tasa addu’ar ba, sannan kuma bai bar su matan sun yi ta su addu’ar ba. Haka kuma za ka ga wadansu da suka fitini kawunansu, har taba (sigari) suke sha a filin Arfa, ba su ko damuwa da cewa warinta yana damun jama’a, sannan kuma yana nisanta su daga Mala’ikun Rahama.Wadansu kuwa, sai ka ga su na gaggawa, domin su bar wannan fili na Arfa kafin faduwar rana, wadansu kuma suna dauke-dauken hotuna.
Hakika yin wadannan abubuwa sun saba wa Sunnar Manzon Allah (SAW) da aikin magabatan kwarai. Domin Hadisi ya tabbata daga Abdullahi Ibnu Amru Ibnu As (RA) ya ce: “Hakika Manzon Allah (SAW) ya kasance yana cewa: “Innal laha Azza wa Jalla yubahi mala’ikatahu ishatu arfa bi ahli arfa, fa yakulu unzuru ila ibadi shu’asa’an gubara.”
Ma’ana: “Hakika Ubangiji Mai girma da Buwaya Yana alfahari ga Mala’ikunSa game da bayinsa da suka halarci filin Arfa a yammacin ranar Arfa, Yana ce musu ku yi duba zuwa ga bayiNa (sun zo miNi) da gizo (gashin da ya cukurkude) da kura.” Sahih al-Targhib: Hadisi na 1153.
Haka kuma, Hadisi ya tabbata daga Nana A’isha (RA) ta ce: Hakika Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ma min yaumin aksara min an yu’utikallahu fihi abdan minan nari min yaumi arfata.”
Ma’ana: “Babu wata rana da Allah ya fi ’yanta bawa daga wuta kamar ranar Arfa…” Sahih Muslim: Kitabul Hajji, Babu Fi Fadlil Hajji Wal Umarati Wa Yaumi Arafata, Hadisi na 1348.
Bayan wannan kuma, Manzon Allah (SAW) bai bar filin Arfa ba, sai bayan faduwar rana, ga shi kuma ya ce: “Li ta’akhuzu manasikakum.”
Ma’ana: “Ku riki ayyukan hajjinku daga gare ni…” Sahih Muslim: Kitabul Hajji, Babus Tihbabi Ramyil Jamratil Akabati Yauman Nahri Rakiban, Hadisi na 1297; da Sunan Abu Dawud: Kitabul Manasik, Babu Fi Ramyil Jimari, Hadisi na 1970. Saboda haka, babu wanda shari’a ta yi wa uzuri ya bar wannan fili kafin faduwar rana sai mara lafiya. Shi ne wanda za a iya kawo shi filin Arfa a wani yanki na yini, kamar rabin rana ko kuma wani bangare na dare.
Haka kuma wanda ya makara bai zo da rana ba, saboda wani uzuri, zai iya tsayawa da daddare matukar alfijir bai keto ba. Saboda Hadisin da ya tabbata daga Urwatu Ibnu Mudarris Ad-da’i (RA) ya ce: “Na zo wurin Manzon Allah (SAW) a maukif wato Muzdalifa, sai na ce: ya Rasulallah! Na zo ne daga dutsen dai’i, na wahalar da dabbata kuma na wahalar da kaina. Wallahi ban bar wani tsauni ba, face na tsaya a kansa, to, shin ina da Hajji? Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya riski wannan Sallar (ta Asuba) tare da mu, ya halarci Arfa kafin wannan da dare ko da rana, to, hakika Hajjinsa ya cika, kuma ya gama mafi yawan ibadarsa ta Hajji. Sunan Abu Dawud: Kitabul Manasiki, Babu Man Lam Yudrik Arafata, Hadisi na 1950.
Wannan ya sa malamai suka yi ijma’i a kan cewa tsayuwar Arfa tana karewa daga ketowar alfijir na ranar Idi ne. Muna rokon Allah Ya ba mu dacewa, Ya karba mana Hajjinmu da sauran ibadojinmu, amin.
Tambaya ta 35: Mene ne hukuncin Alhazan da suka samu hemominsu ba a cikin filin Arfa ba?
Amsa: Alhazan da suka sami hemominsu ba a cikin filin Arfa ba, wajibi ne su tako su shigo filin Arfa domin babu Hajji in ba a tsaya a filin Arfa ba. Ko da bayan faduwar rana suka samu lokaci, su shiga filin Arfa su tsaya su yi addu`a gwargwadon iko. Dalilinmu a nan, fadin Manzon Allah (SAW) cewa: “Tsayuwar Arfa ita ce aikin Hajji.”
Wanda ya riski Arfa da daddare kafin alfijir ya fito, to, hajjinsa ya cika. A duba Sunan Ibnu Majah: Kitabul Manasik, Babu Man Ata Arafata kabla Lailata Jam’in, Hadisi na 3015; da Sunan Tirmizi: Kitabul Hajji, Babu Ma Ja’a Fiman Adrakal Imama Bi Jam’in Fakad Adrakal Hajja, Hadisi na 889. Sai dai wannan lafazin na Ibnu Majah ne.
A kan wannan ne manyan malamai magabta suka tafi, kamar yadda Imam Tirmizi ya fada cewa sahabban Manzon Allah (SAW) da sauran manyan malamai magabatan kwarai kamar babban almajirin Imam Malik, wato Imam Shafi’i da Imam Ahmad da Is’hak da Imam Assauri da sauransu duk sun tafi a kan wannan fahimta. A duba bayanin Hadisi mai lamba 890 a cikin Kitabul Hajji na Sunan Tirmizi, Kitabul Hajji, Babu Ma Ja’a Fiman Adrakal Imama Bi Jam’in Fakad Adrakal Hajja. Allah shi ne mafi sani. Allah Ya karbi ibadarmu.
Tambaya ta 36: Wace irin ibada ya kamata a shagaltu da ita a Muzdalifa?
Amsa: Farkon ibadar da ta wajaba a kula da ita da zarar an isa Muzdalifa ita ce hada Sallar Magriba da Issha kuma kasaru, ba tare da an yi nafila a tsakaninsu ba.
Jabir Ibnu Abdullah (RA) ya fada a cikin Hadisi mai tsawo cewa: “… Da Manzon Allah (SAW) ya iso Muzdalifa, sai ya hada Sallar Magriba da Issha, da kiran Sallah daya da ikama biyu, kuma bai yi wata nafila a tsakaninsu ba. Sannan ya kishingida har sai da alfijir ya keto, sai ya yi Sallar Asuba…” Duba Sahih Muslim: Kitabul Hajji, Babu Hajjatin Nabiyyi (SAW), Hadisi na 1218; da Sunan Abu Dawud: Kitabul Manasiki, Babu Sifati Hajjatin Nabiyyi (SAW), Hadisi na 1905.
Idan an idar da Sallar Asuba, sai a karasa Mash’arul Haram (masallacin Muzdalifa), idan an samu dama. Idan kuma ba a samu dama ba, sai a tsaya a ko’ina cikin Muzdalifa, a fuskanci alkibla, a yi ta yin hailala da hamdala da tasbihi da salatin Annabi (SAW). Za a daga hannuwa a yi ta yin addu’a har gari ya waye kafin fitowar rana. Daga nan, sai a tafi Mina don yin jifar Jamratul Akabah.
Ya kamata a sani cewa, kwana a Muzdalifa da yin Sallar Asuba a wurin yana daga cikin wajiban aikin Hajji, domin haka Manzon Allah (SAW) ya aikata. Domin haka ba wanda zai bar Muzdalifa kafin gari ya waye, sai raunana da kananan yara da marasa lafiya da masu larura. Su ma ba za su bar Muzdalifa ba, sai wata ya bace (watau zuwa tsakiyar dare) sai su tafi Mina, idan sun je kuma ba za su yi jifa ba, sai bayan fitowar alfijir. Wannan ita ce magana mafi rinjaye.
**{Legacy activities, comments etc counter: 665; topic series: 2; forum: MediaHausa; legacy score: 8; legacy ratings: 2; rating_ip: ***.*14.31.188; associated: 2- /*}