Labarai da Ra'ayi
Labaran Duniya Musulmi da Gabas ta Tsakiya

Koma zuwa "Labaran Duniya Musulmi da Gabas ta Tsakiya"

Labaran Duniya Musulmi da Gabas ta Tsakiya
NewsTeam
Masu rubutu: 10
An haɗa: Thu Nuwamba 06, 2025 6:42 am
Lambobi:

     NewsTeam Masu rubutu: 10    An haɗa: Thu Nuwamba 06, 2025 6:42 am    Lambobi:   


Buga by NewsTeam »

Esin020 Kwankwaso Ya Gargaɗi Masu Shirin Juya Masa Baya A Siyasar Kano

By Sadiq, Leadership

Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi gargaɗin cewa cin amana a siyasa ba ya samar da nasara mai ɗorewa.

Kwankwaso ya yi wannan jawabi yayin da yake magana da waɗanda suka amfana da shirin tallafin karatunsa.

Sai dai wasu na ganin Kwankwaso ya tura saƙon ne a matsayin gargaɗi ga Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da wasu da ake zargin suna shirin koma wa APC.

Ya ce waɗanda suka bar tushen siyasa na iya samun nasara na ɗan lokaci, amma tarihi ya nuna cewa nasarorinsu ba masu ɗorewa ba ne.

Ya yi kira ga magoya bayan ‘Kwankwasiyya Movement’ da su kasance masu biyayya ga NNPP kuma su koyi darasi daga kuskuren da aka yi a baya.

Kwankwaso bai yi magana kai-tsaye kan kiran wasu mambobin NNPP ke masa ba na sauya sheƙa.

Shi ma Gwamna Yusuf bai yi bayani ba yayin da ake ta tsammanin yiwuwar sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

NNPP Ta Kori Shugabanta Na Kano, Dungurawa, Kan Zargin Saɓa Dokokinta

Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano, ta kori shugabanta, Hashimu Dungurawa, kan zargin aikata rashin ɗa’a.

Shugabannin Gargari a Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa ne, suka yanke wannan hukunci a taronsu, makonni biyu bayan Dungurawa ya sake zama shugaban jam’iyyar.

Shugabannin sun ce an kore shi ne saboda haifar da rarrabuwar kawuna a jam’iyya, tayar da rikici, rashin biyan kuɗin jam’iyya, da yin maganganu marasa ladabi ga Gwamnan Jihar Kano.

Takardar hukuncin ta bayyana cewa ayyukansa sun haifar da naƙaso ga haɗin kai da ci gaban jam’iyyar, kuma an ɗauki matakin korarsa don samar da zaman lafiya.

Sun aike takardar hukuncin zuwa ofisoshin jam’iyya na ƙasa, jiha, da ƙaramar hukuma, da kuma jagoran jam’iyyar na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Shugabannin sun ce an kore shi ne domin hana sauran mambobi karya dokokin jam’iyyar, sannan sun sake tabbatar da biyayya ga jagoran NNPP da goyon bayansu ga Gwamna Yusuf.

Aika amsa

Kwankwaso Ya Gargaɗi Masu Shirin Juya Masa Baya A Siyasar Kano



Bayar da Amsa

Koma zuwa "Labaran Duniya Musulmi da Gabas ta Tsakiya"

Bayar da Amsa