Shafin 1 na 1

Maraba da Shekarar 1433 BH: Nazari kan shekarar Musulunci da hijira (2)

An buga: Thu Feb 05, 2026 4:32 am
by MediaHausa
*Legacy Post Number 43 from MediaHausa
Topic: Maraba da Shekarar 1433 BH: Nazari kan shekarar Musulunci da hijira (2)
Timeline: 2012-03-27 18:51:34


Maraba da Shekarar 1433 BH: Nazari kan shekarar Musulunci da hijira (2)

A Rubuce Da Salihu Is’hak Makera

An karbo daga Sayyadi Aliyu (RA) cewa ya ji wani mutum yana tambayar Manzon Allah (SAW) alhali yana tsaye sai ya ce: “Ya Manzon Allah! Wane wata ne za ka umarce ni in yi azuminsa a bayan watan Ramadan?” Sai ya ce: “Idan za ka yi azumi a bayan Ramadan ka azumci Muharram, domin lallai shi watan Allah ne, a cikinsa akwai ranar da Allah Ya amshi tubar wadansu mutane, kuma a cikinsa zai karbi tubar wadansu mutanen na daban.”

(Ad-Darimi: Hadisi na 1756; Tirmizi Hadisi na 741, kuma ya ce Hadisin “hasnun ne garibi” a cikin isnadinsa akwai Nu’uman Bin Sa’ad- wanda ya ruwaito daga Aliyu- alhali bai ruwaito daga gare shi ba, face dan ’yar uwarsa Abdurrahman Bin Is’hak Al-Kufi, shi kuma majahuli ne, kuma Abdurrahman din an yi ittifaki kan rauninsa. A duba Almizan, Mujalladi na 4 shafi na 265 da At-Tahzib, Mujalladi na 10 shafi na 453. Kuma don haka ne Albani ya raunata shi ya sanya shi cikin masu rauni a cikin littafinsa At-Targib wat Tarhib, shafi na 614).

Bisa abin da ya gabata, ya bayyana shar’anta azumin watan Muharram da mustahabbantar da hakan. Sheikh Ibnu Baz (RH) ya ce: “Watan Muharram an shar’anta azuminsa haka Sha’aban. Amma azumin goma ga Zul Hajji babu wani dalili a kan haka. Amma da mutum zai azumce su ba tare da I’itikadin cewa su kebantattu ne ba, ko suna da wata kususiyya ayyananniya, babu laifi. Amma watan Allah Muharram hakika Manzon Allah (SAW) ya ce: “Mafi falalar azumi a bayan Ramadan shi ne na watan Allah Al-Muharram.” Idan mutum ya azumce shi gaba daya ya yi kyau, haka idan ya azumci ranakun tara da goma da goma sha daya shi ma ya yi kyau. Haka ma Sha’aban, hakika (SAW) yana azumtarsa.” (Majma’u Fatawa na Sheikh Bin Baz a kan Zakka da Azumi wadda Ad-dayar ya tattara, shafi na 269).

Na uku: Illar rashin yawaita azuminsa (SAW) a cikin Muharram

Annawawi ya ce: “Hakika jawabi ya gabata kan yawaita azumin Annabi (SW) a Sha’aban ban da Muharram. Kuma mun ambaci maganganu biyu kan hakan.

dayarsu ita ce: La’alla ya san falalarsa ce a karshen rayuwarsa.

Na biyu: La’alla ya kasance yana bijiro da wasu uzurori a cikinsa ne na daga tafiya ko rashin lafiya ko waninsu. (Sharh Sahihul Muslim, Mujalladi na 8 shafi na 55).

Alhafiz ya nakalto shi a cikin Fathul Bari, amma bai yi bayani a kansa ba. (Fathul Bari, Mujalladi na 4 shafi na 215).

Hijira a zamanin Annabi (SAW):
Hakika mahsahuran Hijira da suka auku a zamanin Annabi (SAW) guda uku ne:

1. Hijirar farko zuwa Habasha:

Wannan Hijira ta kasance ce a cikin watan Rajab na shekara ta biyar da aiko shi (SAW), inda mazaje 11 da mata hudu suka fita a kafa zuwa bakin teku suka dauki shatar kwale-kwale kan rabin Dinar suka sauka a gidan alheri zuwa makwabcin alheri suka samu, suka samu aminci a bisa addininsu, kuma ba su ji tsoron zalunci ba. (Fathul Bari, Mujalldi na 7 shafi na 188).

2. Hijira ta biyu zuwa Habasha:

Labari ya riski Musulmin da suke Habasha cewa mutanen Makka sun musulunta. Sai wadansu mutane suka dawo Makka daga cikinsu akwai Usman Bin Maz’un, sai suka iske labarin ba gaskiya ba ne. sai suka koma Habasha tare da wadansu mutane masu yawa. Sun haura mazaje 80, wannan ce Hijira ta biyu. (Fathul Bari, Mujalladi na 7 shafi na 189).

3. Hijira daga Makka zuwa Madina:

Wadda a kanta za mu tattauna a takaice.

Zaben Madina don Hijira ga Manzon Allah (SAW) ya kasance ne bisa wahayi daga Allah Madaukaki. Mai tsira da amincin Allah ya ce:

“Na gani a cikin bari cewa ina yin hijira daga Makka zuwa wani gari mai dabinai. Sai mafarkin ya tafi sai na dauka Yamamah ce ko Hijri, sai ga shi ashe Madina ce.” (Buhari, Hadisi na 6629 da Muslim, Hadisi na 2272).

Ibnu Munir ya ce: “Ya kasance an gwada wa Annabi (SAW) gidan Hijira bisa siffar da ta hada Madina da waninta, sannan aka nuna masa siffa kebantacciya da Madina sai aka ayyana ta.”

Mutum na farko da ya fara hijira zuwa Madina kamar yadda littattafan tarihi suka ambata, shi ne Abu Salma bin Abdul’asad. Kuma ya yi hijirar ce gabanin mubaya’ar Ukubah da shekara daya. Haka Mus’ab Bin Umair da Ibnu Ummi Maktum suna daga cikin wadanda suka fara hijira saboda suna karantar da mutane Alkur’ani. Sai masu hijira suka rika bibiyar juna, Bilal bin Ribah da Sa’ad bin Abu Wakkas da Ammaru bin Yassir suka isa Madina, sannan Umar bin Khaddabi a cikin sahabbai 20. (Buhari, Hadisi na 3694)

Sayyid Abubakar (RA) ya so ya yi hijira zuwa Madina, sai Annabi (SAW) ya ce “Ka dakata, ina tsammanin a yi min izini.” Wannan ya faru gabanin hijirar da wata hudu. Don haka Abubakar bai yi hijira ba, bias kwadayin ya kasance tare da Annabi (SAW) har zuwa lokacin da aka yi masa izini. Buhari ya ruwaito, Hadisi na 2176.

Kwatsam sai kuraishawa suka game kai za su kasha Annabi (SAW) kamar yadda Alkur’ani ya ambata. “Kuma a lokacin kafirai suke kulla maka makirci kan su daure ka, ko su kashe ka, ko su fitar da kai…” (k:Anfal:30).

Sai aka yi wa Annabi (SAW) izinin yin hijira a lokacin zafin rana. A’isha (RA) ta ce: “Lokacin da aka yi izini da fita zuwa Madina babu abin da ya firgita mu face ya zo mana a lokacin azahar.

To amma ba su fita daga cikin Makka ba, sai cikin dare kamar yadda malamai da dama suka ruwaito. (A duba Buhari Hadisi na 1365 da Fathul Bari, Mujalladi na 6 shafi na 62).

Kuma wannan ya faru ne a ranar Litinin ko Alhamis. Alhakim ya ce: “Labaran da suka kai haddin tawatur sun ce, fitarsa ta kasance ce ranar Litinin kuma shigarsa Madina ta kasance ranar Litinin.”

Ibnu Hajrin ya ce: “Fitarsa daga Makka ta kasance ce ranar Alhamis, fitarsa daga kogon Hira kuma ta kasance a daren Alhamis.” (Fathul Bari, Mujalladi na 7 shafi na 237). Kamar yana nuna hakan a matsayin farkon tafiyar hijira.

Annabi (SAW) ya fita daga kogon Hira yana mai hijira da addininsa zuwa Madina tare Abubakar da Amir bin Fuhaira da Abdullahi bin Arikad Allaisi ya rika bin hanyoyi mabambanta don bad da sawu ga mushirikai. Kuma (SAW) ya isa kuba a daren 12 ga watan Rabi’ul Awwal ranar Litinin.

A kullum sai sahabbai sun fita suna dakon isowarsa (SAW) tun daga wayewar gari har zuwa rana ta yi zafi kafin su koma gidajensu.

To lokacin da Annabi (SAW) ya isa kuba rana ta yi tsananin zafi sun shiga gidajensu. Sai wani Bayahude ya gan shi, sai ya yi yekuwa cewa: “Ya ku taron Larabawa! Ga wanda kuke jira nan” Sai Musulmi suka fito suka marabce shi yana bisa taguwa har suka isa gidan Amru bin Auf suka sauka a ranar 12 ga Rabi’ul Awwal.


**{Legacy activities, comments etc counter: 934; topic series: 4; forum: MediaHausa; associated: 4- /*}