Tuba da istigfari (6)
An buga: Thu Feb 05, 2026 4:37 am
*Legacy Post Number 46 from MediaHausa
Topic: Tuba da istigfari (6)
Timeline: 2012-03-27 18:55:47
Tuba da istigfari (6)
A Rubuce Da Salihu Is’hak Makera
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Mai gamammiyar kyauta a nan duniya, Mai kebantacciyar kyauta a Lahira. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halitta, Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa da masu bin su da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka a ci gaba da darasinmu kan tuba da istigfari yau za mu dora ne daga falalar tuba da istigfari a cikin Alkur’ani, sannan mu ga falalarta a cikin Sunnah nan gaba:
Falalolin tuba da istigfari a cikin Alkur’ani Mai girma:
Na farko: Karbar tuba da yin gafara na daga cikin siffofin Allah Mai rahama:
Allah Madaukaki Ya ce: “Sai wadanda suka tuba, kuma suka gyara, kuma suka bayyana, to wadannan Ina karbar tuba kansu, kuma Ni ne Mai karbar tuba, Mai jin kai.” (k:2:160)
Ibn Jarir ya ce: kan “to wadannan Ina karbar tuba kansu,” yana nufin wadannan da suka yi abin da aka siffanta daga cikinsu, sune wadanda Nake karbar tubarsu, kuma Na sanya su a cikin ma’abuta komawa zuwa ga yi Min da’a da komawa zuwa da yardaTa. “Kuma Ni ne Mai karbar tuba, Mai jin kai.” Yana cewa ne Ni ne Mai dawo da zukatan bayiNa in dawo da ita zuwa gare Ni, In dawo da ita bayan ta juya baya daga yin Min da’a zuwa ga neman soyayyaTa.” (Tafsirud dabari, Mujalladi na 2 shafi na 60).
Kuma Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma da wadansu, sun yi furuci da laifinsu, sun hada aiki na kwarai da wani mummuna. Akwai tsammanin Allah Ya karbi tuba a kansu. Lallai Allah ne Mai gafara Mai jin kai.” (k:9:102).
As-Sa’adi ya ce: kan fadinSa Madaukaki: “Lallai Allah ne Mai gafara Mai jin kai.” Ma’ana Ya siffanta gafara da rahama wadanda ba mahalukin da bai sonsu. Kai hasali sama da kasa ba za su tabbata ba, in babu su. Domin da Allah Yana kama mutane da zaluncinsu da bai bar wata dabba a bayan kasa ba.” (Tafsirul Karimir Rahman, shafi na 350).
Kuma Allah Madaukaki Ya ce: “Shin ba su sani ba, cewa lallai Allah ne Yake karbar tuba daga bayinSa, kuma Yana karbar sadakokinsu, kuma lallai Allah ne Mai karbar tuba, Mai jin kai.” (k:9:104)
As-Sa’adi ya ce: “Ma’ana Allah ne Mai yawan gafara a kan masu tuba, duk wand ya tuba zuwa gare Shi, Zai karbi tubarsa, koda ya maimaita sabo bila adadin. Allah ba Ya gajiyawa da karbar tuba daga bayinSa, har sun gajiya da tuba zuwa gare Shi.” (Tafsirul Karimir Rahman, shafi na 351).
Kuma Allah Madaukaki Ya ce: “Ha. Mim. Saukar da Littafi daga Allah ne, Mabuwayi, Masani. Mai gafarta zunubi, kuma Mai karbar tuba Mai tsananin azaba, Mai wadatarwa, babu abin bautawa face Shi, zuwa gare Shi makoma take.” (k:40:1-3).
Wahabata Az-Zahili ya ce: “Sannan Allah Ya siffanta kanSa da siffofi shida da suka hada tsakanin alkawari da gargadi da kwadaitarwa da tsoratarwa: Sai Ya ce: “Mai gafarta zunubi, kuma Mai karbar tuba.” Ma’ana lallai Allah ne Mai gafarta zunubi wanda ya gabata ga masoyanSa, shin zunubin karami ne ko babba ne, a bayan tuba ko a gabani bisa sonsa, kuma mai karbar tuba ne matukar aka tuba.” (Tafsirul Munir, Mujalladi na 24 shafi na 73).
Na biyu: Allah Ya umarci bayinSa da tuba da istigfari:
Allah Madaukaki Ya ce: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku koma (tuba) zuwa ga Allah komawar gaskiya.” (k:66:8). Khurdabi ya ce: “(Allah) Ya yi umarni da tuba, kuma ita farilla ce ta aini (wani bai dauke wa wani) a kowane hali a kuma kowane zamani.” (Jami’u Li’ahkamil kur’an, Mujalladi na 18 shafi na 197).
Kuma Allah Madaukaki Ya ce: “Ku koma (tuba) zuwa ga Allah gaba daya, ya ku muminai, tsammaninku za su samu babban rabo.”
Khuradabi ya ce: “Umarni ne, kuma babu sabani a tsakanin al’umma kan wajibcin tuba, kuma ita farali ne na aini.” (Jami’u Li’ahkamil kur’an, Mujalladi na 12 shafi na 238).
Kuma Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma ka nemi Allah gafara. Lallai ne Allah Ya ksance Mai gafara, Mai jin kai.” (k:4: 106). Kuma Allah Madaukaki Ya sake cewa: “Sannan kuma ku malalo daga inda mutane suke malalowa. Ku nemi gafara ga Allah. Lallai Allah Mai gafara ne, Mai jin kai.” (k:2:199).
As-Sa’adi ya ce: “Allah Ya yi umarni da istigfari da yawaita ambatonSa lokacin kammala ayyukan Hajji. Kuma istigfarin don kuskuren da ya auku daga bawa ne yayin yin ibadarsa da kuma gazawar da ya yi a cikinta.” (Tafsirus Sa’adi, shafi na 92).
Kuma Allah Madaukaki Ya ce: “Saboda haka ka sani cewa babu abin bautawa face Allah, kuma ka nemi gafara ga zunubinka, kuma saboda muminai maza da muminai mata, kuma Allah Ya san majuyarku da mazauninku.” (k:47:19).
Ibnu Jarir Ad-dabari ya ce: “Ka roki Ubangijinka gafarar zunubanka da abin da ke haddasa su da kuma zunuban ma’abuta imani da kai na daga maza da mata.” (Tafsirud dabari, Mujalladi na 11 shafi na 318).
Kuma Allah Madaukaki Ya ce: “Idan taimakon Allah ya zo da cin nasara. Kuma ka ga mutane suna shiga addinin Allah kungiya-kungiya. To ka yi tasbihi game da gode wa Ubangjinka, kuma ka neme shi gafara, lallai Shi (Ubangijinka) Ya kasance Mai karbar tuba ne.” (k: 110:1-3). An karbo daga A’isha (RA) ta ce: “Manzon Allah (SAW) bai taba yin Sallah a bayan an saukar masa da surar “Iza ja’a nasrulllahi walfathu-Idan taimakon Allah ya zo da cin nasara.” face ya ce: “Subhanaka rabana wa bihamdika Allahumma agfirli.-ma’ana Tsarki ya tabbata gare Ka Ya Ubangijinmu, kuma godiya gare Ka. Ya Ubangiji Ka gafarta min.” Buhari da Muslim suka ruwaito.
Na uku: Tuba da istigfari yana daga cikin siffofin Annabawa da bayin Allah nagari:
Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma a lokacin da Musa ya je ga mikatinMu, kuma Ubangijinsa Ya yi masa magana, shi Musa ya ce: “Ya Ubanjinmu! Ka nuna mini in yi dubi zuwa gare Ka!” (Allah) Ya ce: “Ba za ka gan Ni ba, kuma amma ka duba zuwa ga dutse, to, idan ya tabbata a wurinsa, to, za ka gan Ni.” Sannan a lokacin da Ubangijinsa Ya kuranye zuwa ga dutsen, Ya sanya shi nikakke. Kuma Musa ya fadi somamme. To, a lokacin da ya farka, ya ce: “TsarkinKa ya tabbata! Na tuba zuwa gare Ka, kuma ni ne farkon muminai.” (k:7:143).
Mujahid ya ce: “Game da mas’alar dubi a duniya an ce: Ya yi tambaya ba tare da an yi masa izini ba, don haka ya tuba. Kuma an ce: Ya fada (tuba) a bisa jihar komawa zuwa ga Allah da yi maSa khushu’I a lokacin bayyanar ayoyin.” (Jami’u Li’ahkamil kur’an, Mujalladi na 7 shafi na 279).
Kuma Allah Madaukaki Ya ce: “Masu tuba, masu bauta, masu godewa, masu tafiya, masu ruku’i, masu tawali’u…” (k:9:112).
Ibnu Kasir ya ce: “Wannan siffar muminai ne wadanda Allah Ya sayi rayukansu da dukiyarsu daga gare su da wadannan siffofi masu kyau da dabi’u masu girma.” (Tafsirul kur’anil Azim, Mujalladi na 2 shafi na 374).
**{Legacy activities, comments etc counter: 809; topic series: 3; forum: MediaHausa; associated: 3- /*}