Shafin 1 na 1

Tuba da istigfari (7)

An buga: Thu Feb 05, 2026 4:41 am
by MediaHausa
*Legacy Post Number 49 from MediaHausa
Topic: Tuba da istigfari (7)
Timeline: 2012-03-27 18:59:45


Tuba da istigfari (7)

A Rubuce Da Salihu Is’hak Makera

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Mai gamammiyar kyauta a nan duniya, Mai kebantacciyar kyauta a Lahira. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halitta, Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa da masu bin su da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako.

Bayan haka a ci gaba da darasinmu kan tuba da istigfari yau za mu kammala bayani kan falalar tuba da istigfari a cikin Alkur’ani:

Na hudu: Kiran Annabawa da salihan bayi ga mutanensu don su tuba kuma su yi istigfari:

Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma zuwa ga Adawa Mun aika dan uwansu Hudu. Ya ce, “Ya ku mutanena! Ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bautawa face Shi. Ba ku kasance ba face kuna masu kirkirawa. Ya mutanena! Ba ni tambayarku wata ijara a kansa, ijarata ba ta zama ba face ga Wanda Ya kaga halitta. Shin fa ba ku hankalta? Ya mutanena! Ku nemi Ubangjinku gafara, sannan ku tuba zuwa gare Shi, zai saki sama a kanku tana mai yawan zubar da ruwa, kuma Ya kara muku wani karfi ga karfinku. Kuma kada ku juya kuna masu laifi.” (k:11: 50-52).

Sa’adi ya ce: kan ma’anar ayar “Wato ku nemi gafarar Ubangijinku kana bin da ya gabata dga gare ku, sannan ku koma zuwa gare shi cikin abin da ya saura na rayuwarku ta hanyar komawa ta gaskiya da juyawa zuwa gare Shi.” (Tafsiru Sa’adi, shafi na 383).

Kuma Allah Madaukaki Ya sake cewa: “Kuma zuwa ga Samudawa (an aika) dan uwansu Salihu. Ya ce ya mutanena! Ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bautawa face Shi. Shi ne Ya kaga halittarku daga kasa, kuma Ya sanya ku masu yi kyarkyara a cikinta. Sai ku neme shi gafara, sannan ku tuba zuwa gare shi. Lallai Ubangijina Makusanci ne Mai karbawa.” (k: 11: 61).

Kuma Madaukaki Ya fadi Yana hakaito kissar Annabi Shu’aibu (AS): “Kuma ku nemi Ubangijinku gafara, sannan ku tuba gare zuwa Shi, lallai Ubangijina Mai jin kai ne, Mai nuna soyayya.” (k: 11: 90).

Sa’adi cikin kawo fa’idojin kissar Annabi Shu’aibu (AS) ya ce: “Daga cikinsu akwai cewa: lallai mai tuba daga zunubi ana shafe masa zunubinsa ne a yafe masa. Domin Allah Yana sonsa kuma Yana nuna masa kauna. Don haka ba za a lura da fadin mai cewa “Idan mai tuba ya tuba iyaka a gafarta masa a koma kansa da afuwa, amma komawa da so da kauna ba a lissafawa a ciki.” Domin Allah Madaukaki Ya ce ne: “Ku nemi Ubangijinku gafara sannan ku tuba zuwa gare Shi. Lallai Ubangijina Mai jin kai ne, Mai nuna soyayya.” (Tafsirus Sa’adi shafi na 389).

Na biyar: Bayanin samakon tuba a duniya da Lahira:

a) Soyayyar Allah ga masu tuba:

Allah Madaukaki Ya ce: “Lallai Allah Yana son masu tuba, kuma Yana son masu tsarkakewa.”

b) Samun gafara daga Allah Madaukaki:

Allah Madaukaki Ya ce: ““Kuma lallai Ni, hakika Mai gafara ne ga wanda ya tuba, kuma ya yi imani, kuma ya aikata aikin kwarai, sannan kuma ya nemi shiryuwa” (k: 20: 82)

Ibnu Kasir ya ce kan fadinSa: “Kuma lallai Ni, hakika Mai gafara ne ga wanda ya tuba, kuma ya yi imani, kuma ya aikata aikin kwarai, sannan kuma ya nemi shiryuwa.” Ma’ana duk wanda ya tuba zuwa gare Ni, Zan gafarta masa kowane zunubi. Kuma har Madaukaki Ya gafarta wa wanda ya bauta wa maraki daga Bani Isra’ila. FadinSa “ya tuba” ma’ana ya koma daga (ya bar) kafirci ko shirka ko sabo ko munafunci. (Tafsiru Ibn Kasir, Mujalladi na 3 shafi na 169).

c- Samun babban rabo a duniya da Lahira:

Allah Madaukaki Ya ce: “Sai wanda ya tuba kuma ya yi imani, kuma ya aikata aiki na kwarai, to, wadancan Allah Yana musanya miyagun ayyukansu da masu kyau. Allah Ya kasance Mai gafara, Mai jin kai.” (k:25:70).

Game da ma’anar “Ku tuba zuwa ga Allah gaba daya.” Sa’adi ya ce: saboda mumini, imaninsa yana kiransa nw zuwa ga tuba, sannan sai Allah Ya alkanta hakan da samun babban rabo inda Ya ce: “Tsammaninku ku samu babban rabo.” Don haka babu hanyar samun babban rabo sai ta tuba, tuba kuma ita ce dawowa daga rakiyar abin Allah Yake ki a fili da boye zuwa ga abin da Yake so a fili da boye.” (Tafsirus Sa’adi, shafi na 567).

d) Musanya mummunan aiki da kyakkyawa:

Allah Madaukaki Ya ce: “: “Sai wanda ya tuba kuma ya yi imani, kuma ya aikata aiki na kwarai, to, wadancan Allah Yana musanya miyagun ayyukansu da masu kyau. Allah Ya kasance Mai gafara, Mai jin kai.” (k:25:70).

Khurdabi ya ce: “Nuhasu ya ce: “Me ya fi dadin ji daga wanda da aka ce za a rubuta masa imani a gurbin a kafircinsa, a gurbin sabo a rubuta mai da’a!” Mujahid da Dahhaku sun ce: “Allah zai musanya musu shirki da imani.” Kuma an ruwaito irinsa daga Alhasan.

Khurdabi ya ce: “Ba za a nesanta shi cikin karimcin Allah ba, idan tubar bawa ta inganta a maye gurbin kowane mummunan aiki da kyakkyawa. Domin hakika Mai tsira da amincin Allah ya ce: “Ka bi bayan mummunan aiki da kyakkyawa sai ya shafe shi, kuma ka yi mu’amala da mutane da kyakkyawan hali.” Tirmizi ya ruwaito.

Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce: “Lallai ni na san dan Aljanna na karshe da zai shiga Aljanna da dan wuta na karshe da zai fita daga gare ta. Shi ne mutumin da za a zo da shi Ranar kiyama sai a ce:”Ku bijiro da kananan zunubansa, kuma ku dauke manyansu.” Sai a bijiro da kananan zunubansa sannan a ce: “Ka aikata kaza a ranar kaza da kaza da kaza.” Sai ya ce, “na’am” ba ya da ikon da zai musanta, alhali yana mai tsoron kada a bijiro da manyan laifuf*****ansa. Sai a ce masa: “To a gurbin kowane mummunan aiki a maye shi da kyakkyawa.” Sai ya ce: “Ya Ubangiji! Hakika na aikata wasu abubuwan da ban gansu a nan ba.” Hakika na ga Manzon Allah ya yi dariya (murmushi) har hakoransa na gaba suka fito.” Buhari ya ruwaito, (a duba Jami’u Li’ahkamil kur’an, Mujalladi na 13 shafi na 78).

Wato saboda jin cewa an maye gurbin munanan ayyukan da kyawawa sai bawa ya so a gabato da manyan laifuf*****ansa domin a mayar da su kyawawa ayyukansa su karu.

e) Kankare munanan ayyuka da shiga Aljanna:

Allah Madaukaki Ya ce: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku koma zuwa ga Allah (tuba) komawar gaskiya, mai yiwuwa Ubangjinku Ya kankare muku miyagun ayyukanku, kuma Ya shigar da ku gidajen Aljanna koramu na gudana a karkashinsu a ranar da Allah ba Ya kunyatar da Annabi da wadanda suka yi imani tare da shi. Haskensu yana tafiya a gaba gare su da jihohin damarsu, suna cewa, “Ya Ubangijinmu! Ka cika mana haskenmu, kuma Ka yi mana gafara. Lallai Kai a kan dukkan komai Mai iko yi ne.” (k:66:8).
S’adi ya ce: “Hakika Allah Ya yi umarni da tuba ta gaskiya a cikin wannan aya, kuma Ya yi alkawari kanta da kankare munanan ayyuka da shiga Aljanna da samun babban rabo.” (Tafsirus Sa’adi shafi na 874).

f) Hana aukuwar azaba a duniya:

Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma Allah bai kasance Yana yi musu azaba ba, alhali kuwa kana cikinsu, kuma Allah bai kasance Mai yi musu azaba alhali kuwa suna yin istigfari.” (k:8:33).


**{Legacy activities, comments etc counter: 760; topic series: 3; forum: MediaHausa; associated: 3- /*}