Wani Abu Kan Hakkin Makwabci A Musulunci
An buga: Thu Feb 05, 2026 5:01 am
*Legacy Post Number 65 from MediaHausa
Topic: Wani Abu Kan Hakkin Makwabci A Musulunci
Timeline: 2012-05-01 05:17:41
Wani Abu Kan Hakkin Makwabci A Musulunci
A Rubuce Da Salihu Is’hak Makera
’Yan uwa Musulmi assalamu alaikum warahamatullah! Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai tarin albarka, muna fata ’yan darussan da muke gabatarwa suna amfanarmu.
Bayan haka, a yau kuma cikin ikon Allah za mu duba wani maudu’i ne mai girma da imanin kowannenmu ke ta’allaka da shi. Wannan maudu’i shi ne na hakkin makwabci a Musulunci. Hakika mutane da yawa sun jahilci wannan hakki ko suna daukarsa da rashin muhimmanci, alhali Allah Madaukaki Ya gwama shi tare da bauta maSa a cikin LittafinSa Mai girma. Kuma Manzon Allah (SAW) ya jingina imani ga kiyaye shi kamar yadda za mu gani a nan gaba.
Allah Ya halicci mutum Ya sanya shi mai son zama tare da wadansu, yana son rayuwa tare da ’yan uwansa mutane yana son cudanya da gogayya da su. Yana son ya rika natsuwa tare da su, mutum ba a halicce shi don ya rayu shi kadai ba, yana son ya rayu ne a tsakiyar alkarya ko birni ko tsakiyar mutane. To wadannan abokan zama nasa su ne fa ake kira makwabta. Ashe mutanen da suke ganin su kadai ya kamata su zauna a garinsu ko unguwarsu ba su fahimcima’ana da manufar halittar dan Adam ba.
Don haka makwabci shi ne mutumin da kuke zaune a gida daya kuna haya ko wanda gidansa ke kusa da naka, har zuwa wani adadi na gidaje a gefn dama da hagu na gidanka. Sannan makwabci yana iya kasancewa mutumin da kuke zaune kusa da juna a wuraren kasuwanci ko sana’a ko aikin kamfani ko na gwamnati.
To abu ne dab a zai yiwu ba a samu rayuwar jama’a mabambanta ya alla bambancin kabila ne ko addini ta daidaita cikin jin dadi da lumana sai an samu alaka mai kyau a tsakanin mutane. Sai an samu kyakkyawar alaka a tsakanin makwabta da ’yan uwa da ’ya’ya da sauran jama’ar da ake zaune tare.
Don haka ne Allah cikin hikimarSa ya saukar wa Manzon Allah (SAW) da cewa: “Kuma ku bauta wa Allah kuma kada ku hada wani da Shi, kuma ga mahaifa ku yi kyautatawa, kuma (ku kyautata) ga ma’abucin zumunta da marayu da matalauta da makwabci ma’abucin kusanta da makwabci manisanci da aboki a gefe da dan hanya...” (k:4:36).
Wannan aya ta gwama bautar Allah da kyautata wa iyaye da ’yan uwa da marayu da matalauta da makwabta da abokan tafiya. Wannan ya nuna kyautata wa makwabci ibada ne da ake samun lada a kai, sannan rashin kyautata masa laifi ne da ake samun zunubi a kai.
Idan Musulmi suka yi aiki da wannan aya za su iya samar da al’umma mai soyayya da girmama juna da taimakon juna koda akwai bambancin addini a tsakaninsu da abokan zamansu. Ayar ta yi magana kan makwabcin da kake da zumunta da shi ko dangantaka kuma ta yi magana kan makwabcin da babu dangantaka tsakaninka da shi dangantaka ta jini da nasaba ko ta addini. Dukkan wadannan makwabta an wajabta maka kyautata musu kamar yadda ayar ta yi magana a kai.
Wannan yana nuna cewa al’ummar Musulmi al’umma ce mai karfafa zaman tare, tunda ga shi Allah Ya umarce mu da girmama makwabci da kyautata masa kuma Ya haramta mana cutar da shi da firgita shi.
Manzon Allah (SAW) ya koyar da mu girmama makwabci inda ya sanya hakan cikin siffofin imani kuma ya karfafa haka cikin fadinsa (SAW): “Wanda ya yi imani da Allah da Ranar Lahira ya girmama bakonsa, kuma wanda ya yi imani da Allah da Ranar Lahira ya girmama makwabcinsa...” A wata ruwayar kuma ya ce: “Wanda ya yi imani da Allah da Ranar Lahira kada ya cutara da makwabcinsa...”
A wadannan hadisai Manzon Allah (SAW) ya sanya girmama makwabci a cikin siffar mai imani da Allah da Ranar Lahira, don haka duk wanda ya yi imani da Allah kada ya cutar da makwabcinsa a dukiyarsa ko mutuncinsa ko martabarsa kai koda iskar da yake shaka kada ya toshe masa ta hanyar yin ginin da zai fi nasa tsawo. Kada ya yi masa ta’adda ta fadin mummunar kalma ko cutarwa ta jiki ko takura wa rayuwarsa ko sace masa dukiya. Domin yin hakan zai canja soyayyar da ta kamata a samu a tsakaninku ta koma kiyayya da tsana, kuma don kada ka kuntata wa rayuwarsa da jin dadinsa.
Addininmu na Musulunci yana son dan Adam da alheri da sa’ada, don haka bai tsaya kan hakkin makwabci na hana cutar da shi kadai ba, har ma yana daga cikin hakkin makwabci, mu taimaka masa wajen biyan bukatunsa. Mu ziyarce shi a gidansa mu taya shi murna ko bakin ciki idan sun same shi. Mu tambaya idan ba mu gan shi ba, mu gaida shi idan ba ya da lafiya, mu fara gaida shi idan muka hadu da shi, kuma kada mu hana shi duk abin da muke da ikon yi masa idan yana bukata.
Kai ta kai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Bai yi imani da ni ba, wanda ya kwana a koshe, amma makwabcinsa yana jin yunwa.”
Kuma daga cikin hakkin makwabci har wa yau, akwai bukatar mu rika yafe masa, mu rika yi masa sassauci kan kuskuren da ya yi, mu rika hakuri a kan cutarwarsa, kuma kada ya zamo mu ne masu jawo matsala a tsakaninmu da makwabci, kada mu bar wata kafa ta adawa a tsakaninmu, a’a mu yi kokarin warware duk wata mushkila da ta auku a tsakaninmu da shi ta kyakkyawar hanya.
Bari mu nanata cewa wadannan hakkoki na makwabci ba su takaita kan makwabci Musulmi ba, a’a sun shafi Musulmi da wanda ba Musulmi ba, matukar zama ya hada ku a gida ko a wurin sana’a, ko kuma tafiya ta hada ku. “Wanda ya yi imani da Allah da Ranar Lahira ya girmama (mutunta) makwabcinsa...”
Wasallallahu Ala Sayyidina Muhammad wa alihi.
**{Legacy activities, comments etc counter: 940; topic series: 4; forum: MediaHausa; associated: 4- /*}