Shafin 1 na 1

Yadda Ake Komawa Ga Allah

An buga: Thu Feb 05, 2026 5:06 am
by MediaHausa
*Legacy Post Number 68 from MediaHausa
Topic: Yadda Ake Komawa Ga Allah
Timeline: 2012-05-01 05:27:20


Yadda Ake Komawa Ga Allah

A Rubuce Da Salihu Is’hak Makera

Duk da cewa a wani lokaci can baya mun yi magana kan tuba da istigfari kuma makonni biyu da suka gabata mun yi kokarin amsa tambayar shin Allah Yana sonmu? A yau mun sake duba darasin tuba ko komawa ga Allah ne, don alfanun hakan gare mu musamman a wannan lokaci da muke fuskantar jarrabawar da ba mu taba ganin irinta ba.

Mu dauki wani abu da ya faru da Bani Isra’ila a karkashin jagorancin Annabi Musa (AS) a lokacin da Fir’auna ya dauki matakin karshe na gamawa da su.

Mu rika kallon ga Annabi Musa (AS) yana jagorantar tsofaffi maza da mata da kananan yara da suke gudun darkakewar Fir’auna, ga su nan sun nufo bakin teku. Ba su da jirgin ruwa, ba su da kwale-kwale da za su hau su gudu. Ga Fir’auna ya taso su a gaba ba su da makamin da za su iya juyawa su fusknaci rundunar Fir’auna. Ga su nan sun iso bakin teku ruwa iya kallo, ga shi sun waiwaya baya ga Fir’auna cike da fushi, mayakansa rike da miyagun makamai, sukwane kan dawaki sun nufo su. Ganin halin tsaka mai wuya da suke fuskanta sai suka koka ga Annabi Musa (AS): “Sa’an nan a lokacin da jama’a biyu suka ga juna, sai abokan Musa suka ce, “Lallai ne mu, hakika, wadanda ake riska ne.” (k:26:61).

To amma Annabi Musa (AS) ya san Allah ba zai bari a shafe da’awar Musulunci a bayan kasa ba. Sai ya ba su amsar da take nuna karfin imani irin na Annabawa da Manzanni (AS):

“Ya ce “Kayya! Lallai ne Ubangijina Yana tare da ni, kuma zai shiryar da ni (hanyar tsira).” (k:26:62).

Nan take sai Allah Ya umarci Annabi Musa (AS) cewa: “Ka doki teku da sandarka.” Sai teku ta tsage, kowane tsagi ya kasance kamar falalen dutse mai girma. Kuma Muka kusantar da wadansu mutane (su Fir’auna). Kuma Muka tserar da Musa da wadanda suke tare da shi gaba daya. Sannan Muka nutsar da wadancan (su Fir’auna).” (k:26: 63-66).

A lokacin da Fir’auna ya ga kansa a tsakiyar teku ya tabbata mutuwa ta zo masa sai ya ce: “Na yi imani cewa, hakika, babu abin bautawa face wannan da ba Banu Isra’ila suka yi imani da Shi. Kuma ni ina daga Musulmi.” (k:10:90).

Ibnu Abbas ya ce a ranar da Fir’auna ya fada cikin teku kuma ya fahimci zai mutu, sai Mala’ika Jibril ya zo ya rika rika watsa masa tabo a fuska yana cika masa baki da shi, don kada ya samu damar rokon rahamar Allah, wanda da ya roka da an ba shi.

Kuma Allah Ya fada wa Fir’auna da sauran mutanen da ba za su tuba su koma ga Allah ba, sai sun ga mutuwa cewa: “Ashe a yanzu (ne za ka tuba ka yi imani)! Alhali kuwa hakika ka saba a gabani, kuma ka kasance daga masu barna?” (k:10:91).

Domin a Musulunci tuba a koma ga Allah abu ne mai sauki wato shi ne a nemi gafarar Allah da harshe da zuciya kamar yadda Allah Madaukaki Ya nuna: “Kuma wanda ya aikata cuta ko kuwa ya zalunci kansa, sannan ya nemi Allah gafara, zai samu Allah Mai gafara ne, Mai jin kai.” (k:4:110).

Sannan Abu Huraira ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Na rantse da wanda raina yake hannunSa, da za a ce ba ku yin kuskure da Allah Ya shafe ku duka Ya kawo wadansu mutanen da za su yi kuskure su roki Allah gafara don Ya gafarta musu.” Muslim ya ruwaito.

Don haka bari mu sake dubi a takaice ga wasu ayoyi da ke magana kan istigfari da komawa ga Allah, domin mu ga irin irin yadda magabata suke daukar zunubi da ka’idojin karbar tuba da yadda ya kamata a yi addu’a:

1. Istigfari dabi’a ce ta mutanen da Allah zai ba su nasara ko babban rabo.

Allah Madaukaki Ya ce: “(Sai ’yan wuta suka ce), Ya Ubangijinmu! Ka fitar da mu daga gare ta, sannan idan mun koma (ga aikata barna), to, lallai ne, mu ne masu zalunci. Ya ce, “Ku tafi (da wulakanci) a cikinta. Kada ku yi Mini magana. Lallai wadansu kungiyoyi daga bayiNa sun kasance suna cewa, “Ya Ubangijinmu! Mun yi imani, sai Ka gafarta mana, kuma Ka yi mana rahama, kuma Kai ne Mafi alherin masu tausayi. Sai kuka rike su leburori (wulakantattu)”. (k: 23;107-110). Sai Allah Ya ce: “Lallai ne, Ni Ina saka musu a yau, saboda abin da suka yi wa hakuri. Domin lallai ne, su, su ne masu samun babban rabo.” (k:23:111).

2. Istigfari yana bude dukkan kofofin alheri a nan duniya da Lahira.

A lokacin Halifancin Amirul Mumina Umar bin Haddabi (RA) an samu kamfan ruwa a Madina. Bayan an yi shelar sallar rokon ruwa, sai Umar (RA) ya hau mumbari a lokacin hudubarsa ya fi karanto ayoyin da suka yi magana ne kan istigfari. A wancan rana ya karanto kalmomin Allah game da abin da Annabi Nuhu (AS) ya fada ga mutanensa: “Na ce, “Ku nemi gafara daga Ubangijinku, lallai ne Shi Ya kasance Mai gafara ne. Ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai bubbuga. Kuma Ya yalwata muku game da dukiya da ’ya’ya, Ya sanya muku (albarka) ga gonaki, kuma Ya sanya muku koguna.” (k: 71:10-12).

3. Istigfari yana nuna mutanen da suka fi soyuwa a wurin Allah.

Abu Huraira (RA) ya ce: “Ya ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Na rantse da Allah, Ni ina rokon Allah gafara da tuba a gare Shi a yini daya fiye da sau saba’in.”

Sannan labarin Annabi Ayyuba (AS) na cewa: “(Muka ce), Kuma ka riki wani kulla da hannunka, ka yi duka da ita, kuma kada ka karya rantsuwarka. Lallai Mu, Mun same shi mai hakuri. Madalla da bawa, shi. Lallai shi mai mayar da al’amari (tuba) ga Allah ne.” (k:38:44).

4. Ganin girma da munin zunubi

Hadisin Ma’iz yana nuna yadda ake istigfari da yadda gaskiyar tuba ga Allah take.

Abin da ya faru Ma’iz ya aikata zina kuma ya zo ga Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ya Manzon Allah, na yi zina!” Sai Manzon Allah ya kawar da kai daga gare shi, ta yadda Ma’iz zai hakura ya tserar da kansa daga haddi, amma sai Ma’iz ya ci gaba da komawa ta gaban fuskar Annabi (SAW) yana maimaita “Na yi zina! Na yi zina!”

Da Ma’iz ya yi ta nanata fadin haka sai Manzon Allah (SAW) ya tambaye shi: “Shin kai mahaukaci ne?”

Ya ce: “A’a.” “Shin ka sha giya ne (ya nemi wani ya sunsuna bakinsa)?” Ya ce, “A’a.”
Ya ce: “Kuma ka shige ta?” Ya ce: “Eh.”

Sai Manzon Allah (SAW) ya tambaye shi a hankali, “To wai me kake so da kake bayyana wannan abu?” Sai Ma’iz ya ce: “Ina son ne ka tsarkake ni!”

Irin wannan karfin imani da ya sa Ma’iz irin wannan tuba ga Allah da za a raba shi da ya ishi dukkan mutane Madina, kamar yadda karshen Hadisin ya nuna.

Sannan Hilal bin Sa’ad ya ce: “Kada ka dubi kankantar zunubinka, ka dubi girman wanda kake saba maSa (Allah)!” 5. ka’idojin tuba ta gaskiya

Anas (RA) ya ruwaito Manzon Allah (SAW) ya ce: “Dukkan ’yan Adam masu kuskure ne. Amma mafi alherin masu kuskure su ne masu tuba.” Tirmizi ya ruwaito.

Imam Nawawi (RH) ya rubuta cewa ana neman gafara kan kowane zunubi. Idan wannan zunubi tsakanin bawa da Ubangiji ne, bai shafi hakkin wani ba, to yana da ka’ida uku na karbar tuba:

1. Daina aikata wannan zunubi. 2. Yin nadama kan abin da ya gabata. 3. Da niyyar ba za a koma ga aikata wannan zunubi ba.

Idan aka rasa daya daga cikin wadannan ka’idoji to akwai nakasu ga wannan tuba. Idan kuma akwai hakkin wani to sharadi na hudu zai shigo. Wato mutum ya mayar wa mai hakki hakkinsa. Misali idan ya saci kayansa ne ya mayar masa. Idan ya mare shi ya ba shi dama ya rama, ko ya nemi ya yafe masa. Idan ya zage shi ne ya nemi ya yafe masa.

A karshe ga wata kissa nan don nazari: Wata rana bayan an tafka ruwan sama Hisham bin Hasan na tafiya a bayan Al’ala bin Ziyad a wata hanya mai tabo a kauyensu. Sai ya lura Ziyad yana kauce wa wurin santsin da ke tare da tabon, sai wani ya tunkude shi har santsa ya ja takalminsa ya zame. Santsi ya debi Ibnu Ziyad zuwa daya gefen.

Bayan sun isa gida sai Ibnu Ziyad ya juyo ga Hisham ya ce: “Yadda muke kauce wa tabo da santsi a kan hanyarmu ta zuwa gida haka ya kamata Musulmi ya rika kauce wa saba wa Allah a daukacin tafiyar da yake yi zuwa Lahira. Kuma kamar yadda ka ga santsi ya ja ni, haka santsin zunubi take jan mutum lokacin da ya fada cikinsa, ya yi ta jansa yana dulmiyar da shi yana dada nutsewa.”
Allah Ya tsare mu.


**{Legacy activities, comments etc counter: 956; topic series: 4; forum: MediaHausa; associated: 4- /*}