Topic: Ya Zan Habaka Son Manzon Allah (SAW) A Zukatan 'Ya'yana? Maganin Bash!
Timeline: 2012-05-13 05:45:28
A Rubuce Da Nuura Abdullahi Madina
Ya Zan Habaka Son Manzon Allah (SAW) A Zukatan 'Ya'yana? Maganin Bash!
Daya daga cikin manyan dalilin da suka sa arnan duniya suka tashi haikan wurin cin zarafi da wulakanta Annabinmu abin kaunarmu (SAW) shi ne su raunana imaninmu da shi da soyayyarsa a cikin zukatanmu, don sun san raba al’umma da annabinta shi ne hanya mafi sauki ta sakwarkwatata, da gamawa da ita,
Don haka wajibi ne iyaye su tashi da gaske wurin habaka kauna da soyayyar manzon Allah (SAW) a zukatan ‘ya’yansu, ta yadda duk wani abin da abokan gaba za su fada akansa, ba zai girgiza imaninsu da kaunarsu gareshi ba.
Wasu daga cikin hanyoyin da iyaye za su iya bi don cimma wannan manufa su ne:
1. Sanar da su tarihinsa (SAW)
2. Tarbiyyantarsu akan sunnarsa, ta yadda duk abin da ya yi a rika sa su suna yi, kuma a rika gaya musu haka Annabi ya yi
3. A koya musu duk lokacin da suka ji an ambace shi su yi masa salati, haka nan a koya musu su rika yawaita yi masa salati a daren juma’a da ranar juma’a
4. A rika yi musu tarihin annabi da yara (kamar yaran da suka tashi ko suke zuwa gidansa (Irin jikokinsa Hasan da Husaini. Ibn Abbas, Anas…) tare da nuna musu yadda annabi yake son yara
5. Haddatar da su hadisan manzon Allah (SAW)
6. Wani lokaci iyaye su yi wa ‘ya’yansu wata kyauta sai su gaya musu cewa Annabi (SAW) shi ya ce a rika kyautata musu.
7. Koya musu son Ahlul baiti da sahabbabn manzon Allah (SAW)
Da shauran hanyoyi da za su tabbatar da wannan manufa wadanda ba su sabawa shari’a ba.
‘Yan uwana iyaye mu tuna cewa aiki da sunnar annabinmu, abin kaunarmu (SAW) ita ce hanya mafi sauki ta hhoras da ‘ya’yanmu wannan ibada mai girma.
MAGANIN BASHI!
Wata rana Annabi (SAW) ya shiga masallaci, sai ya yi kicibis da wani mutumin Madina ana ce masa “Abu Umama” sai Annabi (SAW) ya ce: Abu Umama! ya na gan ka a masallaci a zaune, ga shi kuwa yanzu ba lokacin sallah ba ne?! Sai ya ce” “Bakin ciki, da BASUSSUKA ne suka yi min katutu ya manzon Allah!” Sai Annabi (SAW) ya ce: Me zai hana in koya maka wata magana, da in dai ka fade ta Allah zai ya ye maka bakin cikin da yake damun ka, kuma ya biya maka bashin da yake kanka!” Sai ya ce: Godiya nake ya manzon Allah!” Sai ya ce masa: “Duk safiya da maraice ka rika yin wannan addu’a:
«اللَّهُمَّ إِنِّى أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْهَمِّ وَالْحَزَنِ
وَأَعُوذُ بِكَ مِنَ الْعَجْزِ وَالْكَسَلِ وَأَعُوذُ بِكَ مِنَ الْجُبْنِ
وَالْبُخْلِ وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ غَلَبَةِ الدَّيْنِ وَقَهْرِ الرِّجَالِ»
“ALLAHUMMA INNI A’UZU BIKA MINAL HAMMI WAL HAZANI, WA A’UZU BIKA MINAL AJZI WAL KASALI, WA’A UZU BIKA MINAL JUBNI WAL BUKHLI, WA A’UZU BIKA MIN GALABATIDDAINI WA QAHRIRRIJALI”
Ma’ana” Ya Allah ina neman tsarinKa daga bakin ciki, ina neman tsarinKa daga gajiyawa da kasala, ina neman tsarinKa daga tsoro, ragwanta da rowa, ina neman tsarinKa kar BASHI ya kai ni kasa, ko mazaje su ga bayana”
Wannan sahabi –Abu Umama- ya ce: “Sai na yi yadda Annabi (SAW) ya ce na yi, sai kuwa Allah ya yaye min bakin cikin da ke damuna, kuma ya biya min BASUSSUKAN da suke kaina.
Baya ga addu’a, akwai wasu abubuwa da za su taimaka wurin tseratar da mutum daga masifar bashi da izinin Allah. Ga wasu daga ciki:
(1)Ya tuba daga akidar cin bashi in dai yana da ita. Da yawan hausawa suna da akidar cin bashi koda ba lalurar hakan, shi ya sa ake yi wa malam bahaushe kirari da: “Bahaushe mai ban haushi; NA TANKO MAI KAN BASHI” Irin wadanda wannan akida ta cin bashi ta yi musu katutu a zuciya ko kusa ko alama ba sa fargabar cinsa. Amsar da suke yawo da ita kullum a aljihu ko da za su yi karo da mai yi musu nasiha gameda wannan mummunar akida ita ce: “AI SHI BASHI HANJI NE YANA CIKIN KOWA!”
Talauci: Daga cikin manyan abubuwan dake janyo shi akwai jahilci, da rashin sana’a sai a dage wurin neman ilimi komai wahala; don “bayan wuya sai dadi” kuma a nemi sana’ar yi don a dogara da kai. Sana’a tana daga cikin maganin matsalolin da za’a fada a lamba (3,4).
Akidar “Allah ya ba ku mu samu” a tuba a rungumi akidar “Allah ya ba mu, mu ba ku”
“Tsammanun wa rabbuka “wai malam ya ki noma don zakka” ya daure ya gyara gonarsa.
“Ba ki da gashin wance, ki ce sai kin yi kitson wance” Ma’ana mutum ya dauki rayuwar da ta fi karfinsa, ko ya rika dorawa kansa abin da ba shi da hali, kamar cin bashi saboda ramuwar biki, yin anko, mallakar waya bayan ba halin rike ta, yin aure ko kari bayan ba halin yin hakan. Wata baiwar Allah ta kawo kukunta wurin malam Ja’afar Allah ya jikan sa cewa mijinta ya kara aure amma ko inda zai sa matar babu; don haka da ita uwar gidan gami da ’ya’yanta da amaryar hade da shi kansa mai gidan duk a daki daya suke kwana!!! Kullum in sun yi masa korafi sai ya ce zai kokari ya kama wa amaryar gidan haya! dss.
Tsadar kayayyaki[/b] don haka gwamnati da ’yan kasuwa, su taimaka wurin rage wannan matsala.
Abu Huraira (R.A) ya rawaito cewa: (a farkon lamari) Idan aka kawo mamaci don Annabi (SAW) ya yi masa sallah, sai ya tambaya: “Shin ya bar abin da za’a biya masa bashi da shi”? Idan aka ce “ee” sai ya yi masa sallah, idan aka ce “a’a” sai ya ce da ragowar musulmi ku yi wa sahibinku sallah. Bayan an yi yake-yake (an samu wadata) sai ya ce: “Ni ne mafi cancantar Muminai daga kawukansu (daga yau) wanda duk ya mutu ya bar bashi daga muminai, to (ya komo kaina) ni zan biya, wanda kuma ya bar dukiya ta magadansa ce” (Bukhari da Muslim) Allah ya karawa Annabi daraja.
**{Legacy activities, comments etc counter: 1449; topic series: 8; forum: MediaHausa; legacy score: 10; legacy ratings: 2; rating_ip: ***.*14.31.188; associated: 8- /*}