Kuma Wanda Ya saukar da ruwa daga sama, a kan wani gwargwado, sai Muka rãyar da
gari matacce game da shi. Kamar haka nan ake fitar da ku (daga kabari).
Domin ku daidaitu a kan bãyansa, sa'an nan ku tuna ni'imar Ubangijinku a lõkacin
da kuka daidaita a kansa kuma ku ce, "Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya hõre mana
wannan alhãli kuwa ba mu kasance mãsu iya rinjãya gare Shi ba.
Alhãli kuwa idan an bãyar da bushãra ga ɗayansu da abin da ya buga misãli da shi
ga Mai rahama, sai fuskarsa ta yini tanã wadda aka baƙanta launinta, kuma yanã
cike da baƙin ciki.
Kuma suka mayar da malã'iku ('yã'ya) mãtã, alhãli kuwa sũ, waɗanda suke bãyin
(Allah) Mai rahama ne! Shin, sun halarci halittarsu ne? zã a rubũta shaidarsu
kuma a tambaye su.
Kuma kamar haka, ba Mu aika wani mai gargaɗi ba a gabãninka, a cikin wata
alƙarya, fãce mani'imtanta sun ce, "Lalle mũ, mun sãmi ubanninmu a kan wani
addini kuma lalle mũ, mãsu kõyi nea kan gurãbunsu."
(Sai mai gargaɗin) ya ce: "Shin, ban zo muku da abin da ya fi zama shiriya daga
abin da kuka sãmi ubanninku a kansa ba?" Suka ce, "Lalle mũ dai mãsu kafirta ne
game da abin da aka aiko ku da shi."
Shin, sũ ne ke raba rahamar Ubangijinka? Mũ ne, Muka raba musu abincinsu a cikin
rãyuwar dũniya, kuma Muka ɗaukaka waɗansunsu a kan waɗansu da darajõji dõmin
waɗansunsu su riƙi waɗansu lẽburori kumarahamar Ubangijinka (ta Annabci ), ita
ce mafificiya daga abin da suke tãrãwa.
Kuma bã dõmin mutane su kasance al'umma ɗaya ba, lalle ne, dã Mun sanya wa mãsu
kãfircẽ wa Mai Rahama, a gidãjensu, rufi na azurfa, kuma da matãkalai, ya zama a
kanta suke tãƙãwa.
Har a lõkacin da (abõkin Shaiɗan) ya zo Mana (ya mutu) sai ya ce: (wa Shaiɗan)
"Dã dai a tsakãnina da tsakãninka akwai nĩsan gabas da yamma, sabõda haka, tir
da kai ga zama abõkin mutum!"
Kuma Fir'auna ya yi kira a cikin mutãnensa, ya ce: "Ya mutãnẽna! Ashe mulkin
Masar bã a gare ni yake ba, kuma waɗannan kõguna sunã gudãna daga ƙarƙashĩna?
Ashe, ba ku gani ba?"
Kuma suka ce: "Shin, gumãkanmu ne mafĩfĩta kõ shi (¦an Maryama)?" Ba su buga
wannan misãli ba a gare ka fãce dõmin yin jidãli. Ã'a, sũ mutãne nemãsu husũma.
Kuma a lõkacin da Ĩsã ya jẽ da hujjõji bayyanannu, ya ce: "Lalle ne nã zo muku
da hikima kuma dõmin in bayyana muku, sãshen abin da kuke sãɓã wa jũna acikinsa,
sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'a."
Anã kẽwayãwa a kansu da akussa na zĩnãriya da kõfuna, alhãli kuwa a cikinsu
akwai abin da rãyuka ke marmari kuma idãnu su ji dãɗi, kuma kũ, a cikinta
(Aljannar), madawwama ne.