1st Ayah 1 الأية ١الأوليبِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
طسم
Ta-seen-meem
Hausa
¦. S̃. M̃.
|
Ayah 26:2 الأية
تِلْكَ آيَاتُ الْكِتَابِ الْمُبِينِ
Tilka ayatu alkitabialmubeen
Hausa
Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne.
|
Ayah 26:3 الأية
لَعَلَّكَ بَاخِعٌ نَّفْسَكَ أَلَّا يَكُونُوا مُؤْمِنِينَ
LaAAallaka bakhiAAun nafsaka allayakoonoo mu/mineen
Hausa
Tsammãninka kai mai halakar da ranka ne, dõmin ba su kasance mũminai ba!
|
Ayah 26:4 الأية
إِن نَّشَأْ نُنَزِّلْ عَلَيْهِم مِّنَ السَّمَاءِ آيَةً فَظَلَّتْ أَعْنَاقُهُمْ
لَهَا خَاضِعِينَ
In nasha/ nunazzil AAalayhim mina assama-iayatan fathallat aAAnaquhum
lahakhadiAAeen
Hausa
Idan Mun so zã Mu saukar, a kansu, da wata ãyã daga sama, sai wuyõyinsu su yini
sabõda ita sunã mãsu ƙasƙantar da kai.
|
Ayah 26:5 الأية
وَمَا يَأْتِيهِم مِّن ذِكْرٍ مِّنَ الرَّحْمَٰنِ مُحْدَثٍ إِلَّا كَانُوا عَنْهُ
مُعْرِضِينَ
Wama ya/teehim min thikrin minaarrahmani muhdathin illa kanooAAanhu muAArideen
Hausa
Kuma wata tunãtarwa ba ta jẽ musu ba, daga Mai rahama, sãbuwa, fãce sun kasance
daga barinta sunã mãsu bijirẽwa.
|
Ayah 26:6 الأية
فَقَدْ كَذَّبُوا فَسَيَأْتِيهِمْ أَنبَاءُ مَا كَانُوا بِهِ يَسْتَهْزِئُونَ
Faqad kaththaboo fasaya/teehim anbaoma kanoo bihi yastahzi-oon
Hausa
To, lalle ne, sun ƙaryata, to, lãbãran abin da suka kasance sunã yi na izgili da
shi zã ya je musu.
|
Ayah 26:7 الأية
أَوَلَمْ يَرَوْا إِلَى الْأَرْضِ كَمْ أَنبَتْنَا فِيهَا مِن كُلِّ زَوْجٍ كَرِيمٍ
Awa lam yaraw ila al-ardi kamanbatna feeha min kulli zawjin kareem
Hausa
Shin, ba su dũba ba zuwa ga ƙasa, da yawa Muka tsirar a cikinta, daga dukan
nau'i mai kyau?
|
Ayah 26:8 الأية
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ
Inna fee thalika laayatan wamakana aktharuhum mu/mineen
Hausa
Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mũminai ba.
|
Ayah 26:9 الأية
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ
Wa-inna rabbaka lahuwa alAAazeezu arraheem
Hausa
Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai rahama.
|
Ayah 26:10 الأية
وَإِذْ نَادَىٰ رَبُّكَ مُوسَىٰ أَنِ ائْتِ الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ
Wa-ith nada rabbukamoosa ani i/ti alqawma aththalimeen
Hausa
Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya kirãyi Mũsã, "Ka je wa mutãnen nan azzãlumai.
|
Ayah 26:11 الأية
قَوْمَ فِرْعَوْنَ ۚ أَلَا يَتَّقُونَ
Qawma firAAawna ala yattaqoon
Hausa
"Mutãnen Fir'auna bã zã su yi taƙawa ba?"
|
Ayah 26:12 الأية
قَالَ رَبِّ إِنِّي أَخَافُ أَن يُكَذِّبُونِ
Qala rabbi innee akhafu anyukaththiboon
Hausa
Ya ce: "Ya Ubangijĩna, nĩ inã tsõron su ƙaryata ni.
|
Ayah 26:13 الأية
وَيَضِيقُ صَدْرِي وَلَا يَنطَلِقُ لِسَانِي فَأَرْسِلْ إِلَىٰ هَارُونَ
Wayadeequ sadree walayantaliqu lisanee faarsil ila haroon
Hausa
"Kuma ƙirjĩna ya yi ƙunci kuma harshẽna bã zai saku ba sabõda haka ka aika zuwa
ga Harũna.
|
Ayah 26:14 الأية
وَلَهُمْ عَلَيَّ ذَنبٌ فَأَخَافُ أَن يَقْتُلُونِ
Walahum AAalayya thanbun faakhafuan yaqtuloon
Hausa
"Kuma sunã da wani laifi a kaina, sabõda haka inã tsõron kada su kashe ni."
|
Ayah 26:15 الأية
قَالَ كَلَّا ۖ فَاذْهَبَا بِآيَاتِنَا ۖ إِنَّا مَعَكُم مُّسْتَمِعُونَ
Qala kalla fathhababi-ayatina inna maAAakum mustamiAAoon
Hausa
Ya ce: "Kayya! Ku tafi, kũ biyu, da ÃyõyinMu. Lalle ne, Munã tãre da ku Munã
Mãsu saurãre."
|
Ayah 26:16 الأية
فَأْتِيَا فِرْعَوْنَ فَقُولَا إِنَّا رَسُولُ رَبِّ الْعَالَمِينَ
Fa/tiya firAAawna faqoola innarasoolu rabbi alAAalameen
Hausa
"Sai ku je wa Fir'auna, sa'an nan ku ce, Lalle ne, mu, Manzannin Ubangijin
halitta ne."
|
Ayah 26:17 الأية
أَنْ أَرْسِلْ مَعَنَا بَنِي إِسْرَائِيلَ
An arsil maAAana banee isra-eel
Hausa
"Ka saki Banĩ Isrã'ila tãre da mu."
|
Ayah 26:18 الأية
قَالَ أَلَمْ نُرَبِّكَ فِينَا وَلِيدًا وَلَبِثْتَ فِينَا مِنْ عُمُرِكَ سِنِينَ
Qala alam nurabbika feenawaleedan walabithta feena min AAumurika sineen
Hausa
Ya ce: "Shin, ba mu yi rẽnonka ba a cikinmu kanã jãrĩri, kuma ka zauna a cikinmu
shẽkarudaga lõkacin rãyuwarka?"
|
Ayah 26:19 الأية
وَفَعَلْتَ فَعْلَتَكَ الَّتِي فَعَلْتَ وَأَنتَ مِنَ الْكَافِرِينَ
WafaAAalta faAAlataka allatee faAAaltawaanta mina alkafireen
Hausa
"Kuma ka aikata aikinka wanda ka aikata alhãli kai kanã daga butulai?"
|
Ayah 26:20 الأية
قَالَ فَعَلْتُهَا إِذًا وَأَنَا مِنَ الضَّالِّينَ
Qala faAAaltuha ithanwaana mina addalleen
Hausa
Ya ce: "Na aikata shi a lõkacin inã daga mãsu jãhilcin hushi."
|
Ayah 26:21 الأية
فَفَرَرْتُ مِنكُمْ لَمَّا خِفْتُكُمْ فَوَهَبَ لِي رَبِّي حُكْمًا وَجَعَلَنِي
مِنَ الْمُرْسَلِينَ
Fafarartu minkum lamma khiftukumfawahaba lee rabbee hukman wajaAAalanee mina
almursaleen
Hausa
"Sabõda haka na gudu daga gãre ku a lõkacin da na ji tsõronku, sai Ubangijĩna Ya
bã ni hukunci, kuma Ya sanya ni daga Manzanni."
|
Ayah 26:22 الأية
وَتِلْكَ نِعْمَةٌ تَمُنُّهَا عَلَيَّ أَنْ عَبَّدتَّ بَنِي إِسْرَائِيلَ
Watilka niAAmatun tamunnuha AAalayyaan AAabbadta banee isra-eel
Hausa
"Kuma waccan ni'ima ce, kanã gõrint a kaina, dõmin kã bautar da Banĩ Isrã'ĩla."
|
Ayah 26:23 الأية
قَالَ فِرْعَوْنُ وَمَا رَبُّ الْعَالَمِينَ
Qala firAAawnu wama rabbu alAAalameen
Hausa
Fir'auna ya ce: "Kuma mene ne Ubangijin halittu?"
|
Ayah 26:24 الأية
قَالَ رَبُّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا ۖ إِن كُنتُم مُّوقِنِينَ
Qala rabbu assamawatiwal-ardi wama baynahuma in kuntummooqineen
Hausa
Ya ce: "Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, idan kun kasance
mãsu ƙarfin ĩmãni."
|
Ayah 26:25 الأية
قَالَ لِمَنْ حَوْلَهُ أَلَا تَسْتَمِعُونَ
Qala liman hawlahu alatastamiAAoon
Hausa
Ya ce wa waɗanda suke a gẽfensa, "Bã za ku saurãra ba?"
|
Ayah 26:26 الأية
قَالَ رَبُّكُمْ وَرَبُّ آبَائِكُمُ الْأَوَّلِينَ
Qala rabbukum warabbu aba-ikumual-awwaleen
Hausa
Ya ce: "Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko."
|
Ayah 26:27 الأية
قَالَ إِنَّ رَسُولَكُمُ الَّذِي أُرْسِلَ إِلَيْكُمْ لَمَجْنُونٌ
Qala inna rasoolakumu allatheeorsila ilaykum lamajnoon
Hausa
Ya ce: "Lalle ne Manzonku, wanda aka aiko zuwa gare ku, haƙi ƙa, mahaukaci ne."
|
Ayah 26:28 الأية
قَالَ رَبُّ الْمَشْرِقِ وَالْمَغْرِبِ وَمَا بَيْنَهُمَا ۖ إِن كُنتُمْ
تَعْقِلُونَ
Qala rabbu almashriqi walmaghribiwama baynahuma in kuntum taAAqiloon
Hausa
Ya ce: "Ubangijin mafitar rãnã da maɓũyarta da abin dayake a tsakaninsu, idan
kun kasance kunã hankalta."
|
Ayah 26:29 الأية
قَالَ لَئِنِ اتَّخَذْتَ إِلَٰهًا غَيْرِي لَأَجْعَلَنَّكَ مِنَ الْمَسْجُونِينَ
Qala la-ini ittakhathta ilahanghayree laajAAalannaka mina almasjooneen
Hausa
Ya ce: "Lalle ne idan ka riƙi wani abin bautãwa wanĩna haƙĩƙa, inã sanyã ka daga
ɗaurarru."
|
Ayah 26:30 الأية
قَالَ أَوَلَوْ جِئْتُكَ بِشَيْءٍ مُّبِينٍ
Qala awa law ji/tuka bishay-in mubeen
Hausa
Ya ce: "Ashe, kuma kõ dã nã zõ maka da wani, abu mai bayyanãwa?"
|
Ayah 26:31 الأية
قَالَ فَأْتِ بِهِ إِن كُنتَ مِنَ الصَّادِقِينَ
Qala fa/ti bihi in kunta mina assadiqeen
Hausa
Ya ce: "To, ka zõ da shi idan ka kasance daga, mãsu gaskiya."
|
Ayah 26:32 الأية
فَأَلْقَىٰ عَصَاهُ فَإِذَا هِيَ ثُعْبَانٌ مُّبِينٌ
Faalqa AAasahu fa-ithahiya thuAAbanun mubeen
Hausa
Sai ya jẽfa sandarsa, sai ga ta kumurci bayyananne.
|
Ayah 26:33 الأية
وَنَزَعَ يَدَهُ فَإِذَا هِيَ بَيْضَاءُ لِلنَّاظِرِينَ
WanazaAAa yadahu fa-itha hiya baydaolinnathireen
Hausa
Kuma ya fizge hannunsa, sai ga shi fari ga mãsu kallo.
|
Ayah 26:34 الأية
قَالَ لِلْمَلَإِ حَوْلَهُ إِنَّ هَٰذَا لَسَاحِرٌ عَلِيمٌ
Qala lilmala-i hawlahu inna hathalasahirun AAaleem
Hausa
(Fir'auna) ya ce ga mashãwarta a gẽfensa, "Lalle ne, wannan haƙĩƙa, masihirci
ne, mai ilmi!
|
Ayah 26:35 الأية
يُرِيدُ أَن يُخْرِجَكُم مِّنْ أَرْضِكُم بِسِحْرِهِ فَمَاذَا تَأْمُرُونَ
Yureedu an yukhrijakum min ardikumbisihrihi famatha ta/muroon
Hausa
"Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku game da sihirinSa. To mẽne ne kuke
shãwartãwa?"
|
Ayah 26:36 الأية
قَالُوا أَرْجِهْ وَأَخَاهُ وَابْعَثْ فِي الْمَدَائِنِ حَاشِرِينَ
Qaloo arjih waakhahu wabAAathfee almada-ini hashireen
Hausa
Suka ce: "Ka jinkirtar da shi, shĩ da ɗan'uwansa, kuma ka aika mãsu gayya a
cikin birãne."
|
Ayah 26:37 الأية
يَأْتُوكَ بِكُلِّ سَحَّارٍ عَلِيمٍ
Ya/tooka bikulli sahharin AAaleem
Hausa
"Zã su zõ maka da dukkan mai yawan sihiri masani."
|
Ayah 26:38 الأية
فَجُمِعَ السَّحَرَةُ لِمِيقَاتِ يَوْمٍ مَّعْلُومٍ
FajumiAAa assaharatu limeeqatiyawmin maAAloom
Hausa
Sai aka tãra masihirta dõmin ajalin yini sananne.
|
Ayah 26:39 الأية
وَقِيلَ لِلنَّاسِ هَلْ أَنتُم مُّجْتَمِعُونَ
Waqeela linnasi hal antummujtamiAAoon
Hausa
Kuma aka ce wa mutãne "Kõ kũ mãsu tãruwã ne?
|
Ayah 26:40 الأية
لَعَلَّنَا نَتَّبِعُ السَّحَرَةَ إِن كَانُوا هُمُ الْغَالِبِينَ
LaAAallana nattabiAAu assaharatain kanoo humu alghalibeen
Hausa
"Tsammãninmu mu bi masihirta, idan sun kasance sũ ne marinjãya."
|
Ayah 26:41 الأية
فَلَمَّا جَاءَ السَّحَرَةُ قَالُوا لِفِرْعَوْنَ أَئِنَّ لَنَا لَأَجْرًا إِن
كُنَّا نَحْنُ الْغَالِبِينَ
Falamma jaa assaharatuqaloo lifirAAawna a-inna lana laajran in kunnanahnu
alghalibeen
Hausa
To, a lõkacin da masihirta suka jẽ suka ce wa Fir'auna,"Shin, lalle ne, haƙĩƙa
munã da ijãra idan mun kasance mũ ne marinjãya?"
|
Ayah 26:42 الأية
قَالَ نَعَمْ وَإِنَّكُمْ إِذًا لَّمِنَ الْمُقَرَّبِينَ
Qala naAAam wa-innakum ithanlamina almuqarrabeen
Hausa
Ya ce: "Na'am! Kuma lalle ne, kũ ne a lõkacin haƙĩƙa muƙarrabai."
|
Ayah 26:43 الأية
قَالَ لَهُم مُّوسَىٰ أَلْقُوا مَا أَنتُم مُّلْقُونَ
Qala lahum moosa alqoo maantum mulqoon
Hausa
Mũsã ya ce musu, "Ku jẽfa abin da kuke mãsu jẽfãwa."
|
Ayah 26:44 الأية
فَأَلْقَوْا حِبَالَهُمْ وَعِصِيَّهُمْ وَقَالُوا بِعِزَّةِ فِرْعَوْنَ إِنَّا
لَنَحْنُ الْغَالِبُونَ
Faalqaw hibalahum waAAisiyyahumwaqaloo biAAizzati firAAawna inna
lanahnualghaliboon
Hausa
Sai suka jẽfa igiyõyinsu, da sandunansu, kuma suka ce: "Da ƙarfin Fir'auna lalle
ne mũ, haƙĩƙa, mũ ne marinjãya."
|
Ayah 26:45 الأية
فَأَلْقَىٰ مُوسَىٰ عَصَاهُ فَإِذَا هِيَ تَلْقَفُ مَا يَأْفِكُونَ
Faalqa moosa AAasahufa-itha hiya talqafu ma ya/fikoon
Hausa
Sai Mũsa ya jẽfa sandarsa, sai ga ta tanã harhaɗe abin da suke yi na ƙarya.
|
Ayah 26:46 الأية
فَأُلْقِيَ السَّحَرَةُ سَاجِدِينَ
Faolqiya assaharatu sajideen
Hausa
Sai aka jẽfar da masihirta sunã mãsu sujada.
|
Ayah 26:47 الأية
قَالُوا آمَنَّا بِرَبِّ الْعَالَمِينَ
Qaloo amanna birabbialAAalameen
Hausa
Suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin halitta."
|
Ayah 26:48 الأية
رَبِّ مُوسَىٰ وَهَارُونَ
Rabbi moosa waharoon
Hausa
"Ubangijin Mũsa da Hãrũna."
|
Ayah 26:49 الأية
قَالَ آمَنتُمْ لَهُ قَبْلَ أَنْ آذَنَ لَكُمْ ۖ إِنَّهُ لَكَبِيرُكُمُ الَّذِي
عَلَّمَكُمُ السِّحْرَ فَلَسَوْفَ تَعْلَمُونَ ۚ لَأُقَطِّعَنَّ أَيْدِيَكُمْ
وَأَرْجُلَكُم مِّنْ خِلَافٍ وَلَأُصَلِّبَنَّكُمْ أَجْمَعِينَ
Qala amantum lahu qabla an athanalakum innahu lakabeerukumu allathee
AAallamakumu assihrafalasawfa taAAlamoona laoqattiAAanna aydiyakum
waarjulakummin khilafin walaosallibannakum ajmaAAeen
Hausa
Ya ce: "Ashe, kun yi ĩmãni sabõda shĩ, a gabãnin in yi muku izni? Lalle ne shi,
haƙĩƙa babbanku ne wanda ya kõya muku sihirin, to, zã ku sani. Lalle ne
haƙĩƙa,zan kakkãtse hannuwanku da kafãfunku a tarnaƙi, kuma haƙĩƙa, zan tsĩrẽ ku
gabã ɗaya."
|
Ayah 26:50 الأية
قَالُوا لَا ضَيْرَ ۖ إِنَّا إِلَىٰ رَبِّنَا مُنقَلِبُونَ
Qaloo la dayra innaila rabbina munqaliboon
Hausa
Suka ce: "Bãbu wata cũta! Lalle ne mũ mãsu jũyãwa ne zuwa ga Ubangijinmu."
|
Ayah 26:51 الأية
إِنَّا نَطْمَعُ أَن يَغْفِرَ لَنَا رَبُّنَا خَطَايَانَا أَن كُنَّا أَوَّلَ
الْمُؤْمِنِينَ
Inna natmaAAu an yaghfira lanarabbuna khatayana an kunnaawwala almu/mineen
Hausa
"Lalle ne mu munã kwaɗayin Ubangijinmu, Ya gãfarta mana kurakuranmu dõmin mun
kasance farkon mãsu ĩmãni."
|
Ayah 26:52 الأية
وَأَوْحَيْنَا إِلَىٰ مُوسَىٰ أَنْ أَسْرِ بِعِبَادِي إِنَّكُم مُّتَّبَعُونَ
Waawhayna ila moosaan asri biAAibadee innakum muttabaAAoon
Hausa
Kuma Muka aika zuwa ga Mũsã cẽwa ka yi tafiyar dare da bãyiNa, lalle ne kũ
waɗanda ake biyã ne.
|
Ayah 26:53 الأية
فَأَرْسَلَ فِرْعَوْنُ فِي الْمَدَائِنِ حَاشِرِينَ
Faarsala firAAawnu fee almada-ini hashireen
Hausa
Sai Fir'auna ya aika mãsu gayya a cikin birãne.
|
Ayah 26:54 الأية
إِنَّ هَٰؤُلَاءِ لَشِرْذِمَةٌ قَلِيلُونَ
Inna haola-i lashirthimatunqaleeloon
Hausa
"Lalle ne, waɗannan, haƙĩƙa, ƙungiya ce kaɗan."
|
Ayah 26:55 الأية
وَإِنَّهُمْ لَنَا لَغَائِظُونَ
Wa-innahum lana lagha-ithoon
Hausa
"Kuma lalle ne sũ, a gare Mu, Mãsu fusãtarwa ne."
|
Ayah 26:56 الأية
وَإِنَّا لَجَمِيعٌ حَاذِرُونَ
Wa-inna lajameeAAun hathiroon
Hausa
"Kuma lalle ne mũ haƙĩƙa gabã ɗaya mãsu sauna ne."
|
Ayah 26:57 الأية
فَأَخْرَجْنَاهُم مِّن جَنَّاتٍ وَعُيُونٍ
Faakhrajnahum min jannatinwaAAuyoon
Hausa
Sai Muka fitar da su daga gonaki da marẽmari.
|
Ayah 26:58 الأية
وَكُنُوزٍ وَمَقَامٍ كَرِيمٍ
Wakunoozin wamaqamin kareem
Hausa
Da taskõki da mazauni mai kyau.
|
Ayah 26:59 الأية
كَذَٰلِكَ وَأَوْرَثْنَاهَا بَنِي إِسْرَائِيلَ
Kathalika waawrathnahabanee isra-eel
Hausa
Kamar haka! Kuma Muka gãdar da su ga Banĩ Isrãĩla.
|
Ayah 26:60 الأية
فَأَتْبَعُوهُم مُّشْرِقِينَ
FaatbaAAoohum mushriqeen
Hausa
Sai suka bĩ su sunã mãsu fita a lõkacin hũdõwar rãnã.
|
Ayah 26:61 الأية
فَلَمَّا تَرَاءَى الْجَمْعَانِ قَالَ أَصْحَابُ مُوسَىٰ إِنَّا لَمُدْرَكُونَ
Falamma taraa aljamAAaniqala as-habu moosa innalamudrakoon
Hausa
Sa'an nan a lõkacin da jama'a biyu suka ga jũna, sai abõkan Mũsã suka ce: "Lalle
ne mũ haƙĩ ƙa, waɗanda ake riska ne."
|
Ayah 26:62 الأية
قَالَ كَلَّا ۖ إِنَّ مَعِيَ رَبِّي سَيَهْدِينِ
Qala kalla inna maAAiya rabbeesayahdeen
Hausa
Ya ce: "Kayya! Lalle ne Ubangijina Yanã tare da ni, zai shiryar da ni."
|
Ayah 26:63 الأية
فَأَوْحَيْنَا إِلَىٰ مُوسَىٰ أَنِ اضْرِب بِّعَصَاكَ الْبَحْرَ ۖ فَانفَلَقَ
فَكَانَ كُلُّ فِرْقٍ كَالطَّوْدِ الْعَظِيمِ
Faawhayna ila moosaani idrib biAAasaka albahra fanfalaqafakana kullu firqin
kattawdi alAAatheem
Hausa
Sai Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa "Ka dõki tẽku da sandarka." Sai tẽku ta
tsãge, kõwane tsãgi ya kasance kamar falalen dũtse mai girma.
|
Ayah 26:64 الأية
وَأَزْلَفْنَا ثَمَّ الْآخَرِينَ
Waazlafna thamma al-akhareen
Hausa
Kuma Muka kusantar da waɗansu mutãne a can.
|
Ayah 26:65 الأية
وَأَنجَيْنَا مُوسَىٰ وَمَن مَّعَهُ أَجْمَعِينَ
Waanjayna moosa waman maAAahuajmaAAeen
Hausa
Kuma Muka tsĩrar da Mũsã da waɗanda suke tãre da shi gabã ɗaya.
|
Ayah 26:66 الأية
ثُمَّ أَغْرَقْنَا الْآخَرِينَ
Thumma aghraqna al-akhareen
Hausa
Sa'an nan kuma Muka nutsar da waɗansu mutãnen.
|
Ayah 26:67 الأية
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ
Inna fee thalika laayatan wamakana aktharuhum mu/mineen
Hausa
Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni
ba.
|
Ayah 26:68 الأية
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ
Wa-inna rabbaka lahuwa alAAazeezu arraheem
Hausa
Kuma lalle ne Ubangijinka, kaƙĩƙa, Shĩ ne Mabũwayi, Mai jin ƙai.
|
Ayah 26:69 الأية
وَاتْلُ عَلَيْهِمْ نَبَأَ إِبْرَاهِيمَ
Watlu AAalayhim nabaa ibraheem
Hausa
Kuma ka karanta, a kansu, lãbãrin Ibrãhĩm.
|
Ayah 26:70 الأية
إِذْ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوْمِهِ مَا تَعْبُدُونَ
Ith qala li-abeehi waqawmihi mataAAbudoon
Hausa
A sã'ilin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bauta wa?"
|
Ayah 26:71 الأية
قَالُوا نَعْبُدُ أَصْنَامًا فَنَظَلُّ لَهَا عَاكِفِينَ
Qaloo naAAbudu asnamanfanathallu laha AAakifeen
Hausa
Suka ce: "Munã bauta wa gumãka, sabõda haka munã yini mãsu lazimta a gare su."
|
Ayah 26:72 الأية
قَالَ هَلْ يَسْمَعُونَكُمْ إِذْ تَدْعُونَ
Qala hal yasmaAAoonakum ithtadAAoon
Hausa
Ya ce: "Shin, sunã jin ku, a lõkacin da kuke kira?"
|
Ayah 26:73 الأية
أَوْ يَنفَعُونَكُمْ أَوْ يَضُرُّونَ
Aw yanfaAAoonakum aw yadurroon
Hausa
"Kõ kuwa sunã amfãnin ku, kõ sunã cũtar ku?"
|
Ayah 26:74 الأية
قَالُوا بَلْ وَجَدْنَا آبَاءَنَا كَذَٰلِكَ يَفْعَلُونَ
Qaloo bal wajadna abaanakathalika yafAAaloon
Hausa
Suka ce: "Ã'a mun sãmĩ ubanninmu, kamar haka ne suke aikatãwa."
|
Ayah 26:75 الأية
قَالَ أَفَرَأَيْتُم مَّا كُنتُمْ تَعْبُدُونَ
Qala afaraaytum ma kuntumtaAAbudoon
Hausa
Ya ce: "Shin to, kun ga abin da kuka kasance kunã bautã wa?"
|
Ayah 26:76 الأية
أَنتُمْ وَآبَاؤُكُمُ الْأَقْدَمُونَ
Antum waabaokumu al-aqdamoon
Hausa
"Kũ da ubanninku mafi daɗẽwa?"
|
Ayah 26:77 الأية
فَإِنَّهُمْ عَدُوٌّ لِّي إِلَّا رَبَّ الْعَالَمِينَ
Fa-innahum AAaduwwun lee illa rabbaalAAalameen
Hausa
"To lalle ne, sũ maƙiya ne a gare ni, fãce Ubangijin halittu."
|
Ayah 26:78 الأية
الَّذِي خَلَقَنِي فَهُوَ يَهْدِينِ
Allathee khalaqanee fahuwa yahdeen
Hausa
"Wanda Ya halitta ni, sa'an nan Yanã shiryar da ni."
|
Ayah 26:79 الأية
وَالَّذِي هُوَ يُطْعِمُنِي وَيَسْقِينِ
Wallathee huwa yutAAimuneewayasqeen
Hausa
"Kuma Wanda Yake Shĩ ne Yake ciyar da ni, kuma Yanã shãyar da ni."
|
Ayah 26:80 الأية
وَإِذَا مَرِضْتُ فَهُوَ يَشْفِينِ
Wa-itha maridtu fahuwayashfeen
Hausa
"Kuma idan na yi jiyya, to, Shĩ ne Yake warkar da ni."
|
Ayah 26:81 الأية
وَالَّذِي يُمِيتُنِي ثُمَّ يُحْيِينِ
Wallathee yumeetunee thummayuhyeen
Hausa
"Kuma wanda Yake matar da ni, sa'an nan Ya rãyar da ni."
|
Ayah 26:82 الأية
وَالَّذِي أَطْمَعُ أَن يَغْفِرَ لِي خَطِيئَتِي يَوْمَ الدِّينِ
Wallathee atmaAAu anyaghfira lee khatee-atee yawma addeen
Hausa
"Kuma wanda Yake inã kwaɗayin Ya gãfarta mini kurãkuraina, a rãnar sãkamako."
|
Ayah 26:83 الأية
رَبِّ هَبْ لِي حُكْمًا وَأَلْحِقْنِي بِالصَّالِحِينَ
Rabbi hab lee hukman waalhiqneebissaliheen
Hausa
"Ya Ubangijĩna! Ka ba ni hukunci, kuma Ka riskar da ni ga sãlihai."
|
Ayah 26:84 الأية
وَاجْعَل لِّي لِسَانَ صِدْقٍ فِي الْآخِرِينَ
WajAAal lee lisana sidqinfee al-akhireen
Hausa
"Kuma Ka sanya mini harshen gaskiya a cikin mutãnen ƙarshe."
|
Ayah 26:85 الأية
وَاجْعَلْنِي مِن وَرَثَةِ جَنَّةِ النَّعِيمِ
WajAAalnee min warathati jannati annaAAeem
Hausa
"Kuma Ka sanya ni daga magãdan Aljannar ni'ima."
|
Ayah 26:86 الأية
وَاغْفِرْ لِأَبِي إِنَّهُ كَانَ مِنَ الضَّالِّينَ
Waghfir li-abee innahu kanamina addalleen
Hausa
"Kuma Ka gãfarta wa ubãna, lalle ne shi, ya kasance daga ɓatattu."
|
Ayah 26:87 الأية
وَلَا تُخْزِنِي يَوْمَ يُبْعَثُونَ
Wala tukhzinee yawma yubAAathoon
Hausa
"Kuma kada Ka kunyata ni a rãnar da ake tãyar da su."
|
Ayah 26:88 الأية
يَوْمَ لَا يَنفَعُ مَالٌ وَلَا بَنُونَ
Yawma la yanfaAAu malun walabanoon
Hausa
"A rãnar da dũkiya bã ta amfãni, kuma ɗiya bã su yi."
|
Ayah 26:89 الأية
إِلَّا مَنْ أَتَى اللهَ بِقَلْبٍ سَلِيمٍ
Illa man ata Allahabiqalbin saleem
Hausa
"Fãce wanda ya jẽ wa Allah da zũciya mai tsarki."
|
Ayah 26:90 الأية
وَأُزْلِفَتِ الْجَنَّةُ لِلْمُتَّقِينَ
Waozlifati aljannatu lilmuttaqeen
Hausa
Kuma aka kusantar da Aljanna ga mãsu taƙawa.
|
Ayah 26:91 الأية
وَبُرِّزَتِ الْجَحِيمُ لِلْغَاوِينَ
Waburrizati aljaheemu lilghaween
Hausa
Kuma aka fitar da wutã babba dõmin halakakku.
|
Ayah 26:92 الأية
وَقِيلَ لَهُمْ أَيْنَ مَا كُنتُمْ تَعْبُدُونَ
Waqeela lahum ayna ma kuntumtaAAbudoon
Hausa
Kuma aka ce musu, "Inã abin da kuka kasance kunã bautawa?"
|
Ayah 26:93 الأية
مِن دُونِ اللهِ هَلْ يَنصُرُونَكُمْ أَوْ يَنتَصِرُونَ
Min dooni Allahi hal yansuroonakumaw yantasiroon
Hausa
"Baicin Allah? Shin sunã tamakon ku kõ kuwa sunã tsare kansu?"
|
Ayah 26:94 الأية
فَكُبْكِبُوا فِيهَا هُمْ وَالْغَاوُونَ
Fakubkiboo feeha hum walghawoon
Hausa
Sai aka kikkife su a cikinta, su da halakakkun.
|
Ayah 26:95 الأية
وَجُنُودُ إِبْلِيسَ أَجْمَعُونَ
Wajunoodu ibleesa ajmaAAoon
Hausa
Da rundunar Ibilĩsa gabã ɗaya.
|
Ayah 26:96 الأية
قَالُوا وَهُمْ فِيهَا يَخْتَصِمُونَ
Qaloo wahum feeha yakhtasimoon
Hausa
Suka ce: alhãli sunã a cikinta sunã yin husũma,
|
Ayah 26:97 الأية
تَاللهِ إِن كُنَّا لَفِي ضَلَالٍ مُّبِينٍ
Tallahi in kunna lafeedalalin mubeen
Hausa
"Rantsuwa da Allah! Lalle ne mun kasance, haƙĩƙa, a cikin ɓata bayyananna."
|
Ayah 26:98 الأية
إِذْ نُسَوِّيكُم بِرَبِّ الْعَالَمِينَ
Ith nusawweekum birabbi alAAalameen
Hausa
"A lõkacin da muke daidaita ku da Ubangijin halittu.
|
Ayah 26:99 الأية
وَمَا أَضَلَّنَا إِلَّا الْمُجْرِمُونَ
Wama adallana illaalmujrimoon
Hausa
"Kuma bãbu abin da ya ɓatar da mu fãce mãsu laifi."
|
Ayah 26:100 الأية
فَمَا لَنَا مِن شَافِعِينَ
Fama lana min shafiAAeen
Hausa
"Sabõda haka bã mu da waɗansu macẽta."
|
Ayah 26:101 الأية
وَلَا صَدِيقٍ حَمِيمٍ
Wala sadeeqin hameem
Hausa
"Kuma bã mu da abõki, masõyi."
|
Ayah 26:102 الأية
فَلَوْ أَنَّ لَنَا كَرَّةً فَنَكُونَ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ
Falaw anna lana karratan fanakoonamina almu/mineen
Hausa
"Sabõda haka dã lalle munã da (dãmar) kõmawa, dõmin mu kasance daga mũminai!"
|
Ayah 26:103 الأية
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ
Inna fee thalika laayatan wamakana aktharuhum mu/mineen
Hausa
Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, bã su kasance mũminai ba.
|
Ayah 26:104 الأية
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ
Wa-inna rabbaka lahuwa alAAazeezu arraheem
Hausa
Kuma lalle ne, Ubangijinka, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
|
Ayah 26:105 الأية
كَذَّبَتْ قَوْمُ نُوحٍ الْمُرْسَلِينَ
Kaththabat qawmu noohinalmursaleen
Hausa
Mutãnen Nũhu sun ƙaryata Manzanni.
|
Ayah 26:106 الأية
إِذْ قَالَ لَهُمْ أَخُوهُمْ نُوحٌ أَلَا تَتَّقُونَ
Ith qala lahum akhoohum noohunala tattaqoon
Hausa
A lõkacin da ɗan'uwansu, Nũhu, ya ce musu, "Shin, bã zã ku yi taƙawa ba?"
|
Ayah 26:107 الأية
إِنِّي لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ
Innee lakum rasoolun ameen
Hausa
"Lalle ne, zuwa gare ku, ni Manzo ne amintacce."
|
Ayah 26:108 الأية
فَاتَّقُوا اللهَ وَأَطِيعُونِ
Fattaqoo Allaha waateeAAoon
Hausa
"To, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
|
Ayah 26:109 الأية
وَمَا أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ ۖ إِنْ أَجْرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ
الْعَالَمِينَ
Wama as-alukum AAalayhi min ajrin inajriya illa AAala rabbi alAAalameen
Hausa
"Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãtã ba ta zama ba fãce daga
Ubangijin halittu."
|
Ayah 26:110 الأية
فَاتَّقُوا اللهَ وَأَطِيعُونِ
Fattaqoo Allaha waateeAAoon
Hausa
"Sabõda haka, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
|
Ayah 26:111 الأية
قَالُوا أَنُؤْمِنُ لَكَ وَاتَّبَعَكَ الْأَرْذَلُونَ
Qaloo anu/minu laka wattabaAAakaal-arthaloon
Hausa
Suka ce: "Ashe, zã mu yi ĩmãni sabõda kai alhãli kuwa mafiya ƙasƙanci sun bi
ka?"
|
Ayah 26:112 الأية
قَالَ وَمَا عِلْمِي بِمَا كَانُوا يَعْمَلُونَ
Qala wama AAilmee bimakanoo yaAAmaloon
Hausa
Ya ce: "Kuma bã ni da sani ga abin da suka kasance sanã aikatãwa."
|
Ayah 26:113 الأية
إِنْ حِسَابُهُمْ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّي ۖ لَوْ تَشْعُرُونَ
In hisabuhum illa AAalarabbee law tashAAuroon
Hausa
"Hisãbinsu bai zama ba fãce ga Ubangijina, dã kunã sansancẽwa."
|
Ayah 26:114 الأية
وَمَا أَنَا بِطَارِدِ الْمُؤْمِنِينَ
Wama ana bitaridialmu/mineen
Hausa
"Ban zama mai kõre mũminai ba."
|
Ayah 26:115 الأية
إِنْ أَنَا إِلَّا نَذِيرٌ مُّبِينٌ
In ana illa natheerunmubeen
Hausa
"Nĩ ba kõwa ba ne sai mai gargaɗi mai bayyanãwa."
|
Ayah 26:116 الأية
قَالُوا لَئِن لَّمْ تَنتَهِ يَا نُوحُ لَتَكُونَنَّ مِنَ الْمَرْجُومِينَ
Qaloo la-in lam tantahi yanoohu latakoonanna mina almarjoomeen
Hausa
Suka ce: "Lalle ne, idan ba ka hanu ba, yã Nũhu, (daga maganarka,) haƙĩƙa, kanã
kasancẽwa daga waɗanda ake jẽfewa"
|
Ayah 26:117 الأية
قَالَ رَبِّ إِنَّ قَوْمِي كَذَّبُونِ
Qala rabbi inna qawmee kaththaboon
Hausa
Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle ne mutãnena sun ƙaryatã ni."
|
|