1st Ayah 1 الأية ١الأوليبِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
طس ۚ تِلْكَ آيَاتُ الْقُرْآنِ وَكِتَابٍ مُّبِينٍ
Ta-seen tilka ayatualqur-ani wakitabin mubeen
Hausa
¦.S̃. Waɗancan ãyõyinAlƙur'ãni ne da Littãfi mai bayyanawa.
|
Ayah 27:2 الأية
هُدًى وَبُشْرَىٰ لِلْمُؤْمِنِينَ
Hudan wabushra lilmu/mineen
Hausa
Shiriya ce da bushãra ga mũminai.
|
Ayah 27:3 الأية
الَّذِينَ يُقِيمُونَ الصَّلَاةَ وَيُؤْتُونَ الزَّكَاةَ وَهُم بِالْآخِرَةِ هُمْ
يُوقِنُونَ
Allatheena yuqeemoona assalatawayu/toona azzakata wahum bil-akhiratihum
yooqinoon
Hausa
Waɗanda suke tsayar da salla kuma su bãyar da zakka, alhãli kuwa sũ, game da
Lãhira, to, sũ,sunã yin yaƙĩni.
|
Ayah 27:4 الأية
إِنَّ الَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِالْآخِرَةِ زَيَّنَّا لَهُمْ أَعْمَالَهُمْ
فَهُمْ يَعْمَهُونَ
Inna allatheena la yu/minoonabil-akhirati zayyanna lahum aAAmalahumfahum
yaAAmahoon
Hausa
Lalle ne waɗanda suke bã su yin ĩmãni da Lãhira, Mun ƙawãta musu ayyukansu,
sabõda haka sunã ɗimuwa.
|
Ayah 27:5 الأية
أُولَٰئِكَ الَّذِينَ لَهُمْ سُوءُ الْعَذَابِ وَهُمْ فِي الْآخِرَةِ هُمُ
الْأَخْسَرُونَ
Ola-ika allatheena lahum soo-oalAAathabi wahum fee al-akhirati humu al-akhsaroon
Hausa
Waɗannan ne waɗanda suke sunã da mugunyar azãba (a dũniya), kuma sũ, a Lãhira,
sũ ne mafiya hasãra.
|
Ayah 27:6 الأية
وَإِنَّكَ لَتُلَقَّى الْقُرْآنَ مِن لَّدُنْ حَكِيمٍ عَلِيمٍ
Wa-innaka latulaqqa alqur-anamin ladun hakeemin AAaleem
Hausa
Kuma lalle ne haƙĩƙa, anã haɗa ka da Alƙur'ãni daga gun Mai hikima, Masani.
|
Ayah 27:7 الأية
إِذْ قَالَ مُوسَىٰ لِأَهْلِهِ إِنِّي آنَسْتُ نَارًا سَآتِيكُم مِّنْهَا بِخَبَرٍ
أَوْ آتِيكُم بِشِهَابٍ قَبَسٍ لَّعَلَّكُمْ تَصْطَلُونَ
Ith qala moosa li-ahlihiinnee anastu naran saateekum minhabikhabarin aw ateekum
bishihabin qabasinlaAAallakum tastaloon
Hausa
A lõkacin da Mũsã ya ce wa iyãlinsa "Lalle ni, na tsinkãyi wata wuta, ni mai zo
muku daga gare ta ne, da wani lãbari, ko kuwa mai zo muku ne da Yũla, makãmashi,
tsammãninku, ku ji ɗimi."
|
Ayah 27:8 الأية
فَلَمَّا جَاءَهَا نُودِيَ أَن بُورِكَ مَن فِي النَّارِ وَمَنْ حَوْلَهَا
وَسُبْحَانَ اللهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ
Falamma jaaha noodiya anboorika man fee annari waman hawlahawasubhana Allahi
rabbi alAAalameen
Hausa
To, a lõkacin da ya jẽ mata, sai aka kira shi cẽwa, "An tsarkake wanda yake
cikin (wurin) wutar da yanda yake a gẽfenta kuma tsarki ya tabbata ga Allah
Ubangijin halittu."
|
Ayah 27:9 الأية
يَا مُوسَىٰ إِنَّهُ أَنَا اللهُ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
Ya moosa innahu ana AllahualAAazeezu alhakeem
Hausa
"Yã Mũsã lalle ne shi, Nĩ ne Allah, Mabuwãyi, Mai hikima."
|
Ayah 27:10 الأية
وَأَلْقِ عَصَاكَ ۚ فَلَمَّا رَآهَا تَهْتَزُّ كَأَنَّهَا جَانٌّ وَلَّىٰ مُدْبِرًا
وَلَمْ يُعَقِّبْ ۚ يَا مُوسَىٰ لَا تَخَفْ إِنِّي لَا يَخَافُ لَدَيَّ
الْمُرْسَلُونَ
Waalqi AAasaka falamma raahatahtazzu kaannaha jannun walla mudbiranwalam
yuAAaqqib ya moosa la takhaf innee layakhafu ladayya almursaloon
Hausa
"Kuma ka jẽfa sandarka." To, a lõkacin da ya gan ta tanã girgiza kamar dai ita
ƙaramin macĩji ne, sai ya jũya yanã mai bãyar da bãya, kuma bai kõma ba, "Yã
Musã! Kada ka ji tsõro lalle Ni, Manzanni bã sujin tsõro a wuriNa."
|
Ayah 27:11 الأية
إِلَّا مَن ظَلَمَ ثُمَّ بَدَّلَ حُسْنًا بَعْدَ سُوءٍ فَإِنِّي غَفُورٌ رَّحِيمٌ
Illa man thalama thummabaddala husnan baAAda soo-in fa-innee ghafoorun raheem
Hausa
"Sai wanda ya yi zãlunci, sa'an nan ya musanya kyau a bãyan cũta, to, lalle Nĩ,
Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."
|
Ayah 27:12 الأية
وَأَدْخِلْ يَدَكَ فِي جَيْبِكَ تَخْرُجْ بَيْضَاءَ مِنْ غَيْرِ سُوءٍ ۖ فِي تِسْعِ
آيَاتٍ إِلَىٰ فِرْعَوْنَ وَقَوْمِهِ ۚ إِنَّهُمْ كَانُوا قَوْمًا فَاسِقِينَ
Waadkhil yadaka fee jaybika takhruj baydaamin ghayri soo-in fee tisAAi ayatin
ilafirAAawna waqawmihi innahum kanoo qawman fasiqeen
Hausa
"Kuma ka shigar da hannunka a cikin wuyan rĩgarka, ya fita fari, bãbu wata cũta,
a cikinwasu ãyõyi tara zuwa ga Fir'auna da mutãnensa. Lalle ne sũ, sun kasance
mutãne ne fãsiƙai."
|
Ayah 27:13 الأية
فَلَمَّا جَاءَتْهُمْ آيَاتُنَا مُبْصِرَةً قَالُوا هَٰذَا سِحْرٌ مُّبِينٌ
Falamma jaat-hum ayatunamubsiratan qaloo hatha sihrun mubeen
Hausa
To, a lõkacin da ãyõyinMu suka jẽ musu, sunã mãsu wãyar da kai suka ce wannan
sihiri ne bayyananne.
|
Ayah 27:14 الأية
وَجَحَدُوا بِهَا وَاسْتَيْقَنَتْهَا أَنفُسُهُمْ ظُلْمًا وَعُلُوًّا ۚ فَانظُرْ
كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُفْسِدِينَ
Wajahadoo biha wastayqanat-haanfusuhum thulman waAAuluwwan fanthurkayfa kana
AAaqibatu almufsideen
Hausa
Kuma suka yi musunsu, alhãli zukãtansu sun natsu da su dõmin zãlunci da girman
kai. To, ka dũbi yadda ãƙibar maɓarnata ta kasance.
|
Ayah 27:15 الأية
وَلَقَدْ آتَيْنَا دَاوُودَ وَسُلَيْمَانَ عِلْمًا ۖ وَقَالَا الْحَمْدُ لِلَّهِ
الَّذِي فَضَّلَنَا عَلَىٰ كَثِيرٍ مِّنْ عِبَادِهِ الْمُؤْمِنِينَ
Walaqad atayna dawoodawasulaymana AAilman waqala alhamdulillahi allathee
faddalana AAalakatheerin min AAibadihi almu/mineen
Hausa
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai wa Dãwũda da Sulaimãn ilmi kuma suka ce: "Gõdiya
ta tabbata ga Allah, Wanda Ya fĩfĩta mu a kan mãsu yawa daga bãyinSa mũminai."
|
Ayah 27:16 الأية
وَوَرِثَ سُلَيْمَانُ دَاوُودَ ۖ وَقَالَ يَا أَيُّهَا النَّاسُ عُلِّمْنَا مَنطِقَ
الطَّيْرِ وَأُوتِينَا مِن كُلِّ شَيْءٍ ۖ إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ الْفَضْلُ
الْمُبِينُ
Wawaritha sulaymanu dawoodawaqala ya ayyuha annasuAAullimna mantiqa attayri
waooteenamin kulli shay-in inna hatha lahuwa alfadlualmubeen
Hausa
Kuma sulaimãn ya gãji Dãwũda ya ce: "Yã ku mutãne! An sanar da mu maganar
tsuntsãye, kuma an bã mu daga kõwane abu. Lalle ne wannan haƙĩƙa shi ne falalar
(Allah) bayyananna."
|
Ayah 27:17 الأية
وَحُشِرَ لِسُلَيْمَانَ جُنُودُهُ مِنَ الْجِنِّ وَالْإِنسِ وَالطَّيْرِ فَهُمْ
يُوزَعُونَ
Wahushira lisulaymanajunooduhu mina aljinni wal-insi wattayrifahum yoozaAAoon
Hausa
Kuma aka tattara, dõmin Sulaimãn, rundunõninsa, daga aljannu da mutãne da
tsuntsãye, to, sũ anã kange su (ga tafiya).
|
Ayah 27:18 الأية
حَتَّىٰ إِذَا أَتَوْا عَلَىٰ وَادِ النَّمْلِ قَالَتْ نَمْلَةٌ يَا أَيُّهَا
النَّمْلُ ادْخُلُوا مَسَاكِنَكُمْ لَا يَحْطِمَنَّكُمْ سُلَيْمَانُ وَجُنُودُهُ
وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ
Hatta itha ataw AAalawadi annamli qalat namlatun ya ayyuhaannamlu odkhuloo
masakinakum la yahtimannakumsulaymanu wajunooduhu wahum la yashAAuroon
Hausa
Har a lõkacin da suka je a kan rãfin turũruwa wata turũruwa ta ce, "Yã kũ
jama'ar turũruwa! Ku shiga gidãjenku, kada Sulaimãn da rundunõninsa su kakkarya
ku, alhãli kuwa sũ, ba su sani ba."
|
Ayah 27:19 الأية
فَتَبَسَّمَ ضَاحِكًا مِّن قَوْلِهَا وَقَالَ رَبِّ أَوْزِعْنِي أَنْ أَشْكُرَ
نِعْمَتَكَ الَّتِي أَنْعَمْتَ عَلَيَّ وَعَلَىٰ وَالِدَيَّ وَأَنْ أَعْمَلَ
صَالِحًا تَرْضَاهُ وَأَدْخِلْنِي بِرَحْمَتِكَ فِي عِبَادِكَ الصَّالِحِينَ
Fatabassama dahikan min qawlihawaqala rabbi awziAAnee an ashkura niAAmataka
allateeanAAamta AAalayya waAAala walidayya waan aAAmala salihantardahu
waadkhilnee birahmatika fee AAibadikaassaliheen
Hausa
Sai ya yi murmushi yanã mai dãriya daga maganarta, kuma ya ce, "Yã Ubangijĩna!
Ka cũsa mini in gõde wa ni'imarKa wadda Ka ni'imta ta a gare ni da kuma ga
mahaifãna biyu, kuma in aikata aiki na ƙwarai, wanda Kake yarda da shi, kuma Ka
shigar da ni, sabõda rahamarKa, a cikin bãyinKa sãlihai."
|
Ayah 27:20 الأية
وَتَفَقَّدَ الطَّيْرَ فَقَالَ مَا لِيَ لَا أَرَى الْهُدْهُدَ أَمْ كَانَ مِنَ
الْغَائِبِينَ
Watafaqqada attayra faqalama liya la ara alhudhuda am kana minaalgha-ibeen
Hausa
Kuma ya binciki tsuntsãye, sai ya ce: "Me ya kãre ni bã ni ganin hudhudu, kõ ya
kasance daga mãsu fakuwa ne?"
|
Ayah 27:21 الأية
لَأُعَذِّبَنَّهُ عَذَابًا شَدِيدًا أَوْ لَأَذْبَحَنَّهُ أَوْ لَيَأْتِيَنِّي
بِسُلْطَانٍ مُّبِينٍ
LaoAAaththibannahu AAathabanshadeedan aw laathbahannahu aw laya/tiyannee
bisultaninmubeen
Hausa
"Lalle ne zã ni azabta shi azãba mai tsanani kõ kuwa lalle in yanka shi, kõ kuwa
lalle ya zo mini da dalĩli bayyananne."
|
Ayah 27:22 الأية
فَمَكَثَ غَيْرَ بَعِيدٍ فَقَالَ أَحَطتُ بِمَا لَمْ تُحِطْ بِهِ وَجِئْتُكَ مِن
سَبَإٍ بِنَبَإٍ يَقِينٍ
Famakatha ghayra baAAeedin faqala ahattubima lam tuhit bihi waji/tuka min
saba-inbinaba-in yaqeen
Hausa
Sai ya zauna bã nẽsa ba, sa'an nan ya ce: "Nã san abin da ba ka sani ba, kuma na
zo maka daga Saba da wani lãbari tabbatacce."
|
Ayah 27:23 الأية
إِنِّي وَجَدتُّ امْرَأَةً تَمْلِكُهُمْ وَأُوتِيَتْ مِن كُلِّ شَيْءٍ وَلَهَا
عَرْشٌ عَظِيمٌ
Innee wajadtu imraatan tamlikuhum waootiyatmin kulli shay-in walaha AAarshun
AAatheem
Hausa
"Lalle ni nã sãmi wata mace wadda tanã mulkinsu kuma an bã ta daga dukkan kõme,
kuma tanã da gadon sarauta mai girma.
|
Ayah 27:24 الأية
وَجَدتُّهَا وَقَوْمَهَا يَسْجُدُونَ لِلشَّمْسِ مِن دُونِ اللهِ وَزَيَّنَ
لَهُمُ الشَّيْطَانُ أَعْمَالَهُمْ فَصَدَّهُمْ عَنِ السَّبِيلِ فَهُمْ لَا
يَهْتَدُونَ
Wajadtuha waqawmaha yasjudoonalishshamsi min dooni Allahi wazayyana lahumu
ashshaytanuaAAmalahum fasaddahum AAani assabeeli fahumla yahtadoon
Hausa
"Na sãme ta ita da mutãnenta, sunã yin sujada ga rãnã, baicin Allah, kuma
Shaiɗan ya ƙawãce musu ayyukansu, sabõda haka ya karkatar da su daga hanya,
sa'an nan sũ, ba su shiryuwa."
|
Ayah 27:25 الأية
أَلَّا يَسْجُدُوا لِلَّهِ الَّذِي يُخْرِجُ الْخَبْءَ فِي السَّمَاوَاتِ
وَالْأَرْضِ وَيَعْلَمُ مَا تُخْفُونَ وَمَا تُعْلِنُونَ
Alla yasjudoo lillahi allatheeyukhriju alkhabaa fee assamawati
wal-ardiwayaAAlamu ma tukhfoona wama tuAAlinoon
Hausa
"Ga su yi sujada ga Allah Wanda Yake fitar da abin da yake a ɓõye, a cikin
sammai da ƙasa, kuma Yã san abin da kuke ɓõyẽwada abin da kuke bayyanãwa."
|
Ayah 27:26 الأية
اللهُ لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ رَبُّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ ۩
Allahu la ilaha illahuwa rabbu alAAarshi alAAatheem
Hausa
"Allah bãbu abin bautãwa fãce shĩ Ubangijin Al'arshi, mai girma."
|
Ayah 27:27 الأية
قَالَ سَنَنظُرُ أَصَدَقْتَ أَمْ كُنتَ مِنَ الْكَاذِبِينَ
Qala sananthuru asadaqtaam kunta mina alkathibeen
Hausa
Ya ce: "Za mu dũba shin kã yi gaskiya ne, kõ kuwa kã kasance daga maƙaryata?"
|
Ayah 27:28 الأية
اذْهَب بِّكِتَابِي هَٰذَا فَأَلْقِهْ إِلَيْهِمْ ثُمَّ تَوَلَّ عَنْهُمْ فَانظُرْ
مَاذَا يَرْجِعُونَ
Ithhab bikitabee hathafaalqih ilayhim thumma tawalla AAanhum fanthurmatha
yarjiAAoon
Hausa
"Ka tafi da takardata wannan, sa'an nan ka jẽfa ta zuwa gare su, sa'an nan kuma
ka jũya daga barinsu, sa'an nan ka ga mẽne ne suke mayarwa."
|
Ayah 27:29 الأية
قَالَتْ يَا أَيُّهَا الْمَلَأُ إِنِّي أُلْقِيَ إِلَيَّ كِتَابٌ كَرِيمٌ
Qalat ya ayyuha almalaoinnee olqiya ilayya kitabun kareem
Hausa
Ta ce: "Yã kũ mashawarta! Lalle ne, an jẽfo, zuwa gareni, wata takarda mai
girma."
|
Ayah 27:30 الأية
إِنَّهُ مِن سُلَيْمَانَ وَإِنَّهُ بِسْمِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
Innahu min sulaymana wa-innahu bismiAllahi arrahmani arraheem
Hausa
"Lalle ita daga Sulaiman take, kuma lalle ita da sũnan Allah, Mai rahama, Mai
jin ƙai ne."
|
Ayah 27:31 الأية
أَلَّا تَعْلُوا عَلَيَّ وَأْتُونِي مُسْلِمِينَ
Alla taAAloo AAalayya wa/tooneemuslimeen
Hausa
"Kada ku yi girman kai a gare ni, kuma ku zo mini kunã mãsu sallamãwa."
|
Ayah 27:32 الأية
قَالَتْ يَا أَيُّهَا الْمَلَأُ أَفْتُونِي فِي أَمْرِي مَا كُنتُ قَاطِعَةً
أَمْرًا حَتَّىٰ تَشْهَدُونِ
Qalat ya ayyuha almalaoaftoonee fee amree ma kuntu qatiAAatan amran
hattatashhadoon
Hausa
Ta ce: "Yã ku mashawarta ! Ku yi Mini fatawa ga al'amarĩna, ban kasance mai
yanke wani al'amari ba, sai kun halarta."
|
Ayah 27:33 الأية
قَالُوا نَحْنُ أُولُو قُوَّةٍ وَأُولُو بَأْسٍ شَدِيدٍ وَالْأَمْرُ إِلَيْكِ
فَانظُرِي مَاذَا تَأْمُرِينَ
Qaloo nahnu oloo quwwatinwaoloo ba/sin shadeedin wal-amru ilayki fanthureematha
ta/mureen
Hausa
Suka ce: "Mũ ma'abũta ƙarfi ne, kuma ma'abbũta yãƙi mai tsanani ne, kuma
al'amari yã kõma zuwa gare ki, sabõda haka ki dũbamẽne ne zã ki yi umurui (da
shi)?"
|
Ayah 27:34 الأية
قَالَتْ إِنَّ الْمُلُوكَ إِذَا دَخَلُوا قَرْيَةً أَفْسَدُوهَا وَجَعَلُوا
أَعِزَّةَ أَهْلِهَا أَذِلَّةً ۖ وَكَذَٰلِكَ يَفْعَلُونَ
Qalat inna almulooka ithadakhaloo qaryatan afsadooha wajaAAaloo aAAizzata
ahlihaathillatan wakathalika yafAAaloon
Hausa
Ta ce: "Lalle sarakuna idan sun shiga wata alƙarya, sai su ɓãta ta, kuma su
sanya mãsu darajar mutãnenta ƙasƙantattu. Kuma kamar wancan ne suke likatãwa."
|
Ayah 27:35 الأية
وَإِنِّي مُرْسِلَةٌ إِلَيْهِم بِهَدِيَّةٍ فَنَاظِرَةٌ بِمَ يَرْجِعُ
الْمُرْسَلُونَ
Wa-innee mursilatun ilayhim bihadiyyatin fanathiratunbima yarjiAAu almursaloon
Hausa
"Kuma lalle nĩ mai aikãwa ce zuwa gare su da kyauta, sa'an nan mai dũbawa ce: Da
me manzannin zã su kõmo."
|
Ayah 27:36 الأية
فَلَمَّا جَاءَ سُلَيْمَانَ قَالَ أَتُمِدُّونَنِ بِمَالٍ فَمَا آتَانِيَ اللهُ
خَيْرٌ مِّمَّا آتَاكُم بَلْ أَنتُم بِهَدِيَّتِكُمْ تَفْرَحُونَ
Falamma jaa sulaymana qalaatumiddoonani bimalin fama ataniyaAllahu khayrun mimma
atakum bal antumbihadiyyatikum tafrahoon
Hausa
To, a lõkacin da ya jẽ wa Sulaiman ya ce: "Shin, za ku ƙãra ni da dũkiya ne? To,
abin daAllah Ya bã ni, shi ne mafi alhẽridaga abin da Ya bã ku. A'a, kũ nekuke
yin farin ciki da kyautarku."
|
Ayah 27:37 الأية
ارْجِعْ إِلَيْهِمْ فَلَنَأْتِيَنَّهُم بِجُنُودٍ لَّا قِبَلَ لَهُم بِهَا
وَلَنُخْرِجَنَّهُم مِّنْهَا أَذِلَّةً وَهُمْ صَاغِرُونَ
IrjiAA ilayhim falana/tiyannahum bijunoodinla qibala lahum biha
walanukhrijannahum minhaathillatan wahum saghiroon
Hausa
"Ka kõma zuwa gare su. Sa'an nan lalle munã je musu da rundunõni, bãbu wata
tãɓukawa gare su game da su, kuma lalle munã fitar da su daga gare ta, sunã mafi
wulãkantuwa, kuma sunã ƙasƙantattu."
|
Ayah 27:38 الأية
قَالَ يَا أَيُّهَا الْمَلَأُ أَيُّكُمْ يَأْتِينِي بِعَرْشِهَا قَبْلَ أَن
يَأْتُونِي مُسْلِمِينَ
Qala ya ayyuha almalaoayyukum ya/teenee biAAarshiha qabla an ya/toonee muslimeen
Hausa
Ya ce: "Yã ku mashãwarta! Wannenku zai zo mini da gadonta a gabãnin su zo, sunã
mãsu sallamãwa?"
|
Ayah 27:39 الأية
قَالَ عِفْرِيتٌ مِّنَ الْجِنِّ أَنَا آتِيكَ بِهِ قَبْلَ أَن تَقُومَ مِن
مَّقَامِكَ ۖ وَإِنِّي عَلَيْهِ لَقَوِيٌّ أَمِينٌ
Qala AAifreetun mina aljinni anaateeka bihi qabla an taqooma min maqamika
wa-inneAAalayhi laqawiyyun ameen
Hausa
Wani mai ƙarfi daga aljannu ya ce: "Nĩ inã zo maka da shi a gabãnin ka tãshi
daga matsayinka. Kuma llale nĩ a gare shi, haƙĩƙa, mai ƙarfi ne amintacce."
|
Ayah 27:40 الأية
قَالَ الَّذِي عِندَهُ عِلْمٌ مِّنَ الْكِتَابِ أَنَا آتِيكَ بِهِ قَبْلَ أَن
يَرْتَدَّ إِلَيْكَ طَرْفُكَ ۚ فَلَمَّا رَآهُ مُسْتَقِرًّا عِندَهُ قَالَ هَٰذَا
مِن فَضْلِ رَبِّي لِيَبْلُوَنِي أَأَشْكُرُ أَمْ أَكْفُرُ ۖ وَمَن شَكَرَ
فَإِنَّمَا يَشْكُرُ لِنَفْسِهِ ۖ وَمَن كَفَرَ فَإِنَّ رَبِّي غَنِيٌّ كَرِيمٌ
Qala allathee AAindahu AAilmunmina alkitabi ana ateeka bihi qabla anyartadda
ilayka tarfuka falamma raahumustaqirran AAindahu qala hatha min fadlirabbee
liyabluwanee aashkuru am akfuru waman shakara fa-innamayashkuru linafsihi waman
kafara fa-inna rabbee ghaniyyun kareem
Hausa
Wanda yake a wurinsa akwai wani ilmi daga Littafin ya ce: "Ni inã zo maka da shi
a gabãnin ƙyaftãwar ganinka ta kõma gare ka." To, a lõkacin da ya gan shi
matabbaci a wurinsa, ya ce: "Wannan daga falalar Ubangijĩna yake, dõmin Ya
jarraba ni: Shin, zan gõde ne, kõ kuwa zan butulce! Kuma wanda ya gõde, to, yanã
gõdẽwa ne dõmin kansa, kuma wanda ya kãfirta, to, lalle Ubangijina Wadãtacce ne,
Karĩmi."
|
Ayah 27:41 الأية
قَالَ نَكِّرُوا لَهَا عَرْشَهَا نَنظُرْ أَتَهْتَدِي أَمْ تَكُونُ مِنَ الَّذِينَ
لَا يَهْتَدُونَ
Qala nakkiroo laha AAarshahananthur atahtadee am takoonu mina allatheenala
yahtadoon
Hausa
Ya ce: "Ku canza kamar gadonta gare ta, mu gani, shin zã ta shiryu, kõ kuwa tanã
kasancẽwa daga waɗanda bã su shiryuwa."
|
Ayah 27:42 الأية
فَلَمَّا جَاءَتْ قِيلَ أَهَٰكَذَا عَرْشُكِ ۖ قَالَتْ كَأَنَّهُ هُوَ ۚ
وَأُوتِينَا الْعِلْمَ مِن قَبْلِهَا وَكُنَّا مُسْلِمِينَ
Falamma jaat qeela ahakathaAAarshuki qalat kaannahu huwa waooteena alAAilmamin
qabliha wakunna muslimeen
Hausa
To a lõkacin da ta jẽ aka ce "Shin, kamar wannan gadon sarautarki yake?" Ta ce:
"Kamar dai shĩne. Kuma an bã mu ilmi daga gabãninta kuma mun kasance mãsu
sallamãwar (al'amari ga Allah)."
|
Ayah 27:43 الأية
وَصَدَّهَا مَا كَانَت تَّعْبُدُ مِن دُونِ اللهِ ۖ إِنَّهَا كَانَتْ مِن قَوْمٍ
كَافِرِينَ
Wasaddaha ma kanattaAAbudu min dooni Allahi innaha kanat minqawmin kafireen
Hausa
Kuma abin da ta kasance tanã bautãwa, baicin Allah, ya kange ta. Lalle ita, tã
kasance daga mutãne kãfirai.
|
Ayah 27:44 الأية
قِيلَ لَهَا ادْخُلِي الصَّرْحَ ۖ فَلَمَّا رَأَتْهُ حَسِبَتْهُ لُجَّةً وَكَشَفَتْ
عَن سَاقَيْهَا ۚ قَالَ إِنَّهُ صَرْحٌ مُّمَرَّدٌ مِّن قَوَارِيرَ ۗ قَالَتْ رَبِّ
إِنِّي ظَلَمْتُ نَفْسِي وَأَسْلَمْتُ مَعَ سُلَيْمَانَ لِلَّهِ رَبِّ
الْعَالَمِينَ
Qeela laha odkhulee assarhafalamma raat-hu hasibat-hu lujjatan wakashafat
AAansaqayha qala innahu sarhunmumarradun min qawareera qalat rabbi innee
thalamtunafsee waaslamtu maAAa sulaymana lillahi rabbi alAAalameen
Hausa
Aka ce mata, "Ki shiga a gidan sarauta." To, a lõkacin da ta gan shi, ta yi
zatona wai gurbi ne, kuma ta kuranye daga ƙwaurinta. Ya ce: "Lalle ne shi, gidan
sarauta ne mai santsi daga madũbai." Ta ce: "Yã Ubangijĩna! Bã a rõƙon Allah sai
da sunãyensa mãsu kyau, tis'in da taran nan, sai dai a dunƙule kamar a ce, "Inã
rõƙon Allah da sunãyenSa da na sani da waɗanda ban sani ba." Lalle nĩ, na
zãlunci kaina, kuma nã sallama al'amari tãre da Sulaiman ga Allah, Ubangijin
halittu."
|
Ayah 27:45 الأية
وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا إِلَىٰ ثَمُودَ أَخَاهُمْ صَالِحًا أَنِ اعْبُدُوا اللهَ
فَإِذَا هُمْ فَرِيقَانِ يَخْتَصِمُونَ
Walaqad arsalna ila thamoodaakhahum salihan ani oAAbudoo Allahafa-itha hum
fareeqani yakhtasimoon
Hausa
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, mun aika zuwa Samũdãwa da ɗan'uwansu, Salihu (ya ce), "Ku
bauta wa Allah." Sai gã su ƙungiyõyi biyu sunã ta husũma.
|
Ayah 27:46 الأية
قَالَ يَا قَوْمِ لِمَ تَسْتَعْجِلُونَ بِالسَّيِّئَةِ قَبْلَ الْحَسَنَةِ ۖ
لَوْلَا تَسْتَغْفِرُونَ اللهَ لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ
Qala ya qawmi limatastaAAjiloona bissayyi-ati qabla alhasanati
lawlatastaghfiroona Allaha laAAallakum turhamoon
Hausa
Ya ce: "Yã mutãnẽna! Don me kuke nẽman gaggãwa game da mũnanãwa, a gabãnin
kyautatãwa. Don me bã ku nẽman Allah gãfara, tsammãninku, zã a yi muku rahama?"
|
Ayah 27:47 الأية
قَالُوا اطَّيَّرْنَا بِكَ وَبِمَن مَّعَكَ ۚ قَالَ طَائِرُكُمْ عِندَ اللهِ ۖ
بَلْ أَنتُمْ قَوْمٌ تُفْتَنُونَ
Qaloo ittayyarna bikawabiman maAAaka qala ta-irukum AAinda Allahibal antum
qawmun tuftanoon
Hausa
Suka ce: "Munã shu'umci da kai, kuma da wanda ke tãre da kai." Ya ce:
"Shu'umcinku a wurin Allah yake. Ã'a, kũ mutãne ne, anã fitinar ku."
|
Ayah 27:48 الأية
وَكَانَ فِي الْمَدِينَةِ تِسْعَةُ رَهْطٍ يُفْسِدُونَ فِي الْأَرْضِ وَلَا
يُصْلِحُونَ
Wakana fee almadeenati tisAAatu rahtinyufsidoona fee al-ardi wala yuslihoon
Hausa
Kuma waɗansu jama'a tara sun kasance a cikin birnin, sunã yin ɓarna, kuma bã su
kyautatãwa. Suka ce: "Ku yi rantsuwa da Allah, lalle zã mu kwãnan masa, shi da
mutãnensa sa'an nan mu ce wa waliyyinsa. 'Ba mu halarci halakar mutãnensa ba
kuma mũ, haƙĩ ƙa, mãsu gaskiya ne'."
|
Ayah 27:49 الأية
قَالُوا تَقَاسَمُوا بِاللهِ لَنُبَيِّتَنَّهُ وَأَهْلَهُ ثُمَّ لَنَقُولَنَّ
لِوَلِيِّهِ مَا شَهِدْنَا مَهْلِكَ أَهْلِهِ وَإِنَّا لَصَادِقُونَ
Qaloo taqasamoo billahilanubayyitannahu waahlahu thumma lanaqoolanna liwaliyyihi
mashahidna mahlika ahlihi wa-inna lasadiqoon
Hausa
Kuma suka ƙulla mãkirci, kuma Muka ƙulla sakamakon mãkirci, alhãli sũ ba su sani
ba.
|
Ayah 27:50 الأية
وَمَكَرُوا مَكْرًا وَمَكَرْنَا مَكْرًا وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ
Wamakaroo makran wamakarna makranwahum la yashAAuroon
Hausa
Ka dũba yadda ãƙibar mãkircinsu ta kasance lalle Mũ Mun darkãke su da mutãnensu,
gabã ɗaya.
|
Ayah 27:51 الأية
فَانظُرْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ مَكْرِهِمْ أَنَّا دَمَّرْنَاهُمْ وَقَوْمَهُمْ
أَجْمَعِينَ
Fanthur kayfa kanaAAaqibatu makrihim anna dammarnahumwaqawmahum ajmaAAeen
Hausa
Waɗancan, gidãjensu ne, wõfintattu sabõda zãluncin da suka yi, lalle ne a wancan
akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke sani.
|
Ayah 27:52 الأية
فَتِلْكَ بُيُوتُهُمْ خَاوِيَةً بِمَا ظَلَمُوا ۗ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَةً
لِّقَوْمٍ يَعْلَمُونَ
Fatilka buyootuhum khawiyatan bimathalamoo inna fee thalika laayatanliqawmin
yaAAlamoon
Hausa
Muka tsĩrar da waɗanda suka yi ĩmãni, kuma sun kasance sunã taƙawa.
|
Ayah 27:53 الأية
وَأَنجَيْنَا الَّذِينَ آمَنُوا وَكَانُوا يَتَّقُونَ
Waanjayna allatheena amanoowakanoo yattaqoon
Hausa
Da Lũdu, a lõkacin da ya ce wa mutãnensa, "Shin kunã jẽ wa alfasha ne, alhãli,
kuwa kunã gani?"
|
Ayah 27:54 الأية
وَلُوطًا إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِ أَتَأْتُونَ الْفَاحِشَةَ وَأَنتُمْ تُبْصِرُونَ
Walootan ith qalaliqawmihi ata/toona alfahishata waantum tubsiroon
Hausa
"Shin lalle kũ haƙĩƙa kunã je wa maza da sha'awa baicin mãtã? Ã'a, kũ wasu irin
mutãne ne kuna aikin jãhilci."
|
Ayah 27:55 الأية
أَئِنَّكُمْ لَتَأْتُونَ الرِّجَالَ شَهْوَةً مِّن دُونِ النِّسَاءِ ۚ بَلْ أَنتُمْ
قَوْمٌ تَجْهَلُونَ
A-innakum lata/toona arrijalashahwatan min dooni annisa-i bal antum
qawmuntajhaloon
Hausa
Suka ce: "Ku yi rantsuwa da Allah, lalle zã mu kwãnan masa, shi da mutãnensa sa'an nan mu ce wa waliyyinsa. 'Ba mu halarci halakar mutãnensa ba kuma mũ, haƙĩ ƙa, mãsu gaskiya ne'.". (49..)
|
Ayah 27:56 الأية
فَمَا كَانَ جَوَابَ قَوْمِهِ إِلَّا أَن قَالُوا أَخْرِجُوا آلَ لُوطٍ مِّن
قَرْيَتِكُمْ ۖ إِنَّهُمْ أُنَاسٌ يَتَطَهَّرُونَ
Fama kana jawabaqawmihi illa an qaloo akhrijoo ala lootinmin qaryatikum innahum
onasun yatatahharoon
Hausa
Bãbu abin da ya kasance jawãbin mutãnensa fãce suka ce "Ku fitar da mutãnen Lũɗu
daga alƙaryarku, lalle sũ, wasu irin mutãne ne mãsu da'awar sunã da tsarki."
|
Ayah 27:57 الأية
فَأَنجَيْنَاهُ وَأَهْلَهُ إِلَّا امْرَأَتَهُ قَدَّرْنَاهَا مِنَ الْغَابِرِينَ
Faanjaynahu waahlahu illaimraatahu qaddarnaha mina alghabireen
Hausa
Sai Muka tsĩrar da shi, shi da mutãnensa, fãce mãtarsa, Mun ƙaddara ta a cikin
mãsu wanzuwa.
|
Ayah 27:58 الأية
وَأَمْطَرْنَا عَلَيْهِم مَّطَرًا ۖ فَسَاءَ مَطَرُ الْمُنذَرِينَ
Waamtarna AAalayhim mataranfasaa mataru almunthareen
Hausa
Kuma Muka yi ruwa a kansu da wani irin ruwa. To, ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi
ya mũnana.
|
Ayah 27:59 الأية
قُلِ الْحَمْدُ لِلَّهِ وَسَلَامٌ عَلَىٰ عِبَادِهِ الَّذِينَ اصْطَفَىٰ ۗ آللهُ
خَيْرٌ أَمَّا يُشْرِكُونَ
Quli alhamdu lillahi wasalamunAAala AAibadihi allatheena istafaallahu khayrun
amma yushrikoon
Hausa
Ka ce: "Godiya ta tabbata ga A1lah, kuma aminci ya tabbata bisa ga bãyinSa,
waɗanda Ya zãɓa." Shin Allah ne Mafi alhẽri koabin da suke yin shirki da Shi?
|
Ayah 27:60 الأية
أَمَّنْ خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَأَنزَلَ لَكُم مِّنَ السَّمَاءِ مَاءً
فَأَنبَتْنَا بِهِ حَدَائِقَ ذَاتَ بَهْجَةٍ مَّا كَانَ لَكُمْ أَن تُنبِتُوا
شَجَرَهَا ۗ أَإِلَٰهٌ مَّعَ اللهِ ۚ بَلْ هُمْ قَوْمٌ يَعْدِلُونَ
Amman khalaqa assamawatiwal-arda waanzala lakum mina assama-imaan faanbatna bihi
hada-iqa thatabahjatin ma kana lakum an tunbitoo shajarahaa-ilahun maAAa Allahi
bal hum qawmun yaAAdiloon
Hausa
Kõ wãne ne Ya halitta sammai da ƙasa kuma Ya saukar muku, daga, sama, wani ruwa,
Muka tsirar, game da shi, gõnaki mãsu sha'awa, ba ya kasancẽwa gare ku, ku
tsirar da itãcensu? Shin, akwai abin bautãwa tãre da Allah? Ã'a, sũ mutãne ne
suna daidaitãwa (Allah da wani).
|
Ayah 27:61 الأية
أَمَّن جَعَلَ الْأَرْضَ قَرَارًا وَجَعَلَ خِلَالَهَا أَنْهَارًا وَجَعَلَ لَهَا
رَوَاسِيَ وَجَعَلَ بَيْنَ الْبَحْرَيْنِ حَاجِزًا ۗ أَإِلَٰهٌ مَّعَ اللهِ ۚ
بَلْ أَكْثَرُهُمْ لَا يَعْلَمُونَ
Amman jaAAala al-arda qararanwajaAAala khilalaha anharan wajaAAala laharawasiya
wajaAAala bayna albahrayni hajizana-ilahun maAAa Allahi bal aktharuhum
layaAAlamoon
Hausa
Kõ kuwa wãne ne Ya sanya ƙasa tabbatacciya, kuma Ya sanya kõguna a tsakãninta
kuma Ya sanya mata manyan duwãtsu tabatattu, kuma Ya sanya wani shãmaki a
tsakãnin tẽkuna biyu? Shin akwai wani abin bautãwa tãre da Allah. Ã'a, mafi
yawansu ba su sanĩ ba.
|
Ayah 27:62 الأية
أَمَّن يُجِيبُ الْمُضْطَرَّ إِذَا دَعَاهُ وَيَكْشِفُ السُّوءَ وَيَجْعَلُكُمْ
خُلَفَاءَ الْأَرْضِ ۗ أَإِلَٰهٌ مَّعَ اللهِ ۚ قَلِيلًا مَّا تَذَكَّرُونَ
Amman yujeebu almudtarra ithadaAAahu wayakshifu assoo-a wayajAAalukum
khulafaaal-ardi a-ilahun maAAa Allahi qaleelan matathakkaroon
Hausa
Kõ wãne ne yake karɓã , kuma ya sanya ku mamãyan ƙasa? Shin akwai wani abin
bautawa tãre da Allah? Kaɗan ƙwarai kuke yin tunãni.
|
Ayah 27:63 الأية
أَمَّن يَهْدِيكُمْ فِي ظُلُمَاتِ الْبَرِّ وَالْبَحْرِ وَمَن يُرْسِلُ الرِّيَاحَ
بُشْرًا بَيْنَ يَدَيْ رَحْمَتِهِ ۗ أَإِلَٰهٌ مَّعَ اللهِ ۚ تَعَالَى اللهُ
عَمَّا يُشْرِكُونَ
Amman yahdeekum fee thulumatialbarri walbahri waman yursilu arriyahabushran
bayna yaday rahmatihi a-ilahun maAAa AllahitaAAala Allahu AAamma yushrikoon
Hausa
Kõ wãne ne yake shiryarwa a cikin duffan ƙasa da tẽku,kuma wãne ne Yake aikõwar
iskõki dõmin bãyar da bushãra a gaba ga rahamarSa? Ashe akwai wani abin bautãwa
tãre da Allah? tsarki yã tabbata ga Allah daga barin abin da suke shirki da Shi.
|
Ayah 27:64 الأية
أَمَّن يَبْدَأُ الْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُ وَمَن يَرْزُقُكُم مِّنَ السَّمَاءِ
وَالْأَرْضِ ۗ أَإِلَٰهٌ مَّعَ اللهِ ۚ قُلْ هَاتُوا بُرْهَانَكُمْ إِن كُنتُمْ
صَادِقِينَ
Amman yabdao alkhalqa thumma yuAAeeduhuwaman yarzuqukum mina assama-i
wal-ardia-ilahun maAAa Allahi qul hatoo burhanakumin kuntum sadiqeen
Hausa
Kõ wãne ne yake fã ra halitta sa'an nan kuma ya mayar da ita,kuma Wãne ne Ya
azurta ku daga sama da ƙasa? Ashe, akwai wani abin bautãwa tãre da Allah? Ka ce:
"Ku kãwo dalĩlinku idan kun kasance mãsu gaskiya."
|
Ayah 27:65 الأية
قُل لَّا يَعْلَمُ مَن فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ الْغَيْبَ إِلَّا اللهُ ۚ
وَمَا يَشْعُرُونَ أَيَّانَ يُبْعَثُونَ
Qul la yaAAlamu man fee assamawatiwal-ardi alghayba illa Allahu wamayashAAuroona
ayyana yubAAathoon
Hausa
Ka ce: "Bãbu wanda ya san gaibi a cikin sammai da ƙasa fãce Allah. Kuma bã su
sansancẽwar a yaushe ne zã a tãyar da su."
|
Ayah 27:66 الأية
بَلِ ادَّارَكَ عِلْمُهُمْ فِي الْآخِرَةِ ۚ بَلْ هُمْ فِي شَكٍّ مِّنْهَا ۖ بَلْ
هُم مِّنْهَا عَمُونَ
Bali iddaraka AAilmuhum fee al-akhiratibal hum fee shakkin minha bal hum minha
AAamoon
Hausa
Ã'a, saninsu ya kai a cikin Lãhira Ã'a, sunã cikin shakka daga gare ta. Ã'a, sũ
da gare ta makãfin zũci ne.
|
Ayah 27:67 الأية
وَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا أَإِذَا كُنَّا تُرَابًا وَآبَاؤُنَا أَئِنَّا
لَمُخْرَجُونَ
Waqala allatheena kafaroo a-ithakunna turaban waabaona a-innalamukhrajoon
Hausa
Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Shin idan mun kasance turɓaya, mu da
ubanninmu, shin, haƙĩƙa, waɗanda ake fitarwa ne?"
|
Ayah 27:68 الأية
لَقَدْ وُعِدْنَا هَٰذَا نَحْنُ وَآبَاؤُنَا مِن قَبْلُ إِنْ هَٰذَا إِلَّا
أَسَاطِيرُ الْأَوَّلِينَ
Laqad wuAAidna hatha nahnuwaabaona min qablu in hatha illaasateeru al-awwaleen
Hausa
"Lalle ne, haƙĩƙa, an yi mana wa'adi ga wannan, mũ da ubanninmu, daga gabãnin
haka. Wannan bã kõme ba ne fãce tãtsũniyõyin farko."
|
Ayah 27:69 الأية
قُلْ سِيرُوا فِي الْأَرْضِ فَانظُرُوا كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُجْرِمِينَ
Qul seeroo fee al-ardi fanthurookayfa kana AAaqibatu almujrimeen
Hausa
Ka ce: "Ku yi tafiya a cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba, yãya ãƙibar mãsu laifi
take?"
|
Ayah 27:70 الأية
وَلَا تَحْزَنْ عَلَيْهِمْ وَلَا تَكُن فِي ضَيْقٍ مِّمَّا يَمْكُرُونَ
Wala tahzan AAalayhim walatakun fee dayqin mimma yamkuroon
Hausa
Kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma kada ka kasance a cikin ƙuncin rai daga
abin da suke ƙullãwa na mãkirci.
|
Ayah 27:71 الأية
وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا الْوَعْدُ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ
Wayaqooloona mata hathaalwaAAdu in kuntum sadiqeen
Hausa
Kuma sunã cẽwa, "A yaushe wannan wa'adi (zai auku), idan kun kasance mãsu
gaskiya?"
|
Ayah 27:72 الأية
قُلْ عَسَىٰ أَن يَكُونَ رَدِفَ لَكُم بَعْضُ الَّذِي تَسْتَعْجِلُونَ
Qul AAasa an yakoona radifa lakumbaAAdu allathee tastaAAjiloon
Hausa
Ka ce: "Akwai fatan sãshen abin da kuke, nẽman gaggãwarsa, ya kasance yã kuturta
a gare ku."
|
Ayah 27:73 الأية
وَإِنَّ رَبَّكَ لَذُو فَضْلٍ عَلَى النَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا
يَشْكُرُونَ
Wa-inna rabbaka lathoo fadlinAAala annasi walakinna aktharahum layashkuroon
Hausa
Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa Mai falala ne a kanmutãne kuma amma mafi
yawansu, bã su gõdẽwa.
|
Ayah 27:74 الأية
وَإِنَّ رَبَّكَ لَيَعْلَمُ مَا تُكِنُّ صُدُورُهُمْ وَمَا يُعْلِنُونَ
Wa-inna rabbaka layaAAlamu ma tukinnusudooruhum wama yuAAlinoon
Hausa
Kuma lalle Ubangijinka, haƙĩƙa Yanã sanin abin da ƙirãzansu suke, ɓõyẽwa, da
abin da suke hayyanãwa.
|
Ayah 27:75 الأية
وَمَا مِنْ غَائِبَةٍ فِي السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ إِلَّا فِي كِتَابٍ مُّبِينٍ
Wama min gha-ibatin fee assama-iwal-ardi illa fee kitabin mubeen
Hausa
Kuma bãbu wata (mas'ala) mai bõyuwa, a cikin sama da ƙasa fãce tanã a cikin
littafi bayyananne.
|
Ayah 27:76 الأية
إِنَّ هَٰذَا الْقُرْآنَ يَقُصُّ عَلَىٰ بَنِي إِسْرَائِيلَ أَكْثَرَ الَّذِي هُمْ
فِيهِ يَخْتَلِفُونَ
Inna hatha alqur-ana yaqussuAAala banee isra-eela akthara allathee humfeehi
yakhtalifoon
Hausa
Lalle ne wannan Alƙur'ãni yanã gaya wa Banĩ Isrãĩla mafi yawan abin da sũ suke
sãɓa wa jũnansu a ciki.
|
Ayah 27:77 الأية
وَإِنَّهُ لَهُدًى وَرَحْمَةٌ لِّلْمُؤْمِنِينَ
Wa-innahu lahudan warahmatunlilmu/mineen
Hausa
Kuma lalle shi haƙĩƙa shiriya ce da rahama ga mũminai.
|
Ayah 27:78 الأية
إِنَّ رَبَّكَ يَقْضِي بَيْنَهُم بِحُكْمِهِ ۚ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْعَلِيمُ
Inna rabbaka yaqdee baynahum bihukmihiwahuwa alAAazeezu alAAaleem
Hausa
"Lalle Ubangijinka Yanã yin hukunci a tsakãninsu da hukuncinsa, kuma Shi ne
Mabuwãyi, Masani."
|
Ayah 27:79 الأية
فَتَوَكَّلْ عَلَى اللهِ ۖ إِنَّكَ عَلَى الْحَقِّ الْمُبِينِ
Fatawakkal AAala Allahi innakaAAala alhaqqi almubeen
Hausa
Sabõda haka, ka dõgara ga Allah, lalle ne, kai ne a kan gaskiya bayyananniya.
|
Ayah 27:80 الأية
إِنَّكَ لَا تُسْمِعُ الْمَوْتَىٰ وَلَا تُسْمِعُ الصُّمَّ الدُّعَاءَ إِذَا
وَلَّوْا مُدْبِرِينَ
Innaka la tusmiAAu almawta walatusmiAAu assumma adduAAaa ithawallaw mudbireen
Hausa
Lalle ne kai, bã ka jiyar da matattu, kuma bã ka sa kurãme su ji kiranka, idan
sun jũya sunã mãsu bãyar da bãya.
|
Ayah 27:81 الأية
وَمَا أَنتَ بِهَادِي الْعُمْيِ عَن ضَلَالَتِهِمْ ۖ إِن تُسْمِعُ إِلَّا مَن
يُؤْمِنُ بِآيَاتِنَا فَهُم مُّسْلِمُونَ
Wama anta bihadee alAAumyiAAan dalalatihim in tusmiAAu illa manyu/minu
bi-ayatina fahum muslimoon
Hausa
Kuma kai ba ka zama mai shiryar da ɗimammu daga ɓata ba. Bã ka jiyarwa fãce
wanda yake yin ĩmãni da ãyõyinMu. To, sũ ne mãsu sallamãwa (al'amari zuwa ga
Allah).
|
Ayah 27:82 الأية
وَإِذَا وَقَعَ الْقَوْلُ عَلَيْهِمْ أَخْرَجْنَا لَهُمْ دَابَّةً مِّنَ الْأَرْضِ
تُكَلِّمُهُمْ أَنَّ النَّاسَ كَانُوا بِآيَاتِنَا لَا يُوقِنُونَ
Wa-itha waqaAAa alqawlu AAalayhimakhrajna lahum dabbatan mina
al-arditukallimuhum anna annasa kanoo bi-ayatinala yooqinoon
Hausa
Kuma idan magana ta auku a kansu, Munã fitar musu da wata dabba daga ƙasa, tanã
yi musu magana, cẽwa "Lalle mutãne sun kasance game da ayoyinMu, ba su yin
ĩmãnin yaƙĩni."
|
Ayah 27:83 الأية
وَيَوْمَ نَحْشُرُ مِن كُلِّ أُمَّةٍ فَوْجًا مِّمَّن يُكَذِّبُ بِآيَاتِنَا فَهُمْ
يُوزَعُونَ
Wayawma nahshuru min kulli ommatinfawjan mimman yukaththibu bi-ayatinafahum
yoozaAAoon
Hausa
Kuma a rãnar da Muke tãrãwa daga kõwace al'umma, wata ƙungiya daga waɗanda suke
ƙaryata ãyõyinMu, sai ga su anã kangesu. (ga kõra)
|
Ayah 27:84 الأية
حَتَّىٰ إِذَا جَاءُوا قَالَ أَكَذَّبْتُم بِآيَاتِي وَلَمْ تُحِيطُوا بِهَا
عِلْمًا أَمَّاذَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Hatta itha jaooqala akaththabtum bi-ayatee walam tuheetoobiha AAilman ammatha
kuntum taAAmaloon
Hausa
Har idan sun zo, (Allah) zai ce, "Ashe kun ƙaryata ãyõyinNa, kuma ba ku kẽwaye
su da sani ba? To, mẽne ne kuka kasance kunã aikatãwa?"
|
Ayah 27:85 الأية
وَوَقَعَ الْقَوْلُ عَلَيْهِم بِمَا ظَلَمُوا فَهُمْ لَا يَنطِقُونَ
WawaqaAAa alqawlu AAalayhim bima thalamoofahum la yantiqoon
Hausa
Kuma magana ta auku a kansu, sabõda zãluncin da suka yi. To, sũ bã su da ta
cẽwa.
|
Ayah 27:86 الأية
أَلَمْ يَرَوْا أَنَّا جَعَلْنَا اللَّيْلَ لِيَسْكُنُوا فِيهِ وَالنَّهَارَ
مُبْصِرًا ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ
Alam yaraw anna jaAAalnaallayla liyaskunoo feehi wannahara mubsiraninna fee
thalika laayatin liqawmin yu/minoon
Hausa
Shin, ba su gani ba, cẽwa, lalle Mũ, Mun sanya dare dõmin su natsu a cikinsa,
kuma da yini mai sanya gani? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi! Dõmin mutãne
waɗanda suka yi ĩmãni.
|
Ayah 27:87 الأية
وَيَوْمَ يُنفَخُ فِي الصُّورِ فَفَزِعَ مَن فِي السَّمَاوَاتِ وَمَن فِي الْأَرْضِ
إِلَّا مَن شَاءَ اللهُ ۚ وَكُلٌّ أَتَوْهُ دَاخِرِينَ
Wayawma yunfakhu fee assoorifafaziAAa man fee assamawati waman feeal-ardi illa
man shaa Allahu wakullunatawhu dakhireen
Hausa
Kuma da rãnar da ake hũsa a cikin ƙaho, sai wandayake a cikin sammai da waɗanda
suke a cikin ƙasa su firgita, fãce wanda Allah Ya so, kuma dukansu, su je Masa
sunã ƙasƙantattu.
|
Ayah 27:88 الأية
وَتَرَى الْجِبَالَ تَحْسَبُهَا جَامِدَةً وَهِيَ تَمُرُّ مَرَّ السَّحَابِ ۚ
صُنْعَ اللهِ الَّذِي أَتْقَنَ كُلَّ شَيْءٍ ۚ إِنَّهُ خَبِيرٌ بِمَا تَفْعَلُونَ
Watara aljibala tahsabuhajamidatan wahiya tamurru marra assahabi sunAAaAllahi
allathee atqana kulla shay-in innahukhabeerun bima tafAAaloon
Hausa
Kuma kanã ganin duwãtsu, kanã zaton su sandararru, alhãli kuwa sũ sunã shũɗẽwa
shũɗewar girgije, bisa sanã'ar Allah wanda Ya kyautata kõwane abu. Lalle Shi,
Mai lãbartãwa ne game da abin da kuke aikatãwa.
|
Ayah 27:89 الأية
مَن جَاءَ بِالْحَسَنَةِ فَلَهُ خَيْرٌ مِّنْهَا وَهُم مِّن فَزَعٍ يَوْمَئِذٍ
آمِنُونَ
Man jaa bilhasanatifalahu khayrun minha wahum min fazaAAin yawma-ithinaminoon
Hausa
Wanda ya zo da kyakkyawan aiki guda, to, yanã da mafi alhẽri daga gare shi. Kuma
sũ daga wata firgita, a yinin nan, amintattu ne.
|
Ayah 27:90 الأية
وَمَن جَاءَ بِالسَّيِّئَةِ فَكُبَّتْ وُجُوهُهُمْ فِي النَّارِ هَلْ تُجْزَوْنَ
إِلَّا مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Waman jaa bissayyi-atifakubbat wujoohuhum fee annari hal tujzawna illama kuntum
taAAmaloon
Hausa
Kuma wanda ya zo da mugun aiki, to, an kife fuskõkinsu a cikin wuta. Ko zã a
sãka muku fãce da abin da kuka kasance kũnã aikatãwa?
|
Ayah 27:91 الأية
إِنَّمَا أُمِرْتُ أَنْ أَعْبُدَ رَبَّ هَٰذِهِ الْبَلْدَةِ الَّذِي حَرَّمَهَا
وَلَهُ كُلُّ شَيْءٍ ۖ وَأُمِرْتُ أَنْ أَكُونَ مِنَ الْمُسْلِمِينَ
Innama omirtu an aAAbuda rabba hathihialbaldati allathee harramaha walahu
kullushay-in waomirtu an akoona mina almuslimeen
Hausa
(Ka ce): "An umurce ni, in bauta wa Ubangijin wannan Gari, Wanda Ya mayar da shi
Hurumi, kuma Yanã da dukan kõme. Kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu
sallamãwa."
|
Ayah 27:92 الأية
وَأَنْ أَتْلُوَ الْقُرْآنَ ۖ فَمَنِ اهْتَدَىٰ فَإِنَّمَا يَهْتَدِي لِنَفْسِهِ ۖ
وَمَن ضَلَّ فَقُلْ إِنَّمَا أَنَا مِنَ الْمُنذِرِينَ
Waan atluwa alqur-ana famani ihtadafa-innama yahtadee linafsihi waman dalla
faqulinnama ana mina almunthireen
Hausa
"Kuma inã karanta Alƙur'ãni." To, wanda ya shiryu, yã shiryu ne dõmin kansa
kawai. Kuma wanda ya ɓãce, to, ka ce: "Ni daga mãsu gargaɗi kawai nake."
|
Ayah 27:93 الأية
وَقُلِ الْحَمْدُ لِلَّهِ سَيُرِيكُمْ آيَاتِهِ فَتَعْرِفُونَهَا ۚ وَمَا رَبُّكَ
بِغَافِلٍ عَمَّا تَعْمَلُونَ
Waquli alhamdu lillahisayureekum ayatihi fataAArifoonaha wamarabbuka bighafilin
AAamma taAAmaloon
Hausa
Kuma ka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah. Zai nũna muku ãyõyinSa, har ku sansu."
Kuma Ubangijinka bai zama Mai shagala daga barin abin da kuke aikatãwa ba.
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|