Prev  

29. Surah Al-'Ankabűt سورة العنكبوت

  Next  



1st Ayah  1  الأية ١الأولي
بِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
الم
Alif-lam-meem

Hausa
 
A. L̃. M̃.

Ayah  29:2  الأية
أَحَسِبَ النَّاسُ أَن يُتْرَكُوا أَن يَقُولُوا آمَنَّا وَهُمْ لَا يُفْتَنُونَ
Ahasiba annasu anyutrakoo an yaqooloo amanna wahum layuftanoon

Hausa
 
Ashe, mutăne sun yi zaton a bar su su ce: "Mun yi ĩmăni," alhăli kuwa bă ză a fitine su ba?"

Ayah  29:3  الأية
وَلَقَدْ فَتَنَّا الَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۖ فَلَيَعْلَمَنَّ اللهُ الَّذِينَ صَدَقُوا وَلَيَعْلَمَنَّ الْكَاذِبِينَ
Walaqad fatanna allatheena minqablihim falayaAAlamanna Allahu allatheena sadaqoowalayaAAlamanna alkathibeen

Hausa
 
Kuma lalle Mun fitini waɗanda ke a gabăninsu, dőmin lalle Allah Ya san waɗanda suka yi gaskiya, kuma lalle Ya san maƙaryata.

Ayah  29:4  الأية
أَمْ حَسِبَ الَّذِينَ يَعْمَلُونَ السَّيِّئَاتِ أَن يَسْبِقُونَا ۚ سَاءَ مَا يَحْكُمُونَ
Am hasiba allatheenayaAAmaloona assayyi-ati an yasbiqoona saama yahkumoon

Hausa
 
Kő waɗanda ke aikata miyăgun ayyuka sun yi zaton su tsẽre Mana? Abin da suke hukuntăwa ya mũnana.

Ayah  29:5  الأية
مَن كَانَ يَرْجُو لِقَاءَ اللهِ فَإِنَّ أَجَلَ اللهِ لَآتٍ ۚ وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ
Man kana yarjoo liqaa Allahifa-inna ajala Allahi laatin wahuwa assameeAAualAAaleem

Hausa
 
Wanda ya kasance yană fătan gamuwa da Al1ah to lalle ajalin Allah mai zuwa ne, kuma (Allah) Shĩ ne Mai ji, Masani.

Ayah  29:6  الأية
وَمَن جَاهَدَ فَإِنَّمَا يُجَاهِدُ لِنَفْسِهِ ۚ إِنَّ اللهَ لَغَنِيٌّ عَنِ الْعَالَمِينَ
Waman jahada fa-innama yujahidulinafsihi inna Allaha laghaniyyun AAani alAAalameen

Hausa
 
Kuma wanda ya yi jihădi, to, yană yin jihădin ne dőmin kansa. lalle Allah haƙĩƙa waɗatacce ne daga barin tălikai.

Ayah  29:7  الأية
وَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَنُكَفِّرَنَّ عَنْهُمْ سَيِّئَاتِهِمْ وَلَنَجْزِيَنَّهُمْ أَحْسَنَ الَّذِي كَانُوا يَعْمَلُونَ
Wallatheena amanoowaAAamiloo assalihati lanukaffirannaAAanhum sayyi-atihim walanajziyannahum ahsana allatheekanoo yaAAmaloon

Hausa
 
Kuma waɗanda suka yi ĩmăni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle Mună kankare musu miyăgun ayyukansu, kuma lalle Mună săka musu da mafi kyaun abin da suka kasance sună aikatăwa.

Ayah  29:8  الأية
وَوَصَّيْنَا الْإِنسَانَ بِوَالِدَيْهِ حُسْنًا ۖ وَإِن جَاهَدَاكَ لِتُشْرِكَ بِي مَا لَيْسَ لَكَ بِهِ عِلْمٌ فَلَا تُطِعْهُمَا ۚ إِلَيَّ مَرْجِعُكُمْ فَأُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Wawassayna al-insana biwalidayhihusnan wa-in jahadaka litushrika bee malaysa laka bihi AAilmun fala tutiAAhumailayya marjiAAukum faonabbi-okum bima kuntum taAAmaloon

Hausa
 
Kuma Mun yi wa mutum wasiyyar kyautatăwa ga uwayensa, kuma idan sun tsananta maka dőmin ka yi shirki da Ni game da abin da bă ka da ilmi gare shi, to, kada ka yi musu ɗă'ă. Zuwa gare Ni makőmarku take sa'an nan In bă ku lăbari ga abin da kuka kasance kună aikatăwa.

Ayah  29:9  الأية
وَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَنُدْخِلَنَّهُمْ فِي الصَّالِحِينَ
Wallatheena amanoowaAAamiloo assalihati lanudkhilannahum feeassaliheen

Hausa
 
Kuma waɗanda suka yi ĩmăni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle Mună shigar da su a cikin mutănen kirki.

Ayah  29:10  الأية
وَمِنَ النَّاسِ مَن يَقُولُ آمَنَّا بِاللهِ فَإِذَا أُوذِيَ فِي اللهِ جَعَلَ فِتْنَةَ النَّاسِ كَعَذَابِ اللهِ وَلَئِن جَاءَ نَصْرٌ مِّن رَّبِّكَ لَيَقُولُنَّ إِنَّا كُنَّا مَعَكُمْ ۚ أَوَلَيْسَ اللهُ بِأَعْلَمَ بِمَا فِي صُدُورِ الْعَالَمِينَ
Wamina annasi man yaqoolu amannabillahi fa-itha oothiya fee AllahijaAAala fitnata annasi kaAAathabi Allahiwala-in jaa nasrun min rabbika layaqoolunna innakunna maAAakum awa laysa Allahu bi-aAAlama bimafee sudoori alAAalameen

Hausa
 
Kuma daga cikin mutăne akwai mai cẽwa, 'Mun yi ĩmăni da Allah" sa'an nan idan aka cũce shi wajen aikin Allah, sai ya sanya fitinar mutăne kamar azăbar Allah kuma lalle idan taimakon Ubangijinka ya zo, haƙĩƙa, ya kan ce: "Lalle mũ mun kasance tăre da ku." shin, Allah bai zama Mafi sani ba ga abin da ke a cikin ƙirăzan halittunSa?

Ayah  29:11  الأية
وَلَيَعْلَمَنَّ اللهُ الَّذِينَ آمَنُوا وَلَيَعْلَمَنَّ الْمُنَافِقِينَ
WalayaAAlamanna Allahu allatheenaamanoo walayaAAlamanna almunafiqeen

Hausa
 
Kuma lalle Allah na sanin waɗanda suka yi ĩmăni kuma lalle Yană sanin munfukai.

Ayah  29:12  الأية
وَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا لِلَّذِينَ آمَنُوا اتَّبِعُوا سَبِيلَنَا وَلْنَحْمِلْ خَطَايَاكُمْ وَمَا هُم بِحَامِلِينَ مِنْ خَطَايَاهُم مِّن شَيْءٍ ۖ إِنَّهُمْ لَكَاذِبُونَ
Waqala allatheena kafaroolillatheena amanoo ittabiAAoo sabeelanawalnahmil khatayakum wama hum bihamileenamin khatayahum min shay-in innahum lakathiboon

Hausa
 
Kuma waɗanda suka kăfirta suka ce wa waɗanda suka yi ĩmăni, "Ku bi hanyarmu, kuma Mu ɗauki laifuffukanku," alhăli kőwa ba su zamo măsu ɗauka da a kőme ba daga laifuffukansu. Lalle sũ maƙaryata ne.

Ayah  29:13  الأية
وَلَيَحْمِلُنَّ أَثْقَالَهُمْ وَأَثْقَالًا مَّعَ أَثْقَالِهِمْ ۖ وَلَيُسْأَلُنَّ يَوْمَ الْقِيَامَةِ عَمَّا كَانُوا يَفْتَرُونَ
Walayahmilunna athqalahumwaathqalan maAAa athqalihim walayus-alunna yawmaalqiyamati AAamma kanoo yaftaroon

Hausa
 
Kuma lalle sună ɗaukar kăyan nauyinsu da waɗansu nauyăyan kăya tăre da kăyan nauyinsu, kuma lalle ză a tambaye su a Rănar ˇiyama game da abin da suka kasance sună ƙirƙirăwa na ƙarya.

Ayah  29:14  الأية
وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوْمِهِ فَلَبِثَ فِيهِمْ أَلْفَ سَنَةٍ إِلَّا خَمْسِينَ عَامًا فَأَخَذَهُمُ الطُّوفَانُ وَهُمْ ظَالِمُونَ
Walaqad arsalna noohan ilaqawmihi falabitha feehim alfa sanatin illa khamseena AAamanfaakhathahumu attoofanu wahum thalimoon

Hausa
 
Kuma lalle Mun aika Nũhu zuwa ga mutănensa, sai ya zauna a cikinsu shẽkara dubu făce shẽkara hamsin, sa'an nan cikowar (¦ũfăna) ta kămă su, alhăli kuwa sũ ne măsu zălunci.

Ayah  29:15  الأية
فَأَنجَيْنَاهُ وَأَصْحَابَ السَّفِينَةِ وَجَعَلْنَاهَا آيَةً لِّلْعَالَمِينَ
Faanjaynahu waas-haba assafeenatiwajaAAalnaha ayatan lilAAalameen

Hausa
 
Sa'an nan Muka tsĩrar da shi da mutănen jirgin, kuma Muka sanya jirgin ya zama wata ăyă ga tălikai.

Ayah  29:16  الأية
وَإِبْرَاهِيمَ إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِ اعْبُدُوا اللهَ وَاتَّقُوهُ ۖ ذَٰلِكُمْ خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ
Wa-ibraheema ith qalaliqawmihi oAAbudoo Allaha wattaqoohu thalikumkhayrun lakum in kuntum taAAlamoon

Hausa
 
Da Ibrăhĩm a lőkacin da ya ce wa mutănensa, "Ku baută wa Allah ku bĩ Shi da taƙawa. Wannan Shĩ ne alhẽri a gare ku idan kun kasance kună sani.

Ayah  29:17  الأية
إِنَّمَا تَعْبُدُونَ مِن دُونِ اللهِ أَوْثَانًا وَتَخْلُقُونَ إِفْكًا ۚ إِنَّ الَّذِينَ تَعْبُدُونَ مِن دُونِ اللهِ لَا يَمْلِكُونَ لَكُمْ رِزْقًا فَابْتَغُوا عِندَ اللهِ الرِّزْقَ وَاعْبُدُوهُ وَاشْكُرُوا لَهُ ۖ إِلَيْهِ تُرْجَعُونَ
Innama taAAbudoona min dooni Allahiawthanan watakhluqoona ifkan inna allatheenataAAbudoona min dooni Allahi la yamlikoona lakumrizqan fabtaghoo AAinda Allahi arrizqa waAAbudoohuwashkuroo lahu ilayhi turjaAAoon

Hausa
 
"Abin da dai kuke bautăwa, baiein Allah, gumaka ne, kuma kun ƙirƙira ƙarya. Lalle waɗannan da kuke bauta wa baicin Allah, bă su mallakă muku arziki. Sabőda haka ku nẽmi arziki a wurin Allah kawai, kuma ku bauta Masa, kuma ku yi gődiya zuwa gare Shi. Zuwa gare Shi ake mayar da ku.

Ayah  29:18  الأية
وَإِن تُكَذِّبُوا فَقَدْ كَذَّبَ أُمَمٌ مِّن قَبْلِكُمْ ۖ وَمَا عَلَى الرَّسُولِ إِلَّا الْبَلَاغُ الْمُبِينُ
Wa-in tukaththiboo faqad kaththabaomamun min qablikum wama AAala arrasooliilla albalaghu almubeen

Hausa
 
"Kuma idan kun ƙaryata, to, lalle waɗansu al'ummőmi a gabăninku sun ƙaryata, kuma băbu abin da ke kan Manzo, făce iyar da manzanci, iyarwa bayyananna."

Ayah  29:19  الأية
أَوَلَمْ يَرَوْا كَيْفَ يُبْدِئُ اللهُ الْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُ ۚ إِنَّ ذَٰلِكَ عَلَى اللهِ يَسِيرٌ
Awa lam yaraw kayfa yubdi-o Allahualkhalqa thumma yuAAeeduhu inna thalika AAala Allahiyaseer

Hausa
 
Shin, ba su ga yadda Allah ke făra yin halitta ba, sa'an nan kuma Ya mayar da ita? Lalle wannan abu ne mai sauƙi ga Allah.

Ayah  29:20  الأية
قُلْ سِيرُوا فِي الْأَرْضِ فَانظُرُوا كَيْفَ بَدَأَ الْخَلْقَ ۚ ثُمَّ اللهُ يُنشِئُ النَّشْأَةَ الْآخِرَةَ ۚ إِنَّ اللهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ
Qul seeroo fee al-ardi fanthurookayfa badaa alkhalqa thumma Allahu yunshi-o annash-ataal-akhirata inna Allaha AAala kulli shay-inqadeer

Hausa
 
Ka ce: "Ku yi tafiya cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba yadda (Allah) Ya făra yin halitta, sa'an nan kuma Allah Yană ƙăga wata halittar mayarwa. Lalle Allah Mai ikon yi ne a kan kőme.

Ayah  29:21  الأية
يُعَذِّبُ مَن يَشَاءُ وَيَرْحَمُ مَن يَشَاءُ ۖ وَإِلَيْهِ تُقْلَبُونَ
YuAAaththibu man yashao wayarhamuman yashao wa-ilayhi tuqlaboon

Hausa
 
"Yană azabta wanda Ya so, kuma Yană jin ƙan wanda Ya so. Kuma zuwa gare shi ake jũyaku."

Ayah  29:22  الأية
وَمَا أَنتُم بِمُعْجِزِينَ فِي الْأَرْضِ وَلَا فِي السَّمَاءِ ۖ وَمَا لَكُم مِّن دُونِ اللهِ مِن وَلِيٍّ وَلَا نَصِيرٍ
Wama antum bimuAAjizeena fee al-ardiwala fee assama-i wama lakum mindooni Allahi min waliyyin wala naseer

Hausa
 
"Kuma ba ku zamo măsu buwăya ba a cikin ƙasă, kuma haka a cikin sama kuma bă ku da wani majiɓinci wanda ba Allah ba, kuma ha ku da wani mataimaki."

Ayah  29:23  الأية
وَالَّذِينَ كَفَرُوا بِآيَاتِ اللهِ وَلِقَائِهِ أُولَٰئِكَ يَئِسُوا مِن رَّحْمَتِي وَأُولَٰئِكَ لَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Wallatheena kafaroo bi-ayatiAllahi waliqa-ihi ola-ika ya-isoo min rahmateewaola-ika lahum AAathabun aleem

Hausa
 
Kuma waɗanda suka kăfirta da ăyőyin Allah da gamuwa da shi, waɗannan sun yanke ƙauna daga rahamaTa kuma waɗannan sună da wata azăba mai raɗaɗi.

Ayah  29:24  الأية
فَمَا كَانَ جَوَابَ قَوْمِهِ إِلَّا أَن قَالُوا اقْتُلُوهُ أَوْ حَرِّقُوهُ فَأَنجَاهُ اللهُ مِنَ النَّارِ ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ
Fama kana jawabaqawmihi illa an qaloo oqtuloohu aw harriqoohufaanjahu Allahu mina annari inna feethalika laayatin liqawmin yu/minoon

Hausa
 
Sa'an nan băbu abin da ya kasance jawăbin mutănensa (Ibrăhĩm) făce dai suka ce: "Ku kashe shi kő, ku ƙőnă shi," Sai Allah Ya tsĩrar da shi daga wută. Lallea cikin wannan akwai ayőyi ga mutănen da ke yin ĩmăni.

Ayah  29:25  الأية
وَقَالَ إِنَّمَا اتَّخَذْتُم مِّن دُونِ اللهِ أَوْثَانًا مَّوَدَّةَ بَيْنِكُمْ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا ۖ ثُمَّ يَوْمَ الْقِيَامَةِ يَكْفُرُ بَعْضُكُم بِبَعْضٍ وَيَلْعَنُ بَعْضُكُم بَعْضًا وَمَأْوَاكُمُ النَّارُ وَمَا لَكُم مِّن نَّاصِرِينَ
Waqala innama ittakhathtummin dooni Allahi awthanan mawaddata baynikum fee alhayatiaddunya thumma yawma alqiyamati yakfurubaAAdukum bibaAAdin wayalAAanu baAAdukumbaAAdan wama-wakumu annaru wamalakum min nasireen

Hausa
 
Kuma Ibrahĩm ya ce "Băbu abin da kuka yi sai dai kub bar Allah kun riƙi gumăka sabőda sőyayyar tsakăninku a cikin răyuwar dũniya, a'an nan a Rănar ˇiyăma săshinku zai kăfirce wa săshi, kuma makőmarku ita ce wută kuma bă ku da waɗansu mataimaka."

Ayah  29:26  الأية
فَآمَنَ لَهُ لُوطٌ ۘ وَقَالَ إِنِّي مُهَاجِرٌ إِلَىٰ رَبِّي ۖ إِنَّهُ هُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
Faamana lahu lootun waqalainnee muhajirun ila rabbee innahu huwa alAAazeezualhakeem

Hausa
 
Sai Lũɗu ya yi ĩmăni da shi. Kuma Ibrăhĩm ya ce: "Lallenĩ mai ƙaura ne zuwa ga Ubangijina. Lalle Shĩ Shĩ ne Mabuwăyi, Mai hikima."

Ayah  29:27  الأية
وَوَهَبْنَا لَهُ إِسْحَاقَ وَيَعْقُوبَ وَجَعَلْنَا فِي ذُرِّيَّتِهِ النُّبُوَّةَ وَالْكِتَابَ وَآتَيْنَاهُ أَجْرَهُ فِي الدُّنْيَا ۖ وَإِنَّهُ فِي الْآخِرَةِ لَمِنَ الصَّالِحِينَ
Wawahabna lahu ishaqawayaAAqooba wajaAAalna fee thurriyyatihi annubuwwatawalkitaba waataynahu ajrahu fee addunyawa-innahu fee al-akhirati lamina assaliheen

Hausa
 
Kuma Muka bă shi Ishăƙa da Ya'aƙũba, kuma Muka sanya Annabci da littăfi a cikin zuriyarsa. Kuma Mun bă shi sakamakonsa a dũniya, kuma lalle shĩ a Lăhira, tabbas, yană a cikin sălihai.

Ayah  29:28  الأية
وَلُوطًا إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِ إِنَّكُمْ لَتَأْتُونَ الْفَاحِشَةَ مَا سَبَقَكُم بِهَا مِنْ أَحَدٍ مِّنَ الْعَالَمِينَ
Walootan ith qalaliqawmihi innakum lata/toona alfahishata masabaqakum biha min ahadin mina alAAalameen

Hausa
 
Da Lũɗu, a lőkacin daya ce wa mutănensa, "Lalle kũ, haƙĩƙa kună jẽ wa alfăsha wadda wani mahalũƙi daga cikin dũniya bai riga ku gare ta ba.

Ayah  29:29  الأية
أَئِنَّكُمْ لَتَأْتُونَ الرِّجَالَ وَتَقْطَعُونَ السَّبِيلَ وَتَأْتُونَ فِي نَادِيكُمُ الْمُنكَرَ ۖ فَمَا كَانَ جَوَابَ قَوْمِهِ إِلَّا أَن قَالُوا ائْتِنَا بِعَذَابِ اللهِ إِن كُنتَ مِنَ الصَّادِقِينَ
A-innakum lata/toona arrijalawataqtaAAoona assabeela wata/toona fee nadeekumualmunkara fama kana jawaba qawmihi illaan qaloo i/tina biAAathabi Allahi inkunta mina assadiqeen

Hausa
 
"Ashe, lalle kũ kună je wa maza, kuma ku yi fashin hanya kuma ku je, a cikin majalisarku da abin da bă shi da kyau? To, jawăbin mutănensa bai kasance ba făce dai sun ce: 'Ka zo mana da azăbar Allah, idan ka kasance daga măsu gaskiya.'"

Ayah  29:30  الأية
قَالَ رَبِّ انصُرْنِي عَلَى الْقَوْمِ الْمُفْسِدِينَ
Qala rabbi onsurnee AAalaalqawmi almufsideen

Hausa
 
Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka taimake ni a kan mutănen nan maɓarnata."

Ayah  29:31  الأية
وَلَمَّا جَاءَتْ رُسُلُنَا إِبْرَاهِيمَ بِالْبُشْرَىٰ قَالُوا إِنَّا مُهْلِكُو أَهْلِ هَٰذِهِ الْقَرْيَةِ ۖ إِنَّ أَهْلَهَا كَانُوا ظَالِمِينَ
Walamma jaat rusulunaibraheema bilbushra qaloo innamuhlikoo ahli hathihi alqaryati inna ahlaha kanoothalimeen

Hausa
 
Kuma a lőkacin da ManzanninMu suka jẽ wa Ibrăhĩm da bushăra suka ce: "Lalle mu măsu halaka mutănen, wannan alƙarya ne. Lalle mutănenta sun kasance măsu zălunci."

Ayah  29:32  الأية
قَالَ إِنَّ فِيهَا لُوطًا ۚ قَالُوا نَحْنُ أَعْلَمُ بِمَن فِيهَا ۖ لَنُنَجِّيَنَّهُ وَأَهْلَهُ إِلَّا امْرَأَتَهُ كَانَتْ مِنَ الْغَابِرِينَ
Qala inna feeha lootanqaloo nahnu aAAlamu biman feehalanunajjiyannahu waahlahu illa imraatahu kanat minaalghabireen

Hausa
 
Ya ce: "Lalle akwai Lũɗu a cikinta!" Suka ce: "Mũ ne mafiya sani ga waɗanda suke a cikinta, lalle mună tsĩrar da shi da mutănensa, făce fa mătarsa ta kasance a cikin măsu wanzuwa."

Ayah  29:33  الأية
وَلَمَّا أَن جَاءَتْ رُسُلُنَا لُوطًا سِيءَ بِهِمْ وَضَاقَ بِهِمْ ذَرْعًا وَقَالُوا لَا تَخَفْ وَلَا تَحْزَنْ ۖ إِنَّا مُنَجُّوكَ وَأَهْلَكَ إِلَّا امْرَأَتَكَ كَانَتْ مِنَ الْغَابِرِينَ
Walamma an jaat rusulunalootan see-a bihim wadaqa bihim tharAAan waqaloola takhaf wala tahzan inna munajjookawaahlaka illa imraataka kanat mina alghabireen

Hausa
 
Kuma a lőkacin da ManzanninMu suka je wa Lũɗu ya ɓăta rai sabőda su, kuma yă ƙuntata ga kirji sabőda su. Kuma suka ce: "Kada ka ji tsőro kuma kada ka yi baƙin ciki lalle mũ măsu tsĩrar da kai ne da iyălanka, făce dai matarka ta kasance daga măsu wanzuwa.

Ayah  29:34  الأية
إِنَّا مُنزِلُونَ عَلَىٰ أَهْلِ هَٰذِهِ الْقَرْيَةِ رِجْزًا مِّنَ السَّمَاءِ بِمَا كَانُوا يَفْسُقُونَ
Inna munziloona AAala ahli hathihialqaryati rijzan mina assama-i bima kanooyafsuqoon

Hausa
 
"Lalle mũ, măsu saukar da azăba ne daga sama a kan mutănen wannan alƙarya sabőda abin da suka kasance sună yi na făsiƙanci."

Ayah  29:35  الأية
وَلَقَد تَّرَكْنَا مِنْهَا آيَةً بَيِّنَةً لِّقَوْمٍ يَعْقِلُونَ
Walaqad tarakna minha ayatanbayyinatan liqawmin yaAAqiloon

Hausa
 
Kuma lalle Mun bar wata ăyă bayyananna daga gare ta ga mutăne măsu hankalta.

Ayah  29:36  الأية
وَإِلَىٰ مَدْيَنَ أَخَاهُمْ شُعَيْبًا فَقَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُوا اللهَ وَارْجُوا الْيَوْمَ الْآخِرَ وَلَا تَعْثَوْا فِي الْأَرْضِ مُفْسِدِينَ
Wa-ila madyana akhahumshuAAayban faqala ya qawmi oAAbudoo Allahawarjoo alyawma al-akhira wala taAAthaw feeal-ardi mufsideen

Hausa
 
Kuma zuwa ga Madyana, Mun aika ɗan'uwansu shu'aibu, sai ya ce: "Ya mutănena! Ku bauta wa Allah kuma ku yi fatan (rahamar) Rănar Lăhira, kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasă, alhăli kuwa kună măsu lălătarwa."

Ayah  29:37  الأية
فَكَذَّبُوهُ فَأَخَذَتْهُمُ الرَّجْفَةُ فَأَصْبَحُوا فِي دَارِهِمْ جَاثِمِينَ
Fakaththaboohu faakhathat-humuarrajfatu faasbahoo fee darihim jathimeen

Hausa
 
Sai suka ƙaryata shi, sabőda haka tsăwa ta kămă su, dőmin haka suka wăyi gari sună guggurfăne.

Ayah  29:38  الأية
وَعَادًا وَثَمُودَ وَقَد تَّبَيَّنَ لَكُم مِّن مَّسَاكِنِهِمْ ۖ وَزَيَّنَ لَهُمُ الشَّيْطَانُ أَعْمَالَهُمْ فَصَدَّهُمْ عَنِ السَّبِيلِ وَكَانُوا مُسْتَبْصِرِينَ
WaAAadan wathamooda waqad tabayyanalakum min masakinihim wazayyana lahumu ashshaytanuaAAmalahum fasaddahum AAani assabeeli wakanoomustabsireen

Hausa
 
Da Ădawa da Samũdăwa alhăli kuwa lalle alămun azăba sun bayyana a gare su daga gidăjensu kuma Shaiɗan ya ƙawăta musu ayyukansu, sabőda haka ya kange su daga hanyar Allah, kuma sun kasance măsu basĩra!

Ayah  29:39  الأية
وَقَارُونَ وَفِرْعَوْنَ وَهَامَانَ ۖ وَلَقَدْ جَاءَهُم مُّوسَىٰ بِالْبَيِّنَاتِ فَاسْتَكْبَرُوا فِي الْأَرْضِ وَمَا كَانُوا سَابِقِينَ
Waqaroona wafirAAawna wahamanawalaqad jaahum moosa bilbayyinati fastakbaroofee al-ardi wama kanoo sabiqeen

Hausa
 
Kuma ˇărũna da Fir'auna da Hămăna, kuma lalle Mũsaya je musu da hujjőji, sai suka yi girman kai a cikin ƙasă kuma ba su kasance măsu tsẽrẽwa ba.

Ayah  29:40  الأية
فَكُلًّا أَخَذْنَا بِذَنبِهِ ۖ فَمِنْهُم مَّنْ أَرْسَلْنَا عَلَيْهِ حَاصِبًا وَمِنْهُم مَّنْ أَخَذَتْهُ الصَّيْحَةُ وَمِنْهُم مَّنْ خَسَفْنَا بِهِ الْأَرْضَ وَمِنْهُم مَّنْ أَغْرَقْنَا ۚ وَمَا كَانَ اللهُ لِيَظْلِمَهُمْ وَلَٰكِن كَانُوا أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ
Fakullan akhathna bithanbihifaminhum man arsalna AAalayhi hasiban waminhum manakhathat-hu assayhatu waminhum mankhasafna bihi al-arda waminhum man aghraqnawama kana Allahu liyathlimahumwalakin kanoo anfusahum yathlimoon

Hausa
 
Sabőda haka kőwanensu Mun kama shi da laifinsa. Watau daga cikinsu akwai wanda Muka aika iskar tsakuwa a kansa kuma daga cikinsu akwai wanda tsăwa ta kămă, kuma daga cikinsu akwai wanda Muka birkice ƙasă da shi kuma daga cikinsu akwai wanda Muka nutsar. Bă ya yiwuwa ga Allah Ya zălunce su, amma sun kasance kansu suke zălunta.

Ayah  29:41  الأية
مَثَلُ الَّذِينَ اتَّخَذُوا مِن دُونِ اللهِ أَوْلِيَاءَ كَمَثَلِ الْعَنكَبُوتِ اتَّخَذَتْ بَيْتًا ۖ وَإِنَّ أَوْهَنَ الْبُيُوتِ لَبَيْتُ الْعَنكَبُوتِ ۖ لَوْ كَانُوا يَعْلَمُونَ
Mathalu allatheena ittakhathoomin dooni Allahi awliyaa kamathali alAAankabootiittakhathat baytan wa-inna awhana albuyooti labaytualAAankabooti law kanoo yaAAlamoon

Hausa
 
Misălin waɗanda suka riƙi waɗansu masőya waɗanda bă Allah ba, kamar misălin gizőgizo ne wanda ya riƙi wani ɗan gida, alhăli kuwa lalle mafi raunin gidăje, shĩ ne gidan gizogizo, dă sun kasance sună sane.

Ayah  29:42  الأية
إِنَّ اللهَ يَعْلَمُ مَا يَدْعُونَ مِن دُونِهِ مِن شَيْءٍ ۚ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
Inna Allaha yaAAlamu mayadAAoona min doonihi min shay-in wahuwa alAAazeezu alhakeem

Hausa
 
Lalle Allah Yană sane da abin da suke kira wanda bă Shi ba na wani abu duka kuma shĩ ne Mabuwăyi, Mai hikima.

Ayah  29:43  الأية
وَتِلْكَ الْأَمْثَالُ نَضْرِبُهَا لِلنَّاسِ ۖ وَمَا يَعْقِلُهَا إِلَّا الْعَالِمُونَ
Watilka al-amthalu nadribuhalinnasi wama yaAAqiluha illaalAAalimoon

Hausa
 
Kuma waɗancan misălan Mună bayyana su ga mutăne kuma băbu mai hankalta da su sai măsu ilmi.

Ayah  29:44  الأية
خَلَقَ اللهُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ بِالْحَقِّ ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَةً لِّلْمُؤْمِنِينَ
Khalaqa Allahu assamawatiwal-arda bilhaqqi inna fee thalikalaayatan lilmu-mineen

Hausa
 
Allah Ya halitta sammai da ƙasa da gaskiya. Lalle cikin wancan akwai ăyă ga mũminai.

Ayah  29:45  الأية
اتْلُ مَا أُوحِيَ إِلَيْكَ مِنَ الْكِتَابِ وَأَقِمِ الصَّلَاةَ ۖ إِنَّ الصَّلَاةَ تَنْهَىٰ عَنِ الْفَحْشَاءِ وَالْمُنكَرِ ۗ وَلَذِكْرُ اللهِ أَكْبَرُ ۗ وَاللهُ يَعْلَمُ مَا تَصْنَعُونَ
Otlu ma oohiya ilayka minaalkitabi waaqimi assalata inna assalatatanha AAani alfahsha-i walmunkariwalathikru Allahi akbaru wallahuyaAAlamu ma tasnaAAoon

Hausa
 
Ka karanta abin da ake yin wahayi zuwa gare ka daga Littăfi, kuma ka tsayar da salla. Lalle salla tană hanăwa daga alfăsha da abni ƙyăma, kuma lalle ambaton Allah ya fi girma, kuma Allah Yană sane da abin da kuke aikatăwa.

Ayah  29:46  الأية
وَلَا تُجَادِلُوا أَهْلَ الْكِتَابِ إِلَّا بِالَّتِي هِيَ أَحْسَنُ إِلَّا الَّذِينَ ظَلَمُوا مِنْهُمْ ۖ وَقُولُوا آمَنَّا بِالَّذِي أُنزِلَ إِلَيْنَا وَأُنزِلَ إِلَيْكُمْ وَإِلَٰهُنَا وَإِلَٰهُكُمْ وَاحِدٌ وَنَحْنُ لَهُ مُسْلِمُونَ
Wala tujadiloo ahla alkitabiilla billatee hiya ahsanu illa allatheenathalamoo minhum waqooloo amanna billatheeonzila ilayna waonzila ilaykum wa-ilahunawa-ilahukum wahidun wanahnu lahu muslimoon

Hausa
 
Kada ku yi jayayya da mazowa Littăfi sai fa da magana wadda ta fi kyau, sai fa waɗanda suka yi zălunci daga gare su, kuma ku ce, "Mun yi ĩmăni da abin da aka saukar a gare mu kuma aka saukar a gare ku, kuma Abin bautăwarmu da Abin bautăwarku Guda ne, kama mũ măsu sallamăwa ne a gare shi."

Ayah  29:47  الأية
وَكَذَٰلِكَ أَنزَلْنَا إِلَيْكَ الْكِتَابَ ۚ فَالَّذِينَ آتَيْنَاهُمُ الْكِتَابَ يُؤْمِنُونَ بِهِ ۖ وَمِنْ هَٰؤُلَاءِ مَن يُؤْمِنُ بِهِ ۚ وَمَا يَجْحَدُ بِآيَاتِنَا إِلَّا الْكَافِرُونَ
Wakathalika anzalna ilaykaalkitaba fallatheena ataynahumualkitaba yu/minoona bihi wamin haola-i manyu/minu bihi wama yajhadu bi-ayatinailla alkafiroon

Hausa
 
Kuma kamar haka Muka saukar da Littafi a gare ka, to, waɗannan da Muka bai wa Littăfi sană ĩmăni da shi, daga cikin wăɗannan akwai mai ĩmăni da shi, kuma băbu mai musun ăyőyinMu, făce kăfirai.

Ayah  29:48  الأية
وَمَا كُنتَ تَتْلُو مِن قَبْلِهِ مِن كِتَابٍ وَلَا تَخُطُّهُ بِيَمِينِكَ ۖ إِذًا لَّارْتَابَ الْمُبْطِلُونَ
Wama kunta tatloo min qablihi min kitabinwala takhuttuhu biyameenika ithan lartabaalmubtiloon

Hausa
 
Kuma ba ka kasance kana karătun wani littăfi ba a gabăninsa, kuma bă ka rubũtunsa da dămanka dă haka yă auku, dă măsu ɓarnă sun yi shakka.

Ayah  29:49  الأية
بَلْ هُوَ آيَاتٌ بَيِّنَاتٌ فِي صُدُورِ الَّذِينَ أُوتُوا الْعِلْمَ ۚ وَمَا يَجْحَدُ بِآيَاتِنَا إِلَّا الظَّالِمُونَ
Bal huwa ayatun bayyinatunfee sudoori allatheena ootoo alAAilma wamayajhadu bi-ayatina illa aththalimoon

Hausa
 
Ă'a, shĩ ăyőyi ne bayyanannu a cikin ƙirăzan waɗanda aka bai wa ilmi. Kuma băbu mai musun ăyőyinMu făce azzălumai.

Ayah  29:50  الأية
وَقَالُوا لَوْلَا أُنزِلَ عَلَيْهِ آيَاتٌ مِّن رَّبِّهِ ۖ قُلْ إِنَّمَا الْآيَاتُ عِندَ اللهِ وَإِنَّمَا أَنَا نَذِيرٌ مُّبِينٌ
Waqaloo lawla onzila AAalayhi ayatunmin rabbihi qul innama al-ayatu AAinda Allahiwa-innama ana natheerun mubeen

Hausa
 
Kuma suka ce: "Don me ba a saukar masa da ăyői ba daga Ubangijinsa? "Ka ce: "Su ăyőyi a wurin Allah kawai suke, kuma lalle ni mai gargaɗi kawai ne, mai bayyanăwa."

Ayah  29:51  الأية
أَوَلَمْ يَكْفِهِمْ أَنَّا أَنزَلْنَا عَلَيْكَ الْكِتَابَ يُتْلَىٰ عَلَيْهِمْ ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَرَحْمَةً وَذِكْرَىٰ لِقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ
Awa lam yakfihim anna anzalnaAAalayka alkitaba yutla AAalayhim inna fee thalikalarahmatan wathikra liqawmin yu/minoon

Hausa
 
Shin bai ishe su ba cẽwa lalle Mũ, Mun saukar da Littăfin akanka, ană karanta shi a kansu? Lalle a cikin wancan haƙĩƙa akwai rahama da tunătawa ga mutanen da ke yin ĩmăni.

Ayah  29:52  الأية
قُلْ كَفَىٰ بِاللهِ بَيْنِي وَبَيْنَكُمْ شَهِيدًا ۖ يَعْلَمُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۗ وَالَّذِينَ آمَنُوا بِالْبَاطِلِ وَكَفَرُوا بِاللهِ أُولَٰئِكَ هُمُ الْخَاسِرُونَ
Qul kafa billahibaynee wabaynakum shaheedan yaAAlamu ma fee assamawatiwal-ardi wallatheena amanoobilbatili wakafaroo billahi ola-ikahumu alkhasiroon

Hausa
 
Ka ce: "Allah Yă isa shaida a tsakănĩna da tsakănĩnku Yană sane da abin da ke a cikin sammai da ƙasă, kuma waɗanda suka yi ĩmăni da ɗarya kuma suka kăfirta da Allah, waɗannan sũ nemăsu hasăra."

Ayah  29:53  الأية
وَيَسْتَعْجِلُونَكَ بِالْعَذَابِ ۚ وَلَوْلَا أَجَلٌ مُّسَمًّى لَّجَاءَهُمُ الْعَذَابُ وَلَيَأْتِيَنَّهُم بَغْتَةً وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ
WayastaAAjiloonaka bilAAathabiwalawla ajalun musamman lajaahumu alAAathabuwalaya/tiyannahum baghtatan wahum la yashAAuroon

Hausa
 
Kuma suna nẽman ka da gaggauta azăba, to, bă dőmin ajali ƙayyadadde ba, dă azăba ta jẽ musu kuma lalle dă tană iske su bisa ia abke, alhăli kuwa sũ ba su sani ba.

Ayah  29:54  الأية
يَسْتَعْجِلُونَكَ بِالْعَذَابِ وَإِنَّ جَهَنَّمَ لَمُحِيطَةٌ بِالْكَافِرِينَ
YastaAAjiloonaka bilAAathabiwa-inna jahannama lamuheetatun bilkafireen

Hausa
 
Sună nẽman ka da gaggauta azăba, kuma lalle Jahannama, tabbas, mai kẽwayewa ce gakăfirai.

Ayah  29:55  الأية
يَوْمَ يَغْشَاهُمُ الْعَذَابُ مِن فَوْقِهِمْ وَمِن تَحْتِ أَرْجُلِهِمْ وَيَقُولُ ذُوقُوا مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Yawma yaghshahumu alAAathabumin fawqihim wamin tahti arjulihim wayaqoolu thooqooma kuntum taAAmaloon

Hausa
 
Rănar da azăba ke rufe su daga samansu da kuma ƙasan ƙafafunsu kuma Ya ce: "Ku ɗanɗani abin da kuka kasance kună aikatăwa."

Ayah  29:56  الأية
يَا عِبَادِيَ الَّذِينَ آمَنُوا إِنَّ أَرْضِي وَاسِعَةٌ فَإِيَّايَ فَاعْبُدُونِ
Ya AAibadiya allatheenaamanoo inna ardee wasiAAatun fa-iyyayafaAAbudoon

Hausa
 
Yă băyiNa, waɗanda suka yi ĩmăni! Lalle fa ƙasăTa mai yalwă ce, sabăda haka ku bauta Mini.

Ayah  29:57  الأية
كُلُّ نَفْسٍ ذَائِقَةُ الْمَوْتِ ۖ ثُمَّ إِلَيْنَا تُرْجَعُونَ
Kullu nafsin tha-iqatu almawti thummailayna turjaAAoon

Hausa
 
Kőwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne, sa'an nan zuwa gare Mu ake mayar da ku.

Ayah  29:58  الأية
وَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَنُبَوِّئَنَّهُم مِّنَ الْجَنَّةِ غُرَفًا تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا ۚ نِعْمَ أَجْرُ الْعَامِلِينَ
Wallatheena amanoowaAAamiloo assalihati lanubawwi-annahummina aljannati ghurafan tajree min tahtiha al-anharukhalideena feeha niAAma ajru alAAamileen

Hausa
 
Kuma waɗanda suka yi ĩmăni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle ză Mu zaunar da su daga cikin Aljanna a gidăjen bẽne, ƙoramu nă gudăna daga ƙarƙashinsu, sună madawwama a cikinsu. To, madalla da sakamakon măsu aikin ƙwarai.

Ayah  29:59  الأية
الَّذِينَ صَبَرُوا وَعَلَىٰ رَبِّهِمْ يَتَوَكَّلُونَ
Allatheena sabaroo waAAalarabbihim yatawakkaloon

Hausa
 
Waɗanda suka yi haƙuri, kuma sună dőgara ga Ubangijinsu kawai.

Ayah  29:60  الأية
وَكَأَيِّن مِّن دَابَّةٍ لَّا تَحْمِلُ رِزْقَهَا اللهُ يَرْزُقُهَا وَإِيَّاكُمْ ۚ وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ
Wakaayyin min dabbatin la tahmilurizqaha Allahu yarzuquha wa-iyyakumwahuwa assameeAAu alAAaleem

Hausa
 
Kuma da yawa dabba wadda bă ta ɗaukar abincinta Allah Yană ciyar da ita tăre da ku, kuma Shĩ ne Mai ji, Mai ilmi.

Ayah  29:61  الأية
وَلَئِن سَأَلْتَهُم مَّنْ خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَسَخَّرَ الشَّمْسَ وَالْقَمَرَ لَيَقُولُنَّ اللهُ ۖ فَأَنَّىٰ يُؤْفَكُونَ
Wala-in saaltahum man khalaqa assamawatiwal-arda wasakhkhara ashshamsa walqamaralayaqoolunna Allahu faanna yu/fakoon

Hausa
 
Lalle idan ka tambaye su: "Wăne ne ya halitta sammai da ƙasă kuma ya hőre rănă da wată?" Lalle sună cẽwa Allah ne. TO, yăya ake karkatar da su ?

Ayah  29:62  الأية
اللهُ يَبْسُطُ الرِّزْقَ لِمَن يَشَاءُ مِنْ عِبَادِهِ وَيَقْدِرُ لَهُ ۚ إِنَّ اللهَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ
Allahu yabsutu arrizqaliman yashao min AAibadihi wayaqdiru lahu inna Allahabikulli shay-in AAaleem

Hausa
 
A1lah ne ke shimfiɗa arziki ga wanda Yake so daga cikin băyinsa kuma Yană ƙuntătăwa ga (wanda, Yake so). Lalle Allah, Masani ne ga dukan kőme.

Ayah  29:63  الأية
وَلَئِن سَأَلْتَهُم مَّن نَّزَّلَ مِنَ السَّمَاءِ مَاءً فَأَحْيَا بِهِ الْأَرْضَ مِن بَعْدِ مَوْتِهَا لَيَقُولُنَّ اللهُ ۚ قُلِ الْحَمْدُ لِلَّهِ ۚ بَلْ أَكْثَرُهُمْ لَا يَعْقِلُونَ
Wala-in saaltahum man nazzala mina assama-imaan faahya bihi al-arda min baAAdimawtiha layaqoolunna Allahu quli alhamdulillahi bal aktharuhum la yaAAqiloon

Hausa
 
Kuma lalle idan ka tambaye su. "Wăne ne ya saukar da ruwa daga sama, har ya răyar da ƙasă game da shi a băyan mutuwarta?" Lalle sună cẽwa, "Allah ne." Ka ce: "Gődiya tă tabbata ga Allah." Ă'a, mafi yawansu bă su hankalta.

Ayah  29:64  الأية
وَمَا هَٰذِهِ الْحَيَاةُ الدُّنْيَا إِلَّا لَهْوٌ وَلَعِبٌ ۚ وَإِنَّ الدَّارَ الْآخِرَةَ لَهِيَ الْحَيَوَانُ ۚ لَوْ كَانُوا يَعْلَمُونَ
Wama hathihi alhayatuaddunya illa lahwun walaAAibun wa-inna addaraal-akhirata lahiya alhayawanu law kanooyaAAlamoon

Hausa
 
Kuma wannan răyuwa ta dũniya ba ta zamo ba, făce abar shagala da wăsă kuma lalle Lăhira tabbas, ita ce răyuwa, dă sun kasance sună sani.

Ayah  29:65  الأية
فَإِذَا رَكِبُوا فِي الْفُلْكِ دَعَوُا اللهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ فَلَمَّا نَجَّاهُمْ إِلَى الْبَرِّ إِذَا هُمْ يُشْرِكُونَ
Fa-itha rakiboo fee alfulki daAAawooAllaha mukhliseena lahu addeena falammanajjahum ila albarri itha hum yushrikoon

Hausa
 
To, a lőkacin da suka shiga cikin jirgin ruwa, sun kirăyi Allah sună măsu tsarkake addini a gare shi, to, a lőkacin da Ya tsĩrar da su zuwa ga tudun ƙasă, sai gă su sună shirki.

Ayah  29:66  الأية
لِيَكْفُرُوا بِمَا آتَيْنَاهُمْ وَلِيَتَمَتَّعُوا ۖ فَسَوْفَ يَعْلَمُونَ
Liyakfuroo bima ataynahumwaliyatamattaAAoo fasawfa yaAAlamoon

Hausa
 
Dőmin su kăfirce wa abin da Muka bă su kuma dőmin su ji dăɗi sa'an nan kuma ză su sani.

Ayah  29:67  الأية
أَوَلَمْ يَرَوْا أَنَّا جَعَلْنَا حَرَمًا آمِنًا وَيُتَخَطَّفُ النَّاسُ مِنْ حَوْلِهِمْ ۚ أَفَبِالْبَاطِلِ يُؤْمِنُونَ وَبِنِعْمَةِ اللهِ يَكْفُرُونَ
Awa lam yaraw anna jaAAalna haramanaminan wayutakhattafu annasu min hawlihimafabilbatili yu/minoona wabiniAAmati Allahiyakfuroon

Hausa
 
Shin, ba su ga cẽwa, lalle Mun sanya Hurumi amintacce ba alhăli kuwa ană fisge mutăne a gẽfensu? Shin, da ɓătaccen abu suke ĩmăni kuma da ni'imarAllah suka kăfirta?

Ayah  29:68  الأية
وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ افْتَرَىٰ عَلَى اللهِ كَذِبًا أَوْ كَذَّبَ بِالْحَقِّ لَمَّا جَاءَهُ ۚ أَلَيْسَ فِي جَهَنَّمَ مَثْوًى لِّلْكَافِرِينَ
Waman athlamu mimmani iftaraAAala Allahi kathiban aw kaththaba bilhaqqilamma jaahu alaysa fee jahannama mathwan lilkafireen

Hausa
 
Kuma wăne ne ya fi zălunci bisa ga wanda ya ƙirƙira ƙarya ya jingina ta ga Allah, kő kuma ya ƙaryata gaskiya a lőkacin da ta je masa? Ashe a cikin Jahannama băbu mazauna ga kăfirai?

Ayah  29:69  الأية
وَالَّذِينَ جَاهَدُوا فِينَا لَنَهْدِيَنَّهُمْ سُبُلَنَا ۚ وَإِنَّ اللهَ لَمَعَ الْمُحْسِنِينَ
Wallatheena jahadoofeena lanahdiyannahum subulana wa-inna AllahalamaAAa almuhsineen

Hausa
 
Kuma wadannan da suka yi ƙőƙari ga nẽman yardarMu, lalle Mună shiryar da su ga hanyőyinMu, kuma lalle Allah, tabbas, Yană tăre da măsu kyautatăwa (ga addĩninsu). 




© EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us