Prev  

42. Surah Ash-Shűra سورة الشورى

  Next  



1st Ayah  1  الأية ١الأولي
بِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
حم
Ha-meem

Hausa
 
Ḥ. M̃.

Ayah  42:2  الأية
عسق
AAayn-seen-qaf

Hausa
 
Ĩ. Ṣ̃.

Ayah  42:3  الأية
كَذَٰلِكَ يُوحِي إِلَيْكَ وَإِلَى الَّذِينَ مِن قَبْلِكَ اللهُ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
Kathalika yoohee ilayka wa-ilaallatheena min qablika Allahu alAAazeezu alhakeem

Hausa
 
Kamar wancăn (asĩrin) Allah, Mabuwayi, Mai hikima, ke yin wahayi zuwa gare ka da zuwa ga waɗanda ke gabăninka .

Ayah  42:4  الأية
لَهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ ۖ وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ
Lahu ma fee assamawatiwama fee al-ardi wahuwa alAAaliyyu alAAatheem

Hausa
 
(Allah) Shi ne da abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa, kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma.

Ayah  42:5  الأية
تَكَادُ السَّمَاوَاتُ يَتَفَطَّرْنَ مِن فَوْقِهِنَّ ۚ وَالْمَلَائِكَةُ يُسَبِّحُونَ بِحَمْدِ رَبِّهِمْ وَيَسْتَغْفِرُونَ لِمَن فِي الْأَرْضِ ۗ أَلَا إِنَّ اللهَ هُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ
Takadu assamawatuyatafattarna min fawqihinna walmala-ikatuyusabbihoona bihamdi rabbihim wayastaghfiroonaliman fee al-ardi ala inna Allaha huwaalghafooru arraheem

Hausa
 
Sammai nă kusan su tsăge daga bisansu, kuma mală'iku nă yin tasĩhi game da gődẽ wa Ubangijinsu kuma sună istigfări dőmin wanda ke cikin ƙasa. To, lalle Allah Shĩ ne Mai găfara, Mai jin ƙai.

Ayah  42:6  الأية
وَالَّذِينَ اتَّخَذُوا مِن دُونِهِ أَوْلِيَاءَ اللهُ حَفِيظٌ عَلَيْهِمْ وَمَا أَنتَ عَلَيْهِم بِوَكِيلٍ
Wallatheena ittakhathoomin doonihi awliyaa Allahu hafeethunAAalayhim wama anta AAalayhim biwakeel

Hausa
 
Kuma waɗanda suka riƙi waɗansu majiɓinta waɗanda bă Shĩ ba Allah ne Mai tsaro a kansu, kuma kai, bă wakili ne a kansu ba.

Ayah  42:7  الأية
وَكَذَٰلِكَ أَوْحَيْنَا إِلَيْكَ قُرْآنًا عَرَبِيًّا لِّتُنذِرَ أُمَّ الْقُرَىٰ وَمَنْ حَوْلَهَا وَتُنذِرَ يَوْمَ الْجَمْعِ لَا رَيْبَ فِيهِ ۚ فَرِيقٌ فِي الْجَنَّةِ وَفَرِيقٌ فِي السَّعِيرِ
Wakathalika awhaynailayka qur-anan AAarabiyyan litunthira omma alqurawaman hawlaha watunthira yawma aljamAAi larayba feehi fareequn fee aljannati wafareequn fee assaAAeer

Hausa
 
Kuma kamar haka ne Muka yi wahayin abin karăntăwa (Alƙur'ăni) na Lărabci zuwa gare ka, dőmin ka yi gargaɗi ga Uwar Alƙaryu (Makka) da wanda ke a kẽwayenta, kuma ka yi gargaɗi game da rănar taruwa, băbu shakka gare ta, wata ƙungiya tană a cikin Aljanna kuma wata ƙungiya tăna a cikin sa'ĩr.

Ayah  42:8  الأية
وَلَوْ شَاءَ اللهُ لَجَعَلَهُمْ أُمَّةً وَاحِدَةً وَلَٰكِن يُدْخِلُ مَن يَشَاءُ فِي رَحْمَتِهِ ۚ وَالظَّالِمُونَ مَا لَهُم مِّن وَلِيٍّ وَلَا نَصِيرٍ
Walaw shaa Allahu lajaAAalahumommatan wahidatan walakin yudkhilu man yashaofee rahmatihi waththalimoonama lahum min waliyyin wala naseer

Hausa
 
Kuma dă Allah Ya so, da Ya haɗă su al'umma guda, kuma Amma Yană shigar da wanda Ya so a cikin rahamarSa alhăli kuwa azzăluMai bă su da, wani majiɓinci, kuma bă su da wani mataimaki.

Ayah  42:9  الأية
أَمِ اتَّخَذُوا مِن دُونِهِ أَوْلِيَاءَ ۖ فَاللهُ هُوَ الْوَلِيُّ وَهُوَ يُحْيِي الْمَوْتَىٰ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ
Ami ittakhathoo min doonihi awliyaafallahu huwa alwaliyyu wahuwa yuhyee almawtawahuwa AAala kulli shay-in qadeer

Hausa
 
Kő kuma sun riƙi waninSa majiɓinta? To Allah Shĩ ne Majiɓinci, kuma Shĩ ne ke răyar da matattu alhăli kuwa Shĩ, Maiĩkon yi ne a kan dukan kőme.

Ayah  42:10  الأية
وَمَا اخْتَلَفْتُمْ فِيهِ مِن شَيْءٍ فَحُكْمُهُ إِلَى اللهِ ۚ ذَٰلِكُمُ اللهُ رَبِّي عَلَيْهِ تَوَكَّلْتُ وَإِلَيْهِ أُنِيبُ
Wama ikhtalaftum feehi min shay-in fahukmuhuila Allahi thalikumu Allahu rabbeeAAalayhi tawakkaltu wa-ilayhi oneeb

Hausa
 
Kuma abin da kuka săɓă wa jũna a cikinsa kő męne ne, to, hukuncinsa (a mayar da shi) zuwa ga Allah. Wancan Shĩ ne Allah Ubangijĩna, a gare Shi na dőgara, kuma zuwa gare Shi nake mayar da al'amarĩna.

Ayah  42:11  الأية
فَاطِرُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ جَعَلَ لَكُم مِّنْ أَنفُسِكُمْ أَزْوَاجًا وَمِنَ الْأَنْعَامِ أَزْوَاجًا ۖ يَذْرَؤُكُمْ فِيهِ ۚ لَيْسَ كَمِثْلِهِ شَيْءٌ ۖ وَهُوَ السَّمِيعُ الْبَصِيرُ
Fatiru assamawatiwal-ardi jaAAala lakum min anfusikum azwajanwamina al-anAAami azwajan yathraokum feehilaysa kamithlihi shay-on wahuwa assameeAAu albaseer

Hausa
 
(Shĩ ne) Mai ƙăga halittar sammai da ƙasa, Ya sanya muku ma'aura daga jinsinku, kuma (Ya sanya) daga dabbőbi maza da mătă, Yană halitta ku a cikinsu, wani abu bai zama kamar tamkarSa ba, kuma Shĩ ne Mai ji, Mai gani.

Ayah  42:12  الأية
لَهُ مَقَالِيدُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ يَبْسُطُ الرِّزْقَ لِمَن يَشَاءُ وَيَقْدِرُ ۚ إِنَّهُ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ
Lahu maqaleedu assamawatiwal-ardi yabsutu arrizqa liman yashaowayaqdiru innahu bikulli shay-in AAaleem

Hausa
 
Shĩ ne da mabuɗan sammai da ƙasa Yană shimfiɗa arziki ga wanda ya so kuma Yană hukuntăwa. Lalle ne, Shĩ Masani ne ga dukan kőme.

Ayah  42:13  الأية
شَرَعَ لَكُم مِّنَ الدِّينِ مَا وَصَّىٰ بِهِ نُوحًا وَالَّذِي أَوْحَيْنَا إِلَيْكَ وَمَا وَصَّيْنَا بِهِ إِبْرَاهِيمَ وَمُوسَىٰ وَعِيسَىٰ ۖ أَنْ أَقِيمُوا الدِّينَ وَلَا تَتَفَرَّقُوا فِيهِ ۚ كَبُرَ عَلَى الْمُشْرِكِينَ مَا تَدْعُوهُمْ إِلَيْهِ ۚ اللهُ يَجْتَبِي إِلَيْهِ مَن يَشَاءُ وَيَهْدِي إِلَيْهِ مَن يُنِيبُ
SharaAAa lakum mina addeeni mawassa bihi noohan wallathee awhaynailayka wama wassayna bihi ibraheemawamoosa waAAeesa an aqeemoo addeena walatatafarraqoo feehi kabura AAala almushrikeena matadAAoohum ilayhi Allahu yajtabee ilayhi man yashaowayahdee ilayhi man yuneeb

Hausa
 
Ya shar'anta muku, game da addini, abin da Ya yi wasiyya da shi ga Nũhu da abin da Muka yi wahayi da shi zuwa gare ka, da abin da Muka yi wasiyya da shi ga Ibrăhĩm da Mũsă da Ĩsă, cẽwa ku tsayar da addini sősai kuma kada ku rarrabu a cikinsa. Abin da kuke kira zuwa gare shi, ya yi nauyi a kan măsu shirki. Allah na zăɓen wanda Yake so zuwa gare Shi, kuma Yană shiryar da wanda ke tawakkali gare Shi, ga hanyarSa.

Ayah  42:14  الأية
وَمَا تَفَرَّقُوا إِلَّا مِن بَعْدِ مَا جَاءَهُمُ الْعِلْمُ بَغْيًا بَيْنَهُمْ ۚ وَلَوْلَا كَلِمَةٌ سَبَقَتْ مِن رَّبِّكَ إِلَىٰ أَجَلٍ مُّسَمًّى لَّقُضِيَ بَيْنَهُمْ ۚ وَإِنَّ الَّذِينَ أُورِثُوا الْكِتَابَ مِن بَعْدِهِمْ لَفِي شَكٍّ مِّنْهُ مُرِيبٍ
Wama tafarraqoo illa minbaAAdi ma jaahumu alAAilmu baghyan baynahum walawlakalimatun sabaqat min rabbika ila ajalin musamman laqudiyabaynahum wa-inna allatheena oorithoo alkitaba minbaAAdihim lafee shakkin minhu mureeb

Hausa
 
Kuma ba su rarraba ba făce băyan da ilmi ya jẽ musu, dőmin zălunci a tsakăninsu kuma bă dőmin wata kalma tă gabata ba daga Ubangijinka, zuwa ga wani ajali ambatacce, dă an yi hukunci a tsakaninsu. Kuma lalle ne waɗanda aka gădar wa Littafi daga băyansu, haƙiƙa, sună cikin shakka a gare shi, mai sanya kokanto.

Ayah  42:15  الأية
فَلِذَٰلِكَ فَادْعُ ۖ وَاسْتَقِمْ كَمَا أُمِرْتَ ۖ وَلَا تَتَّبِعْ أَهْوَاءَهُمْ ۖ وَقُلْ آمَنتُ بِمَا أَنزَلَ اللهُ مِن كِتَابٍ ۖ وَأُمِرْتُ لِأَعْدِلَ بَيْنَكُمُ ۖ اللهُ رَبُّنَا وَرَبُّكُمْ ۖ لَنَا أَعْمَالُنَا وَلَكُمْ أَعْمَالُكُمْ ۖ لَا حُجَّةَ بَيْنَنَا وَبَيْنَكُمُ ۖ اللهُ يَجْمَعُ بَيْنَنَا ۖ وَإِلَيْهِ الْمَصِيرُ
Falithalika fadAAu wastaqimkama omirta wala tattabiAA ahwaahum waqul amantubima anzala Allahu min kitabin waomirtuli-aAAdila baynakum Allahu rabbuna warabbukum lanaaAAmaluna walakum aAAmalukum la hujjatabaynana wabaynakumu Allahu yajmaAAu baynanawa-ilayhi almaseer

Hausa
 
Sabőda haka, sai ka yi kira kuma kai ka daidaitu kamar yadda aka umurce ka, kuma kada ka bi son zũciyőyinsu, kumaka ce, "Nă yi ĩmăni da abin da Allah Ya saukar na littăfi, kuma an umurce ni da in yi ădalci a tsakăninku. Allah ne Ubangijinmu, kuma Shĩ ne Ubangijinku, ayyukanmu nă gare mu, kuma ayyukanku nă gare ku, kuma băbu wata hujja a tsakăninmu da tsakăninku. Allah zai tara mu, kuma zuwa gare Shi makőma take."

Ayah  42:16  الأية
وَالَّذِينَ يُحَاجُّونَ فِي اللهِ مِن بَعْدِ مَا اسْتُجِيبَ لَهُ حُجَّتُهُمْ دَاحِضَةٌ عِندَ رَبِّهِمْ وَعَلَيْهِمْ غَضَبٌ وَلَهُمْ عَذَابٌ شَدِيدٌ
Wallatheena yuhajjoonafee Allahi min baAAdi ma istujeeba lahu hujjatuhumdahidatun AAinda rabbihim waAAalayhim ghadabunwalahum AAathabun shadeed

Hausa
 
Kuma waɗannan da ke jăyayya a cikin al'amarin Allah daga băyan an karɓa masa, hujjarsu ɓătăcciya ce a wurin Ubangijinsu, kuma akwai fushi a kansu, kuma sună da wata azăba mai tsanani.

Ayah  42:17  الأية
اللهُ الَّذِي أَنزَلَ الْكِتَابَ بِالْحَقِّ وَالْمِيزَانَ ۗ وَمَا يُدْرِيكَ لَعَلَّ السَّاعَةَ قَرِيبٌ
Allahu allathee anzala alkitababilhaqqi walmeezani wamayudreeka laAAalla assaAAata qareeb

Hausa
 
Allah ne Wanda Ya saukar da Littăfi da gaskiya, da sikeli. Kuma me ya sanar da kai (cẽwa ană) tsammănin Sa'ar kusa take?

Ayah  42:18  الأية
يَسْتَعْجِلُ بِهَا الَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِهَا ۖ وَالَّذِينَ آمَنُوا مُشْفِقُونَ مِنْهَا وَيَعْلَمُونَ أَنَّهَا الْحَقُّ ۗ أَلَا إِنَّ الَّذِينَ يُمَارُونَ فِي السَّاعَةِ لَفِي ضَلَالٍ بَعِيدٍ
YastaAAjilu biha allatheena layu/minoona biha wallatheena amanoomushfiqoona minha wayaAAlamoona annaha alhaqquala inna allatheena yumaroona fee assaAAatilafee dalalin baAAeed

Hausa
 
Waɗanda ba su yi ĩmănida ita ba, (sũ) ke nẽman gaggautőwarta. Alhăli kuwa waɗanda suka yi ĩmăni, măsu tsőro ne daga gare ta, kuma sun sani, cẽwa ita gaskiya ce. To, lalle ne waɗanda ke shakka a cikin Sa'a, haƙĩƙa,sună a cikin ɓata Mai nĩsa.

Ayah  42:19  الأية
اللهُ لَطِيفٌ بِعِبَادِهِ يَرْزُقُ مَن يَشَاءُ ۖ وَهُوَ الْقَوِيُّ الْعَزِيزُ
Allahu lateefun biAAibadihiyarzuqu man yashao wahuwa alqawiyyu alAAazeez

Hausa
 
Allah Mai tausasăwa ne ga băyinsa. Yană azurta wanda yake so, alhăli kuma Shĩ ne Maiƙarfi, Mabuwăyi.

Ayah  42:20  الأية
مَن كَانَ يُرِيدُ حَرْثَ الْآخِرَةِ نَزِدْ لَهُ فِي حَرْثِهِ ۖ وَمَن كَانَ يُرِيدُ حَرْثَ الدُّنْيَا نُؤْتِهِ مِنْهَا وَمَا لَهُ فِي الْآخِرَةِ مِن نَّصِيبٍ
Man kana yureedu hartha al-akhiratinazid lahu fee harthihi waman kana yureedu harthaaddunya nu/tihi minha wama lahu feeal-akhirati min naseeb

Hausa
 
Wanda ya kasance yană nufin nőman Lăhira ză Mu ƙăra masa a cikin nőmansa, kuma wanda ya kasance yană nufin nőman dũniya, ză Mu sam masa daga gare ta, alhăli kuwa bă shi da wani rabo a cikin Lăhira.

Ayah  42:21  الأية
أَمْ لَهُمْ شُرَكَاءُ شَرَعُوا لَهُم مِّنَ الدِّينِ مَا لَمْ يَأْذَن بِهِ اللهُ ۚ وَلَوْلَا كَلِمَةُ الْفَصْلِ لَقُضِيَ بَيْنَهُمْ ۗ وَإِنَّ الظَّالِمِينَ لَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Am lahum shurakao sharaAAoo lahummina addeeni ma lam ya/than bihi Allahuwalawla kalimatu alfasli laqudiya baynahumwa-inna aththalimeena lahum AAathabunaleem

Hausa
 
Kő sună da waɗansu abőkan tărayya (da Allah) waɗanda suka shar'anta musu, game da addini, abin da Allah bai yi izni ba da shi? Kuma bă dőmin kalmar hukunci ba, da lalle, an yi hukunci a tsakăninsu. Kuma lalle azzălumai sună da azăba mai raɗaɗi.

Ayah  42:22  الأية
تَرَى الظَّالِمِينَ مُشْفِقِينَ مِمَّا كَسَبُوا وَهُوَ وَاقِعٌ بِهِمْ ۗ وَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ فِي رَوْضَاتِ الْجَنَّاتِ ۖ لَهُم مَّا يَشَاءُونَ عِندَ رَبِّهِمْ ۚ ذَٰلِكَ هُوَ الْفَضْلُ الْكَبِيرُ
Tara aththalimeenamushfiqeena mimma kasaboo wahuwa waqiAAun bihim wallatheenaamanoo waAAamiloo assalihati fee rawdatialjannati lahum ma yashaoona AAinda rabbihimthalika huwa alfadlu alkabeer

Hausa
 
Kană ganin azzălumai sună măsu tsőro daga abin da suka sană'anta alhăli kuwa shi abin tsoron, mai aukuwa ne gare su, kuma waɗanda suka yi ĩmăni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai sună a cikin fadamun Aljanna sună da abin da suke so a wurin Ubangijinsu. Waccan fa ita ce falala mai girma.

Ayah  42:23  الأية
ذَٰلِكَ الَّذِي يُبَشِّرُ اللهُ عِبَادَهُ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ ۗ قُل لَّا أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ أَجْرًا إِلَّا الْمَوَدَّةَ فِي الْقُرْبَىٰ ۗ وَمَن يَقْتَرِفْ حَسَنَةً نَّزِدْ لَهُ فِيهَا حُسْنًا ۚ إِنَّ اللهَ غَفُورٌ شَكُورٌ
Thalika allathee yubashshiruAllahu AAibadahu allatheena amanoowaAAamiloo assalihati qul laas-alukum AAalayhi ajran illa almawaddata fee alqurbawaman yaqtarif hasanatan nazid lahu feeha husnaninna Allaha ghafoorun shakoor

Hausa
 
Wancan shĩ ne Allah ke băyar da bushăra da shi ga băyinSa waɗanda suka yi ĩmăni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai. Ka ce: "Bă ni tambayar ku wata ijăra a kansa, făce dai sőyayya ta cikin zumunta." Kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau, ză Mu ƙară masa kyau a cikinsa, lalle Allah Mai găfara ne, Mai gődiya.

Ayah  42:24  الأية
أَمْ يَقُولُونَ افْتَرَىٰ عَلَى اللهِ كَذِبًا ۖ فَإِن يَشَإِ اللهُ يَخْتِمْ عَلَىٰ قَلْبِكَ ۗ وَيَمْحُ اللهُ الْبَاطِلَ وَيُحِقُّ الْحَقَّ بِكَلِمَاتِهِ ۚ إِنَّهُ عَلِيمٌ بِذَاتِ الصُّدُورِ
Am yaqooloona iftara AAala Allahikathiban fa-in yasha-i Allahu yakhtim AAalaqalbika wayamhu Allahu albatila wayuhiqqualhaqqa bikalimatihi innahu AAaleemun bithatiassudoor

Hausa
 
Kő ză su ce: "Ya ƙirƙira ƙarya ga Allah ne?" To, idan Allah Ya so, zai yunƙe a kan zũciyarka, kuma Allah Yana shăfe ƙarya kuma Yana tabbatar da gaskiya da kalmőminSa. Lalle ne Shĩ Masani ne ga abin da ke cikin zukata.

Ayah  42:25  الأية
وَهُوَ الَّذِي يَقْبَلُ التَّوْبَةَ عَنْ عِبَادِهِ وَيَعْفُو عَنِ السَّيِّئَاتِ وَيَعْلَمُ مَا تَفْعَلُونَ
Wahuwa allathee yaqbalu attawbataAAan AAibadihi wayaAAfoo AAani assayyi-atiwayaAAlamu ma tafAAaloon

Hausa
 
Kuma Shi ne ke karɓar tũba daga băyinSa, kuma Yană Yafe ƙananan laifuffuka, alhăli kuwa Yană sanin abin da kuke aikatăwa.

Ayah  42:26  الأية
وَيَسْتَجِيبُ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ وَيَزِيدُهُم مِّن فَضْلِهِ ۚ وَالْكَافِرُونَ لَهُمْ عَذَابٌ شَدِيدٌ
Wayastajeebu allatheena amanoowaAAamiloo assalihati wayazeeduhum min fadlihiwalkafiroona lahum AAathabun shadeed

Hausa
 
Kuma Yană karɓa wa waɗannan da suka yi ĩmăni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma Yană ƙăra musu (sakamako) daga falalarSa. Kuma kăfirai sună da wata azăba mai tsanani.

Ayah  42:27  الأية
وَلَوْ بَسَطَ اللهُ الرِّزْقَ لِعِبَادِهِ لَبَغَوْا فِي الْأَرْضِ وَلَٰكِن يُنَزِّلُ بِقَدَرٍ مَّا يَشَاءُ ۚ إِنَّهُ بِعِبَادِهِ خَبِيرٌ بَصِيرٌ
Walaw basata Allahu arrizqaliAAibadihi labaghaw fee al-ardi walakinyunazzilu biqadarin ma yashao innahu biAAibadihikhabeerun baseer

Hausa
 
Kuma dă Allah Ya shimfiɗa arziki ga băyinSa, dă sun yi zăluncin rarraba jama'a a cikin ƙasa, kuma amma Yană sassaukarwa gwargwado ga abin da Yake so. Lalle ne Shĩ, game da băyinSa, Mai labartawa ne, Mai gani.

Ayah  42:28  الأية
وَهُوَ الَّذِي يُنَزِّلُ الْغَيْثَ مِن بَعْدِ مَا قَنَطُوا وَيَنشُرُ رَحْمَتَهُ ۚ وَهُوَ الْوَلِيُّ الْحَمِيدُ
Wahuwa allathee yunazzilu alghaythamin baAAdi ma qanatoo wayanshuru rahmatahuwahuwa alwaliyyu alhameed

Hausa
 
Kuma Shĩ ne ke sassaukar da girgije (ruwa) a băyan sun yanke ƙauna kuma Yana wătsa rahamarSa, alhăli kuwa Shĩ ne Majiɓinci, Mai gődiya.

Ayah  42:29  الأية
وَمِنْ آيَاتِهِ خَلْقُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَثَّ فِيهِمَا مِن دَابَّةٍ ۚ وَهُوَ عَلَىٰ جَمْعِهِمْ إِذَا يَشَاءُ قَدِيرٌ
Wamin ayatihi khalqu assamawatiwal-ardi wama baththa feehima min dabbatinwahuwa AAala jamAAihim itha yashao qadeer

Hausa
 
Kuma akwai daga ăyőyinSa, halittar sammai da ƙasa da abin da Ya wătsa a cikinsu na dabba alhăli kuwa Shĩ Mai ĩko ne ga tăra su, a lőkacin da Yake so.

Ayah  42:30  الأية
وَمَا أَصَابَكُم مِّن مُّصِيبَةٍ فَبِمَا كَسَبَتْ أَيْدِيكُمْ وَيَعْفُو عَن كَثِيرٍ
Wama asabakum min museebatinfabima kasabat aydeekum wayaAAfoo AAan katheer

Hausa
 
Kuma abin da ya săme ku na wata masifa, to, game da abin da hannăyenku suka sana' anta ne kuma (Alah) Yană Yafẽwar (waɗansu laifuffuka) măsu yawa.

Ayah  42:31  الأية
وَمَا أَنتُم بِمُعْجِزِينَ فِي الْأَرْضِ ۖ وَمَا لَكُم مِّن دُونِ اللهِ مِن وَلِيٍّ وَلَا نَصِيرٍ
Wama antum bimuAAjizeena fee al-ardiwama lakum min dooni Allahi min waliyyin walanaseer

Hausa
 
Kuma ba ku zama măsu buwăya ba a cikin ƙasa kuma bă ku da wani majiɓinci, wanin Allah, kuma bă ku da wani mataimaki.

Ayah  42:32  الأية
وَمِنْ آيَاتِهِ الْجَوَارِ فِي الْبَحْرِ كَالْأَعْلَامِ
Wamin ayatihi aljawarifee albahri kal-aAAlam

Hausa
 
Kuma akwai daga ăyőyinsa, jirăge măsu gudăna a cikin tẽku kamar duwătsu.

Ayah  42:33  الأية
إِن يَشَأْ يُسْكِنِ الرِّيحَ فَيَظْلَلْنَ رَوَاكِدَ عَلَىٰ ظَهْرِهِ ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّكُلِّ صَبَّارٍ شَكُورٍ
In yasha/ yuskini arreehafayathlalna rawakida AAala thahrihiinna fee thalika laayatin likulli sabbarinshakoor

Hausa
 
Idan Ya so, sai Ya kwantar da iskar, sai jirăgen su yini sună măsu kawaici a kan băyan tẽkun,Lalle ne ga wancan, haƙĩƙa, akwai ăyőyi ga dukan mai haƙuri, Mai gődiya.

Ayah  42:34  الأية
أَوْ يُوبِقْهُنَّ بِمَا كَسَبُوا وَيَعْفُ عَن كَثِيرٍ
Aw yoobiqhunna bima kasaboo wayaAAfuAAan katheer

Hausa
 
Kő Ya halakă su (sũ jirăgen) sabőda abin da măsu su suka sană'anta, alhăli kuwa Yană yăfe (laifuffuka) măsu yawa.

Ayah  42:35  الأية
وَيَعْلَمَ الَّذِينَ يُجَادِلُونَ فِي آيَاتِنَا مَا لَهُم مِّن مَّحِيصٍ
WayaAAlama allatheena yujadiloonafee ayatina ma lahum min mahees

Hausa
 
Kuma dőmin waɗanda ke jăyayya a cikin ăyőyinMu su sani (cẽwa) bă su da wata mafaka.

Ayah  42:36  الأية
فَمَا أُوتِيتُم مِّن شَيْءٍ فَمَتَاعُ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا ۖ وَمَا عِندَ اللهِ خَيْرٌ وَأَبْقَىٰ لِلَّذِينَ آمَنُوا وَعَلَىٰ رَبِّهِمْ يَتَوَكَّلُونَ
Fama ooteetum min shay-in famataAAualhayati addunya wama AAindaAllahi khayrun waabqa lillatheena amanoowaAAala rabbihim yatawakkaloon

Hausa
 
Sabőda haka abin da aka bă ku, kő mẽne ne, to, jin dăɗin rayuwar dũniya ne, kuma abin da ke a wurin Allah Shĩ ne mafĩfĩci,kuma Shĩ ne mafi wanzuwa ga waɗanda suka yi ĩmăni kuma sună dőgara a kan Ubangijinsu kawai.

Ayah  42:37  الأية
وَالَّذِينَ يَجْتَنِبُونَ كَبَائِرَ الْإِثْمِ وَالْفَوَاحِشَ وَإِذَا مَا غَضِبُوا هُمْ يَغْفِرُونَ
Wallatheena yajtaniboona kaba-iraal-ithmi walfawahisha wa-itha ma ghadiboohum yaghfiroon

Hausa
 
Kuma waɗanda ke nisantar manyan zunubbai da ayyukan alfăsha, kuma idan sun yi fushi, sũ, sună găfartawa.

Ayah  42:38  الأية
وَالَّذِينَ اسْتَجَابُوا لِرَبِّهِمْ وَأَقَامُوا الصَّلَاةَ وَأَمْرُهُمْ شُورَىٰ بَيْنَهُمْ وَمِمَّا رَزَقْنَاهُمْ يُنفِقُونَ
Wallatheena istajaboolirabbihim waaqamoo assalatawaamruhum shoora baynahum wamimma razaqnahumyunfiqoon

Hausa
 
Da waɗanda suka karɓa kira ga Ubangijinsu, kuma suka tsayar da salla, kuma al'amarinsu shăwara ne a tsakăninsu, kuma daga abin da Muka azurta su sună ciyarwa.

Ayah  42:39  الأية
وَالَّذِينَ إِذَا أَصَابَهُمُ الْبَغْيُ هُمْ يَنتَصِرُونَ
Wallatheena itha asabahumualbaghyu hum yantasiroon

Hausa
 
Da waɗanda idan zălunci ya săme su, sună nẽman taimako (su răma).

Ayah  42:40  الأية
وَجَزَاءُ سَيِّئَةٍ سَيِّئَةٌ مِّثْلُهَا ۖ فَمَنْ عَفَا وَأَصْلَحَ فَأَجْرُهُ عَلَى اللهِ ۚ إِنَّهُ لَا يُحِبُّ الظَّالِمِينَ
Wajazao sayyi-atin sayyi-atun mithluhafaman AAafa waaslaha faajruhu AAalaAllahi innahu la yuhibbu aththalimeen

Hausa
 
Kuma sakamakon cũta shĩ ne wata cũta kamarta, sai dai wanda Ya yăfe kuma ya kyautata, to lădarsa nă ga Allah. Lalle ne, Shĩ (Allah) bă Ya son azzălumai.

Ayah  42:41  الأية
وَلَمَنِ انتَصَرَ بَعْدَ ظُلْمِهِ فَأُولَٰئِكَ مَا عَلَيْهِم مِّن سَبِيلٍ
Walamani intasara baAAda thulmihifaola-ika ma AAalayhim min sabeel

Hausa
 
Kuma Lalle ne, wanda ya nẽmi taimakon rămăwa a băyan an zălunce shi, to waɗannan băbu wata hanyar zargi a kansu.

Ayah  42:42  الأية
إِنَّمَا السَّبِيلُ عَلَى الَّذِينَ يَظْلِمُونَ النَّاسَ وَيَبْغُونَ فِي الْأَرْضِ بِغَيْرِ الْحَقِّ ۚ أُولَٰئِكَ لَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Innama assabeelu AAalaallatheena yathlimoona annasawayabghoona fee al-ardi bighayri alhaqqi ola-ikalahum AAathabun aleem

Hausa
 
lnda hanyar zargi kawai take, shĩ ne a kan waɗanda ke zăluntar mutăne kuma sună ƙẽtare haddin shari'a cikin ƙasa bă tare da haƙƙi ba. Waɗannan sună da azăba Mai raɗaɗi.

Ayah  42:43  الأية
وَلَمَن صَبَرَ وَغَفَرَ إِنَّ ذَٰلِكَ لَمِنْ عَزْمِ الْأُمُورِ
Walaman sabara waghafara inna thalikalamin AAazmi al-omoor

Hausa
 
Kuma Lalle ne, wanda ya yi haƙuri kuma ya găfarta (wa wanda ya zălunce shi), to shĩ wancan aiki haƙĩƙa, yană daga manyan al'amura (da Allah ke so).

Ayah  42:44  الأية
وَمَن يُضْلِلِ اللهُ فَمَا لَهُ مِن وَلِيٍّ مِّن بَعْدِهِ ۗ وَتَرَى الظَّالِمِينَ لَمَّا رَأَوُا الْعَذَابَ يَقُولُونَ هَلْ إِلَىٰ مَرَدٍّ مِّن سَبِيلٍ
Waman yudlili Allahu famalahu min waliyyin min baAAdihi watara aththalimeenalamma raawoo alAAathaba yaqooloona hal ilamaraddin min sabeel

Hausa
 
Kuma wanda (Allah Ya ɓatar, to, bă shi da wani majiɓinci băyanSa, kuma ză ka ga azzălumai, a lőkacin da suka ga azăba, sună cẽwa, "Shin, akwai hanya zuwa ga kőmăwa?"

Ayah  42:45  الأية
وَتَرَاهُمْ يُعْرَضُونَ عَلَيْهَا خَاشِعِينَ مِنَ الذُّلِّ يَنظُرُونَ مِن طَرْفٍ خَفِيٍّ ۗ وَقَالَ الَّذِينَ آمَنُوا إِنَّ الْخَاسِرِينَ الَّذِينَ خَسِرُوا أَنفُسَهُمْ وَأَهْلِيهِمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ ۗ أَلَا إِنَّ الظَّالِمِينَ فِي عَذَابٍ مُّقِيمٍ
Watarahum yuAAradoona AAalayhakhashiAAeena mina aththulli yanthuroonamin tarfin khafiyyin waqala allatheena amanooinna alkhasireena allatheena khasiroo anfusahumwaahleehim yawma alqiyamati ala inna aththalimeenafee AAathabin muqeem

Hausa
 
Kuma kană ganin su ană gitta su a kanta, sună ƙasƙantattu sabőda wulăkanci, sună hange daga gefen gani ɓoyayye. Kuma waɗanda suka yi ĩmăni sai su ce, "Lalle ne, măsu hasăra, sũ ne waɗanda suka yi hasărar răyukansu da iyălansu a Rănar ˇiyăma." To, lalle ne, azzălumai sună a cikin wata azăba zaunanniya.

Ayah  42:46  الأية
وَمَا كَانَ لَهُم مِّنْ أَوْلِيَاءَ يَنصُرُونَهُم مِّن دُونِ اللهِ ۗ وَمَن يُضْلِلِ اللهُ فَمَا لَهُ مِن سَبِيلٍ
Wama kana lahum min awliyaayansuroonahum min dooni Allahi waman yudliliAllahu fama lahu min sabeel

Hausa
 
Kuma waɗansu majiɓinta ba su kasance ba a gare su, waɗanda ke iya taimakonsu, baicin Allah. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, bă shi da wani gődabe na tsĩra.

Ayah  42:47  الأية
اسْتَجِيبُوا لِرَبِّكُم مِّن قَبْلِ أَن يَأْتِيَ يَوْمٌ لَّا مَرَدَّ لَهُ مِنَ اللهِ ۚ مَا لَكُم مِّن مَّلْجَإٍ يَوْمَئِذٍ وَمَا لَكُم مِّن نَّكِيرٍ
Istajeeboo lirabbikum min qabli an ya/tiyayawmun la maradda lahu mina Allahi ma lakummin malja-in yawma-ithin wama lakum min nakeer

Hausa
 
Ku karɓă wa Ubangijinku tun gabănin wani yini ya zo, băbu makawa gare shi daga Allah, bă ku da wata mafaka a rănar nan, kuma bă ku iya yin wani musu.

Ayah  42:48  الأية
فَإِنْ أَعْرَضُوا فَمَا أَرْسَلْنَاكَ عَلَيْهِمْ حَفِيظًا ۖ إِنْ عَلَيْكَ إِلَّا الْبَلَاغُ ۗ وَإِنَّا إِذَا أَذَقْنَا الْإِنسَانَ مِنَّا رَحْمَةً فَرِحَ بِهَا ۖ وَإِن تُصِبْهُمْ سَيِّئَةٌ بِمَا قَدَّمَتْ أَيْدِيهِمْ فَإِنَّ الْإِنسَانَ كَفُورٌ
Fa-in aAAradoo fama arsalnakaAAalayhim hafeethan in AAalayka illaalbalaghu wa-inna itha athaqnaal-insana minna rahmatan fariha bihawa-in tusibhum sayyi-atun bima qaddamat aydeehimfa-inna al-insana kafoor

Hausa
 
To, idan sun bijire, to, ba Mu aike ka kană mai tsaro a kansu ba, băbu abin da ke a kanka făce iyar da Manzanci. Kuma lalle ne, Mũ idan Mun ɗanɗana wa mutum wata rahama daga gare Mu, sai ya yi farin ciki da ita, kuma idan wata masĩfa ta săme su sabőda abin da hannayensu suka gabătar, to, lalle ne mutum mai tsananin kăfirci ne.

Ayah  42:49  الأية
لِّلَّهِ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ يَخْلُقُ مَا يَشَاءُ ۚ يَهَبُ لِمَن يَشَاءُ إِنَاثًا وَيَهَبُ لِمَن يَشَاءُ الذُّكُورَ
Lillahi mulku assamawatiwal-ardi yakhluqu ma yashao yahabuliman yashao inathan wayahabu liman yashao aththukoor

Hausa
 
Mulkin sammai da ƙasa na Allah kawai ne. Yană halitta abin da Yake so. Yană băyar da 'ya'ya mătă ga wanda yake so, kuma Yană băyar da ɗiya maza ga wanda Yake so.

Ayah  42:50  الأية
أَوْ يُزَوِّجُهُمْ ذُكْرَانًا وَإِنَاثًا ۖ وَيَجْعَلُ مَن يَشَاءُ عَقِيمًا ۚ إِنَّهُ عَلِيمٌ قَدِيرٌ
Aw yuzawwijuhum thukrananwa-inathan wayajAAalu man yashao AAaqeeman innahuAAaleemun qadeer

Hausa
 
Kő kuma Ya haɗa su maza da mătă, kuma Yană sanya wanda Ya so bakarăre. Lalle shi, Mai ilmi ne, Mai ĩkon yi.

Ayah  42:51  الأية
وَمَا كَانَ لِبَشَرٍ أَن يُكَلِّمَهُ اللهُ إِلَّا وَحْيًا أَوْ مِن وَرَاءِ حِجَابٍ أَوْ يُرْسِلَ رَسُولًا فَيُوحِيَ بِإِذْنِهِ مَا يَشَاءُ ۚ إِنَّهُ عَلِيٌّ حَكِيمٌ
Wama kana libasharin anyukallimahu Allahu illa wahyan aw min wara-ihijabin aw yursila rasoolan fayoohiya bi-ithnihima yashao innahu AAaliyyun hakeem

Hausa
 
Kuma bă ya kasancẽwa ga wani mutum Allah Ya yi masa magana făce da wahayi, kő daga băYan wani shămaki, kő Ya aika wani Manzo, sa'an nan Ya yi wahayi, da izninsa ga abin da Yake so. Lalle Shĩ, Maɗaukaki ne Mai hikima.

Ayah  42:52  الأية
وَكَذَٰلِكَ أَوْحَيْنَا إِلَيْكَ رُوحًا مِّنْ أَمْرِنَا ۚ مَا كُنتَ تَدْرِي مَا الْكِتَابُ وَلَا الْإِيمَانُ وَلَٰكِن جَعَلْنَاهُ نُورًا نَّهْدِي بِهِ مَن نَّشَاءُ مِنْ عِبَادِنَا ۚ وَإِنَّكَ لَتَهْدِي إِلَىٰ صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ
Wakathalika awhaynailayka roohan min amrina ma kunta tadree maalkitabu wala al-eemanu walakinjaAAalnahu nooran nahdee bihi man nashao min AAibadinawa-innaka latahdee ila siratin mustaqeem

Hausa
 
Kuma kamar wancan Mun aika wani rũhi (rai mai haɗa jama'a) zuwa gare ka, daga gare Mu. Ba ka kasance kă san abin da yake littăfi ba, kő abin da Yake ĩmăni, kuma amma Mun sanya shi (rũhin, watau Alƙur'ăni) wani haske ne, Mună shiryar da wanda Muke so daga cikin băyĩnMu game da shi. Kuma Lalle kai, haƙĩƙa, kană shiryarwa zuwa ga hanya, madaidaiciya.

Ayah  42:53  الأية
صِرَاطِ اللهِ الَّذِي لَهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ ۗ أَلَا إِلَى اللهِ تَصِيرُ الْأُمُورُ
Sirati Allahi allatheelahu ma fee assamawati wamafee al-ardi ala ila Allahi taseerual-omoor

Hausa
 
Hanyar Allah wanda ke da mulkin abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa. To, zuwa ga Allah kawai al'amura ke kőmăwa. 




© EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us