Prev  

43. Surah Az-Zukhruf سورة الزخرف

  Next  




1st Ayah  1  الأية ١الأولي
بِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
حم
Ha-meem

Hausa
 
Ḥ. M̃.

Ayah  43:2  الأية
وَالْكِتَابِ الْمُبِينِ
Walkitabi almubeen

Hausa
 
Ina rantsuwa da Littăfi Mabayyani.

Ayah  43:3  الأية
إِنَّا جَعَلْنَاهُ قُرْآنًا عَرَبِيًّا لَّعَلَّكُمْ تَعْقِلُونَ
Inna jaAAalnahu qur-ananAAarabiyyan laAAallakum taAAqiloona

Hausa
 
Lalle Mũ, Mun sanya shi abin karătu na Lărabci, tsammăninku, kună hankalta.

Ayah  43:4  الأية
وَإِنَّهُ فِي أُمِّ الْكِتَابِ لَدَيْنَا لَعَلِيٌّ حَكِيمٌ
Wa-innahu fee ommi alkitabi ladaynalaAAaliyyun hakeem

Hausa
 
Kuma lalle, shĩ, a cikin uwar littăfi a wurin Mu, haƙĩƙa, maɗaukaki ne, bayyananne.

Ayah  43:5  الأية
أَفَنَضْرِبُ عَنكُمُ الذِّكْرَ صَفْحًا أَن كُنتُمْ قَوْمًا مُّسْرِفِينَ
Afanadribu AAankumu aththikrasafhan an kuntum qawman musrifeen

Hausa
 
Shin, ză Mu kau da kai daga saukar da hukunci daga gare ku ne dőmin kun kasance mutane măsu ɓarna?

Ayah  43:6  الأية
وَكَمْ أَرْسَلْنَا مِن نَّبِيٍّ فِي الْأَوَّلِينَ
Wakam arsalna min nabiyyin feeal-awwaleen

Hausa
 
Alhăli kuwa sau nawa Muka aika wani Annabi a cikin mutănen fărko!

Ayah  43:7  الأية
وَمَا يَأْتِيهِم مِّن نَّبِيٍّ إِلَّا كَانُوا بِهِ يَسْتَهْزِئُونَ
Wama ya/teehim min nabiyyin illakanoo bihi yastahzi-oon

Hausa
 
Kuma wani Annabi bai je musu ba făce sun kasance, game da shi, sună măsu yin izgili.

Ayah  43:8  الأية
فَأَهْلَكْنَا أَشَدَّ مِنْهُم بَطْشًا وَمَضَىٰ مَثَلُ الْأَوَّلِينَ
Faahlakna ashadda minhum batshanwamada mathalu al-awwaleen

Hausa
 
Sai Muka halakar da waɗanda suke sũ ne mafiya ƙarfin damƙa daga gare su. Kuma abin misălin mutănen farkon ya shũɗe.

Ayah  43:9  الأية
وَلَئِن سَأَلْتَهُم مَّنْ خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ لَيَقُولُنَّ خَلَقَهُنَّ الْعَزِيزُ الْعَلِيمُ
Wala-in saaltahum man khalaqa assamawatiwal-arda layaqoolunna khalaqahunna alAAazeezualAAaleem

Hausa
 
Kuma lalle ne, idan ka tambaye su, "Wăne ne ya halitta sammai da ƙasa?" Lalle ză su ce, "Mabuwăyi Mai ilmi ne Ya halitta su."

Ayah  43:10  الأية
الَّذِي جَعَلَ لَكُمُ الْأَرْضَ مَهْدًا وَجَعَلَ لَكُمْ فِيهَا سُبُلًا لَّعَلَّكُمْ تَهْتَدُونَ
Allathee jaAAala lakumu al-ardamahdan wajaAAala lakum feeha subulan laAAallakum tahtadoon

Hausa
 
Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa kuma Ya sanya muku hanyőyi a cikinta, tsammăninku za ku nẽmi shiryuwa.'

Ayah  43:11  الأية
وَالَّذِي نَزَّلَ مِنَ السَّمَاءِ مَاءً بِقَدَرٍ فَأَنشَرْنَا بِهِ بَلْدَةً مَّيْتًا ۚ كَذَٰلِكَ تُخْرَجُونَ
Wallathee nazzala mina assama-imaan biqadarin faansharna bihi baldatan maytan kathalikatukhrajoon

Hausa
 
Kuma Wanda Ya saukar da ruwa daga sama, a kan wani gwargwado, sai Muka răyar da gari matacce game da shi. Kamar haka nan ake fitar da ku (daga kabari).

Ayah  43:12  الأية
وَالَّذِي خَلَقَ الْأَزْوَاجَ كُلَّهَا وَجَعَلَ لَكُم مِّنَ الْفُلْكِ وَالْأَنْعَامِ مَا تَرْكَبُونَ
Wallathee khalaqa al-azwajakullaha wajaAAala lakum mina alfulki wal-anAAamima tarkaboon

Hausa
 
Kuma Wanda Ya halitta ma'aura dukansu, kuma Ya sanya muku, daga jirgi da dabbőbin ni'ima, abin da kuke hawa.

Ayah  43:13  الأية
لِتَسْتَوُوا عَلَىٰ ظُهُورِهِ ثُمَّ تَذْكُرُوا نِعْمَةَ رَبِّكُمْ إِذَا اسْتَوَيْتُمْ عَلَيْهِ وَتَقُولُوا سُبْحَانَ الَّذِي سَخَّرَ لَنَا هَٰذَا وَمَا كُنَّا لَهُ مُقْرِنِينَ
Litastawoo AAala thuhoorihithumma tathkuroo niAAmata rabbikum itha istawaytumAAalayhi wataqooloo subhana allathee sakhkhara lanahatha wama kunna lahu muqrineen

Hausa
 
Domin ku daidaitu a kan băyansa, sa'an nan ku tuna ni'imar Ubangijinku a lőkacin da kuka daidaita a kansa kuma ku ce, "Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya hőre mana wannan alhăli kuwa ba mu kasance măsu iya rinjăya gare Shi ba.

Ayah  43:14  الأية
وَإِنَّا إِلَىٰ رَبِّنَا لَمُنقَلِبُونَ
Wa-inna ila rabbinalamunqaliboon

Hausa
 
"Kuma lalle mũ haƙĩƙa măsu jũyăwa muke, zuwa ga Ubangijinmu."

Ayah  43:15  الأية
وَجَعَلُوا لَهُ مِنْ عِبَادِهِ جُزْءًا ۚ إِنَّ الْإِنسَانَ لَكَفُورٌ مُّبِينٌ
WajaAAaloo lahu min AAibadihi juz-aninna al-insana lakafoorun mubeen

Hausa
 
Kuma suka sanya Masa juz'i daga băyinsa. Lalle ne mutum, haƙĩƙa, mai yawan kăfirci ne, mai bayyanăwar kăfircin.

Ayah  43:16  الأية
أَمِ اتَّخَذَ مِمَّا يَخْلُقُ بَنَاتٍ وَأَصْفَاكُم بِالْبَنِينَ
Ami ittakhatha mimma yakhluqubanatin waasfakum bilbaneen

Hausa
 
Kő ză Ya ɗauki 'ya'ya mătă daga abin da Yake halittawa ne, kuma Ya zăɓe ku da ɗiya maza?

Ayah  43:17  الأية
وَإِذَا بُشِّرَ أَحَدُهُم بِمَا ضَرَبَ لِلرَّحْمَٰنِ مَثَلًا ظَلَّ وَجْهُهُ مُسْوَدًّا وَهُوَ كَظِيمٌ
Wa-itha bushshira ahaduhum bimadaraba lirrahmani mathalan thallawajhuhu muswaddan wahuwa katheem

Hausa
 
Alhăli kuwa idan an băyar da bushăra ga ɗayansu da abin da ya buga misăli da shi ga Mai rahama, sai fuskarsa ta yini tană wadda aka baƙanta launinta, kuma yană cike da baƙin ciki.

Ayah  43:18  الأية
أَوَمَن يُنَشَّأُ فِي الْحِلْيَةِ وَهُوَ فِي الْخِصَامِ غَيْرُ مُبِينٍ
Awaman yunashshao fee alhilyatiwahuwa fee alkhisami ghayru mubeen

Hausa
 
Ashe, kuma (Allah zai zăɓi) wanda ake rẽno a cikin ƙawa alhăli kuwa gă shi a husũma bă mai iya bayyanawar magana ba?

Ayah  43:19  الأية
وَجَعَلُوا الْمَلَائِكَةَ الَّذِينَ هُمْ عِبَادُ الرَّحْمَٰنِ إِنَاثًا ۚ أَشَهِدُوا خَلْقَهُمْ ۚ سَتُكْتَبُ شَهَادَتُهُمْ وَيُسْأَلُونَ
WajaAAaloo almala-ikata allatheenahum AAibadu arrahmani inathanashahidoo khalqahum satuktabu shahadatuhum wayus-aloon

Hausa
 
Kuma suka mayar da mală'iku ('yă'ya) mătă, alhăli kuwa sũ, waɗanda suke băyin (Allah) Mai rahama ne! Shin, sun halarci halittarsu ne? ză a rubũta shaidarsu kuma a tambaye su.

Ayah  43:20  الأية
وَقَالُوا لَوْ شَاءَ الرَّحْمَٰنُ مَا عَبَدْنَاهُم ۗ مَّا لَهُم بِذَٰلِكَ مِنْ عِلْمٍ ۖ إِنْ هُمْ إِلَّا يَخْرُصُونَ
Waqaloo law shaa arrahmanuma AAabadnahum ma lahum bithalika minAAilmin in hum illa yakhrusoon

Hausa
 
Kuma suka ce: "Dă Mai rahama ya so, dă ba mu bauta musu ba." Bă su da wani ilmi game da wancan! Băbu abin da suke yi făce yanki-faɗi.

Ayah  43:21  الأية
أَمْ آتَيْنَاهُمْ كِتَابًا مِّن قَبْلِهِ فَهُم بِهِ مُسْتَمْسِكُونَ
Am ataynahum kitabanmin qablihi fahum bihi mustamsikoon

Hausa
 
Kő Mun bă su wani littăfi ne a gabăninsa (Alƙur'ăni) sabőda haka da shĩ suke riƙe?

Ayah  43:22  الأية
بَلْ قَالُوا إِنَّا وَجَدْنَا آبَاءَنَا عَلَىٰ أُمَّةٍ وَإِنَّا عَلَىٰ آثَارِهِم مُّهْتَدُونَ
Bal qaloo inna wajadna abaanaAAala ommatin wa-inna AAala atharihimmuhtadoon

Hausa
 
Ă'a, sun ce dai, "Lalle mũ, mun sămi ubanninmu a kan wani addini (na al'ăda) kuma lalle mũ, a kan gurăbunsu muke măsu nẽman shiryuwa."

Ayah  43:23  الأية
وَكَذَٰلِكَ مَا أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ فِي قَرْيَةٍ مِّن نَّذِيرٍ إِلَّا قَالَ مُتْرَفُوهَا إِنَّا وَجَدْنَا آبَاءَنَا عَلَىٰ أُمَّةٍ وَإِنَّا عَلَىٰ آثَارِهِم مُّقْتَدُونَ
Wakathalika ma arsalnamin qablika fee qaryatin min natheerin illa qalamutrafooha inna wajadna abaanaAAala ommatin wa-inna AAala atharihimmuqtadoon

Hausa
 
Kuma kamar haka, ba Mu aika wani mai gargaɗi ba a gabăninka, a cikin wata alƙarya, făce mani'imtanta sun ce, "Lalle mũ, mun sămi ubanninmu a kan wani addini kuma lalle mũ, măsu kőyi nea kan gurăbunsu."

Ayah  43:24  الأية
قَالَ أَوَلَوْ جِئْتُكُم بِأَهْدَىٰ مِمَّا وَجَدتُّمْ عَلَيْهِ آبَاءَكُمْ ۖ قَالُوا إِنَّا بِمَا أُرْسِلْتُم بِهِ كَافِرُونَ
Qala awa law ji/tukum bi-ahdamimma wajadtum AAalayhi abaakum qalooinna bima orsiltum bihi kafiroon

Hausa
 
(Sai mai gargaɗin) ya ce: "Shin, ban zo muku da abin da ya fi zama shiriya daga abin da kuka sămi ubanninku a kansa ba?" Suka ce, "Lalle mũ dai măsu kafirta ne game da abin da aka aiko ku da shi."

Ayah  43:25  الأية
فَانتَقَمْنَا مِنْهُمْ ۖ فَانظُرْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُكَذِّبِينَ
Fantaqamna minhum fanthurkayfa kana AAaqibatu almukaththibeen

Hausa
 
Sabőda haka Muka yi musu azăbar rămuwa. To, ka dũbi yadda ăƙibar măsu ƙaryatăwa take.

Ayah  43:26  الأية
وَإِذْ قَالَ إِبْرَاهِيمُ لِأَبِيهِ وَقَوْمِهِ إِنَّنِي بَرَاءٌ مِّمَّا تَعْبُدُونَ
Wa-ith qala ibraheemuli-abeehi waqawmihi innanee baraon mimma taAAbudoon

Hausa
 
Kuma (ka ambaci) lőkacin da Ibrăhĩm ya ce wa ubansada mutănensa, "Lalle nĩ mai barranta ne daga abin da kuke bautăwa."

Ayah  43:27  الأية
إِلَّا الَّذِي فَطَرَنِي فَإِنَّهُ سَيَهْدِينِ
Illa allathee fataraneefa-innahu sayahdeen

Hausa
 
"Făce wannan da Ya ƙăga halittata, to, lalle Shĩ ne zai shiryar da ni."

Ayah  43:28  الأية
وَجَعَلَهَا كَلِمَةً بَاقِيَةً فِي عَقِبِهِ لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ
WajaAAalaha kalimatan baqiyatanfee AAaqibihi laAAallahum yarjiAAoon

Hausa
 
Kuma (Ibrăhĩm) ya sanya (ita wannan magana) kalma mai wanzuwa a cikin zuriyarsa, tsammăninsu su kőmo daga ɓata.

Ayah  43:29  الأية
بَلْ مَتَّعْتُ هَٰؤُلَاءِ وَآبَاءَهُمْ حَتَّىٰ جَاءَهُمُ الْحَقُّ وَرَسُولٌ مُّبِينٌ
Bal mattaAAtu haola-i waabaahumhatta jaahumu alhaqqu warasoolunmubeen

Hausa
 
Ă'a, Na jiyar da waɗannan mutăne dăɗi sũ da ubanninsu har gaskiya, da Manzo mai bayyanawar gaskiyar, ya zo musu.

Ayah  43:30  الأية
وَلَمَّا جَاءَهُمُ الْحَقُّ قَالُوا هَٰذَا سِحْرٌ وَإِنَّا بِهِ كَافِرُونَ
Walamma jaahumu alhaqquqaloo hatha sihrun wa-inna bihi kafiroon

Hausa
 
Kuma a lőkacin da gaskiyar ta jẽ musu sai suka ce: "Wannan sihiri ne kuma mũ măsu kăfirta da shi ne."

Ayah  43:31  الأية
وَقَالُوا لَوْلَا نُزِّلَ هَٰذَا الْقُرْآنُ عَلَىٰ رَجُلٍ مِّنَ الْقَرْيَتَيْنِ عَظِيمٍ
Waqaloo lawla nuzzila hathaalqur-anu AAala rajulin mina alqaryatayni AAatheem

Hausa
 
Kuma suka ce: "Don me ba a saukar da wannan Alƙur'ăni a kan wani mutum mai girma daga alƙaryun nan biyu ba?"

Ayah  43:32  الأية
أَهُمْ يَقْسِمُونَ رَحْمَتَ رَبِّكَ ۚ نَحْنُ قَسَمْنَا بَيْنَهُم مَّعِيشَتَهُمْ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا ۚ وَرَفَعْنَا بَعْضَهُمْ فَوْقَ بَعْضٍ دَرَجَاتٍ لِّيَتَّخِذَ بَعْضُهُم بَعْضًا سُخْرِيًّا ۗ وَرَحْمَتُ رَبِّكَ خَيْرٌ مِّمَّا يَجْمَعُونَ
Ahum yaqsimoona rahmata rabbika nahnuqasamna baynahum maAAeeshatahum fee alhayatiaddunya warafaAAna baAAdahum fawqabaAAdin darajatin liyattakhitha baAAduhumbaAAdan sukhriyyan warahmatu rabbika khayrun mimmayajmaAAoon

Hausa
 
Shin, sũ ne ke raba rahamar Ubangijinka? Mũ ne, Muka raba musu abincinsu a cikin răyuwar dũniya, kuma Muka ɗaukaka waɗansunsu a kan waɗansu da darajőji dőmin waɗansunsu su riƙi waɗansu lẽburori kumarahamar Ubangijinka (ta Annabci ), ita ce mafificiya daga abin da suke tărăwa.

Ayah  43:33  الأية
وَلَوْلَا أَن يَكُونَ النَّاسُ أُمَّةً وَاحِدَةً لَّجَعَلْنَا لِمَن يَكْفُرُ بِالرَّحْمَٰنِ لِبُيُوتِهِمْ سُقُفًا مِّن فِضَّةٍ وَمَعَارِجَ عَلَيْهَا يَظْهَرُونَ
Walawla an yakoona annasuommatan wahidatan lajaAAalna liman yakfuru birrahmanilibuyootihim suqufan min fiddatin wamaAAarijaAAalayha yathharoon

Hausa
 
Kuma bă dőmin mutane su kasance al'umma ɗaya ba, lalle ne, dă Mun sanya wa măsu kăfircẽ wa Mai Rahama, a gidăjensu, rufi na azurfa, kuma da matăkalai, ya zama a kanta suke tăƙăwa.

Ayah  43:34  الأية
وَلِبُيُوتِهِمْ أَبْوَابًا وَسُرُرًا عَلَيْهَا يَتَّكِئُونَ
Walibuyootihim abwaban wasururanAAalayha yattaki-oon

Hausa
 
Kuma a gidăjensu, Mu sanya) ƙyamăre da gadăje, a kansu suke kishingiɗa.

Ayah  43:35  الأية
وَزُخْرُفًا ۚ وَإِن كُلُّ ذَٰلِكَ لَمَّا مَتَاعُ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا ۚ وَالْآخِرَةُ عِندَ رَبِّكَ لِلْمُتَّقِينَ
Wazukhrufan wa-in kullu thalika lammamataAAu alhayati addunya wal-akhiratuAAinda rabbika lilmuttaqeen

Hausa
 
Da zĩnăriya. Kuma dukan wancan abu bai zama ba, sai jin dăɗin răyuwar dũniya nekawai' alhăli kuwa Lăhira, a wurin Ubangijinka, ta măsu taƙawa ce.

Ayah  43:36  الأية
وَمَن يَعْشُ عَن ذِكْرِ الرَّحْمَٰنِ نُقَيِّضْ لَهُ شَيْطَانًا فَهُوَ لَهُ قَرِينٌ
Waman yaAAshu AAan thikri arrahmaninuqayyid lahu shaytanan fahuwa lahu qareen

Hausa
 
Kuma wanda ya makanta daga barin hukuncin Mai rahama, to, ză Mu lulluɓe shi da shaiɗan, watau shĩ ne abőkinsa.

Ayah  43:37  الأية
وَإِنَّهُمْ لَيَصُدُّونَهُمْ عَنِ السَّبِيلِ وَيَحْسَبُونَ أَنَّهُم مُّهْتَدُونَ
Wa-innahum layasuddoonahum AAani assabeeliwayahsaboona annahum muhtadoon

Hausa
 
Kuma lalle su haƙĩƙa sună kange su daga hanya, kuma sună Zaton cẽwa sũ măsu shiryuwa ne.

Ayah  43:38  الأية
حَتَّىٰ إِذَا جَاءَنَا قَالَ يَا لَيْتَ بَيْنِي وَبَيْنَكَ بُعْدَ الْمَشْرِقَيْنِ فَبِئْسَ الْقَرِينُ
Hatta itha jaanaqala ya layta baynee wabaynaka buAAda almashriqaynifabi/sa alqareen

Hausa
 
Har a lőkacin da (abőkin Shaiɗan) ya zo Mana (ya mutu) sai ya ce: (wa Shaiɗan) "Dă dai a tsakănina da tsakăninka akwai nĩsan gabas da yamma, sabőda haka, tir da kai ga zama abőkin mutum!"

Ayah  43:39  الأية
وَلَن يَنفَعَكُمُ الْيَوْمَ إِذ ظَّلَمْتُمْ أَنَّكُمْ فِي الْعَذَابِ مُشْتَرِكُونَ
Walan yanfaAAakumu alyawma ith thalamtumannakum fee alAAathabi mushtarikoon

Hausa
 
Kuma (wannan magana) bă za ta amfăne ku ba, a yau, dőmin kun yi zălunci, lalle ku măsu tărẽwa ne a cikin azăba.

Ayah  43:40  الأية
أَفَأَنتَ تُسْمِعُ الصُّمَّ أَوْ تَهْدِي الْعُمْيَ وَمَن كَانَ فِي ضَلَالٍ مُّبِينٍ
Afaanta tusmiAAu assumma awtahdee alAAumya waman kana fee dalalinmubeen

Hausa
 
Shin to, kai kană jiyar da kurma ne, ko kană shiryar da makăho da wanda ke a cikin ɓata bayyananna?

Ayah  43:41  الأية
فَإِمَّا نَذْهَبَنَّ بِكَ فَإِنَّا مِنْهُم مُّنتَقِمُونَ
Fa-imma nathhabanna bikafa-inna minhum muntaqimoon

Hausa
 
To, kő dai Mu tafi da kai to, lalle Mũ, măsu yin azăbarrămu, wa ne a kansu.

Ayah  43:42  الأية
أَوْ نُرِيَنَّكَ الَّذِي وَعَدْنَاهُمْ فَإِنَّا عَلَيْهِم مُّقْتَدِرُونَ
Aw nuriyannaka allathee waAAadnahumfa-inna AAalayhim muqtadiroon

Hausa
 
Kő kuma Mu nũna maka abin da Muka yi musu wa'adi, to, lalle Mũ, Măsu ĩkon tasarrufi a kansu ne.

Ayah  43:43  الأية
فَاسْتَمْسِكْ بِالَّذِي أُوحِيَ إِلَيْكَ ۖ إِنَّكَ عَلَىٰ صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ
Fastamsik billatheeoohiya ilayka innaka AAala siratinmustaqeem

Hausa
 
Sabőda haka, ka yi riƙo ga abin da aka yi wahayi da shi zuwa gaie ka. Lalle ne kai, kană a kan hanya madaidaiciyl.

Ayah  43:44  الأية
وَإِنَّهُ لَذِكْرٌ لَّكَ وَلِقَوْمِكَ ۖ وَسَوْفَ تُسْأَلُونَ
Wa-innahu lathikrun laka waliqawmikawasawfa tus-aloon

Hausa
 
Kuma shi (abin wahayin) ambato (na ɗaukaka) ne a gare ka da kuma ga mutănenka, kuma ză a tambaye ku.

Ayah  43:45  الأية
وَاسْأَلْ مَنْ أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ مِن رُّسُلِنَا أَجَعَلْنَا مِن دُونِ الرَّحْمَٰنِ آلِهَةً يُعْبَدُونَ
Was-al man arsalna minqablika min rusulina ajaAAalna min dooni arrahmanialihatan yuAAbadoon

Hausa
 
Kuma ka tambayi waɗanda Muka aika a gabăninka daga Manzannin Mu, "Shin, Mun sanya waɗansu gumăka, wasun (Allah), Mai rahama, ană bauta musu?"

Ayah  43:46  الأية
وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا مُوسَىٰ بِآيَاتِنَا إِلَىٰ فِرْعَوْنَ وَمَلَئِهِ فَقَالَ إِنِّي رَسُولُ رَبِّ الْعَالَمِينَ
Walaqad arsalna moosa bi-ayatinaila firAAawna wamala-ihi faqala innee rasoolu rabbialAAalameen

Hausa
 
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Mũsă, game da ăyőyin Mu, zuwa ga Fir'auna da mashăwartansa, sai ya ce: "Lalle nĩ, Manzo ne daga Ubangijin halittu."

Ayah  43:47  الأية
فَلَمَّا جَاءَهُم بِآيَاتِنَا إِذَا هُم مِّنْهَا يَضْحَكُونَ
Falamma jaahum bi-ayatinaitha hum minha yadhakoon

Hausa
 
To, a lőkacin da ya jẽ musu da ăyőyinMu, sai gă su sună yi musu dăriya.

Ayah  43:48  الأية
وَمَا نُرِيهِم مِّنْ آيَةٍ إِلَّا هِيَ أَكْبَرُ مِنْ أُخْتِهَا ۖ وَأَخَذْنَاهُم بِالْعَذَابِ لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ
Wama nureehim min ayatin illahiya akbaru min okhtiha waakhathnahum bilAAathabilaAAallahum yarjiAAoon

Hausa
 
Kuma ba Mu nũna musu wata ăyă ba, făce ita ce mafi girma daga 'yar'uwarta. Kuma Muka kăma su da azăba, tsammăninsu kő sună kőmőwa.

Ayah  43:49  الأية
وَقَالُوا يَا أَيُّهَ السَّاحِرُ ادْعُ لَنَا رَبَّكَ بِمَا عَهِدَ عِندَكَ إِنَّنَا لَمُهْتَدُونَ
Waqaloo ya ayyuha asahiruodAAu lana rabbaka bima AAahida AAindaka innanalamuhtadoon

Hausa
 
Kuma suka ce: "Yă kai mai sihiri! Ka rőƙa mana Ubangijinka da albarkacin abin da yi alkawari a wurinka, lalle mũ, haƙĩƙa, măsu shiryuwa ne."

Ayah  43:50  الأية
فَلَمَّا كَشَفْنَا عَنْهُمُ الْعَذَابَ إِذَا هُمْ يَنكُثُونَ
Falamma kashafna AAanhumualAAathaba itha hum yankuthoon

Hausa
 
To, a lőkacin da duk Muka kuranye musu azăba, sai gă su sună warware alkawarinsu.

Ayah  43:51  الأية
وَنَادَىٰ فِرْعَوْنُ فِي قَوْمِهِ قَالَ يَا قَوْمِ أَلَيْسَ لِي مُلْكُ مِصْرَ وَهَٰذِهِ الْأَنْهَارُ تَجْرِي مِن تَحْتِي ۖ أَفَلَا تُبْصِرُونَ
Wanada firAAawnu fee qawmihi qalaya qawmi alaysa lee mulku misra wahathihial-anharu tajree min tahtee afala tubsiroon

Hausa
 
Kuma Fir'auna ya yi kira a cikin mutănensa, ya ce: "Ya mutănẽna! Ashe mulkin Masar bă a gare ni yake ba, kuma waɗannan kőguna sună gudăna daga ƙarƙashĩna? Ashe, ba ku gani ba?"

Ayah  43:52  الأية
أَمْ أَنَا خَيْرٌ مِّنْ هَٰذَا الَّذِي هُوَ مَهِينٌ وَلَا يَكَادُ يُبِينُ
Am ana khayrun min hatha allatheehuwa maheenun wala yakadu yubeen

Hausa
 
"Kő kuma bă nĩ ne mafĩfĩci ba daga wannan wanda yake shĩ wulakantacce ne kuma bă ya iya bayyanawar magana sai da ƙyar?

Ayah  43:53  الأية
فَلَوْلَا أُلْقِيَ عَلَيْهِ أَسْوِرَةٌ مِّن ذَهَبٍ أَوْ جَاءَ مَعَهُ الْمَلَائِكَةُ مُقْتَرِنِينَ
Falawla olqiya AAalayhi aswiratun minthahabin aw jaa maAAahu almala-ikatumuqtarineen

Hausa
 
"To, don me, ba a jẽfa mundăye na zĩnăriya a kansaba, kő kuma mală'iku su taho tăre da shi haɗe?"

Ayah  43:54  الأية
فَاسْتَخَفَّ قَوْمَهُ فَأَطَاعُوهُ ۚ إِنَّهُمْ كَانُوا قَوْمًا فَاسِقِينَ
Fastakhaffa qawmahu faataAAoohuinnahum kanoo qawman fasiqeen

Hausa
 
Sai ya sassabce hankalin mutănensa, sabőda haka suka bĩ shi. Lalle sũ, sun kasance waɗansu irin mutăne ne făsiƙai.

Ayah  43:55  الأية
فَلَمَّا آسَفُونَا انتَقَمْنَا مِنْهُمْ فَأَغْرَقْنَاهُمْ أَجْمَعِينَ
Falamma asafoonaintaqamna minhum faaghraqnahum ajmaAAeen

Hausa
 
Sabőda haka a lőkacin da suka husătar da Mu, Muka yi musu azăbar rămuwa sai Muka nutsar da su gabă ɗaya.

Ayah  43:56  الأية
فَجَعَلْنَاهُمْ سَلَفًا وَمَثَلًا لِّلْآخِرِينَ
FajaAAalnahum salafan wamathalan lil-akhireen

Hausa
 
Sai Muka sanya su magabăta kuma abin misăli ga mutănen ƙarshe.

Ayah  43:57  الأية
وَلَمَّا ضُرِبَ ابْنُ مَرْيَمَ مَثَلًا إِذَا قَوْمُكَ مِنْهُ يَصِدُّونَ
Walamma duriba ibnu maryamamathalan itha qawmuka minhu yasiddoon

Hausa
 
Kuma a lőkacin da aka buga misăli da ¦an Maryama, sai gă mutănenka daga gare shi (shi misalin) sună dăriya da izgili.

Ayah  43:58  الأية
وَقَالُوا أَآلِهَتُنَا خَيْرٌ أَمْ هُوَ ۚ مَا ضَرَبُوهُ لَكَ إِلَّا جَدَلًا ۚ بَلْ هُمْ قَوْمٌ خَصِمُونَ
Waqaloo aalihatunakhayrun am huwa ma daraboohu laka illajadalan bal hum qawmun khasimoon

Hausa
 
Kuma suka ce: "Shin, gumăkanmu ne mafĩfĩta kő shi (¦an Maryama)?" Ba su buga wannan misăli ba a gare ka făce dőmin yin jidăli. Ă'a, sũ mutăne nemăsu husũma.

Ayah  43:59  الأية
إِنْ هُوَ إِلَّا عَبْدٌ أَنْعَمْنَا عَلَيْهِ وَجَعَلْنَاهُ مَثَلًا لِّبَنِي إِسْرَائِيلَ
In huwa illa AAabdun anAAamnaAAalayhi wajaAAalnahu mathalan libanee isra-eel

Hausa
 
Shi (¦an Maryama) bai zama ba făce wani băwa ne, Mun yi ni'ima a gare shi, kuma Muka sanya shi abin kőyi ga Banĩ Isră'ĩla.

Ayah  43:60  الأية
وَلَوْ نَشَاءُ لَجَعَلْنَا مِنكُم مَّلَائِكَةً فِي الْأَرْضِ يَخْلُفُونَ
Walaw nashao lajaAAalna minkummala-ikatan fee al-ardi yakhlufoon

Hausa
 
Kuma dă Mună so lalle ne dă Mun sanya mală'iku, daga ci, kinku, a cikin ƙasa, sună mayẽwa

Ayah  43:61  الأية
وَإِنَّهُ لَعِلْمٌ لِّلسَّاعَةِ فَلَا تَمْتَرُنَّ بِهَا وَاتَّبِعُونِ ۚ هَٰذَا صِرَاطٌ مُّسْتَقِيمٌ
Wa-innahu laAAilmun lissaAAatifala tamtarunna biha wattabiAAooni hathasiratun mustaqeem

Hausa
 
Kuma lalle shĩ, haƙĩƙa, wani ilmi ne na Sa'a, sabőda haka, kada ku yi shakka a gare ta, kuma ku bĩ Ni. Wannan ita ce hanya madaidaiciya.

Ayah  43:62  الأية
وَلَا يَصُدَّنَّكُمُ الشَّيْطَانُ ۖ إِنَّهُ لَكُمْ عَدُوٌّ مُّبِينٌ
Wala yasuddannakumu ashshaytanuinnahu lakum AAaduwwun mubeen

Hausa
 
Kuma kada Shaiɗan ya taushe ku (daga hanyar). Lalle shĩ maƙiyi ne a gare ku, mai bayyanăwar ƙiyayya.

Ayah  43:63  الأية
وَلَمَّا جَاءَ عِيسَىٰ بِالْبَيِّنَاتِ قَالَ قَدْ جِئْتُكُم بِالْحِكْمَةِ وَلِأُبَيِّنَ لَكُم بَعْضَ الَّذِي تَخْتَلِفُونَ فِيهِ ۖ فَاتَّقُوا اللهَ وَأَطِيعُونِ
Walamma jaa AAeesa bilbayyinatiqala qad ji/tukum bilhikmati wali-obayyinalakum baAAda allathee takhtalifoona feehi fattaqooAllaha waateeAAoon

Hausa
 
Kuma a lőkacin da Ĩsă ya jẽ da hujjőji bayyanannu, ya ce: "Lalle ne nă zo muku da hikima kuma dőmin in bayyana muku, săshen abin da kuke săɓă wa jũna acikinsa, sabőda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗă'a."

Ayah  43:64  الأية
إِنَّ اللهَ هُوَ رَبِّي وَرَبُّكُمْ فَاعْبُدُوهُ ۚ هَٰذَا صِرَاطٌ مُّسْتَقِيمٌ
Inna Allaha huwa rabbee warabbukum faAAbudoohuhatha siratun mustaqeem

Hausa
 
"Lalle ne, Allah Shĩ ne Ubangijina kuma Shi ne Ubangijinku sabőda haka ku bauta Masa. Wannan ita ce hanya madaidaiciya."

Ayah  43:65  الأية
فَاخْتَلَفَ الْأَحْزَابُ مِن بَيْنِهِمْ ۖ فَوَيْلٌ لِّلَّذِينَ ظَلَمُوا مِنْ عَذَابِ يَوْمٍ أَلِيمٍ
Fakhtalafa al-ahzabumin baynihim fawaylun lillatheena thalamoomin AAathabi yawmin aleem

Hausa
 
Sai ƙungiyőyi suka săɓa a tsakăninsu. To, bone yă tabbata ga waɗanda suka yi zălunci daga azăbar yini mai raɗaɗi!

Ayah  43:66  الأية
هَلْ يَنظُرُونَ إِلَّا السَّاعَةَ أَن تَأْتِيَهُم بَغْتَةً وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ
Hal yanthuroona illa assaAAataan ta/tiyahum baghtatan wahum la yashAAuroon

Hausa
 
Shin sună jiran wani abu ne? sai dai Sa'a ta jẽ musu bisaga abke, alhăli kuwa ba su sani ba.

Ayah  43:67  الأية
الْأَخِلَّاءُ يَوْمَئِذٍ بَعْضُهُمْ لِبَعْضٍ عَدُوٌّ إِلَّا الْمُتَّقِينَ
Al-akhillao yawma-ithin baAAduhumlibaAAdin AAaduwwun illa almuttaqeen

Hausa
 
Masőya a yinin nan, săshensu zuwa ga săshe maƙiya ne, făce măsu taƙawa (sũ kam măsu son jũna ne).

Ayah  43:68  الأية
يَا عِبَادِ لَا خَوْفٌ عَلَيْكُمُ الْيَوْمَ وَلَا أَنتُمْ تَحْزَنُونَ
Ya AAibadi la khawfunAAalaykumu alyawma wala antum tahzanoon

Hausa
 
Ya băyĩNa! Băbu tsőro a kanku a yau, kuma bă ză ku yi baƙin ciki ba.

Ayah  43:69  الأية
الَّذِينَ آمَنُوا بِآيَاتِنَا وَكَانُوا مُسْلِمِينَ
Allatheena amanoo bi-ayatinawakanoo muslimeen

Hausa
 
Waɗanda suka yi ĩmăni da ăyőyinMu, kuma suka kasance măsu sallamawar al'amari (ga Allah).

Ayah  43:70  الأية
ادْخُلُوا الْجَنَّةَ أَنتُمْ وَأَزْوَاجُكُمْ تُحْبَرُونَ
Odkhuloo aljannata antum waazwajukumtuhbaroon

Hausa
 
Ku shiga Aljanna, kũ da mătan aurenku, ană girmama ku.

Ayah  43:71  الأية
يُطَافُ عَلَيْهِم بِصِحَافٍ مِّن ذَهَبٍ وَأَكْوَابٍ ۖ وَفِيهَا مَا تَشْتَهِيهِ الْأَنفُسُ وَتَلَذُّ الْأَعْيُنُ ۖ وَأَنتُمْ فِيهَا خَالِدُونَ
Yutafu AAalayhim bisihafinmin thahabin waakwabin wafeeha matashtaheehi al-anfusu watalaththu al-aAAyunu waantum feehakhalidoon

Hausa
 
Ană kẽwayăwa a kansu da akussa na zĩnăriya da kőfuna, alhăli kuwa a cikinsu akwai abin da răyuka ke marmari kuma idănu su ji dăɗi, kuma kũ, a cikinta (Aljannar), madawwama ne.

Ayah  43:72  الأية
وَتِلْكَ الْجَنَّةُ الَّتِي أُورِثْتُمُوهَا بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Watilka aljannatu allatee oorithtumoohabima kuntum taAAmaloon

Hausa
 
Kuma waccan ita ce Aljannar, wannan da aka gădar da ku ita sabőda abin da kuka kasance kună aikatăwa.

Ayah  43:73  الأية
لَكُمْ فِيهَا فَاكِهَةٌ كَثِيرَةٌ مِّنْهَا تَأْكُلُونَ
Lakum feeha fakihatunkatheeratun minha ta/kuloon

Hausa
 
Kună sămu, a cikinta, 'yă'yan ităcen marmari măsu yawa, daga cikinsu kuke ci.

Ayah  43:74  الأية
إِنَّ الْمُجْرِمِينَ فِي عَذَابِ جَهَنَّمَ خَالِدُونَ
Inna almujrimeena fee AAathabijahannama khalidoon

Hausa
 
Lalle măsu laifi madawwama ne a cikin azăbar Jahannama.

Ayah  43:75  الأية
لَا يُفَتَّرُ عَنْهُمْ وَهُمْ فِيهِ مُبْلِسُونَ
La yufattaru AAanhum wahum feehimublisoon

Hausa
 
Bă a sauƙaƙar da ita (azăbar) daga gare su, alhăli kuwa sũ,a cikinta, măsu kăsa magana ne.

Ayah  43:76  الأية
وَمَا ظَلَمْنَاهُمْ وَلَٰكِن كَانُوا هُمُ الظَّالِمِينَ
Wama thalamnahumwalakin kanoo humu aththalimeen

Hausa
 
Kuma ba Mu zălunce su ba, amma sũ ne suka kasance azzălumai.

Ayah  43:77  الأية
وَنَادَوْا يَا مَالِكُ لِيَقْضِ عَلَيْنَا رَبُّكَ ۖ قَالَ إِنَّكُم مَّاكِثُونَ
Wanadaw ya maliku liyaqdiAAalayna rabbuka qala innakum makithoon

Hausa
 
Kuma suka yi kira, "Ya Măliku! Ubangijinka Ya kashe mu mana " (Măliku) ya ce: "Lalle kũ mazauna ne."

Ayah  43:78  الأية
لَقَدْ جِئْنَاكُم بِالْحَقِّ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَكُمْ لِلْحَقِّ كَارِهُونَ
Laqad ji/nakum bilhaqqiwalakinna aktharakum lilhaqqi karihoon

Hausa
 
Lalle ne, haƙĩƙa, Mun jẽ muku da gaskiya, kuma amma mafi yawanku măsu ƙi ga gaskiyar ne.

Ayah  43:79  الأية
أَمْ أَبْرَمُوا أَمْرًا فَإِنَّا مُبْرِمُونَ
Am abramoo amran fa-inna mubrimoon

Hausa
 
Kő kuma sun tukka wani al'amari ne? To, lalle Mũ, Măsu tukkăwa ne.

Ayah  43:80  الأية
أَمْ يَحْسَبُونَ أَنَّا لَا نَسْمَعُ سِرَّهُمْ وَنَجْوَاهُم ۚ بَلَىٰ وَرُسُلُنَا لَدَيْهِمْ يَكْتُبُونَ
Am yahsaboona anna lanasmaAAu sirrahum wanajwahum bala warusulunaladayhim yaktuboon

Hausa
 
Ko sună zaton lalle Mũ, bă Mu jin asĩrinsu da gănăwarsu? Na'am! Kuma manzannin Mu na tăre da su sună rubũtăwa.

Ayah  43:81  الأية
قُلْ إِن كَانَ لِلرَّحْمَٰنِ وَلَدٌ فَأَنَا أَوَّلُ الْعَابِدِينَ
Qul in kana lirrahmaniwaladun faana awwalu alAAabideen

Hausa
 
Ka ce: "Idan har akwai ɗă ga Mai rahama, to, nĩ ne farkon măsu bauta (wa ɗan)."

Ayah  43:82  الأية
سُبْحَانَ رَبِّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ رَبِّ الْعَرْشِ عَمَّا يَصِفُونَ
Subhana rabbi assamawatiwal-ardi rabbi alAAarshi AAamma yasifoon

Hausa
 
Tsarkin Ubangijin sammai da ƙasa, Ubangijin Al'arshi, ya tabbata daga abin da suke sifantăwa.

Ayah  43:83  الأية
فَذَرْهُمْ يَخُوضُوا وَيَلْعَبُوا حَتَّىٰ يُلَاقُوا يَوْمَهُمُ الَّذِي يُوعَدُونَ
Fatharhum yakhoodoowayalAAaboo hatta yulaqoo yawmahumu allatheeyooAAadoon

Hausa
 
Sabőda haka, ka ƙyălẽ su, su kũtsa kuma su yi wăsă har su haɗu da yininsu, wanda ake yi musu wa'adi da shi.

Ayah  43:84  الأية
وَهُوَ الَّذِي فِي السَّمَاءِ إِلَٰهٌ وَفِي الْأَرْضِ إِلَٰهٌ ۚ وَهُوَ الْحَكِيمُ الْعَلِيمُ
Wahuwa allathee fee assama-iilahun wafee al-ardi ilahun wahuwa alhakeemualAAaleem

Hausa
 
Kuma Shĩ ne wanda ke abin bautăwa a sama kuma abin bautăwa a ƙasa, kuma, Shĩ ne Mai hikima, Masani.

Ayah  43:85  الأية
وَتَبَارَكَ الَّذِي لَهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا وَعِندَهُ عِلْمُ السَّاعَةِ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ
Watabaraka allathee lahu mulkuassamawati wal-ardi wamabaynahuma waAAindahu AAilmu assaAAatiwa-ilayhi turjaAAoon

Hausa
 
Kuma albarkar wanda ke da mulkin sammai da ƙasă abin da ke a tsakăninsu tă bayyana, kuma a wurinSa ne ilmin Sa'a yake, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku.

Ayah  43:86  الأية
وَلَا يَمْلِكُ الَّذِينَ يَدْعُونَ مِن دُونِهِ الشَّفَاعَةَ إِلَّا مَن شَهِدَ بِالْحَقِّ وَهُمْ يَعْلَمُونَ
Wala yamliku allatheenayadAAoona min doonihi ashshafaAAata illaman shahida bilhaqqi wahum yaAAlamoon

Hausa
 
Kuma waɗanda suke kira baicinSa ba su mallaki cẽto ba, făce wanda ya yi shaida da gaskiya, kuma sũ, sună sane (da haka).

Ayah  43:87  الأية
وَلَئِن سَأَلْتَهُم مَّنْ خَلَقَهُمْ لَيَقُولُنَّ اللهُ ۖ فَأَنَّىٰ يُؤْفَكُونَ
Wala-in saaltahum man khalaqahumlayaqoolunna Allahu faanna yu/fakoon

Hausa
 
Kuma lalle idan ka tambaye su: "Wăne ne ya halitta su?" Lalle ne ză su ce Allah ne. To, yăya ake jũyar da su?

Ayah  43:88  الأية
وَقِيلِهِ يَا رَبِّ إِنَّ هَٰؤُلَاءِ قَوْمٌ لَّا يُؤْمِنُونَ
Waqeelihi ya rabbi inna haola-iqawmun la yu/minoon

Hausa
 
Kuma da (ilmin) maganarSa (Annabi) "Ya Ubangijĩna! Lalle waɗannan mutăne ne waɗanda bă ză su yi ĩmăni ba."

Ayah  43:89  الأية
فَاصْفَحْ عَنْهُمْ وَقُلْ سَلَامٌ ۚ فَسَوْفَ يَعْلَمُونَ
Fasfah AAanhum waqulsalamun fasawfa yaAAlamoon

Hausa
 
To, sai ka kau da kai daga gare su, kuma ka ce, "salămă." Sa'an nan kuma ză su sani. 





© EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us