1st Ayah 1 الأية ١الأوليبِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
Ayah 44:2 الأية
وَالْكِتَابِ الْمُبِينِ
Walkitabi almubeen
Hausa
Ină rantsuwa da Littăfi Mabayyani.
|
Ayah 44:3 الأية
إِنَّا أَنزَلْنَاهُ فِي لَيْلَةٍ مُّبَارَكَةٍ ۚ إِنَّا كُنَّا مُنذِرِينَ
Inna anzalnahu fee laylatin mubarakatininna kunna munthireen
Hausa
Lalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ' Mun
kasance Măsu yin gargaɗi.
|
Ayah 44:4 الأية
فِيهَا يُفْرَقُ كُلُّ أَمْرٍ حَكِيمٍ
Feeha yufraqu kullu amrin hakeem
Hausa
A cikinsa (shi daren) ake rarrabe kőwane umurui bayyananne.
|
Ayah 44:5 الأية
أَمْرًا مِّنْ عِندِنَا ۚ إِنَّا كُنَّا مُرْسِلِينَ
Amran min AAindina inna kunnamursileen
Hausa
Umurni na daga wurinMu. Lalle Mũ ne Muka kasanceMăsu aikăwă.
|
Ayah 44:6 الأية
رَحْمَةً مِّن رَّبِّكَ ۚ إِنَّهُ هُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ
Rahmatan min rabbika innahu huwa assameeAAualAAaleem
Hausa
Sabőda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shĩ, Shi ne Mai ji, Măsani.
|
Ayah 44:7 الأية
رَبِّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا ۖ إِن كُنتُم مُّوقِنِينَ
Rabbi assamawati wal-ardiwama baynahuma in kuntum mooqineen
Hausa
(Shĩ ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakăninsu, idan kun kasance
măsu yaƙĩni (za ku găne haka).
|
Ayah 44:8 الأية
لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ يُحْيِي وَيُمِيتُ ۖ رَبُّكُمْ وَرَبُّ آبَائِكُمُ
الْأَوَّلِينَ
La ilaha illa huwa yuhyeewayumeetu rabbukum warabbu aba-ikumu al-awwaleen
Hausa
Babu abin bautăwa făce Shi. Yana răyarwa Kuma Yana kashẽwa. (Shi ne)
Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko.
|
Ayah 44:9 الأية
بَلْ هُمْ فِي شَكٍّ يَلْعَبُونَ
Bal hum fee shakkin yalAAaboon
Hausa
A'a sũ, sună wăsă a cikin shakka.
|
Ayah 44:10 الأية
فَارْتَقِبْ يَوْمَ تَأْتِي السَّمَاءُ بِدُخَانٍ مُّبِينٍ
Fartaqib yawma ta/tee assamaobidukhanin mubeen
Hausa
Sabőda haka, ka dakata rănar da sama ză tă zo da hayăƙi bayyananne.
|
Ayah 44:11 الأية
يَغْشَى النَّاسَ ۖ هَٰذَا عَذَابٌ أَلِيمٌ
Yaghsha annasa hathaAAathabun aleem
Hausa
Yană rufe mutăne. Wannan wata azăba ce mai raɗaɗi.
|
Ayah 44:12 الأية
رَّبَّنَا اكْشِفْ عَنَّا الْعَذَابَ إِنَّا مُؤْمِنُونَ
Rabbana ikshif AAanna alAAathabainna mu/minoon
Hausa
Ya Ubangijinmu! Ka kuranye mana azăba. Lalle Mũ, măsu ĩmăni ne.
|
Ayah 44:13 الأية
أَنَّىٰ لَهُمُ الذِّكْرَىٰ وَقَدْ جَاءَهُمْ رَسُولٌ مُّبِينٌ
Anna lahumu aththikrawaqad jaahum rasoolun mubeen
Hausa
Ină tunăwa take a gare su, alhăli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanăwa Ya je musu
(da gargaɗin saukar azăbar, ba su karɓa ba)?
|
Ayah 44:14 الأية
ثُمَّ تَوَلَّوْا عَنْهُ وَقَالُوا مُعَلَّمٌ مَّجْنُونٌ
Thumma tawallaw AAanhu waqaloomuAAallamun majnoon
Hausa
Sa'an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: "Wanda ake gayăwa ne,
mahaukaci."
|
Ayah 44:15 الأية
إِنَّا كَاشِفُو الْعَذَابِ قَلِيلًا ۚ إِنَّكُمْ عَائِدُونَ
Inna kashifoo alAAathabiqaleelan innakum AAa-idoon
Hausa
Lalle Mũ, Măsu kuranyẽwar azăba ne, a ɗan lőkaci kaɗan, lalle kũ, măsu kőmăwa ne
(ga laifin).
|
Ayah 44:16 الأية
يَوْمَ نَبْطِشُ الْبَطْشَةَ الْكُبْرَىٰ إِنَّا مُنتَقِمُونَ
Yawma nabtishu albatshataalkubra inna muntaqimoon
Hausa
Rănar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ măsu azăbar rămuwa ne.
|
Ayah 44:17 الأية
وَلَقَدْ فَتَنَّا قَبْلَهُمْ قَوْمَ فِرْعَوْنَ وَجَاءَهُمْ رَسُولٌ كَرِيمٌ
Walaqad fatanna qablahum qawmafirAAawna wajaahum rasoolun kareem
Hausa
Kuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutănen Fir'auna, kuma wani Manzo
karĩmi ya jẽ musu.
|
Ayah 44:18 الأية
أَنْ أَدُّوا إِلَيَّ عِبَادَ اللهِ ۖ إِنِّي لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ
An addoo ilayya AAibada Allahiinnee lakum rasoolun ameen
Hausa
(Mazon ya ce): "Ku kăwo mini (ĩmăninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne
amintacce zuwa gare ku."
|
Ayah 44:19 الأية
وَأَن لَّا تَعْلُوا عَلَى اللهِ ۖ إِنِّي آتِيكُم بِسُلْطَانٍ مُّبِينٍ
Waan la taAAloo AAala Allahiinnee ateekum bisultanin mubeen
Hausa
"Kuma kada ku nẽmi ɗaukaka a kan Allah. Lalle nĩ mai zo muku ne da dalĩli
bayyananne."
|
Ayah 44:20 الأية
وَإِنِّي عُذْتُ بِرَبِّي وَرَبِّكُمْ أَن تَرْجُمُونِ
Wa-innee AAuthtu birabbee warabbikuman tarjumoon
Hausa
"Kuma lalle nĩ na nẽmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dőmin kada ku jẽfe
ni."
|
Ayah 44:21 الأية
وَإِن لَّمْ تُؤْمِنُوا لِي فَاعْتَزِلُونِ
Wa-in lam tu/minoo lee faAAtaziloon
Hausa
"Kuma idan ba ku yi ĩmăni sabőda nĩ ba, to, ku nĩsance ni."
|
Ayah 44:22 الأية
فَدَعَا رَبَّهُ أَنَّ هَٰؤُلَاءِ قَوْمٌ مُّجْرِمُونَ
FadaAAa rabbahu anna haola-iqawmun mujrimoon
Hausa
Sai ya kirayi Ubangjinsa cẽwa waɗannan mutănene măsu laifi.
|
Ayah 44:23 الأية
فَأَسْرِ بِعِبَادِي لَيْلًا إِنَّكُم مُّتَّبَعُونَ
Faasri biAAibadee laylan innakummuttabaAAoon
Hausa
(Allah Ya ce): "To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle kũ, waɗanda ake
bĩ ne (dőmin a kăma ku.)"
|
Ayah 44:24 الأية
وَاتْرُكِ الْبَحْرَ رَهْوًا ۖ إِنَّهُمْ جُندٌ مُّغْرَقُونَ
Watruki albahra rahwaninnahum jundun mughraqoon
Hausa
"Kuma ka bar tẽku rarrabe. Lalle sũ, runduna ce abar nutsarwa."
|
Ayah 44:25 الأية
كَمْ تَرَكُوا مِن جَنَّاتٍ وَعُيُونٍ
Kam tarakoo min jannatin waAAuyoon
Hausa
Da yawa suka bar gőnaki da marẽmari.
|
Ayah 44:26 الأية
وَزُرُوعٍ وَمَقَامٍ كَرِيمٍ
WazurooAAin wamaqamin kareem
Hausa
Da shuke-shuke da matsayi mai kyau.
|
Ayah 44:27 الأية
وَنَعْمَةٍ كَانُوا فِيهَا فَاكِهِينَ
WanaAAmatin kanoo feeha fakiheen
Hausa
Da wata ni'ima da suka kasance a cikinta sună măsu hutu.
|
Ayah 44:28 الأية
كَذَٰلِكَ ۖ وَأَوْرَثْنَاهَا قَوْمًا آخَرِينَ
Kathalika waawrathnahaqawman akhareen
Hausa
Kamar haka! Kuma Muka gădar da ita ga waɗansu mutăne na dabam.
|
Ayah 44:29 الأية
فَمَا بَكَتْ عَلَيْهِمُ السَّمَاءُ وَالْأَرْضُ وَمَا كَانُوا مُنظَرِينَ
Fama bakat AAalayhimu assamaowal-ardu wama kanoo munthareen
Hausa
Sa'an nan samă da ƙasă ba su yi kũka a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake
yi wa jinkiri ba.
|
Ayah 44:30 الأية
وَلَقَدْ نَجَّيْنَا بَنِي إِسْرَائِيلَ مِنَ الْعَذَابِ الْمُهِينِ
Walaqad najjayna banee isra-eelamina alAAathabi almuheen
Hausa
Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun tsĩrar da Banĩ Isră'ĩla daga, azăba mai wulăkantăwa.
|
Ayah 44:31 الأية
مِن فِرْعَوْنَ ۚ إِنَّهُ كَانَ عَالِيًا مِّنَ الْمُسْرِفِينَ
Min firAAawna innahu kana AAaliyanmina almusrifeen
Hausa
Daga Fir'auna. Lalle shi, ya kasance maɗaukaki daga cikin măsu ɓarna.
|
Ayah 44:32 الأية
وَلَقَدِ اخْتَرْنَاهُمْ عَلَىٰ عِلْمٍ عَلَى الْعَالَمِينَ
Walaqadi ikhtarnahum AAalaAAilmin AAala alAAalameen
Hausa
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zăɓe su sabőda wani ilmi (na Taurata) a kan mutăne.
|
Ayah 44:33 الأية
وَآتَيْنَاهُم مِّنَ الْآيَاتِ مَا فِيهِ بَلَاءٌ مُّبِينٌ
Waataynahum mina al-ayatima feehi balaon mubeen
Hausa
Kuma Muka bă su, daga ăyőyin mu'ujizőji, abin da yake a cikinsa, akwai ni'ima
bayyananna
|
Ayah 44:34 الأية
إِنَّ هَٰؤُلَاءِ لَيَقُولُونَ
Inna haola-i layaqooloon
Hausa
Lalle waɗannan mutăne , haƙĩka, sună cẽwa,
|
Ayah 44:35 الأية
إِنْ هِيَ إِلَّا مَوْتَتُنَا الْأُولَىٰ وَمَا نَحْنُ بِمُنشَرِينَ
In hiya illa mawtatuna al-oolawama nahnu bimunshareen
Hausa
"Babu wani abu sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake tăyarwa ba."
|
Ayah 44:36 الأية
فَأْتُوا بِآبَائِنَا إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ
Fa/too bi-aba-ina inkuntum sadiqeen
Hausa
"Sai ku zo da ubanninmu, idan kun kasance măsu gaskiya."
|
Ayah 44:37 الأية
أَهُمْ خَيْرٌ أَمْ قَوْمُ تُبَّعٍ وَالَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۚ أَهْلَكْنَاهُمْ ۖ
إِنَّهُمْ كَانُوا مُجْرِمِينَ
Ahum khayrun am qawmu tubbaAAin wallatheenamin qablihim ahlaknahum innahum kanoo
mujrimeen
Hausa
shin, sũ ne mafĩfĩta kő kuwa mutănen Tubba'u, kuma da waɗanda ke a gabăninsu?
Mun halaka su, lalle sũ, sun kasance măsu laifi.
|
Ayah 44:38 الأية
وَمَا خَلَقْنَا السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا لَاعِبِينَ
Wama khalaqna assamawatiwal-arda wama baynahuma laAAibeen
Hausa
Kuma ba Mu halitta slmmai da ƙasa da abin da ke a tsakăninsu ba, alhăli kuwa
Mună măsu wăsă.
|
Ayah 44:39 الأية
مَا خَلَقْنَاهُمَا إِلَّا بِالْحَقِّ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ
Ma khalaqnahuma illabilhaqqi walakinna aktharahum layaAAlamoon
Hausa
Ba Mu halitta su ba făce da manufa ta gaskiya, kuma amma mafi yawansu, ba su
sani ba.
|
Ayah 44:40 الأية
إِنَّ يَوْمَ الْفَصْلِ مِيقَاتُهُمْ أَجْمَعِينَ
Inna yawma alfasli meeqatuhumajmaAAeen
Hausa
Lalle rănar rarrabẽwa, ita ce lőkacin wa'adinsu gabă ɗaya.
|
Ayah 44:41 الأية
يَوْمَ لَا يُغْنِي مَوْلًى عَن مَّوْلًى شَيْئًا وَلَا هُمْ يُنصَرُونَ
Yawma la yughnee mawlan AAan mawlanshay-an wala hum yunsaroon
Hausa
Rănar da wani zumu bă ya amfănin wani zumu da kőme kuma ba su zama ană taimakon
su ba.
|
Ayah 44:42 الأية
إِلَّا مَن رَّحِمَ اللهُ ۚ إِنَّهُ هُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ
Illa man rahima Allahuinnahu huwa alAAazeezu arraheem
Hausa
făce wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi (Allah), shĩ ne Mabuwăyi, Mai jin
ƙai.
|
Ayah 44:43 الأية
إِنَّ شَجَرَتَ الزَّقُّومِ
Inna shajarata azzaqqoom
Hausa
Lalle ităciyar zaƙƙũm (ɗanyen wută),
|
Ayah 44:44 الأية
طَعَامُ الْأَثِيمِ
TaAAamu al-atheem
Hausa
Ita ce abincin mai laifi.
|
Ayah 44:45 الأية
كَالْمُهْلِ يَغْلِي فِي الْبُطُونِ
Kalmuhli yaghlee fee albutoon
Hausa
Kamar narkakken kwalta yană tafasa a cikin cikunna.
|
Ayah 44:46 الأية
كَغَلْيِ الْحَمِيمِ
Kaghalyi alhameem
Hausa
Kamar tafasar ruwan zăfi.
|
Ayah 44:47 الأية
خُذُوهُ فَاعْتِلُوهُ إِلَىٰ سَوَاءِ الْجَحِيمِ
Khuthoohu faAAtiloohu ilasawa-i aljaheem
Hausa
(A cẽ wa mală'ikun wută), "Ku kămă shi, sa'an nan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar
Jahĩm."
|
Ayah 44:48 الأية
ثُمَّ صُبُّوا فَوْقَ رَأْسِهِ مِنْ عَذَابِ الْحَمِيمِ
Thumma subboo fawqa ra/sihi min AAathabialhameem
Hausa
"Sa'an nan ku zuba, a kansa, daga azăbar ruwan zăfi."
|
Ayah 44:49 الأية
ذُقْ إِنَّكَ أَنتَ الْعَزِيزُ الْكَرِيمُ
Thuq innaka anta alAAazeezu alkareem
Hausa
(A ce masă), "Ka ɗanɗana! Lalle kai, kai ne mabuwăyi mai girma!"
|
Ayah 44:50 الأية
إِنَّ هَٰذَا مَا كُنتُم بِهِ تَمْتَرُونَ
Inna hatha ma kuntum bihitamtaroon
Hausa
"Lalle wannan, shi ne abin da kuka kasance kună shakka game da shi."
|
Ayah 44:51 الأية
إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي مَقَامٍ أَمِينٍ
Inna almuttaqeena fee maqamin ameen
Hausa
Lalle măsu taƙawa sună cikin matsayi amintacce.
|
Ayah 44:52 الأية
فِي جَنَّاتٍ وَعُيُونٍ
Fee jannatin waAAuyoon
Hausa
A cikin gidăjen Aljanna da marẽmari.
|
Ayah 44:53 الأية
يَلْبَسُونَ مِن سُندُسٍ وَإِسْتَبْرَقٍ مُّتَقَابِلِينَ
Yalbasoona min sundusin wa-istabraqin mutaqabileen
Hausa
Sună tufanta daga tufăfin alharĩni raƙĩƙi, da mai kauri, sună măsu zaman
fuskantar jũna.
|
Ayah 44:54 الأية
كَذَٰلِكَ وَزَوَّجْنَاهُم بِحُورٍ عِينٍ
Kathalika wazawwajnahum bihoorinAAeen
Hausa
Kamar haka, kuma Mun aurar da su da mătă măsu kyaun idănu, măsu girmansu.
|
Ayah 44:55 الأية
يَدْعُونَ فِيهَا بِكُلِّ فَاكِهَةٍ آمِنِينَ
YadAAoona feeha bikulli fakihatinamineen
Hausa
Sună kira, a cikinsu (gidẽjen) ga dukan 'ya'yan ităcen marmari, sună amintattu
(daga dukan abin tsőro).
|
Ayah 44:56 الأية
لَا يَذُوقُونَ فِيهَا الْمَوْتَ إِلَّا الْمَوْتَةَ الْأُولَىٰ ۖ وَوَقَاهُمْ
عَذَابَ الْجَحِيمِ
La yathooqoona feehaalmawta illa almawtata al-oola wawaqahum AAathabaaljaheem
Hausa
Bă su ɗanɗanar mutuwa, a cikinsu, făce mutuwar farko, kuma (Allah), Ya tsare
musu azăbar Jahĩm.
|
Ayah 44:57 الأية
فَضْلًا مِّن رَّبِّكَ ۚ ذَٰلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ
Fadlan min rabbika thalikahuwa alfawzu alAAatheem
Hausa
Sabőda falala daga Ubangijinka. Wancan shi ne babban rabo, mai girma.
|
Ayah 44:58 الأية
فَإِنَّمَا يَسَّرْنَاهُ بِلِسَانِكَ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ
Fa-innama yassarnahu bilisanikalaAAallahum yatathakkaroon
Hausa
Dőmin haka kawai Muka sauƙaƙar da shi (Alƙur'ăni) da harshenka, tsammăninsu, su
riƙa tunăwa.
|
Ayah 44:59 الأية
فَارْتَقِبْ إِنَّهُم مُّرْتَقِبُونَ
Fartaqib innahum murtaqiboon
Hausa
Sai ka yi jira. Lalle sũ, măsu jira ne.
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|