1st Ayah 1 الأية ١الأوليبِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
ق ۚ وَالْقُرْآنِ الْمَجِيدِ
Qaf walqur-ani almajeed
Hausa
¡̃ . Inã rantsuwa da Alƙur'ãni Mai girma.
|
Ayah 50:2 الأية
بَلْ عَجِبُوا أَن جَاءَهُم مُّنذِرٌ مِّنْهُمْ فَقَالَ الْكَافِرُونَ هَٰذَا
شَيْءٌ عَجِيبٌ
Bal AAajiboo an jaahum munthirunminhum faqala alkafiroona hatha shay-onAAajeeb
Hausa
Ã'a, sun yi mãmãki, cewa mai gargaɗi, daga gare su, yã zo musu, sai kãfirai suka
ce: "Wannan wani abu ne mai ban mãmãki."
|
Ayah 50:3 الأية
أَإِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا ۖ ذَٰلِكَ رَجْعٌ بَعِيدٌ
A-itha mitna wakunna turabanthalika rajAAun baAAeed
Hausa
"Shin idan muka mutu kuma muka kasance turɓãya (zã a kõmo da mu)? Waccan kõmowa
ce mai nĩsa."
|
Ayah 50:4 الأية
قَدْ عَلِمْنَا مَا تَنقُصُ الْأَرْضُ مِنْهُمْ ۖ وَعِندَنَا كِتَابٌ حَفِيظٌ
Qad AAalimna ma tanqusual-ardu minhum waAAindana kitabun hafeeth
Hausa
Lalle ne Mun san abin da ƙasã ke ragẽwo daga gare su, kuma wurinMu akwai wani
littãfi mai tsarẽwa.
|
Ayah 50:5 الأية
بَلْ كَذَّبُوا بِالْحَقِّ لَمَّا جَاءَهُمْ فَهُمْ فِي أَمْرٍ مَّرِيجٍ
Bal kaththaboo bilhaqqilamma jaahum fahum fee amrin mareej
Hausa
Ã'a, sun ƙaryata ne game da gaskiyar a lõkacin da ta je musu, sabõda haka sunã a
cikin wani al'amari mai raurawa.
|
Ayah 50:6 الأية
أَفَلَمْ يَنظُرُوا إِلَى السَّمَاءِ فَوْقَهُمْ كَيْفَ بَنَيْنَاهَا
وَزَيَّنَّاهَا وَمَا لَهَا مِن فُرُوجٍ
Afalam yanthuroo ila assama-ifawqahum kayfa banaynaha wazayyannahawama laha min
furooj
Hausa
Shin, to, ba su yi dubi ba zuwa ga samã a bisa gare su, yadda Muka gĩna ta, kuma
Muka ƙawãce ta, kuma bã ta da waɗansu tsãgogi?
|
Ayah 50:7 الأية
وَالْأَرْضَ مَدَدْنَاهَا وَأَلْقَيْنَا فِيهَا رَوَاسِيَ وَأَنبَتْنَا فِيهَا مِن
كُلِّ زَوْجٍ بَهِيجٍ
Wal-arda madadnahawaalqayna feeha rawasiya waanbatnafeeha min kulli zawjin
baheej
Hausa
Da ƙasã, Mun mĩƙe ta, kuma Mun jẽfa kafaffun duwãtsu a cikinta, kuma Mun tsirar,
a cikinta daga kõwane ma'auri mai ban sha'awa?
|
Ayah 50:8 الأية
تَبْصِرَةً وَذِكْرَىٰ لِكُلِّ عَبْدٍ مُّنِيبٍ
Tabsiratan wathikralikulli AAabdin muneeb
Hausa
Dõmin wãyar da ido da tunãtarwa ga dukan bãwa mai tawakkali?
|
Ayah 50:9 الأية
وَنَزَّلْنَا مِنَ السَّمَاءِ مَاءً مُّبَارَكًا فَأَنبَتْنَا بِهِ جَنَّاتٍ
وَحَبَّ الْحَصِيدِ
Wanazzalna mina assama-imaan mubarakan faanbatna bihi jannatinwahabba alhaseed
Hausa
Kuma Mun sassakar, daga samã ruwa mai albarka sa'an nan Muka tsirar game da shi
(itãcen) lambuna da ƙwãya abin girbẽwa.
|
Ayah 50:10 الأية
وَالنَّخْلَ بَاسِقَاتٍ لَّهَا طَلْعٌ نَّضِيدٌ
Wannakhla basiqatinlaha talAAun nadeed
Hausa
Da itãcen dabĩno dõgãye, sunã da'ya'yan itãce gunda mãsu hauhawar jũna.
|
Ayah 50:11 الأية
رِّزْقًا لِّلْعِبَادِ ۖ وَأَحْيَيْنَا بِهِ بَلْدَةً مَّيْتًا ۚ كَذَٰلِكَ
الْخُرُوجُ
Rizqan lilAAibadi waahyaynabihi baldatan maytan kathalika alkhurooj
Hausa
Dõmin arziki ga bãyi, kuma Muka rãyar da ƙasa matacciya game da shi. Kamar
wannan ne fitar daga kabari kake.
|
Ayah 50:12 الأية
كَذَّبَتْ قَبْلَهُمْ قَوْمُ نُوحٍ وَأَصْحَابُ الرَّسِّ وَثَمُودُ
Kaththabat qablahum qawmu noohinwaas-habu arrassi wathamood
Hausa
Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu (mutãnen yanzu) da ma'abũta Rassi, da
Samũdãwa.
|
Ayah 50:13 الأية
وَعَادٌ وَفِرْعَوْنُ وَإِخْوَانُ لُوطٍ
WaAAadun wafirAAawnu wa-ikhwanuloot
Hausa
Da Ãdãwa da Fir'auna da 'yan'uwan Lũɗu.
|
Ayah 50:14 الأية
وَأَصْحَابُ الْأَيْكَةِ وَقَوْمُ تُبَّعٍ ۚ كُلٌّ كَذَّبَ الرُّسُلَ فَحَقَّ
وَعِيدِ
Waas-habu al-aykati waqawmutubbaAAin kullun kaththaba arrusula fahaqqawaAAeed
Hausa
Da ma'abũta ƙunci da mutãnen Tubba'u, kõwanensu ya ƙaryata Manzanni, sai
ƙyacẽwaTa ta tabbata.
|
Ayah 50:15 الأية
أَفَعَيِينَا بِالْخَلْقِ الْأَوَّلِ ۚ بَلْ هُمْ فِي لَبْسٍ مِّنْ خَلْقٍ جَدِيدٍ
AfaAAayeena bilkhalqial-awwali bal hum fee labsin min khalqin jadeed
Hausa
Shin, to, Mun kãsa ne game da halittar farko? Ã'a, su sunã a cikin rikici daga
halitta sãbuwa.
|
Ayah 50:16 الأية
وَلَقَدْ خَلَقْنَا الْإِنسَانَ وَنَعْلَمُ مَا تُوَسْوِسُ بِهِ نَفْسُهُ ۖ
وَنَحْنُ أَقْرَبُ إِلَيْهِ مِنْ حَبْلِ الْوَرِيدِ
Walaqad khalaqna al-insanawanaAAlamu ma tuwaswisu bihi nafsuhu wanahnu
aqrabuilayhi min habli alwareed
Hausa
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta mutum kuma Mun san abin da ransa ke yin waswãsi
da shi, kuma Mũ ne mafi kusanta zuwa gare shi daga lakar jannayẽnsa.
|
Ayah 50:17 الأية
إِذْ يَتَلَقَّى الْمُتَلَقِّيَانِ عَنِ الْيَمِينِ وَعَنِ الشِّمَالِ قَعِيدٌ
Ith yatalaqqa almutalaqqiyaniAAani alyameeni waAAani ashshimali qaAAeed
Hausa
A lõkacin da mãsu haɗuwa biyu suke haɗuwa daga dãma, kuma daga hagu akwai wani
(malã'ika) zaunanne.
|
Ayah 50:18 الأية
مَّا يَلْفِظُ مِن قَوْلٍ إِلَّا لَدَيْهِ رَقِيبٌ عَتِيدٌ
Ma yalfithu min qawlinilla ladayhi raqeebun AAateed
Hausa
Bã ya lafazi da wata magana fãce a lĩƙe da shi akwai mai tsaro halartacce.
|
Ayah 50:19 الأية
وَجَاءَتْ سَكْرَةُ الْمَوْتِ بِالْحَقِّ ۖ ذَٰلِكَ مَا كُنتَ مِنْهُ تَحِيدُ
Wajaat sakratu almawti bilhaqqithalika ma kunta minhu taheed
Hausa
Kuma mãyen mutuwa ya jẽ da gaskiya. Wannan shĩ ne abin da ka kasance daga gare
shi kanã bijirẽwa.
|
Ayah 50:20 الأية
وَنُفِخَ فِي الصُّورِ ۚ ذَٰلِكَ يَوْمُ الْوَعِيدِ
Wanufikha fee assoori thalikayawmu alwaAAeed
Hausa
Kuma aka hũra a cikin ƙaho. Wancan yinin ƙyacẽwar ne fa.
|
Ayah 50:21 الأية
وَجَاءَتْ كُلُّ نَفْسٍ مَّعَهَا سَائِقٌ وَشَهِيدٌ
Wajaat kullu nafsin maAAaha sa-iqunwashaheed
Hausa
Kuma kõwane rai ya zo, tãre da shi akwai mai kõra da mai shaida.
|
Ayah 50:22 الأية
لَّقَدْ كُنتَ فِي غَفْلَةٍ مِّنْ هَٰذَا فَكَشَفْنَا عَنكَ غِطَاءَكَ فَبَصَرُكَ
الْيَوْمَ حَدِيدٌ
Laqad kunta fee ghaflatin min hathafakashafna AAanka ghitaaka fabasarukaalyawma
hadeed
Hausa
(Sai a ce masa): "Lalle ne, haƙĩƙa, ka kasance a cikin gafala daga wannan. To,
Mun kuranye maka rufinka, sabõda haka ganinka a yau, mai kaifi ne."
|
Ayah 50:23 الأية
وَقَالَ قَرِينُهُ هَٰذَا مَا لَدَيَّ عَتِيدٌ
Waqala qareenuhu hatha maladayya AAateed
Hausa
Kuma abõkin haɗinsa ya ce: "Wannan shi ne abin da ke tãre da ni halarce."
|
Ayah 50:24 الأية
أَلْقِيَا فِي جَهَنَّمَ كُلَّ كَفَّارٍ عَنِيدٍ
Alqiya fee jahannama kulla kaffarinAAaneed
Hausa
(A ce wa Malã'iku), "Ku jẽfa, a cikin Jahannama, dukan mai yawan kãfirci, mai
tsaurin rai."
|
Ayah 50:25 الأية
مَّنَّاعٍ لِّلْخَيْرِ مُعْتَدٍ مُّرِيبٍ
MannaAAin lilkhayri muAAtadin mureeb
Hausa
"Mai yawan hanãwa ga alhẽri, mai zãlunci, mai shakka."
|
Ayah 50:26 الأية
الَّذِي جَعَلَ مَعَ اللهِ إِلَٰهًا آخَرَ فَأَلْقِيَاهُ فِي الْعَذَابِ
الشَّدِيدِ
Allathee jaAAala maAAa Allahiilahan akhara faalqiyahu fee alAAathabiashshadeed
Hausa
"Wanda ya sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, sabõda haka kujẽfa
shi a cikin azãba mai tsanani."
|
Ayah 50:27 الأية
قَالَ قَرِينُهُ رَبَّنَا مَا أَطْغَيْتُهُ وَلَٰكِن كَانَ فِي ضَلَالٍ بَعِيدٍ
Qala qareenuhu rabbana maatghaytuhu walakin kana fee dalalinbaAAeed
Hausa
Abõkin haɗinsa ya ce: "Ya Ubangijinmu! Ban sanya shi girman kai ba, kuma amma ya
kasance a cikin ɓata mai nĩsa."
|
Ayah 50:28 الأية
قَالَ لَا تَخْتَصِمُوا لَدَيَّ وَقَدْ قَدَّمْتُ إِلَيْكُم بِالْوَعِيدِ
Qala la takhtasimooladayya waqad qaddamtu ilaykum bilwaAAeed
Hausa
Ya ce: "Kada ku yi husũma a wuriNa, alhãli Na gabãtar da ƙyacewa zuwa gare ku."
|
Ayah 50:29 الأية
مَا يُبَدَّلُ الْقَوْلُ لَدَيَّ وَمَا أَنَا بِظَلَّامٍ لِّلْعَبِيدِ
Ma yubaddalu alqawlu ladayya wamaana bithallamin lilAAabeed
Hausa
"Ba a musanya magana a wuriNa, Kuma Ban zama Mai zãlunci ba ga bãyiNa."
|
Ayah 50:30 الأية
يَوْمَ نَقُولُ لِجَهَنَّمَ هَلِ امْتَلَأْتِ وَتَقُولُ هَلْ مِن مَّزِيدٍ
Yawma naqoolu lijahannama hali imtala/tiwataqoolu hal min mazeed
Hausa
Rãnar da Muke cẽwa ga Jahannama "Shin, kin cika?" Kuma ta ce: "Ashe, akwai wani
ƙãri?"
|
Ayah 50:31 الأية
وَأُزْلِفَتِ الْجَنَّةُ لِلْمُتَّقِينَ غَيْرَ بَعِيدٍ
Waozlifati aljannatu lilmuttaqeena ghayrabaAAeed
Hausa
Kuma a kusantar dã Aljanna ga mãsu taƙawa, ba da nĩsa ba.
|
Ayah 50:32 الأية
هَٰذَا مَا تُوعَدُونَ لِكُلِّ أَوَّابٍ حَفِيظٍ
Hatha ma tooAAadoona likulliawwabin hafeeth
Hausa
"Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi da shi ga dukan mai yawan kõmawa ga
Allah, mai tsarewar (umurninSa).
|
Ayah 50:33 الأية
مَّنْ خَشِيَ الرَّحْمَٰنَ بِالْغَيْبِ وَجَاءَ بِقَلْبٍ مُّنِيبٍ
Man khashiya arrahmanabilghaybi wajaa biqalbin muneeb
Hausa
"Wanda ya ji tsõron Mai rahama a fake, kuma ya zo da wata irin zũciya mai
tawakkali."
|
Ayah 50:34 الأية
ادْخُلُوهَا بِسَلَامٍ ۖ ذَٰلِكَ يَوْمُ الْخُلُودِ
Odkhulooha bisalamin thalikayawmu alkhulood
Hausa
(A ce musu) "Ku shige ta da aminci, waccan ita ce rãnar dawwama."
|
Ayah 50:35 الأية
لَهُم مَّا يَشَاءُونَ فِيهَا وَلَدَيْنَا مَزِيدٌ
Lahum ma yashaoona feehawaladayna mazeed
Hausa
Sunã da abin da suke so a cikinta, kuma tãre da Mũ akwai ƙãrin ni'ima,
|
Ayah 50:36 الأية
وَكَمْ أَهْلَكْنَا قَبْلَهُم مِّن قَرْنٍ هُمْ أَشَدُّ مِنْهُم بَطْشًا
فَنَقَّبُوا فِي الْبِلَادِ هَلْ مِن مَّحِيصٍ
Wakam ahlakna qablahum min qarnin humashaddu minhum batshan fanaqqaboo fee
albiladi halmin mahees
Hausa
Kuma da yawa Muka halakar, a gabãninsu, (mutãnen yanzu) ɗaga waɗansu al'ummomi,
(waɗanda suke) sũ ne mafi ƙarfin damƙa daga gare su, sa'an nan suka yi bincike a
cikin ƙasãshe: 'Kõ akwai wurin tsĩra'? ( Babu).
|
Ayah 50:37 الأية
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَذِكْرَىٰ لِمَن كَانَ لَهُ قَلْبٌ أَوْ أَلْقَى السَّمْعَ
وَهُوَ شَهِيدٌ
Inna fee thalika lathikraliman kana lahu qalbun aw alqa assamAAawahuwa shaheed
Hausa
Lalle ne, a cikin wancan, akwai tunãtarwa ga wanda zũciyarsa ta kasance gare
shi, kõ kuwa ya jẽfa saurãro, alhãli kuwa yanã halarce (da hankalinsa).
|
Ayah 50:38 الأية
وَلَقَدْ خَلَقْنَا السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا فِي سِتَّةِ
أَيَّامٍ وَمَا مَسَّنَا مِن لُّغُوبٍ
Walaqad khalaqna assamawatiwal-arda wama baynahuma fee sittatiayyamin wama
massana min lughoob
Hausa
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu, a
cikin kwãnaki shida, alhãli wata'yar wahala ba ta shãfe Mu ba.
|
Ayah 50:39 الأية
فَاصْبِرْ عَلَىٰ مَا يَقُولُونَ وَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ قَبْلَ طُلُوعِ
الشَّمْسِ وَقَبْلَ الْغُرُوبِ
Fasbir AAala mayaqooloona wasabbih bihamdi rabbika qabla tulooAAiashshamsi
waqabla alghuroob
Hausa
Sabõda haka, ka yi haƙuri a kan abin da suke fadã, kuma ka yi tasĩhi game da
gõdẽ wa Ubangijinka (watau ka yi salla) a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin
ɓacẽwarta.
|
Ayah 50:40 الأية
وَمِنَ اللَّيْلِ فَسَبِّحْهُ وَأَدْبَارَ السُّجُودِ
Wamina allayli fasabbihhu waadbaraassujood
Hausa
Kuma daga dare, sai ka yi tasbĩhi a gare Shi da bãyan sujada.
|
Ayah 50:41 الأية
وَاسْتَمِعْ يَوْمَ يُنَادِ الْمُنَادِ مِن مَّكَانٍ قَرِيبٍ
WastamiAA yawma yunadi almunadimin makanin qareeb
Hausa
Kuma ka saurãra a rãnar da mai kira ke yin kira daga wuri makusanci.
|
Ayah 50:42 الأية
يَوْمَ يَسْمَعُونَ الصَّيْحَةَ بِالْحَقِّ ۚ ذَٰلِكَ يَوْمُ الْخُرُوجِ
Yawma yasmaAAoona assayhatabilhaqqi thalika yawmu alkhurooj
Hausa
Rãnar da suke saurãron tsãwa da gaskiya. Wancan shĩ ne yinin fita (daga kabari).
|
Ayah 50:43 الأية
إِنَّا نَحْنُ نُحْيِي وَنُمِيتُ وَإِلَيْنَا الْمَصِيرُ
Inna nahnu nuhyeewanumeetu wa-ilayna almaseer
Hausa
Lalle Mũ ne haƙĩƙa, Mu ne ke rãyarwa, kuma Mũ ne ke kashẽwa, kuma zuwa gare Mu
kawai ne makõmar take.
|
Ayah 50:44 الأية
يَوْمَ تَشَقَّقُ الْأَرْضُ عَنْهُمْ سِرَاعًا ۚ ذَٰلِكَ حَشْرٌ عَلَيْنَا يَسِيرٌ
Yawma tashaqqaqu al-ardu AAanhum siraAAanthalika hashrun AAalayna yaseer
Hausa
Rãnar da ƙasã ke tsattsãgẽwa daga gare su, sunã mãsu gaggãwa. Wancan tãrãwar
mutãne ne, mai sauƙi a gare Mu.
|
Ayah 50:45 الأية
نَّحْنُ أَعْلَمُ بِمَا يَقُولُونَ ۖ وَمَا أَنتَ عَلَيْهِم بِجَبَّارٍ ۖ فَذَكِّرْ
بِالْقُرْآنِ مَن يَخَافُ وَعِيدِ
Nahnu aAAlamu bima yaqooloonawama anta AAalayhim bijabbarin fathakkir
bilqur-animan yakhafu waAAeed
Hausa
Mũ ne mafi sani game da abin da suke faɗi, kuma bã zã ka zama mai tĩlasta su ba.
Sabõda haka ka tunatar game da Alƙur'ani, ga wanda ke tsõron ƙyacewaTa.
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|