1st Ayah 1 الأية ١الأوليبِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
اقْتَرَبَتِ السَّاعَةُ وَانشَقَّ الْقَمَرُ
Iqtarabati assaAAatu wanshaqqaalqamar
Hausa
Sã'a ta yi kusa, kuma wata ya tsãge.
|
Ayah 54:2 الأية
وَإِن يَرَوْا آيَةً يُعْرِضُوا وَيَقُولُوا سِحْرٌ مُّسْتَمِرٌّ
Wa-in yaraw ayatan yuAAridoowayaqooloo sihrun mustamirr
Hausa
Kuma idan sun ga wata ãyã, sai su juya baya su ce: "Sihiri ne mai dõgẽwa!"
|
Ayah 54:3 الأية
وَكَذَّبُوا وَاتَّبَعُوا أَهْوَاءَهُمْ ۚ وَكُلُّ أَمْرٍ مُّسْتَقِرٌّ
Wakaththaboo wattabaAAoo ahwaahumwakullu amrin mustaqirr
Hausa
Kuma suka ƙaryata, kuma suka bi son zũciyarsu, alhãli kuwa kõwane al'amari
(wanda suke son su tũre daga Annabi) an tabbatar da shi.
|
Ayah 54:4 الأية
وَلَقَدْ جَاءَهُم مِّنَ الْأَنبَاءِ مَا فِيهِ مُزْدَجَرٌ
Walaqad jaahum mina al-anba-i mafeehi muzdajar
Hausa
Kuma lalle, abin da yake akwai tsãwatarwa a cikinsa na lãbãraiya zo musu.
|
Ayah 54:5 الأية
حِكْمَةٌ بَالِغَةٌ ۖ فَمَا تُغْنِ النُّذُرُ
Hikmatun balighatun famatughnee annuthur
Hausa
Hikima cikakka! Sai dai abũbuwan gargaɗi bã su amfãni.
|
Ayah 54:6 الأية
فَتَوَلَّ عَنْهُمْ ۘ يَوْمَ يَدْعُ الدَّاعِ إِلَىٰ شَيْءٍ نُّكُرٍ
Fatawalla AAanhum yawma yadAAu addaAAiila shay-in nukur
Hausa
Sabõda haka, ka bar su! Rãnar da mai kiran zai yi kira zuwa ga wani abu abin
ƙyama.
|
Ayah 54:7 الأية
خُشَّعًا أَبْصَارُهُمْ يَخْرُجُونَ مِنَ الْأَجْدَاثِ كَأَنَّهُمْ جَرَادٌ
مُّنتَشِرٌ
KhushshaAAan absaruhum yakhrujoonamina al-ajdathi kaannahum jaradun muntashir
Hausa
¡asƙantattu ga idanunsu zã su fito daga kaburburansu, kamar dai sũ fãri ne
waɗandasuka wãtse.
|
Ayah 54:8 الأية
مُّهْطِعِينَ إِلَى الدَّاعِ ۖ يَقُولُ الْكَافِرُونَ هَٰذَا يَوْمٌ عَسِرٌ
MuhtiAAeena ila addaAAiyaqoolu alkafiroona hatha yawmun AAasir
Hausa
Sunã gaggãwar tafiya zuwa ga mai kiran, kãfirai na cẽwa, "Wannan yini ne mai
wuya!"
|
Ayah 54:9 الأية
كَذَّبَتْ قَبْلَهُمْ قَوْمُ نُوحٍ فَكَذَّبُوا عَبْدَنَا وَقَالُوا مَجْنُونٌ
وَازْدُجِرَ
Kaththabat qablahum qawmu noohinfakaththaboo AAabdana waqaloo majnoonun wazdujir
Hausa
Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, sai suka ƙaryata BawanMu, kuma suka ce:
"Shi mahaukaci ne." Kuma aka tsãwace shi.
|
Ayah 54:10 الأية
فَدَعَا رَبَّهُ أَنِّي مَغْلُوبٌ فَانتَصِرْ
FadaAAa rabbahu annee maghloobun fantasir
Hausa
Sabõda haka, ya kira Ubangijinsa (ya ce), "Lalle nĩ, an rinjãye ni, sai Ka yi
taimako."
|
Ayah 54:11 الأية
فَفَتَحْنَا أَبْوَابَ السَّمَاءِ بِمَاءٍ مُّنْهَمِرٍ
Fafatahna abwaba assama-ibima-in munhamir
Hausa
Sai Muka bũɗe kõfõfin sama da ruwa mai zuba.
|
Ayah 54:12 الأية
وَفَجَّرْنَا الْأَرْضَ عُيُونًا فَالْتَقَى الْمَاءُ عَلَىٰ أَمْرٍ قَدْ قُدِرَ
Wafajjarna al-arda AAuyoonanfaltaqa almao AAala amrin qad qudir
Hausa
Kuma Muka ɓuɓɓugar da ƙasã ta zama idãnun ruwa, daɗa ruwa ya haɗu a kan wani
umurni da aka riga aka ƙaddara shi.
|
Ayah 54:13 الأية
وَحَمَلْنَاهُ عَلَىٰ ذَاتِ أَلْوَاحٍ وَدُسُرٍ
Wahamalnahu AAala thatialwahin wadusur
Hausa
Kuma Muka ɗauke Nũhu a kan (jirgi) na alluna da ƙũsõshi.
|
Ayah 54:14 الأية
تَجْرِي بِأَعْيُنِنَا جَزَاءً لِّمَن كَانَ كُفِرَ
Tajree bi-aAAyunina jazaanliman kana kufir
Hausa
Tanã gudãna, a kan idãnunMu, dõmin sakamako ga wanda aka yi wa kãfircin.
|
Ayah 54:15 الأية
وَلَقَد تَّرَكْنَاهَا آيَةً فَهَلْ مِن مُّدَّكِرٍ
Walaqad taraknaha ayatanfahal min muddakir
Hausa
Kuma lalle, Mun bar ta ta zama ãyã. To, Shin, akwai mai tunãni
|
Ayah 54:16 الأية
فَكَيْفَ كَانَ عَذَابِي وَنُذُرِ
Fakayfa kana AAathabee wanuthur
Hausa
To, yãyã azãbãTa take da gargaɗiNa?
|
Ayah 54:17 الأية
وَلَقَدْ يَسَّرْنَا الْقُرْآنَ لِلذِّكْرِ فَهَلْ مِن مُّدَّكِرٍ
Walaqad yassarna alqur-ana liththikrifahal min muddakir
Hausa
Kuma lalle ne, haƙĩkƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ãni, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai
tunãwa?
|
Ayah 54:18 الأية
كَذَّبَتْ عَادٌ فَكَيْفَ كَانَ عَذَابِي وَنُذُرِ
Kaththabat AAadun fakayfa kanaAAathabee wanuthur
Hausa
Ãdãwa sun ƙaryata, to, yãya azãbãTa take, da gargaɗiNa?
|
Ayah 54:19 الأية
إِنَّا أَرْسَلْنَا عَلَيْهِمْ رِيحًا صَرْصَرًا فِي يَوْمِ نَحْسٍ مُّسْتَمِرٍّ
Inna arsalna AAalayhim reehansarsaran fee yawmi nahsin mustamirr
Hausa
Lalle Mũ, Mun aika da iska mai tsananin sauti a kansu, a cikin wani yinin nahĩsa
mai dõgẽwa.
|
Ayah 54:20 الأية
تَنزِعُ النَّاسَ كَأَنَّهُمْ أَعْجَازُ نَخْلٍ مُّنقَعِرٍ
TanziAAu annasa kaannahumaAAjazu nakhlin munqaAAir
Hausa
Tanã fizgar mutãne kamar dai sũ kututturan dabĩno tumɓukakku ne.
|
Ayah 54:21 الأية
فَكَيْفَ كَانَ عَذَابِي وَنُذُرِ
Fakayfa kana AAathabee wanuthur
Hausa
To, yãya azãbãTa take da gargaɗiNa?
|
Ayah 54:22 الأية
وَلَقَدْ يَسَّرْنَا الْقُرْآنَ لِلذِّكْرِ فَهَلْ مِن مُّدَّكِرٍ
Walaqad yassarna alqur-ana liththikrifahal min muddakir
Hausa
Kuma lalle ne, haƙiƙa Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai
tunãwa?
|
Ayah 54:23 الأية
كَذَّبَتْ ثَمُودُ بِالنُّذُرِ
Kaththabat thamoodu binnuthur
Hausa
Samũdãwa sun ƙaryata game da gargaɗin.
|
Ayah 54:24 الأية
فَقَالُوا أَبَشَرًا مِّنَّا وَاحِدًا نَّتَّبِعُهُ إِنَّا إِذًا لَّفِي ضَلَالٍ
وَسُعُرٍ
Faqaloo abasharan minna wahidannattabiAAuhu inna ithan lafee dalalinwasuAAur
Hausa
Sai suka ce: "Wani mutum daga cikinmu, shi kaɗai, wai mu bĩ shi! Lalle mũ a
lõkacin, haƙĩƙa mun shiga wata ɓata da haukã.
|
Ayah 54:25 الأية
أَأُلْقِيَ الذِّكْرُ عَلَيْهِ مِن بَيْنِنَا بَلْ هُوَ كَذَّابٌ أَشِرٌ
Aolqiya aththikru AAalayhimin baynina bal huwa kaththabun ashir
Hausa
"Shin, an jẽfa masa Manzancin ne, a tsakãninmu? Ã'a, shĩ dai gawurtaccen
maƙaryaci ne mai girman kai!"
|
Ayah 54:26 الأية
سَيَعْلَمُونَ غَدًا مَّنِ الْكَذَّابُ الْأَشِرُ
SayaAAlamoona ghadan mani alkaththabual-ashir
Hausa
Zã su sani a gõbe, wãne ne gawurtaccen mai ƙaryar, mai girman kan?
|
Ayah 54:27 الأية
إِنَّا مُرْسِلُو النَّاقَةِ فِتْنَةً لَّهُمْ فَارْتَقِبْهُمْ وَاصْطَبِرْ
Inna mursiloo annaqatifitnatan lahum fartaqibhum wastabir
Hausa
Lalle Mũ, mãsu aikãwa da rãƙumar ne, ta zame musu fitina, sai ka tsare su da
kallo, kuma ka yi haƙuri.
|
Ayah 54:28 الأية
وَنَبِّئْهُمْ أَنَّ الْمَاءَ قِسْمَةٌ بَيْنَهُمْ ۖ كُلُّ شِرْبٍ مُّحْتَضَرٌ
Wanabbi/hum anna almaa qismatunbaynahum kullu shirbin muhtadar
Hausa
Kuma ka bã su lãbãri cẽwa ruwa rababbe ne a tsakãninsu (da rãƙumar), kõwane sha,
mai shi yanã halartar sa.
|
Ayah 54:29 الأية
فَنَادَوْا صَاحِبَهُمْ فَتَعَاطَىٰ فَعَقَرَ
Fanadaw sahibahum fataAAatafaAAaqar
Hausa
Sai suka kira abokinsu, sai ya karɓa, sa'an nan ya sõke ta,
|
Ayah 54:30 الأية
فَكَيْفَ كَانَ عَذَابِي وَنُذُرِ
Fakayfa kana AAathabee wanuthur
Hausa
To, yãya azãbaTa take da gargaɗiNa?
|
Ayah 54:31 الأية
إِنَّا أَرْسَلْنَا عَلَيْهِمْ صَيْحَةً وَاحِدَةً فَكَانُوا كَهَشِيمِ
الْمُحْتَظِرِ
Inna arsalna AAalayhim sayhatanwahidatan fakanoo kahasheemi almuhtathir
Hausa
Lalle Mũ, Mun aika tsãwa guda a kansu, sai suka kasance kamar yãyin mai shinge.
|
Ayah 54:32 الأية
وَلَقَدْ يَسَّرْنَا الْقُرْآنَ لِلذِّكْرِ فَهَلْ مِن مُّدَّكِرٍ
Walaqad yassarna alqur-ana liththikrifahal min muddakir
Hausa
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai
tunãwa?
|
Ayah 54:33 الأية
كَذَّبَتْ قَوْمُ لُوطٍ بِالنُّذُرِ
Kaththabat qawmu lootin binnuthur
Hausa
Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata, game da gargaɗi.
|
Ayah 54:34 الأية
إِنَّا أَرْسَلْنَا عَلَيْهِمْ حَاصِبًا إِلَّا آلَ لُوطٍ ۖ نَّجَّيْنَاهُم
بِسَحَرٍ
Inna arsalna AAalayhim hasibanilla ala lootin najjaynahum bisahar
Hausa
Lalle Mun aika iskar tsakuwa a kansu, fãce mabiyan Lũɗu, Mun tsirar da su a
lõkacin asuba.
|
Ayah 54:35 الأية
نِّعْمَةً مِّنْ عِندِنَا ۚ كَذَٰلِكَ نَجْزِي مَن شَكَرَ
NiAAmatan min AAindina kathalikanajzee man shakar
Hausa
Sabõda wata ni'ima ta daga gare Mu. Kamar haka Muke sãka wa wanda ya gõde.
|
Ayah 54:36 الأية
وَلَقَدْ أَنذَرَهُم بَطْشَتَنَا فَتَمَارَوْا بِالنُّذُرِ
Walaqad antharahum batshatanafatamaraw binnuthur
Hausa
Kuma lalle, haƙĩƙa, ya yi musu gargaɗin damƙarMu, sai suka yi musu game da
gargaɗin.
|
Ayah 54:37 الأية
وَلَقَدْ رَاوَدُوهُ عَن ضَيْفِهِ فَطَمَسْنَا أَعْيُنَهُمْ فَذُوقُوا عَذَابِي
وَنُذُرِ
Walaqad rawadoohu AAan dayfihifatamasna aAAyunahum fathooqoo AAathabeewanuthur
Hausa
Kuma lalle haƙĩƙa, su, sun nẽme shi ta wajen bãƙinsa, sai Muka shãfe idãnunsu.
"To, ku ɗanɗani azãbaTa da gargaɗĩNa."
|
Ayah 54:38 الأية
وَلَقَدْ صَبَّحَهُم بُكْرَةً عَذَابٌ مُّسْتَقِرٌّ
Walaqad sabbahahum bukratanAAathabun mustaqirr
Hausa
Kuma lalle, haƙĩƙa, wata azãba matabbaciya tã wãye musu gari da yãƙi, tun da
sãfe.
|
Ayah 54:39 الأية
فَذُوقُوا عَذَابِي وَنُذُرِ
Fathooqoo AAathabee wanuthur
Hausa
To, ku ɗanɗani azãbãTa da gargaɗĩNa.
|
Ayah 54:40 الأية
وَلَقَدْ يَسَّرْنَا الْقُرْآنَ لِلذِّكْرِ فَهَلْ مِن مُّدَّكِرٍ
Walaqad yassarna alqur-ana liththikrifahal min muddakir
Hausa
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur,ani dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai
tunãwa?
|
Ayah 54:41 الأية
وَلَقَدْ جَاءَ آلَ فِرْعَوْنَ النُّذُرُ
Walaqad jaa ala firAAawna annuthur
Hausa
Kuma lalle, haƙĩƙa, gargaɗin ya jẽ wa mabiyan Fir'auna.
|
Ayah 54:42 الأية
كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا كُلِّهَا فَأَخَذْنَاهُمْ أَخْذَ عَزِيزٍ مُّقْتَدِرٍ
Kaththaboo bi-ayatinakulliha faakhathnahum akhthaAAazeezin muqtadir
Hausa
Sun ƙaryata game da ãyõyinMu, dukansu sai Muka kãma su, irin kãmun Mabuwãyi, Mai
ĩkon yi.
|
Ayah 54:43 الأية
أَكُفَّارُكُمْ خَيْرٌ مِّنْ أُولَٰئِكُمْ أَمْ لَكُم بَرَاءَةٌ فِي الزُّبُرِ
Akuffarukum khayrun min ola-ikumam lakum baraatun fee azzubur
Hausa
Shin, kãfiranku ne mafi alhẽri daga waɗancan, ko kuwa kunã da wata barã'a a
cikin littattafai?
|
Ayah 54:44 الأية
أَمْ يَقُولُونَ نَحْنُ جَمِيعٌ مُّنتَصِرٌ
Am yaqooloona nahnu jameeAAun muntasir
Hausa
Kõ zã su ce: "Mũ duka mãsu haɗa ƙarfi ne dõmin cin nasara?"
|
Ayah 54:45 الأية
سَيُهْزَمُ الْجَمْعُ وَيُوَلُّونَ الدُّبُرَ
Sayuhzamu aljamAAu wayuwalloona addubur
Hausa
Zã a karya tãron, kuma su jũya bãya dõmin gudu.
|
Ayah 54:46 الأية
بَلِ السَّاعَةُ مَوْعِدُهُمْ وَالسَّاعَةُ أَدْهَىٰ وَأَمَرُّ
Bali assaAAatu mawAAiduhum wassaAAatuadha waamar
Hausa
Ã'a, Sã'a ita cẽ lõkacin wa'adinsu, kuma Sã'ar tã fi tsananin masĩfa, kuma ta
fiɗãci.
|
Ayah 54:47 الأية
إِنَّ الْمُجْرِمِينَ فِي ضَلَالٍ وَسُعُرٍ
Inna almujrimeena fee dalalinwasuAAur
Hausa
Lalle ne, mãsu laifi sunã a cikin ɓata da hauka.
|
Ayah 54:48 الأية
يَوْمَ يُسْحَبُونَ فِي النَّارِ عَلَىٰ وُجُوهِهِمْ ذُوقُوا مَسَّ سَقَرَ
Yawma yushaboona fee annariAAala wujoohihim thooqoo massa saqar
Hausa
Rãnar da zã a jã su a cikin wuta a kan fuskõkinsu. "Ku ɗanɗani shãfar wutar
Saƙar."
|
Ayah 54:49 الأية
إِنَّا كُلَّ شَيْءٍ خَلَقْنَاهُ بِقَدَرٍ
Inna kulla shay-in khalaqnahubiqadar
Hausa
Lalle Mũ, kõwane irin abu Mun halitta shi a kan tsãri.
|
Ayah 54:50 الأية
وَمَا أَمْرُنَا إِلَّا وَاحِدَةٌ كَلَمْحٍ بِالْبَصَرِ
Wama amruna illa wahidatunkalamhin bilbasar
Hausa
Kuma umurninMu bai zamo ba fãce da kalma ɗaya, kamar walƙãwar ido.
|
Ayah 54:51 الأية
وَلَقَدْ أَهْلَكْنَا أَشْيَاعَكُمْ فَهَلْ مِن مُّدَّكِرٍ
Walaqad ahlakna ashyaAAakumfahal min muddakir
Hausa
Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun halaka irin gayyarku. To, shin, akwai mai tunãni?
|
Ayah 54:52 الأية
وَكُلُّ شَيْءٍ فَعَلُوهُ فِي الزُّبُرِ
Wakullu shay-in faAAaloohu fee azzubur
Hausa
Kuma kõwane abu, da suka aikata shi, yanã a cikin littattafai.
|
Ayah 54:53 الأية
وَكُلُّ صَغِيرٍ وَكَبِيرٍ مُّسْتَطَرٌ
Wakullu sagheerin wakabeerin mustatar
Hausa
Kuma dukkan ƙarami da babba, rubutacce ne.
|
Ayah 54:54 الأية
إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي جَنَّاتٍ وَنَهَرٍ
Inna almuttaqeena fee jannatinwanahar
Hausa
Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna da kõguna.
|
Ayah 54:55 الأية
فِي مَقْعَدِ صِدْقٍ عِندَ مَلِيكٍ مُّقْتَدِرٍ
Fee maqAAadi sidqin AAinda maleekinmuqtadir
Hausa
A cikin mazaunin gaskiya, wurin Mai ikon yi, Mai iya zartaswa.
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|