1st Ayah 1 الأية ١الأوليبِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
يَا أَيُّهَا النَّاسُ اتَّقُوا رَبَّكُمْ ۚ إِنَّ زَلْزَلَةَ السَّاعَةِ شَيْءٌ
عَظِيمٌ
Ya ayyuha annasuittaqoo rabbakum inna zalzalata assaAAati shay-onAAatheem
Hausa
Yă ku mutăne! Ku bi Ubangijinku da taƙawa. Lalle ne girgizar ƙasa ta tsayuwar
Sa'a wata aba ce mai girma.
|
Ayah 22:2 الأية
يَوْمَ تَرَوْنَهَا تَذْهَلُ كُلُّ مُرْضِعَةٍ عَمَّا أَرْضَعَتْ وَتَضَعُ كُلُّ
ذَاتِ حَمْلٍ حَمْلَهَا وَتَرَى النَّاسَ سُكَارَىٰ وَمَا هُم بِسُكَارَىٰ
وَلَٰكِنَّ عَذَابَ اللهِ شَدِيدٌ
Yawma tarawnaha tathhalu kullumurdiAAatin AAamma ardaAAat watadaAAukullu thati
hamlin hamlaha wataraannasa sukara wama hum bisukarawalakinna AAathaba Allahi
shadeed
Hausa
A rănar da kuke ganin ta dukan mai shăyar da măma tană shagala daga abin da ta
shăyar, kuma dukan mai ciki tană haihuwar cikinta, kuma kană ganin mutăne sună
măsu măyẽ alhăli kuwa su bă măsu măye ba, amma azăbar Allah ce mai tsanani.
|
Ayah 22:3 الأية
وَمِنَ النَّاسِ مَن يُجَادِلُ فِي اللهِ بِغَيْرِ عِلْمٍ وَيَتَّبِعُ كُلَّ
شَيْطَانٍ مَّرِيدٍ
Wamina annasi man yujadilufee Allahi bighayri AAilmin wayattabiAAu kulla
shaytaninmareed
Hausa
Akwai daga mutăne wanda yake yin musũ ga sha'anin Allah bă da wani ilmi ba, kuma
yană biyar kőwane Shaiɗan mai taurin kai.
|
Ayah 22:4 الأية
كُتِبَ عَلَيْهِ أَنَّهُ مَن تَوَلَّاهُ فَأَنَّهُ يُضِلُّهُ وَيَهْدِيهِ إِلَىٰ
عَذَابِ السَّعِيرِ
Kutiba AAalayhi annahu man tawallahufaannahu yudilluhu wayahdeehi ila AAathabi
assaAAeer
Hausa
An wajabta masa cẽwa wanda ya jiɓince shi, to, lalle ne sai ya ɓatar da shi,
kuma ya shiryar da shi zuwa ga azăbar sa'ĩr.
|
Ayah 22:5 الأية
يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِن كُنتُمْ فِي رَيْبٍ مِّنَ الْبَعْثِ فَإِنَّا
خَلَقْنَاكُم مِّن تُرَابٍ ثُمَّ مِن نُّطْفَةٍ ثُمَّ مِنْ عَلَقَةٍ ثُمَّ مِن
مُّضْغَةٍ مُّخَلَّقَةٍ وَغَيْرِ مُخَلَّقَةٍ لِّنُبَيِّنَ لَكُمْ ۚ وَنُقِرُّ فِي
الْأَرْحَامِ مَا نَشَاءُ إِلَىٰ أَجَلٍ مُّسَمًّى ثُمَّ نُخْرِجُكُمْ طِفْلًا
ثُمَّ لِتَبْلُغُوا أَشُدَّكُمْ ۖ وَمِنكُم مَّن يُتَوَفَّىٰ وَمِنكُم مَّن يُرَدُّ
إِلَىٰ أَرْذَلِ الْعُمُرِ لِكَيْلَا يَعْلَمَ مِن بَعْدِ عِلْمٍ شَيْئًا ۚ وَتَرَى
الْأَرْضَ هَامِدَةً فَإِذَا أَنزَلْنَا عَلَيْهَا الْمَاءَ اهْتَزَّتْ وَرَبَتْ
وَأَنبَتَتْ مِن كُلِّ زَوْجٍ بَهِيجٍ
Ya ayyuha annasuin kuntum fee raybin mina albaAAthi fa-inna khalaqnakummin
turabin thumma min nutfatin thumma minAAalaqatin thumma min mudghatin
mukhallaqatin waghayrimukhallaqatin linubayyina lakum wanuqirru fee al-arhami
manashao ila ajalin musamman thumma nukhrijukum tiflanthumma litablughoo
ashuddakum waminkum man yutawaffawaminkum man yuraddu ila arthali alAAumuri
likaylayaAAlama min baAAdi AAilmin shay-an watara al-ardahamidatan fa-itha
anzalna AAalayhaalmaa ihtazzat warabat waanbatat min kulli zawjin baheej
Hausa
Ya ku mutăne! Idan kun kasance a cikin shakka a Tăshin ˇiyăma, to, lalle ne Mũ,
Man halittaku daga turɓaya, sa'an nan kuma daga gudăjin jini, sa'an nan kuma
daga taőka wadda ake halittăwa da wadda ba a halittawa dőmin, Mu bayyana muku.
Kuma Mună tab batar da abin da Muke so a cikin mahaifa zuwa ga wani ajali
ambatacce, sa'an nan kuma Mună fitar da ku kună jărĩri, sa'an nan kuma dőmin ku
kai ga cikar ƙarfinku. Kuma daga cikin ku akwai wanda ke mutuwa, kuma daga gare
ku akwai wanda ake mayarwa zuwa ga mafi ƙasƙancin răyuwa dőmin kada ya san kőme
a băyan ya sani. Kuma kană ganin ƙasa shiru, sa'an nan idan Muka saukar da ruwa
a kanta, sai ta girgiza kuma ta kumbura, kuma ta tsirar da tsirrai daga kőwane
nau'i mai ban sha'awa.
|
Ayah 22:6 الأية
ذَٰلِكَ بِأَنَّ اللهَ هُوَ الْحَقُّ وَأَنَّهُ يُحْيِي الْمَوْتَىٰ وَأَنَّهُ
عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ
Thalika bi-anna Allaha huwa alhaqquwaannahu yuhyee almawta waannahu AAala
kullishay-in qadeer
Hausa
Wancan ne dőmin lalle Allah Shi ne Gaskiya, kuma lalle ne shi Yake răyar da
matattu, kuma lalle Shi Mai ikon yi ne a kan kőme.
|
Ayah 22:7 الأية
وَأَنَّ السَّاعَةَ آتِيَةٌ لَّا رَيْبَ فِيهَا وَأَنَّ اللهَ يَبْعَثُ مَن فِي
الْقُبُورِ
Waanna assaAAata atiyatunla rayba feeha waanna Allaha yabAAathu manfee alquboor
Hausa
Kuma lalle ne Sa'ar Tăshin ˇiyăma mai zuwa ce, băbu shakka a cikinta kuma lalle
ne Allah Yană tăyar da waɗanda suke a cikin ƙaburbura.
|
Ayah 22:8 الأية
وَمِنَ النَّاسِ مَن يُجَادِلُ فِي اللهِ بِغَيْرِ عِلْمٍ وَلَا هُدًى وَلَا
كِتَابٍ مُّنِيرٍ
Wamina annasi man yujadilufee Allahi bighayri AAilmin wala hudan walakitabin
muneer
Hausa
Kuma daga mutăne akwai mai yin musu ga Allah bă da wani ilmi ba kuma bă da wata
shiriya ba, kuma bă da wani littăfi mai haskakăwa ba.
|
Ayah 22:9 الأية
ثَانِيَ عِطْفِهِ لِيُضِلَّ عَن سَبِيلِ اللهِ ۖ لَهُ فِي الدُّنْيَا خِزْيٌ ۖ
وَنُذِيقُهُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ عَذَابَ الْحَرِيقِ
Thaniya AAitfihi liyudillaAAan sabeeli Allahi lahu fee addunyakhizyun
wanutheequhu yawma alqiyamati AAathabaalhareeq
Hausa
Yană mai karkatar da săshensa dőmin ya ɓatar (da wasu) daga tafarkin Allah! Yană
da wani wulăkanci a dũniya, kuma Mună ɗanɗana masa azăbar gőbara a Rănar ˇiyăma.
|
Ayah 22:10 الأية
ذَٰلِكَ بِمَا قَدَّمَتْ يَدَاكَ وَأَنَّ اللهَ لَيْسَ بِظَلَّامٍ لِّلْعَبِيدِ
Thalika bima qaddamat yadakawaanna Allaha laysa bithallaminlilAAabeed
Hausa
(A ce masa): "Wancan azaba sabőda abin da hannayenka biyu suka gabatar ne, kuma
lalle ne Allah bai zama Mai zălunci ga băyinSa ba."
|
Ayah 22:11 الأية
وَمِنَ النَّاسِ مَن يَعْبُدُ اللهَ عَلَىٰ حَرْفٍ ۖ فَإِنْ أَصَابَهُ خَيْرٌ
اطْمَأَنَّ بِهِ ۖ وَإِنْ أَصَابَتْهُ فِتْنَةٌ انقَلَبَ عَلَىٰ وَجْهِهِ خَسِرَ
الدُّنْيَا وَالْآخِرَةَ ۚ ذَٰلِكَ هُوَ الْخُسْرَانُ الْمُبِينُ
Wamina annasi man yaAAbuduAllaha AAala harfin fa-in asabahukhayrun itmaanna bihi
wa-in asabat-hu fitnatuninqalaba AAala wajhihi khasira addunya
wal-akhiratathalika huwa alkhusranu almubeen
Hausa
Kuma daga mutăne akwai mai bauta wa Allah a kan wani gefe. Sa'an nan idan wani
alhẽri ya săme shi, sai ya natsu da shi, kuma idan wata fitina ta săme shi, sai
ya jũya băya a kan fuskarsa. Yă yi hasărar dũniya da Lăhira. Waccan ita ce
hasăra bayyananna.
|
Ayah 22:12 الأية
يَدْعُو مِن دُونِ اللهِ مَا لَا يَضُرُّهُ وَمَا لَا يَنفَعُهُ ۚ ذَٰلِكَ هُوَ
الضَّلَالُ الْبَعِيدُ
YadAAoo min dooni Allahi ma layadurruhu wama la yanfaAAuhu thalikahuwa addalalu
albaAAeed
Hausa
Yană kiran baicin Allah, abin da bă ya cũtarsa da abin da bă ya amfăninsa!
waccan ita ce ɓata mai nĩsa.
|
Ayah 22:13 الأية
يَدْعُو لَمَن ضَرُّهُ أَقْرَبُ مِن نَّفْعِهِ ۚ لَبِئْسَ الْمَوْلَىٰ وَلَبِئْسَ
الْعَشِيرُ
YadAAoo laman darruhu aqrabu minnafAAihi labi/sa almawla walabi/sa alAAasheer
Hausa
Yană kiran wanda yake lalle cũtarwarsa ce mafi kusa daga amfăninsa! Lalle ne,
tir da shi ya zama majiɓinci, kuma tir da ya zama abőkin zama!
|
Ayah 22:14 الأية
إِنَّ اللهَ يُدْخِلُ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ جَنَّاتٍ
تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ ۚ إِنَّ اللهَ يَفْعَلُ مَا يُرِيدُ
Inna Allaha yudkhilu allatheenaamanoo waAAamiloo assalihati jannatintajree min
tahtiha al-anharu inna AllahayafAAalu ma yureed
Hausa
Lalle ne Allah Yană shigar da waɗanda suka yi ĩmăni kuma suka aikata ayyukan
ƙwarai a cikin gidăjen Aljanna, ƙoramu na gudăna daga ƙarƙashinsu. Lalle ne
Allah Yană aikata abin da Yake nufi.
|
Ayah 22:15 الأية
مَن كَانَ يَظُنُّ أَن لَّن يَنصُرَهُ اللهُ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ
فَلْيَمْدُدْ بِسَبَبٍ إِلَى السَّمَاءِ ثُمَّ لْيَقْطَعْ فَلْيَنظُرْ هَلْ
يُذْهِبَنَّ كَيْدُهُ مَا يَغِيظُ
Man kana yathunnu anlan yansurahu Allahu fee addunya wal-akhiratifalyamdud
bisababin ila assama-i thummaliyaqtaAA falyanthur hal yuthhibannakayduhu ma
yagheeth
Hausa
Wanda ya kasance yană zaton cẽwa Allah bă zai taimake shi ba a cikin dũniya da
Lăhira to sai ya mĩƙa wata igiya zuwa sama, sa'an nan kuma ya yanke ta, sa'an
nan ya dũba. Shin, ko lalle kaidinsa zai gusar da abin da yake ji na takaici?
|
Ayah 22:16 الأية
وَكَذَٰلِكَ أَنزَلْنَاهُ آيَاتٍ بَيِّنَاتٍ وَأَنَّ اللهَ يَهْدِي مَن يُرِيدُ
Wakathalika anzalnahu ayatinbayyinatin waanna Allaha yahdee man yureed
Hausa
Kuma kamar haka Muka saukar da shi (Alƙur'ăni) yană ăyőyi bayyanannu. Kuma lalle
ne Allah Yană shiryar da wanda Yake nufi.
|
Ayah 22:17 الأية
إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَالَّذِينَ هَادُوا وَالصَّابِئِينَ وَالنَّصَارَىٰ
وَالْمَجُوسَ وَالَّذِينَ أَشْرَكُوا إِنَّ اللهَ يَفْصِلُ بَيْنَهُمْ يَوْمَ
الْقِيَامَةِ ۚ إِنَّ اللهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ شَهِيدٌ
Inna allatheena amanoo wallatheenahadoo wassabi-eena wannasarawalmajoosa
wallatheena ashrakoo inna Allahayafsilu baynahum yawma alqiyamati inna
AllahaAAala kulli shay-in shaheed
Hausa
Lalle ne waɗanda suka yi ĩmăni da waɗanda suka tũba (Yahũdu) da waɗanda suka
karkace (Saba'ăwa) da Nasăra da Majũsăwa da waɗanda suka yi shirka, lalle ne
Allah Yană yin hukunci a tsakăninsu a Ranăr ˇiyăma.Lalle ne Allah Mahalarci ne a
kan dukkan kőme.
|
Ayah 22:18 الأية
أَلَمْ تَرَ أَنَّ اللهَ يَسْجُدُ لَهُ مَن فِي السَّمَاوَاتِ وَمَن فِي
الْأَرْضِ وَالشَّمْسُ وَالْقَمَرُ وَالنُّجُومُ وَالْجِبَالُ وَالشَّجَرُ
وَالدَّوَابُّ وَكَثِيرٌ مِّنَ النَّاسِ ۖ وَكَثِيرٌ حَقَّ عَلَيْهِ الْعَذَابُ ۗ
وَمَن يُهِنِ اللهُ فَمَا لَهُ مِن مُّكْرِمٍ ۚ إِنَّ اللهَ يَفْعَلُ مَا
يَشَاءُ ۩
Alam tara anna Allaha yasjudu lahuman fee assamawati waman fee al-ardiwashshamsu
walqamaru wannujoomu waljibaluwashshajaru waddawabbu wakatheerun minaannasi
wakatheerun haqqa AAalayhi alAAathabuwaman yuhini Allahu fama lahu min mukrimin
inna AllahayafAAalu ma yasha/
Hausa
Ashe, ba ka gani ba, lalle Allah, wanda yake a cikin sammai da wanda yake a
cikin ƙasa yană yin sujada a gare shi, da kuma răna da wată da taurări da
duwătsu da ităce da dabbőbi, da kuma măsu yawa daga mutăne? Kuma waɗansu măsu
yawa azăba tă tabbata a kansu. Kuma wanda Allah Ya wulăkantar, to, bă ya da wani
mai girmamăwa. Kuma Lalle ne Allah Yană aikata abin da Yake so.
|
Ayah 22:19 الأية
هَٰذَانِ خَصْمَانِ اخْتَصَمُوا فِي رَبِّهِمْ ۖ فَالَّذِينَ كَفَرُوا قُطِّعَتْ
لَهُمْ ثِيَابٌ مِّن نَّارٍ يُصَبُّ مِن فَوْقِ رُءُوسِهِمُ الْحَمِيمُ
Hathani khasmani ikhtasamoofee rabbihim fallatheena kafaroo quttiAAatlahum
thiyabun min narin yusabbu min fawqiruoosihimu alhameem
Hausa
waɗannan ƙungiyőyi biyu ne măsu husũma, sun yi husũma ga sha'anin Ubangijinsu.
To, waɗanda suka kăfirta an yanka musu waɗansu tufafi daga wata irin wuta, ană
zuba tafasasshen ruwa daga bisa kăwunansu.
|
Ayah 22:20 الأية
يُصْهَرُ بِهِ مَا فِي بُطُونِهِمْ وَالْجُلُودُ
Yusharu bihi ma fee butoonihimwaljulood
Hausa
Da shĩ ake narkar da abin da yake a cikin cikunansu da fătun jikinsu.
|
Ayah 22:21 الأية
وَلَهُم مَّقَامِعُ مِنْ حَدِيدٍ
Walahum maqamiAAu min hadeed
Hausa
Kuma sună da waɗansu gwalmőmin dũka na baƙin ƙarfe.
|
Ayah 22:22 الأية
كُلَّمَا أَرَادُوا أَن يَخْرُجُوا مِنْهَا مِنْ غَمٍّ أُعِيدُوا فِيهَا وَذُوقُوا
عَذَابَ الْحَرِيقِ
Kullama aradoo an yakhrujoominha min ghammin oAAeedoo feeha wathooqooAAathaba
alhareeq
Hausa
A kőyaushe suka yi nufin fita daga gare ta, daga baƙin ciki, sai a mayar da su a
cikinta, (a ce musu) "Ku ɗanɗani azăbar gőbara."
|
Ayah 22:23 الأية
إِنَّ اللهَ يُدْخِلُ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ جَنَّاتٍ
تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ يُحَلَّوْنَ فِيهَا مِنْ أَسَاوِرَ مِن ذَهَبٍ
وَلُؤْلُؤًا ۖ وَلِبَاسُهُمْ فِيهَا حَرِيرٌ
Inna Allaha yudkhilu allatheenaamanoo waAAamiloo assalihati jannatintajree min
tahtiha al-anharu yuhallawnafeeha min asawira min thahabin walu/lu-anwalibasuhum
feeha hareer
Hausa
Lalle ne, Allah Yana shigar da waɗanda suka yi ĩmăni kuma suka aikata ayyukan
ƙwarai a cikin gidăjen Aljanna, ƙoramu sună gudăna daga ƙarƙashinsu, ană ƙawăta
su, a cikinsu, da waɗansu mundăye na zĩnări da lu'u-lu'u. Kuma tufăfinsu a
cikinsu alharĩni ne.
|
Ayah 22:24 الأية
وَهُدُوا إِلَى الطَّيِّبِ مِنَ الْقَوْلِ وَهُدُوا إِلَىٰ صِرَاطِ الْحَمِيدِ
Wahudoo ila attayyibimina alqawli wahudoo ila sirati alhameed
Hausa
Kuma an shiryar da su zuwa ga mai kyau na zance kuma an shiryar da su zuwa ga,
hanyar wanda ake gode wa.
|
Ayah 22:25 الأية
إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا وَيَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ اللهِ وَالْمَسْجِدِ
الْحَرَامِ الَّذِي جَعَلْنَاهُ لِلنَّاسِ سَوَاءً الْعَاكِفُ فِيهِ وَالْبَادِ ۚ
وَمَن يُرِدْ فِيهِ بِإِلْحَادٍ بِظُلْمٍ نُّذِقْهُ مِنْ عَذَابٍ أَلِيمٍ
Inna allatheena kafaroo wayasuddoonaAAan sabeeli Allahi walmasjidi
alharamiallathee jaAAalnahu linnasi sawaanalAAakifu feehi walbadi waman yurid
feehibi-ilhadin bithulmin nuthiqhu min AAathabinaleem
Hausa
Lalle ne waɗanda suka kăfirta kuma suka taushe (mutăne) daga hanyar Allah da
masallaci mai alfarma wanda Muka sanya shi ga mutăne alhăli kuwa mazauni a ciki
da baƙauye daidai suke kuma wanda ya yi nufin karkatar da gaskiya a cikinsa da
zălunci ză Mu ɗanɗana masa daga wata azăba mai raɗadi.
|
Ayah 22:26 الأية
وَإِذْ بَوَّأْنَا لِإِبْرَاهِيمَ مَكَانَ الْبَيْتِ أَن لَّا تُشْرِكْ بِي شَيْئًا
وَطَهِّرْ بَيْتِيَ لِلطَّائِفِينَ وَالْقَائِمِينَ وَالرُّكَّعِ السُّجُودِ
Wa-ith bawwa/na li-ibraheemamakana albayti an la tushrik bee shay-an
watahhirbaytiya litta-ifeena walqa-imeenawarrukkaAAi assujood
Hausa
Kuma a lőkacin da Muka iyăkance wa Ibrăhim wurin ¦akin (Muka ce masa), "Kada ka
haɗa kőme da Ni ga bauta, kuma ka tsarkake ¦ăkiNa dőmin măsu ɗawăfi da măsu
tsayuwa da măsu ruku'u da măsu sujada.
|
Ayah 22:27 الأية
وَأَذِّن فِي النَّاسِ بِالْحَجِّ يَأْتُوكَ رِجَالًا وَعَلَىٰ كُلِّ ضَامِرٍ
يَأْتِينَ مِن كُلِّ فَجٍّ عَمِيقٍ
Waaththin fee annasibilhajji ya/tooka rijalan waAAalakulli damirin ya/teena min
kulli fajjin AAameeq
Hausa
"Kuma ka yi yẽkuwa ga mutăne da wajabcin Hajji su je maka suna măsu tafiya da
ƙafăfu da kuma a kan kőwane maɗankwarin răƙumi măsu zuwa daga kőwane rango mai
zurfi."
|
Ayah 22:28 الأية
لِّيَشْهَدُوا مَنَافِعَ لَهُمْ وَيَذْكُرُوا اسْمَ اللهِ فِي أَيَّامٍ
مَّعْلُومَاتٍ عَلَىٰ مَا رَزَقَهُم مِّن بَهِيمَةِ الْأَنْعَامِ ۖ فَكُلُوا
مِنْهَا وَأَطْعِمُوا الْبَائِسَ الْفَقِيرَ
Liyashhadoo manafiAAa lahum wayathkurooisma Allahi fee ayyamin maAAloomatin
AAalama razaqahum min baheemati al-anAAami fakuloo minhawaatAAimoo alba-isa
alfaqeer
Hausa
"Dőmin su halarci abũbuwan amfăni a gare su, kuma su ambăci sunan Allah a cikin
'yan kwănuka sanannu sabőda abin da Ya azurta su da shĩ daga dabbőbin jin dăɗi.
Sai ku ci daga gare su, kuma ku ciyar da matsattse matalauci."
|
Ayah 22:29 الأية
ثُمَّ لْيَقْضُوا تَفَثَهُمْ وَلْيُوفُوا نُذُورَهُمْ وَلْيَطَّوَّفُوا بِالْبَيْتِ
الْعَتِيقِ
Thumma lyaqdoo tafathahum walyoofoonuthoorahum walyattawwafoo bilbaytialAAateeq
Hausa
"Sa'an nan kuma sai su ƙăre ibădarsu da gusar da ƙazanta, knma sai su cika
alkawuransu kuma sai su yi ɗawăfi (sună gẽwaya) ga ¦ăkin nin 'yantacce."
|
Ayah 22:30 الأية
ذَٰلِكَ وَمَن يُعَظِّمْ حُرُمَاتِ اللهِ فَهُوَ خَيْرٌ لَّهُ عِندَ رَبِّهِ ۗ
وَأُحِلَّتْ لَكُمُ الْأَنْعَامُ إِلَّا مَا يُتْلَىٰ عَلَيْكُمْ ۖ فَاجْتَنِبُوا
الرِّجْسَ مِنَ الْأَوْثَانِ وَاجْتَنِبُوا قَوْلَ الزُّورِ
Thalika waman yuAAaththimhurumati Allahi fahuwa khayrun lahu AAindarabbihi
waohillat lakumu al-anAAamu illa mayutla AAalaykum fajtaniboo arrijsa
minaal-awthani wajtaniboo qawla azzoor
Hausa
Wancan ne. Kuma wanda ya girmama hukunce-hukuncen Allah to shĩ ne mafĩfĩci a
gare shi, a wurin Ubangijinsa. Kuma an halatta muku dabbőbin ni'ima făce abin da
ake karantăwa a kanku. Sabőda haka ku nĩsanci ƙazanta daga gumăka kuma ku
nĩsanci ƙazanta daga shaidar zur.
|
Ayah 22:31 الأية
حُنَفَاءَ لِلَّهِ غَيْرَ مُشْرِكِينَ بِهِ ۚ وَمَن يُشْرِكْ بِاللهِ
فَكَأَنَّمَا خَرَّ مِنَ السَّمَاءِ فَتَخْطَفُهُ الطَّيْرُ أَوْ تَهْوِي بِهِ
الرِّيحُ فِي مَكَانٍ سَحِيقٍ
Hunafaa lillahi ghayramushrikeena bihi waman yushrik billahi fakaannamakharra
mina assama-i fatakhtafuhu attayruaw tahwee bihi arreehu fee makanin saheeq
Hausa
Kuna măsu tsayuwa ga gaskiya dőmin Allah, ba masu yin shirka da Shi ba. Kuma
wanda ya yi shirka da Allah, to, yană kamar abin da ya făɗo daga sama, sa'an nan
tsuntsăye su cafe shi, ko iska ta făɗa da shi a cikin wani wuri mai nisa.
|
Ayah 22:32 الأية
ذَٰلِكَ وَمَن يُعَظِّمْ شَعَائِرَ اللهِ فَإِنَّهَا مِن تَقْوَى الْقُلُوبِ
Thalika waman yuAAaththimshaAAa-ira Allahi fa-innaha min taqwaalquloob
Hausa
Wancan ne. Kuma wanda ya girmama ibădődin Allah, to, lalle ne ita (girmamăwar)
tană daga ayyukan zukăta na ibăda.
|
Ayah 22:33 الأية
لَكُمْ فِيهَا مَنَافِعُ إِلَىٰ أَجَلٍ مُّسَمًّى ثُمَّ مَحِلُّهَا إِلَى الْبَيْتِ
الْعَتِيقِ
Lakum feeha manafiAAu ilaajalin musamman thumma mahilluha ila albaytialAAateeq
Hausa
Kuna da waɗansu abũbuwan amfăni a cikinta (dabbar hadaya) har ya zuwa ga wani
ajali ambatacce, sa'an nan kuma wurin halattăta zuwa ga ¦ăkin 'yantacce ne.
|
Ayah 22:34 الأية
وَلِكُلِّ أُمَّةٍ جَعَلْنَا مَنسَكًا لِّيَذْكُرُوا اسْمَ اللهِ عَلَىٰ مَا
رَزَقَهُم مِّن بَهِيمَةِ الْأَنْعَامِ ۗ فَإِلَٰهُكُمْ إِلَٰهٌ وَاحِدٌ فَلَهُ
أَسْلِمُوا ۗ وَبَشِّرِ الْمُخْبِتِينَ
Walikulli ommatin jaAAalna mansakanliyathkuroo isma Allahi AAala marazaqahum min
baheemati al-anAAami fa-ilahukum ilahunwahidun falahu aslimoo wabashshiri
almukhbiteen
Hausa
Kuma ga kőwace al'umma Mun sanya ibădar yanka, dőmin su ambaci sũnan Allah a kan
abin da Ya azurta su da shi daga dabbőbin ni'ima. Sa'an nan kuma Abin bautawarku
Abin bautawa ne Guda, sai ku sallama Masa. Kuma ka yi bushăra ga măsu ƙanƙantar
da kai.
|
Ayah 22:35 الأية
الَّذِينَ إِذَا ذُكِرَ اللهُ وَجِلَتْ قُلُوبُهُمْ وَالصَّابِرِينَ عَلَىٰ مَا
أَصَابَهُمْ وَالْمُقِيمِي الصَّلَاةِ وَمِمَّا رَزَقْنَاهُمْ يُنفِقُونَ
Allatheena itha thukiraAllahu wajilat quloobuhum wassabireenaAAala ma asabahum
walmuqeemee assalatiwamimma razaqnahum yunfiqoon
Hausa
Waɗanda suke idan an ambaci Allah sai zukătansu su firgita, da măsu haƙuri a kan
abin da ya săme su, da măsu tsayar da salla, kuma sună ciyarwa daga abin da Muka
azurta su.
|
Ayah 22:36 الأية
وَالْبُدْنَ جَعَلْنَاهَا لَكُم مِّن شَعَائِرِ اللهِ لَكُمْ فِيهَا خَيْرٌ ۖ
فَاذْكُرُوا اسْمَ اللهِ عَلَيْهَا صَوَافَّ ۖ فَإِذَا وَجَبَتْ جُنُوبُهَا
فَكُلُوا مِنْهَا وَأَطْعِمُوا الْقَانِعَ وَالْمُعْتَرَّ ۚ كَذَٰلِكَ
سَخَّرْنَاهَا لَكُمْ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ
Walbudna jaAAalnahalakum min shaAAa-iri Allahi lakum feehakhayrun fathkuroo isma
Allahi AAalayhasawaffa fa-itha wajabat junoobuhafakuloo minha waatAAimoo
alqaniAAa walmuAAtarrakathalika sakhkharnaha lakum laAAallakumtashkuroon
Hausa
Kuma răƙuman, Mun sanya su a gare ku, a ibădőjin Allah. Kună da wani alhẽri
babba a cikinsu. Sai ku ambaci sũnan Allah a kansu sună tsaye a kan ƙafăfu uku.
Sa'an nan idan săsanninsu suka făɗi, to, ku ci daga gare su, kuma ku ciyar da
mai wadar zũci da mai bara. Kamar haka Muka hőre muku su, tsammăninku kună
gődẽwa.
|
Ayah 22:37 الأية
لَن يَنَالَ اللهَ لُحُومُهَا وَلَا دِمَاؤُهَا وَلَٰكِن يَنَالُهُ التَّقْوَىٰ
مِنكُمْ ۚ كَذَٰلِكَ سَخَّرَهَا لَكُمْ لِتُكَبِّرُوا اللهَ عَلَىٰ مَا هَدَاكُمْ
ۗ وَبَشِّرِ الْمُحْسِنِينَ
Lan yanala Allaha luhoomuhawala dimaoha walakin yanaluhuattaqwa minkum kathalika
sakhkharahalakum litukabbiroo Allaha AAala ma hadakumwabashshiri almuhsineen
Hausa
Nămőminsu bă za su sămi Allah ba haka jinainansu amma taƙawa daga gare ku tană,
sămun Sa. Kamar haka Ya hőre su sabőda ku dőmin ku girmama Allah sabőda shiriyar
da Ya yi muku. Kuma ka yi bushăra ga măsu kyautata yi.
|
Ayah 22:38 الأية
إِنَّ اللهَ يُدَافِعُ عَنِ الَّذِينَ آمَنُوا ۗ إِنَّ اللهَ لَا يُحِبُّ كُلَّ
خَوَّانٍ كَفُورٍ
Inna Allaha yudafiAAu AAaniallatheena amanoo inna Allaha la yuhibbukulla
khawwanin kafoor
Hausa
Lalle ne, Allah Yană yin faɗa sabőda waɗanda suka yi ĩmăni. Lalle ne Allah bă Ya
son dukkan mayaudari, mai yawan kăfirci.
|
Ayah 22:39 الأية
أُذِنَ لِلَّذِينَ يُقَاتَلُونَ بِأَنَّهُمْ ظُلِمُوا ۚ وَإِنَّ اللهَ عَلَىٰ
نَصْرِهِمْ لَقَدِيرٌ
Othina lillatheena yuqataloonabi-annahum thulimoo wa-inna Allaha AAalanasrihim
laqadeer
Hausa
An yi izni ga waɗanda ake yăƙar su da cẽwa lalle an zălunce su, kuma lalle ne
Allah, haƙĩƙa,Mai ĩkon yi ne a kan taimakonsu.
|
Ayah 22:40 الأية
الَّذِينَ أُخْرِجُوا مِن دِيَارِهِم بِغَيْرِ حَقٍّ إِلَّا أَن يَقُولُوا رَبُّنَا
اللهُ ۗ وَلَوْلَا دَفْعُ اللهِ النَّاسَ بَعْضَهُم بِبَعْضٍ لَّهُدِّمَتْ
صَوَامِعُ وَبِيَعٌ وَصَلَوَاتٌ وَمَسَاجِدُ يُذْكَرُ فِيهَا اسْمُ اللهِ
كَثِيرًا ۗ وَلَيَنصُرَنَّ اللهُ مَن يَنصُرُهُ ۗ إِنَّ اللهَ لَقَوِيٌّ
عَزِيزٌ
Allatheena okhrijoo min diyarihimbighayri haqqin illa an yaqooloo rabbuna
Allahuwalawla dafAAu Allahi annasa baAAdahumbibaAAdin lahuddimat sawamiAAu
wabiyaAAun wasalawatunwamasajidu yuthkaru feeha ismu Allahikatheeran
walayansuranna Allahu man yansuruhuinna Allaha laqawiyyun AAazeez
Hausa
Waɗanda aka fitina daga gidajensu bă da wani hakki ba făce sună cẽwa,
Ubangijinmu Allah ne."Kuma ba dőmin tunkuɗẽwar Allah ga mutăne ba, săshensu da
săshe, haƙĩƙa, da an rũsa sauma'ő'in (Ruhbănăwa) dă majămi'ő'in Nasăra da
gidăjen ibădar Yahudu da masallatai waɗanda ake ambatar Allah a cikinsu da yawa.
Kuma lalle, haƙĩƙa, Allah Yană taimakon wanda yake taimakon Sa. Lalle Allah ne
haƙĩƙa Mai ƙarfi Mabuwăyi.
|
Ayah 22:41 الأية
الَّذِينَ إِن مَّكَّنَّاهُمْ فِي الْأَرْضِ أَقَامُوا الصَّلَاةَ وَآتَوُا
الزَّكَاةَ وَأَمَرُوا بِالْمَعْرُوفِ وَنَهَوْا عَنِ الْمُنكَرِ ۗ وَلِلَّهِ
عَاقِبَةُ الْأُمُورِ
Allatheena in makkannahum feeal-ardi aqamoo assalata waatawooazzakata waamaroo
bilmaAAroofi wanahawAAani almunkari walillahi AAaqibatu al-omoor
Hausa
Waɗanda suke idan Muka bă su ĩko a cikin ƙasa sai su tsai da salla, kuma su
baybr da zakka kuma su yi umurni da abin da aka sani, kuma su hana daga abin da
ba a sani ba. Kuma ăƙibar al'amura ga Allah take.
|
Ayah 22:42 الأية
وَإِن يُكَذِّبُوكَ فَقَدْ كَذَّبَتْ قَبْلَهُمْ قَوْمُ نُوحٍ وَعَادٌ وَثَمُودُ
Wa-in yukaththibooka faqad kaththabatqablahum qawmu noohin waAAadun wathamood
Hausa
Kuma idan sun ƙaryata ka, to lalle haƙĩƙa, mutănen Nũhu da Ădăwa da Samũdawa,
sun ƙaryata a gabaninsu.
|
Ayah 22:43 الأية
وَقَوْمُ إِبْرَاهِيمَ وَقَوْمُ لُوطٍ
Waqawmu ibraheema waqawmu loot
Hausa
Da mutănen Ibrahim da mutănen Lũɗu.
|
Ayah 22:44 الأية
وَأَصْحَابُ مَدْيَنَ ۖ وَكُذِّبَ مُوسَىٰ فَأَمْلَيْتُ لِلْكَافِرِينَ ثُمَّ
أَخَذْتُهُمْ ۖ فَكَيْفَ كَانَ نَكِيرِ
Waas-habu madyana wakuththibamoosa faamlaytu lilkafireena thumma
akhathtuhumfakayfa kana nakeer
Hausa
Da măsu Madyana, kuma an ƙaryata Mũsă. Sai Na jinkirtawa kăfiran, sa'an nan kuma
Na kăma su. To, yăya musũNa (gare su) ya kasance?
|
Ayah 22:45 الأية
فَكَأَيِّن مِّن قَرْيَةٍ أَهْلَكْنَاهَا وَهِيَ ظَالِمَةٌ فَهِيَ خَاوِيَةٌ عَلَىٰ
عُرُوشِهَا وَبِئْرٍ مُّعَطَّلَةٍ وَقَصْرٍ مَّشِيدٍ
Fakaayyin min qaryatin ahlaknahawahiya thalimatun fahiya khawiyatunAAala
AAurooshiha wabi/rin muAAattalatinwaqasrin masheed
Hausa
Sa'an nan da yawa daga alƙarya, Muka halaka ta, alhăli kuwa tană mai zalũnci sai
ta zama făɗaɗɗa a kan rassanta, da yawa daga rĩjiya wadda aka wőfintar, da kuma
gidăjen sarauta maɗaukaka.
|
Ayah 22:46 الأية
أَفَلَمْ يَسِيرُوا فِي الْأَرْضِ فَتَكُونَ لَهُمْ قُلُوبٌ يَعْقِلُونَ بِهَا أَوْ
آذَانٌ يَسْمَعُونَ بِهَا ۖ فَإِنَّهَا لَا تَعْمَى الْأَبْصَارُ وَلَٰكِن تَعْمَى
الْقُلُوبُ الَّتِي فِي الصُّدُورِ
Afalam yaseeroo fee al-ardi fatakoonalahum quloobun yaAAqiloona biha aw
athanunyasmaAAoona biha fa-innaha la taAAmaal-absaru walakin taAAma alquloobu
allateefee assudoor
Hausa
Shin, to, ba su yi tafiya ba a cikin ƙasa dőmin zukăta waɗanda ză su yi hankali
da su da kunnuwa da za su yi saurăre da su su kasance a gare su? Dőmin lalle ne
idănun ba su makanta, amma zukăta waɗanda ke a cikin ƙirăza sũ ke makanta.
|
Ayah 22:47 الأية
وَيَسْتَعْجِلُونَكَ بِالْعَذَابِ وَلَن يُخْلِفَ اللهُ وَعْدَهُ ۚ وَإِنَّ
يَوْمًا عِندَ رَبِّكَ كَأَلْفِ سَنَةٍ مِّمَّا تَعُدُّونَ
WayastaAAjiloonaka bilAAathabiwalan yukhlifa Allahu waAAdahu wa-inna yawman
AAindarabbika kaalfi sanatin mimma taAAuddoon
Hausa
Kuma sună nẽman ka yi gaggăwa da azăba, alhăli kuwa Allah bă zai săɓa wa'adinSa
ba kuma lalle ne, yini ɗaya a wurin Ubangijinka kamar shẽkara dubu yake daga
abin da kuke ƙidăyăwa.
|
Ayah 22:48 الأية
وَكَأَيِّن مِّن قَرْيَةٍ أَمْلَيْتُ لَهَا وَهِيَ ظَالِمَةٌ ثُمَّ أَخَذْتُهَا
وَإِلَيَّ الْمَصِيرُ
Wakaayyin min qaryatin amlaytu lahawahiya thalimatun thumma akhathtuhawa-ilayya
almaseer
Hausa
Kuma da yawa daga alƙarya, Na yi jinkirin azăba gare ta (da laifinta) sa'an nan
Na kăma ta, kuma zuwa gare Ni makőma take.
|
Ayah 22:49 الأية
قُلْ يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِنَّمَا أَنَا لَكُمْ نَذِيرٌ مُّبِينٌ
Qul ya ayyuha annasuinnama ana lakum natheerun mubeen
Hausa
Ka ce: "Ya ku mutăne! Nĩ wani mai gargaɗi ne kawai zuwa gare ku, mai bayyanawa."
|
Ayah 22:50 الأية
فَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَهُم مَّغْفِرَةٌ وَرِزْقٌ كَرِيمٌ
Fallatheena amanoowaAAamiloo assalihati lahum maghfiratunwarizqun kareem
Hausa
To, waɗanda suka yi ĩmăni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, sună da găfara da
arziki na karimci.
|
Ayah 22:51 الأية
وَالَّذِينَ سَعَوْا فِي آيَاتِنَا مُعَاجِزِينَ أُولَٰئِكَ أَصْحَابُ الْجَحِيمِ
Wallatheena saAAaw fee ayatinamuAAajizeena ola-ika as-habu aljaheem
Hausa
Kuma waɗanda suka yi aikin ɓătăwa a cikin ayőyinMu, sună măsu gajiyarwa,
waɗancan 'yan Jahĩm ne.
|
Ayah 22:52 الأية
وَمَا أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ مِن رَّسُولٍ وَلَا نَبِيٍّ إِلَّا إِذَا تَمَنَّىٰ
أَلْقَى الشَّيْطَانُ فِي أُمْنِيَّتِهِ فَيَنسَخُ اللهُ مَا يُلْقِي
الشَّيْطَانُ ثُمَّ يُحْكِمُ اللهُ آيَاتِهِ ۗ وَاللهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ
Wama arsalna min qablika minrasoolin wala nabiyyin illa itha tamannaalqa
ashshaytanu fee omniyyatihi fayansakhuAllahu ma yulqee ashshaytanu thummayuhkimu
Allahu ayatihi wallahuAAaleemun hakeem
Hausa
Kuma ba Mu aika wani manzo ba a gabăninka, kuma ba Mu umurci wani Annabi ba făce
idan ya yi bũri, sai Shaiɗan ya jẽfa (wani abu) a cikin bũrinsa, sa'an nan Allah
Ya shăfe abin da Shaiɗan ke jefăwa. Sa'an nan kuma Allah Ya kyautata ăyőyinSa.
Kuma Allah Masani ne, Mai hikima.
|
Ayah 22:53 الأية
لِّيَجْعَلَ مَا يُلْقِي الشَّيْطَانُ فِتْنَةً لِّلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٌ
وَالْقَاسِيَةِ قُلُوبُهُمْ ۗ وَإِنَّ الظَّالِمِينَ لَفِي شِقَاقٍ بَعِيدٍ
LiyajAAala ma yulqee ashshaytanufitnatan lillatheena fee quloobihim maradun
walqasiyatiquloobuhum wa-inna aththalimeenalafee shiqaqin baAAeed
Hausa
Dőmin Ya sanya abin da Shaiɗan ke jẽfăwa ya zama fitina ga waɗanda a cikin
zukătansu akwai cũta, da măsu ƙẽƙasassun zukătansu. Kuma lalle ne azzălumai
haƙĩƙa, sună a cikin săɓănimai nĩsa.
|
Ayah 22:54 الأية
وَلِيَعْلَمَ الَّذِينَ أُوتُوا الْعِلْمَ أَنَّهُ الْحَقُّ مِن رَّبِّكَ
فَيُؤْمِنُوا بِهِ فَتُخْبِتَ لَهُ قُلُوبُهُمْ ۗ وَإِنَّ اللهَ لَهَادِ
الَّذِينَ آمَنُوا إِلَىٰ صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ
WaliyaAAlama allatheena ootooalAAilma annahu alhaqqu min rabbika fayu/minoo
bihifatukhbita lahu quloobuhum wa-inna Allaha lahadiallatheena amanoo ila
siratinmustaqeem
Hausa
Kuma dőmin waɗanda aka bai wa ilmi su sani lalle shi ne gaskiya daga Ubangijinka
dőmin su yi ĩmăni da shi sabőda zukătansu su natsu gare shi. Kuma lalle ne
Allah, haƙĩƙa, Mai shiryar da waɗanda suka yi ĩmăni ne zuwa ga hanya
madaidaiciya.
|
Ayah 22:55 الأية
وَلَا يَزَالُ الَّذِينَ كَفَرُوا فِي مِرْيَةٍ مِّنْهُ حَتَّىٰ تَأْتِيَهُمُ
السَّاعَةُ بَغْتَةً أَوْ يَأْتِيَهُمْ عَذَابُ يَوْمٍ عَقِيمٍ
Wala yazalu allatheenakafaroo fee miryatin minhu hatta ta/tiyahumu
assaAAatubaghtatan aw ya/tiyahum AAathabu yawmin AAaqeem
Hausa
Kuma waɗanda suka kăfirta bă ză su gushe ba sună a cikin shakka daga gare shi,
har Sa'a ta jẽ musu bisa ga abke, kő kuwa azăbar wani yini bakarăre ta jẽ musu.
|
Ayah 22:56 الأية
الْمُلْكُ يَوْمَئِذٍ لِّلَّهِ يَحْكُمُ بَيْنَهُمْ ۚ فَالَّذِينَ آمَنُوا
وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ فِي جَنَّاتِ النَّعِيمِ
Almulku yawma-ithin lillahi yahkumubaynahum fallatheena amanoo waAAamiloo
assalihatifee jannati annaAAeem
Hausa
Mulki a rănar nan ga Allah yake, Yană hukunci a tsakăninsu. To, waɗanda suka yi
ĩmăni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sună a cikin gidăjen Aljannar ni'ima.
|
Ayah 22:57 الأية
وَالَّذِينَ كَفَرُوا وَكَذَّبُوا بِآيَاتِنَا فَأُولَٰئِكَ لَهُمْ عَذَابٌ
مُّهِينٌ
Wallatheena kafaroo wakaththaboobi-ayatina faola-ika lahum AAathabunmuheen
Hausa
Kuma waɗandra suka kăfirta kuma suka ƙaryata, game da ăyőyinMu, to, waɗannan
sună da azăba mai wulăkantarwa.
|
Ayah 22:58 الأية
وَالَّذِينَ هَاجَرُوا فِي سَبِيلِ اللهِ ثُمَّ قُتِلُوا أَوْ مَاتُوا
لَيَرْزُقَنَّهُمُ اللهُ رِزْقًا حَسَنًا ۚ وَإِنَّ اللهَ لَهُوَ خَيْرُ
الرَّازِقِينَ
Wallatheena hajaroofee sabeeli Allahi thumma qutiloo aw matoolayarzuqannahumu
Allahu rizqan hasanan wa-inna Allahalahuwa khayru arraziqeen
Hausa
Kuma waɗanda suka yi hijira a cikin tafarkin Allah sa'an nan kuma aka kashe su,
kő suka mutu, lalle ne Allah Yană azurta su da arziki mai kyau. Kuma lalle ne
Allah, haƙĩƙa, Shĩ ne Mafi alhẽrin măsu azurtăwa.
|
Ayah 22:59 الأية
لَيُدْخِلَنَّهُم مُّدْخَلًا يَرْضَوْنَهُ ۗ وَإِنَّ اللهَ لَعَلِيمٌ حَلِيمٌ
Layudkhilannahum mudkhalan yardawnahuwa-inna Allaha laAAaleemun haleem
Hausa
Lalle ne, Yană shigar da su a wata mashiga wadda ză su yarda da ita. Kuma lalle
ne Allah, haƙĩƙa Masani ne, Mai haƙuri.
|
Ayah 22:60 الأية
ذَٰلِكَ وَمَنْ عَاقَبَ بِمِثْلِ مَا عُوقِبَ بِهِ ثُمَّ بُغِيَ عَلَيْهِ
لَيَنصُرَنَّهُ اللهُ ۗ إِنَّ اللهَ لَعَفُوٌّ غَفُورٌ
Thalika waman AAaqaba bimithlima AAooqiba bihi thumma bughiya AAalayhi
layansurannahuAllahu inna Allaha laAAafuwwun ghafoor
Hausa
Wancan! Kuma wanda ya răma azăba da misălin abin da aka yi masa, sa'an nan kuma
aka zălunce shi, lalle ne Allah Yană taimakon sa. Lalle ne Allah haƙĩƙa Mai
yăfẽwa ne, Mai găfara.
|
Ayah 22:61 الأية
ذَٰلِكَ بِأَنَّ اللهَ يُولِجُ اللَّيْلَ فِي النَّهَارِ وَيُولِجُ النَّهَارَ
فِي اللَّيْلِ وَأَنَّ اللهَ سَمِيعٌ بَصِيرٌ
Thalika bi-anna Allaha yoolijuallayla fee annahari wayooliju annaharafee allayli
waanna Allaha sameeAAun baseer
Hausa
Wancan! sabőda Allah Yană shigar da dare a cikin yini, kuma Yană shigar da yini
a cikin dare, kuma lalle, Allah Mai jĩ ne,Mai gani.
|
Ayah 22:62 الأية
ذَٰلِكَ بِأَنَّ اللهَ هُوَ الْحَقُّ وَأَنَّ مَا يَدْعُونَ مِن دُونِهِ هُوَ
الْبَاطِلُ وَأَنَّ اللهَ هُوَ الْعَلِيُّ الْكَبِيرُ
Thalika bi-anna Allaha huwa alhaqquwaanna ma yadAAoona min doonihi huwa
albatiluwaanna Allaha huwa alAAaliyyu alkabeer
Hausa
Wancan! sabőda lalle ne Allah, shĩ ne Gaskiya, kuma lalle ne, abin da suke kira
waninSa shi ne ƙarya. Kuma lalle ne Allah, Shĩ ne Maɗaukaki, Mai girma.
|
Ayah 22:63 الأية
أَلَمْ تَرَ أَنَّ اللهَ أَنزَلَ مِنَ السَّمَاءِ مَاءً فَتُصْبِحُ الْأَرْضُ
مُخْضَرَّةً ۗ إِنَّ اللهَ لَطِيفٌ خَبِيرٌ
Alam tara anna Allaha anzala mina assama-imaan fatusbihu al-ardu
mukhdarrataninna Allaha lateefun khabeer
Hausa
Ashe, ba ka gani ba, lalle ne, Allah Yă saukar da ruwa daga sama, sai ƙasa ta
wăyi gari kőriya? Lalle Allah Mai tausasawa ne, Mai ƙididdigewa.
|
Ayah 22:64 الأية
لَّهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ ۗ وَإِنَّ اللهَ لَهُوَ
الْغَنِيُّ الْحَمِيدُ
Lahu ma fee assamawatiwama fee al-ardi wa-inna Allaha lahuwaalghaniyyu alhameed
Hausa
Abin da ke a cikin sammai, da abin da ke a cikin ƙasa, Nasa ne, kuma lalle ne
Allah, haƙĩƙa,Shi ne wadatacce, Gődadde.
|
Ayah 22:65 الأية
أَلَمْ تَرَ أَنَّ اللهَ سَخَّرَ لَكُم مَّا فِي الْأَرْضِ وَالْفُلْكَ تَجْرِي
فِي الْبَحْرِ بِأَمْرِهِ وَيُمْسِكُ السَّمَاءَ أَن تَقَعَ عَلَى الْأَرْضِ إِلَّا
بِإِذْنِهِ ۗ إِنَّ اللهَ بِالنَّاسِ لَرَءُوفٌ رَّحِيمٌ
Alam tara anna Allaha sakhkhara lakumma fee al-ardi walfulka tajree fee
albahribi-amrihi wayumsiku assamaa an taqaAAa AAalaal-ardi illa bi-ithnihi inna
Allahabinnasi laraoofun raheem
Hausa
Shin ba ka gani ba, lalle ne Allah Ya hőre muku abin da yake a cikin ƙasa, kuma
jirăge sună gudăna a cikin tẽku, da umurninSa kuma Yană riƙe sama dőmin kada ta
făɗi a kan ƙasa făce da izninsa? Lalle ne Allah ga mutăne haƙĩƙa, Mai tausayi
ne, Mai jin ƙai.
|
Ayah 22:66 الأية
وَهُوَ الَّذِي أَحْيَاكُمْ ثُمَّ يُمِيتُكُمْ ثُمَّ يُحْيِيكُمْ ۗ إِنَّ
الْإِنسَانَ لَكَفُورٌ
Wahuwa allathee ahyakumthumma yumeetukum thumma yuhyeekum inna al-insanalakafoor
Hausa
Kuma shĩ ne wanda Ya răya ku, sa'an nan kuma Yană matar da ku, sa'an nan kuma
Yană răyar da ku. Lalle mutum, haƙĩƙa, mai kăfirci ne.
|
Ayah 22:67 الأية
لِّكُلِّ أُمَّةٍ جَعَلْنَا مَنسَكًا هُمْ نَاسِكُوهُ ۖ فَلَا يُنَازِعُنَّكَ فِي
الْأَمْرِ ۚ وَادْعُ إِلَىٰ رَبِّكَ ۖ إِنَّكَ لَعَلَىٰ هُدًى مُّسْتَقِيمٍ
Likulli ommatin jaAAalna mansakan humnasikoohu fala yunaziAAunnaka fee al-amri
wadAAuila rabbika innaka laAAala hudan mustaqeem
Hausa
Ga kőwace al'umma Mun sanya wurin yanka, su ne masu yin baiko gare Shi, sabőda
haka, kada su yi maka jăyayya a cikin al'amarin (hadaya). Kuma ka yi kira zuwa
ga Ubangijinka lalle kai kana a kan shiriya madaidaiciya.
|
Ayah 22:68 الأية
وَإِن جَادَلُوكَ فَقُلِ اللهُ أَعْلَمُ بِمَا تَعْمَلُونَ
Wa-in jadalooka faquli AllahuaAAlamu bima taAAmaloon
Hausa
Kuma idan sun yi maka jidăli, sai ka ce: "Allah ne Mafi sani game da abin da
kuke aikatăwa."
|
Ayah 22:69 الأية
اللهُ يَحْكُمُ بَيْنَكُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ فِيمَا كُنتُمْ فِيهِ
تَخْتَلِفُونَ
Allahu yahkumu baynakum yawmaalqiyamati feema kuntum feehi takhtalifoon
Hausa
"Allah ne zai yi hukunci a tsakăninku, a Rănar ˇiyăma a cikin abin da kuka
kasance a cikinsa kună săɓawa jũna."
|
Ayah 22:70 الأية
أَلَمْ تَعْلَمْ أَنَّ اللهَ يَعْلَمُ مَا فِي السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ ۗ إِنَّ
ذَٰلِكَ فِي كِتَابٍ ۚ إِنَّ ذَٰلِكَ عَلَى اللهِ يَسِيرٌ
Alam taAAlam anna Allaha yaAAlamu mafee assama-i wal-ardi inna thalikafee
kitabin inna thalika AAala Allahiyaseer
Hausa
Ashe, ba ka sani ba, lalle ne Allah Yană sanin abin da yake a cikin sama da
ƙasa? Lalle ne wancan yană cikin Littafi lalle wancan ga Allah mai sauƙi ne.
|
Ayah 22:71 الأية
وَيَعْبُدُونَ مِن دُونِ اللهِ مَا لَمْ يُنَزِّلْ بِهِ سُلْطَانًا وَمَا لَيْسَ
لَهُم بِهِ عِلْمٌ ۗ وَمَا لِلظَّالِمِينَ مِن نَّصِيرٍ
WayaAAbudoona min dooni Allahi malam yunazzil bihi sultanan wama laysa lahum
bihiAAilmun wama liththalimeenamin naseer
Hausa
Kuma sună bautăwa baicin Allah, abin da (Allah) bai saukar da wani dalili ba
game da shi, kuma abin da bă su da wani ilmi game da shi, kuma băbu wani mai
taimako ga azzălumai.
|
Ayah 22:72 الأية
وَإِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِمْ آيَاتُنَا بَيِّنَاتٍ تَعْرِفُ فِي وُجُوهِ الَّذِينَ
كَفَرُوا الْمُنكَرَ ۖ يَكَادُونَ يَسْطُونَ بِالَّذِينَ يَتْلُونَ عَلَيْهِمْ
آيَاتِنَا ۗ قُلْ أَفَأُنَبِّئُكُم بِشَرٍّ مِّن ذَٰلِكُمُ ۗ النَّارُ وَعَدَهَا
اللهُ الَّذِينَ كَفَرُوا ۖ وَبِئْسَ الْمَصِيرُ
Wa-itha tutla AAalayhim ayatunabayyinatin taAArifu fee wujoohi allatheena
kafarooalmunkara yakadoona yastoona billatheenayatloona AAalayhim ayatina
qulafaonabbi-okum bisharrin min thalikum annaruwaAAadaha Allahu allatheena
kafaroo wabi/saalmaseer
Hausa
Kuma idan ană karanta ăyőyinMu bayyanannu a kansu kană sanin abin ƙyăma a cikin
fuskőkin waɗanda suka kăfirta sună kusa su yi danƙa ga waɗanda ke karătun
ayőyinMu a kansu. Ka ce: "Shin to in gaya muku abin da yake mafi sharri daga
wannan? (Ita ce) Wuta." Allah Yă yi alkawarinta ga waɗanda suka kăfirta. Kuma
makőmarsu ta mũnana.
|
Ayah 22:73 الأية
يَا أَيُّهَا النَّاسُ ضُرِبَ مَثَلٌ فَاسْتَمِعُوا لَهُ ۚ إِنَّ الَّذِينَ
تَدْعُونَ مِن دُونِ اللهِ لَن يَخْلُقُوا ذُبَابًا وَلَوِ اجْتَمَعُوا لَهُ ۖ
وَإِن يَسْلُبْهُمُ الذُّبَابُ شَيْئًا لَّا يَسْتَنقِذُوهُ مِنْهُ ۚ ضَعُفَ
الطَّالِبُ وَالْمَطْلُوبُ
Ya ayyuha annasuduriba mathalun fastamiAAoo lahu inna allatheenatadAAoona min
dooni Allahi lan yakhluqoo thubabanwalawi ijtamaAAoo lahu wa-in yaslubuhumu
aththubabushay-an la yastanqithoohu minhu daAAufa attalibuwalmatloob
Hausa
"Ya ku mutăne! An buga wani misăli, sai ku saurăra zuwa gare shi. Lalle ne
waɗanda kuke kira baicin Allah, bă ză su halitta ƙudă ba, kő da sun tăru gare
shi, kuma idan ƙudăn ya ƙwăce musu wani abu, bă ză su kuɓutar da shi ba daga
gare shi. Mai nẽma da wanda ake nẽman gare shi sun raunana."
|
Ayah 22:74 الأية
مَا قَدَرُوا اللهَ حَقَّ قَدْرِهِ ۗ إِنَّ اللهَ لَقَوِيٌّ عَزِيزٌ
Ma qadaroo Allaha haqqaqadrihi inna Allaha laqawiyyun AAazeez
Hausa
Ba su ƙaddara wa Allah hakkin girmanSa ba. Lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai ƙarfi ne,
Mabuwăyi.
|
Ayah 22:75 الأية
اللهُ يَصْطَفِي مِنَ الْمَلَائِكَةِ رُسُلًا وَمِنَ النَّاسِ ۚ إِنَّ اللهَ
سَمِيعٌ بَصِيرٌ
Allahu yastafee mina almala-ikatirusulan wamina annasi inna Allaha
sameeAAunbaseer
Hausa
Allah nă zăɓen Manzanni daga mală'iku kuma daga mutăne. Lalle Allah, Mai ji ne,
Mai gani.
|
Ayah 22:76 الأية
يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ ۗ وَإِلَى اللهِ تُرْجَعُ
الْأُمُورُ
YaAAlamu ma bayna aydeehim wamakhalfahum wa-ila Allahi turjaAAu al-omoor
Hausa
Yană sanin abin da ke gaba gare su da abin da ke băyansu, kuma zuwa ga Allah ake
mayar da al'amura.
|
Ayah 22:77 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا ارْكَعُوا وَاسْجُدُوا وَاعْبُدُوا رَبَّكُمْ
وَافْعَلُوا الْخَيْرَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ ۩
Ya ayyuha allatheena amanooirkaAAoo wasjudoo waAAbudoo rabbakum
wafAAalooalkhayra laAAallakum tuflihoon
Hausa
Yă kũ waɗanda suka yi ĩmăni! Ku yi rukũ'i, kuma ku yi sujada, kuma ku bauta wa
Ubangijinku, kuma ku aikata alhẽri, tsammăninku, ku sami babban rabo.
|
Ayah 22:78 الأية
وَجَاهِدُوا فِي اللهِ حَقَّ جِهَادِهِ ۚ هُوَ اجْتَبَاكُمْ وَمَا جَعَلَ
عَلَيْكُمْ فِي الدِّينِ مِنْ حَرَجٍ ۚ مِّلَّةَ أَبِيكُمْ إِبْرَاهِيمَ ۚ هُوَ
سَمَّاكُمُ الْمُسْلِمِينَ مِن قَبْلُ وَفِي هَٰذَا لِيَكُونَ الرَّسُولُ شَهِيدًا
عَلَيْكُمْ وَتَكُونُوا شُهَدَاءَ عَلَى النَّاسِ ۚ فَأَقِيمُوا الصَّلَاةَ وَآتُوا
الزَّكَاةَ وَاعْتَصِمُوا بِاللهِ هُوَ مَوْلَاكُمْ ۖ فَنِعْمَ الْمَوْلَىٰ
وَنِعْمَ النَّصِيرُ
Wajahidoo fee Allahi haqqajihadihi huwa ijtabakum wama jaAAalaAAalaykum fee
addeeni min harajin millata abeekumibraheema huwa sammakumu almuslimeena min
qabluwafee hatha liyakoona arrasoolu shaheedanAAalaykum watakoonoo shuhadaa
AAala annasifaaqeemoo assalata waatoo azzakatawaAAtasimoo billahi huwa
mawlakumfaniAAma almawla waniAAma annaseer
Hausa
Kuma ku yi jihădi a cikin (al'amarin) Allah, hakkin JihădinSa. shĩ ne Ya zăɓe ku
alhăli kuwa bai sanya wani ƙunci ba a kanku a cikin addĩni. Bisa ƙudurcẽwar
ubanku Ibrăhĩm, shĩ ne ya yi muku sũna Musulmi daga gabănin haka. Kuma a cikin
wannan (Littăfi ya yi muku sũna Musulmi), dőmin Manzo ya kasance mai shaida a
kanku, kũ kuma ku kasancemăsu shaida a kan mutăne. Sabőda haka ku tsayar da
salla kuma ku băyar da zakka kuma ku amince da Allah, Shi ne Majiɓincinku.
Săbőda haka mădalla da Shi Ya zama Majiɓinci, mădalla da Shi ya zama Mai
taimako.
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|