| First Ayah 1 الأية الأولي |
| بِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ | | First Ayah 1 الأية الأولي |
|
|
إِنَّا أَرْسَلْنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوْمِهِ أَنْ أَنذِرْ قَوْمَكَ مِن قَبْلِ أَن
يَأْتِيَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Inna arsalna noohan ilaqawmihi an anthir qawmaka min qabli an ya/tiyahum
AAathabunaleem
Hausa
Lalle ne Mun aiki Nũhu zuwa ga mutãnensa, cẽwa ka yi gargaɗi ga mutãnenka
gabãnin wata azãba mai raɗaɗi ta zo musu.
|
Ayah 71:2 الأية
قَالَ يَا قَوْمِ إِنِّي لَكُمْ نَذِيرٌ مُّبِينٌ
Qala ya qawmi innee lakum natheerunmubeen
Hausa
Ya ce: "Ya mutãnena ni, a gare ku, mai gargaɗi ne, mai bayyanãwa."
|
Ayah 71:3 الأية
أَنِ اعْبُدُوا اللهَ وَاتَّقُوهُ وَأَطِيعُونِ
Ani oAAbudoo Allaha wattaqoohuwaateeAAoon
Hausa
"Cewa ku bauta wa Allah, ku ji tsõronSa, kuma ku bĩ ni."
|
Ayah 71:4 الأية
يَغْفِرْ لَكُم مِّن ذُنُوبِكُمْ وَيُؤَخِّرْكُمْ إِلَىٰ أَجَلٍ مُّسَمًّى ۚ إِنَّ
أَجَلَ اللهِ إِذَا جَاءَ لَا يُؤَخَّرُ ۖ لَوْ كُنتُمْ تَعْلَمُونَ
Yaghfir lakum min thunoobikumwayu-akhkhirkum ila ajalin musamman inna ajala
Allahiitha jaa la yu-akhkharu law kuntumtaAAlamoon
Hausa
"Allah zai gãfarta muku daga zunubanku kuma Ya jinkirta muku zuwa ga ajalin da
aka ambata. Lalle ne ajalin Allah idan ya zo, ba za a jinkirta Shi ba, dã kun
kasance masana (ga abin da nake faɗã dã, kun bar kãfirci)."
|
Ayah 71:5 الأية
قَالَ رَبِّ إِنِّي دَعَوْتُ قَوْمِي لَيْلًا وَنَهَارًا
Qala rabbi innee daAAawtu qawmeelaylan wanahara
Hausa
Nũhu) ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne, na kirãyi mutãnena, a cikin dare da
yini."
|
Ayah 71:6 الأية
فَلَمْ يَزِدْهُمْ دُعَائِي إِلَّا فِرَارًا
Falam yazidhum duAAa-ee illafirara
Hausa
"To, amma kirana bai ƙãre su ba sai da, gudu (daga gare ni)."
|
Ayah 71:7 الأية
وَإِنِّي كُلَّمَا دَعَوْتُهُمْ لِتَغْفِرَ لَهُمْ جَعَلُوا أَصَابِعَهُمْ فِي
آذَانِهِمْ وَاسْتَغْشَوْا ثِيَابَهُمْ وَأَصَرُّوا وَاسْتَكْبَرُوا اسْتِكْبَارًا
Wa-innee kullama daAAawtuhumlitaghfira lahum jaAAaloo asabiAAahum fee
athanihimwastaghshaw thiyabahum waasarroo wastakbarooistikbara
Hausa
"Kuma lalle ne ni, kõ da yaushe na kirãye su dõmin Ka gãfarta musu, sai su sanya
yatsunsu a cikin kunnuwansu, su lulluɓe da tufãfinsu, su dõge ga yin laifi. Sun
yi girman kai iyãkar girman kai."
|
Ayah 71:8 الأية
ثُمَّ إِنِّي دَعَوْتُهُمْ جِهَارًا
Thumma innee daAAawtuhum jihara
Hausa
"Sa'an nan lalle ne ni, na kira su, a bayyane."
|
Ayah 71:9 الأية
ثُمَّ إِنِّي أَعْلَنتُ لَهُمْ وَأَسْرَرْتُ لَهُمْ إِسْرَارًا
Thumma innee aAAlantu lahum waasrartu lahumisrara
Hausa
"Sa'an nan lalle ne, na yi yẽkuwa sabõda su, kuma na gãna da su a cikin asĩri."
|
Ayah 71:10 الأية
فَقُلْتُ اسْتَغْفِرُوا رَبَّكُمْ إِنَّهُ كَانَ غَفَّارًا
Faqultu istaghfiroo rabbakum innahu kanaghaffara
Hausa
"Shi na ce, 'Ku nẽmi gãfara daga Ubangijinku, lalle ne shi Ya kasance Mai gãfara
ne."
|
Ayah 71:11 الأية
يُرْسِلِ السَّمَاءَ عَلَيْكُم مِّدْرَارًا
Yursili assamaa AAalaykummidrara
Hausa
"Ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai ɓuɓɓuga."
|
Ayah 71:12 الأية
وَيُمْدِدْكُم بِأَمْوَالٍ وَبَنِينَ وَيَجْعَل لَّكُمْ جَنَّاتٍ وَيَجْعَل لَّكُمْ
أَنْهَارًا
Wayumdidkum bi-amwalin wabaneenawayajAAal lakum jannatin wayajAAal lakum anhara
Hausa
"Kuma ya yalwata muku game da dũkiya da ɗiya,Ya sanya muku (albarka) ga gõnaki,
kuma Ya sanya muku koguna."
|
Ayah 71:13 الأية
مَّا لَكُمْ لَا تَرْجُونَ لِلَّهِ وَقَارًا
Ma lakum la tarjoona lillahiwaqara
Hausa
"Me ya sãme ku, bã ku fãtar sãmun natsuwa daga Allah,"
|
Ayah 71:14 الأية
وَقَدْ خَلَقَكُمْ أَطْوَارًا
Waqad khalaqakum atwara
Hausa
"Alhãli kuwa, lalle ne, Ya halitta. ku, a cikin hãlãye?"
|
Ayah 71:15 الأية
أَلَمْ تَرَوْا كَيْفَ خَلَقَ اللهُ سَبْعَ سَمَاوَاتٍ طِبَاقًا
Alam taraw kayfa khalaqa AllahusabAAa samawatin tibaqa
Hausa
"Ba ku ga yadda Allah Ya halitta wasu sammai bakwai ɗabaƙõƙĩ a kan jũna ba?"
|
Ayah 71:16 الأية
وَجَعَلَ الْقَمَرَ فِيهِنَّ نُورًا وَجَعَلَ الشَّمْسَ سِرَاجًا
WajaAAala alqamara feehinna nooran wajaAAalaashshamsa siraja
Hausa
"Ya sanya watã a cikinsu, yana mai haske, Ya sanya rãnã babbar fitila?"
|
Ayah 71:17 الأية
وَاللهُ أَنبَتَكُم مِّنَ الْأَرْضِ نَبَاتًا
Wallahu anbatakum mina al-ardinabata
Hausa
"Kuma Allah Ya tsirar da ku daga ƙasa (kamar ganye) tsirarwa."
|
Ayah 71:18 الأية
ثُمَّ يُعِيدُكُمْ فِيهَا وَيُخْرِجُكُمْ إِخْرَاجًا
Thumma yuAAeedukum feehawayukhrijukum ikhraja
Hausa
"Sa'an nan Ya mayar da ku a cikinta, kuma Ya fitar da ku fitarwa."
|
Ayah 71:19 الأية
وَاللهُ جَعَلَ لَكُمُ الْأَرْضَ بِسَاطًا
Wallahu jaAAala lakumu al-ardabisata
Hausa
"Kuma Allah Ya sanya muku ƙasa shimfidaɗɗiya."
|
Ayah 71:20 الأية
لِّتَسْلُكُوا مِنْهَا سُبُلًا فِجَاجًا
Litaslukoo minha subulan fijaja
Hausa
"Dõmin ku shiga a cikinta, hanyõyi mãsu fãɗi."
|
Ayah 71:21 الأية
قَالَ نُوحٌ رَّبِّ إِنَّهُمْ عَصَوْنِي وَاتَّبَعُوا مَن لَّمْ يَزِدْهُ مَالُهُ
وَوَلَدُهُ إِلَّا خَسَارًا
Qala noohun rabbi innahum AAasawneewattabaAAoo man lam yazidhu maluhu wawaladuhu
illakhasara
Hausa
Nũhu ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne sũ sun saɓa mini sun bi wanda dukiyarsa da
ɗiyansa ba su ƙãre shi da kõme ba sai da hasãra."
|
Ayah 71:22 الأية
وَمَكَرُوا مَكْرًا كُبَّارًا
Wamakaroo makran kubbara
Hausa
"Kuma sun yi wani mãkirci, mãkirci babba."
|
Ayah 71:23 الأية
وَقَالُوا لَا تَذَرُنَّ آلِهَتَكُمْ وَلَا تَذَرُنَّ وَدًّا وَلَا سُوَاعًا وَلَا
يَغُوثَ وَيَعُوقَ وَنَسْرًا
Waqaloo la tatharunna alihatakumwala tatharunna waddan wala suwaAAanwala
yaghootha wayaAAooqa wanasra
Hausa
"Kuma suka ce: Faufau kada ku bar gumãkanku, kuma faufau, kada ku bar wadda,
kuma kada ku bar suwã kuma kada ku bar Yagũsa da Ya'ũƙa da Nasra."
|
Ayah 71:24 الأية
وَقَدْ أَضَلُّوا كَثِيرًا ۖ وَلَا تَزِدِ الظَّالِمِينَ إِلَّا ضَلَالًا
Waqad adalloo katheeran walatazidi aththalimeena illa dalala
Hausa
"Kuma lalle ne sun ɓatar da (mutãne) mãsu yawa, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai
(kõme) sai ɓata."
|
Ayah 71:25 الأية
مِّمَّا خَطِيئَاتِهِمْ أُغْرِقُوا فَأُدْخِلُوا نَارًا فَلَمْ يَجِدُوا لَهُم مِّن
دُونِ اللهِ أَنصَارًا
Mimma khatee-atihimoghriqoo faodkhiloo naran falam yajidoo lahum min dooniAllahi
ansara
Hausa
Sabõda laifukansu na ganganci aka nutsar da su, sa'an nan aka sanya su a wuta.
Saboda haka ba su sãmã wa kansu wani mataimaki wanin Allah ba.
|
Ayah 71:26 الأية
وَقَالَ نُوحٌ رَّبِّ لَا تَذَرْ عَلَى الْأَرْضِ مِنَ الْكَافِرِينَ دَيَّارًا
Waqala noohun rabbi latathar AAala al-ardi mina alkafireenadayyara
Hausa
Kuma Nũhu ya ce: "Ya Ublngijina! Kada Ka bari, a kan ƙasa, daga cikin kãfirai,
wanda ke zama a cikin gida."
|
Ayah 71:27 الأية
إِنَّكَ إِن تَذَرْهُمْ يُضِلُّوا عِبَادَكَ وَلَا يَلِدُوا إِلَّا فَاجِرًا
كَفَّارًا
Innaka in tatharhum yudillooAAibadaka wala yalidoo illa fajirankaffara
Hausa
"Lalle ne, Kai idan Ka bar su, zã su ɓatar da bãyinKa, kuma bã zã su haifi kowa
ba fãce fãjiri mai yawan kãfirci"
|
Ayah 71:28 الأية
رَّبِّ اغْفِرْ لِي وَلِوَالِدَيَّ وَلِمَن دَخَلَ بَيْتِيَ مُؤْمِنًا
وَلِلْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ وَلَا تَزِدِ الظَّالِمِينَ إِلَّا تَبَارًا
Rabbi ighfir lee waliwalidayyawaliman dakhala baytiya mu/minan walilmu/mineena
walmu/minatiwala tazidi aththalimeena illatabaran
Hausa
"Ya Ubanginjina! Ka yi mini gãfara (ni) da mahaifana biyu, da wanda ya shiga
gidana, yana mai ĩmãni, da mũminai maza da mũminai mãtã, kuma kada Ka ƙãrã wa
azzãlumai kõme sai halaka."
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|
|