Muhawara Hausa
 



MARTANI: Yadda rikicin Izala da darika ya kasance a Sabo Ibadan: Kwan-gaba kwan-
 
Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai A Rubuce Da Ahmad Muhammadil’amin

MARTANI: Yadda rikicin Izala da darika ya kasance a Sabo Ibadan: Kwan-gaba kwan-Kwan-gaba kwan-baya, mulkin Shugaba Jonathan
 
Assalam alaikum. 

Ni ma’abocin karanta Aminiya ne kowane mako, na karanta babban labarin Aminiya ta ranar juma’a 27 ga Agusta, 2010 wakalinku ya rawaito labari da  ya sha bamban da abin da ya auku a rikicin da ya auku a Sabo Ibadan. 

Gaskiya ne a ranar Lahadi an yi rikici har da ba hammata iska, inda wani malami ya zo ya ce an turo shi daga hedikwatar Izala don yin wa’azin Islama. Zuwansa bai yi alfanu ba, wanda a karshe ya kunyata malaman Izala, komawa ya yi yana dambe a kan titi da wasu yara.



A cikin labarin, ya rawaito cewa an lalata masallatai guda uku mallakar ’yan Izala. Amma kash, sai bai fadi irin abin da ya shafi ’yan darika ba, a ganina ya kamata a ce idan aka doki jaki a kuma doki taiki. Ba kamar yadda aka rawaito ba.

A sakin layi na biyu, ya cigaba da cewa boren ya biyo bayan Hukuncin da kotun majistrate ta 2 da ke a Iyagaku ta yanke, a nan ma ba hakan ne ya faru ba. 

Amma idan har gaske ne sifika ce ta haddasa, me ya sa da kafin zuwan azumi babu sifika a hedikwatar Izala, amma aka mayar, sauran wuraren kamar gidan Alhaji Yakubu Hashidu da Zawiyar Malam Bawalle ba su ta da jijiyar wuya ba a kan sifika, ita ce addini ko tsarkin zuciya? Gaskiya ne kwamishinan ‘yansanda na Jihar Oyo ya kira taron sulhu kamar yadda aka rawaito. Sai dai ba a fadi cewa a lokaci gayyatar har da shi malamin Izalar, amman ya ki zuwa. Haka kuma, ba a bayyana cewa babu wata matsaya da aka cimma a taron, wani dan Izala ne ya yi furucin cewa za a cigaba da kashe-kashe,wannan furucin ya fusata kwamishinan ‘yansanda shi ya sa ya tura mu zuwa kotu. 

A sakin layi na hudu, wakilin Aminiya ya dogara ne wajen dora mai karatu ya fahimci cewa Alkalin kotun Mai-shari’a Hajiya Safiyat Oyediran ta yanke hunkunci. Amman bangaren darika sun ki bin umarnin kotu. Wannan ba gaskiya ba ne, duk wuraren da ’yan Izala suka ware don nuna kyamar babban Masallaci daidai ne a kira su masallatai? Shin ’yan Izalan ba sa amfana da babban Masallacin wajen cusa wa yara akida? Wa ya hana su? 

Har ilayau, an buga hoton wani masallaci da irin kayayyakin da aka lalata a lokacin rikicin, amma mene ne ya sa bai nuna Alkur’anin da littatafan Hadisai da ya ce an lallata ba? A nan ina mai ba da shawara cewa ya kamata a dinga gudanar da bincike sosai kafin a buga labari rashin yin hakan yana nuna tabarbarewar aikin jarida na tsage gaskiya.

“A fahimtarmu wannan cin zarafin Musulunci ne, mace ta hana jami’in tsaro gudanar da aikin da dokar kasa ta dora masa, duk wanda ya saba ta kama shi”. An bayar da dokar cewa duk a cire sifiku amma sun ki, D.P.O ya zo don daukar hoton manyan sifiku, sai aka tura masa mata don a nuna cewa sun fi kowa iya katobara. Dangane da wannan a wata majiyar saboda irin wannan katobarar ne wasu daga cikin matan sun rasa igiyar aurensu.

Wannan ya tabbatar da cewa ba ’yan darika ba ne sanadiyyar aukuwar wannan rikici, sai ga jerin sunayen mutane ya fito ’yansanda sun kama mutane 25 a ranar Litinin, 15 daga cikinsu ’yan darika ne ba su ji ba ba, su gani ba, sharri kawai aka yi musu. 

Fadin cewa wadansu shugabanni sun tsoma baki, amma ba su iya shawo kan matsalar ba, ba daidai ba ne, don har rattaba hannun yarjejeniyar zaman lafiya da sasantawa duk sun yi wa bangarorin biyu. amman daga karshe Izala ta ce basu isa ba, sai suka maka mu da CP din a kotu. Babbar kotan tarrayya ta Ibadan za ta fara sauraron karar, masu lambobi kamar haka 4110110 da 18110110. 

Jama’a ku zama adalai, wajen yanke wannan hukunci. Shin wanda ya tanadi makamai ya fito da su karara shi ya yi cuta ko shi aka cuta?
 
Daga Alhaji Ahmad Muhammadil’amin (Bawalle) Shugaban Mahadul-Khamis Li ta’alimil-araby wal-islamy, Sabo Ibadan 07066024828 i-mel: nyasalamin@yahoo.com)
 

Kwan-gaba kwan-baya, mulkin Shugaba Jonathan

Daga Yasser Ramadan Gwale

Kusan shi ne shugaba na farko da za a iya kira da sunan dan baiwa a Najeriya, don ya zama gwamna ba tare da an zabe shi ba. Ya dare kan kujerar Gwamnan Jihar Bayelsa bayan da aka kama mai gidansa da almundahana da dukiyar jihar, D S P. Alighemiesiegh, wanda hakan ya kai ga tsige gwamnan, wannan ta bai wa Jonathan damar zama Gwamna a bagas. 

Haka tsohon shugaba kasa, Obasanjo ya dauko shi a matsayin wanda zai dafa wa marigayi Shugaba Yar’aduwa baya a matsayin mataimaki ba tare da ya nema ba, wanda wannan ta ba shi damar zama mataimakin shugaban kasa a cikin wani yanayi mai cike da cece-kuce. Tun daga kwanciyar marigayi ’Yar’aduwa a gadon asibiti, hakan ta kai aka nada Jonathan a matsayin mukaddashin shugaban kasa, bayan kai ruwa rana da aka yi a kan batun. 

Zamansa mukaddashi ke da wuya, ya tafka katuwar katobara, inda aka ji shi yana fada ta hanyar kakakinsa Mista Emma Niboro yana umartar da a karkatar da kudin yashe kogin Kwara zuwa aikin zaizayar kasa a yankin da ya fito wato Neja Delta. Bayan kasar ta dauki dumi kan wannan batu, ya fito ya ce shi ba haka yake nufi ba, kuskuren fahimta aka yi masa. 

Baya ga haka, Shugaba Jonathan ya sake  yin kwan-gaba kwan-baya, bayan da ya zama shugaba mai cikakken iko, inda ya ce ya dakatar da kungiyar wasan kwallon kafa ta kasa Super Eagles. Wannan ta sanya hukumar gudanar da wasan kwallon kafa ta duniya FIFA ta yi barazanar dakatar da Najeriya, hakan ta sa ya janye dakatarwar da ya yi musu. Ashe bai cika jarumi ba.

Shugaba Jonathan ya zama shugaba mai cikakken iko bayan da mutuwa ta katse hanzarin marigayi Shugaba ’Yar’aduwa ba tare da ya cika muhimman kudurorin nan nasa guda bakwai ba. Tun da Shugaba Jonathan ya zama GCFR yake harar wasu daga cikin muhimman ayyuka da marigayi mai gidansa ya fara aiwatarwa kafin kwanciyarsa rashin lafiya ya yi alkawarin samar da wutar lantarki mai karfin mega watt 6000, kuma yadda aikin ya fara gudana ’Yar’aduwa ya nuna da gaske yake a kan wannan nufin nasa amma sai dai kash mutuwa ta yi masa yankan hanzari bai iya ganin wannan buri nasa ya cika ba. Maimakon Shugaba Jonathan ya dora daga inda Yar’aduwa ya tsaya sai ya fito yana gaya wa ‘yan Najeriya su yi hakauri wannan aiki ba zai ci gaba, ba saboda yadda mutanen yankin da yake ikirari daga nan ya fito suka hana zaune tsaye. Hakan ne ya haifar da samun cikas gurin samun iskar gas din da za a yi amfani da ita wajen samar da wutar lantarkin. 

Wadanan da suka hana samar da iskar gas su ne mutanen da ake kira tsagerun yankin Neja Delta. yana daga cikin manufofin Shugaba ’Yara’aduwa na samar da zaman lafiya a wannan yanki, amma bayan da ya kwanta dama Shugaba Jonathan ya yi wa batun rikon sakainar kasha. Haka rana a tsaka aka jiyo kakakin wannan kungiya ta tsagerun Neja Delta mai suna MEND, wanda ake kira da suna Jomo Gbomo ya bayar da sanarwa za su ci gaba da tada kura a wannan yankin a sakamakon wasu dalilai da ya bayyana. Amma Shugaba Jonathan bai iya yin komai na hana su ba. Wadannan tsageru suka yi ta kai hare-hare, nan da can, har aka zo lokacin bikin cika “jaririya” Najeriya shekaru hamsin da haihuwa inda suka bayar da sanarwar tashin bom a gurin taron fita kunya. Abu kamar da wasa, sai ga bama-bamai guda biyu sun tarwatse a yayin da ake tsaka da gudanar da wannan taro. Amma saboda rashin son gaskiya da kuma rashin tsoron Allah aka ji Shugaba Jonathan da kansa yana cewa shi ya san wadanda suka tada wadannan bama-bamai, ba wadannan tsageru da suka yi ikirari ba ne.Wannan ya nuna cewa ya ci amanar Najeriya tunda har yana da masaniyar tashin bom, ya kasa yin komai a kai. Don haka, yana da alhakin dukkan wadanda suka rasa ransu a wannan hari, wannan magana tana cigaba da tada kura a yankin Arewacin Najeriya, inda adaidai wannan lokaci ne Shugaba Jonathan ya sake cewa shi fa ba haka yake nufi ba fahimtarsa ne ba a yi ba. 

Bayan tuni an ji Shugaban wannan kungiya a wata tashar watsa labarai yana cewa shugaban ya ce su ce ba su ba ne suka kai wannan hari don yana son goga wa ’yan Arewa kashin kaji a kan wannan batu. Alamu sun nuna haka don an kama wani dan siyasa da  aka alakanta shi da batun, amma duk da wannan dambarwa da ake yi ba ka taba ji an kira wadannan yara da sunan ’yan ta’adda ba, sai aka yi wa abin kwaskwarima aka ce tsageru. Na tabbata da musulmi ne da tuni labarin ba haka yake ba. 

Shin Shugaba Jonathan ya cancanta kasancewarsa Shugaban tarayyar Najeriya kuwa? Don karara yana kokarin tada tsimin kabilancin da aka dade ana fama da shi a tsakanin ’yan Najeriya. Sannan a daidai wannan lokacin ne shugaban ya tattare manyan mukaman da suka jibanci tsaro zuwa yankin kudancin kasar nan. Sannan kuma, manyan ministoci ya karkatar da su zuwa kudancin kasar, sannan duk inda aka cire wani dan arewa daga wata ma’aikata sai a maye gurbinsa da dan Kudu. Saboda rashin adalci da rashin iya jagoranci. Ka duba irin yadda ake kashe makudan kudi wajen horar da jami’an tsaro a kasashen ketare haka kurun lokaci guda aka yi wa manyan sojoji ritayar dole bayan da suka riga suka samu kwarewa. 

A  haka ne Shugaban yake kokarin lallai sai ya zama shugaban kasa, ko ana so ko ba a so, bayan tsarin mulkin  jam’iyyar da ya ke bi ya yi batun karba-karba. Gashi muna cikin yanayin da yake nuna babu tsaro ko kadan a kasar nan don abin da yake faruwa a Jihar Borno a yau. Wannan shi ne alamun babu tsaro, muna da masaniyar hakkin kowane shugaba ne ya kare rayukan al’umar da yake mulka, don haka wannan ya nuna cewa jonathan din da ya kasa samar da tsaro a yankinsa ina zai iya samar da tsaro a kasa gaba daya. Don haka, wannan yana nuna bukata ta gaggawa ga Shugaba Jonathan ya yi murabus don ba zai iya rike kasar nan ba, ko ya rike ba zai iya gudanar da adalci ba, don haka daidai wannan gaba nake son yin kira ga wakilanmu lallai su tabbata sun tilasta shugaban kasa yin murabus kamar yadda Firimiyan Birtaniya Tony Blair da Gordon Brown suka yi murabus ba tare da sun cika wa’adinsu ba. Ko kuma, su yi amfani da tsarin mulki wajen tsige shi tun da ya cancanci a tsige shi. Kwanakin baya ne a Jihar Ogun ’yan majalisa 8 sun rinjayi 15 wajen tsige kakakin majalisa. Wannan ya nuna a Najeriya yawan lamba ba shi ke nuna ku kuka fi yawa ba, ko ba haka ba mai karatu?

Anan ya kamata ’yan Najeriya mu ci gaba da addu’a, Allah Mai kowa Mai komai Ya zaba mana shugabanni nagari a wannan zabe mai zuwa, wadanda za su wanzar da adalci a tsakanin ’yan Najeriya. kuma Allah Ya zaunar da kasarmu lafiya, Ya kuma ba mu abin da lafiya za ta bukata. Allah Ya yi mana jagora Amin. 

Yasir Ramadan Gwale, Shugaban kungiyar Muryar Talakawan Najeriya Reshen Jihar Kano


 Posted By Aka Sanya A Thursday, November 18 @ 15:09:31 PST Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 3.66
Kurioi: 9


Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai



"MARTANI: Yadda rikicin Izala da darika ya kasance a Sabo Ibadan: Kwan-gaba kwan-" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 



Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com