Daga Jamilu Adamu, Daga Sagir Kano Saleh
Ma'aikatar ta ƙara da cewa an kashe mutane 85 tare da jikkata wasu 200.
Aƙalla Falasɗinawa 35,647 ne aka kashe tare da jikkata 79,852 a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa a Zirin Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba, in ji ma’aikatar lafiya ta ƙasar.
Ma’aikatar ta ƙara da cewa an kashe mutane 85 tare da jikkata wasu 200 a cikin sa’o’i 24 na baya-bayan nan zuwa ranar Talata
Yaƙin Gaza: Hamas da Isra’ila sun fara sakin fursunoni
Daga Sagir Kano Saleh
An fara musayar fursunonin yaƙi tsakanin Hamas da Isra'ila a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar zaman lafiya a Gaza
A safiyar Litinin ɗin nan ƙungiyar Hamas ta saki rukunin farko na ’yan ƙasar Isra’ila bakwai da ta yi garkuwa da su a Zirin Gaza.
A ɗaya ɓangaren kuma Falsɗinawa sun yi cincirindo a yankin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan domin tarbar ’yan uwansu kimanin 2,000 da Isra’ila za ta sako.
Tuni jami’an kungiyar agaji ta Red Cross suka shiga gidan yarin Wada a safiyar domin ɗaukar wani fursuna Bafalasdine da za fitar, wanda ke fama da rashin lafiya.
Hamas ta mika su ne ga kungiyar Red Cross a Gaza a yayin da ake da ran sako wasu ƙarin mutum 13 na gaba a Litinin ɗin nanm a cewar hukumomin Isra’ila.
Wannan na faruwa ne a yayin da Shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya taka muhimmiyar rawa a sulhun, yake ziyara a ƙasar Isra’ilan a safiyar Litinin.
Wannan na zuwa ne bayan yarjejeniyar zaman lafiyar da ɓangarorin biyu suka sanya hannu a kai a baya-bayan nan.
A bangare guda kuma Falsɗinawa sun yi cincirindo a yankin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan domin tarbar ’yan uwansu kimanin 2,000 da Isra’ila za ta sako, a matsayin ɓangarenta na musayar fursunonin yaƙin.
Ma’aikatar Harkokin Gida ta Isara’ila ta fitar da jerin sunayen mutanen da aka saki da shekarunsu:
Na gaba ake da ran muka su ga iyalansu a wani sansanin soji a Kudancin Isra’ila.
A ɗaya bangaren kuma kungiyar kula da Fursunoni ta Palastinu ta fitar da jerin sunayen mutane 1,718 da Isra’ila za ta sako.

