Labarai da Ra'ayi
Labaran Duniya Musulmi da Gabas ta Tsakiya

Koma zuwa "Labaran Duniya Musulmi da Gabas ta Tsakiya"


Labaran Duniya Musulmi da Gabas ta Tsakiya

Koma zuwa "Labaran Duniya Musulmi da Gabas ta Tsakiya"

NewsTeam
Masu rubutu: 5
An haɗa: Thu Nuwamba 06, 2025 6:42 am

     NewsTeam Masu rubutu: 5    An haɗa: Thu Nuwamba 06, 2025 6:42 am      


Buga by NewsTeam »

Esin033 Ganduje ya janye shirin kafa ‘sabuwar Hisbah’ a Kano

Daga Sani Ibrahim Paki da Sagir Kano Saleh

Tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya dakatar da shirinsa na kafa rundunar Hisbah mai zaman kanta a jihar.

Ganduje ya dakatar da shirin nasa ne bayan ce-ce-ku-ce da hakan ya haifar da kuma haramcin da gwamnatin jihar ta sanya kan lamarin.

A cikin wata sanarwa da jigo a Jam’iyyar APC, Baffa Babba Dan-Agundi, ya fitar a madadin Gandujen, ya ce matakin ya biyo bayan tattaunawa da Gwamnatin Kano, da hukumar tsaro ta DSS, domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

A kwanakin baya, Ganduje, wanda shi ne tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, ya bayyana shirin daukar ma’aikatan Hisbah 12,000 da gwamnatin jihar ta sallama, domin su shiga wata kungiyarsa ta Hisbah mai zaman kanta.

Ya ce kungiyar za ta yi aiki ne karkashin gidauniyarsa ta Ganduje Foundation, kuma tuni aka fara raba takardun rijista ga masu sha’awar shiga a matsayin ’yan sa-kai.

Sai dai gwamnatin jihar ta haramta wannan shiri, tare da bayar da umarnin daukar matakan tsaro kan duk wani yunkuri da ya shafi hakan.

Amma bayan wasu ’yan kwanaki, wani jigo a jam’iyyar APC a Kano kuma Darakta-Janar na Cibiyar Kasa ta Samar da Aiki, Baffa Babba Dan-Agundi, ya sanar da sabon matakin a madadin tsohon gwamnan.

Dan-Agundi, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce an dauki wannan mataki ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki da ya hada wakilai daga kananan hukumomi 44 na jihar.

Ya ce an gudanar da taron ne a ofishin kamfen din Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da ke Kano.

Dan-Agundi ya bayyana cewa an yanke shawarar janye shirin ne bayan martanin jama’a da damuwar da aka nuna sosai game da shirin kafa wata rundunar Hisbah ta daban.

Ya kara da cewa manyan masu ruwa da tsaki sun shiga tsakani a lamarin, ciki har da Gwamnatin Jihar Kano, Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Kasa (DSS), da kuma Ganduje da kansa, da nufin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Sanarwar ta kuma jaddada girmamawa ga Hukumar Hisbah ta Jihar Kano da aka kafa bisa doka, tare da nuna kudurin goyon bayan hukumomin tsaro na kasa wajen tabbatar da doka da oda, da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin jihar da kasa baki daya.



Ganduje ya janye shirin kafa ‘sabuwar Hisbah’ a Kano



Bayar da Amsa
Bayar da Amsa